Showing 279001 words to 282000 words out of 456519 words

Chapter 94 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70698

dai MD kallonta kawai yake, ta jawo tissue kan table din gabanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata, MD yayi karfin halin cewa "Are you alright Ma?" Da kyar tana ci gaba da goge hawayen dake ta zuba idonta cikin breaking voice tace "Kasan me Aliyu?" Ya girgiza kai yana kallonta, cike da karfin hali tace "Ina son za mu je gidana yanzu, i want to show you something" Yace "Ok Ma'am" Mikewa tayi ta wuce Bedroom dinta ya bi ta da kallo, wondering why she is crying tun dazu, he is just confuse at this point, ba a dau lokaci ba ta fito sanye da kayanta, ko wayoyinta da jaka bata dauka ba ta nufi kofa, ya bi bayanta suka fita daga office din.




[8/25, 5:32 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Personal Driver din Ceo yayi parking a babban parking space din dake cikin gidanta, ta bude back seat ta sauka MD ma ya sakko daga front seat yana kallonta, entrance din shiga mansion din nata ta nufa yana biye da ita a baya, babu kowa a babban parlon gidan ta wuce upstairs, MD ya zauna a parlon ya bi ta da kallo har ta haura sama, bayan dan lokaci daya daga ma'aikatan ta da ya sani a gidan ta sauko kasa ta gaishesa da ladabi sannan tace "Sir tace ka sameta upstairs" MD ya mike tayi leading dinsa zuwa wani babban parlor a sama, nan ma dai babu kowa ciki ya zauna, zuwa yanzu shi kansa ya kagu ya ji dalilin kawosa gidanta da tayi by this time, yayi sensing akwai wani abu me muhimmanci da yasa ta kawosa gidan and he is eager to know what that is, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon tana kallonsa a hankali tace "Come in Aliyu" Mikewa yayi ya bi bayanta suka bi wani corridor me fadi sannan ta bude daya daga kofofi hudu dake wajen ta shiga yana biye da ita a baya, babban daki ne sosai that is well furnished, babu abinda babu a cikin dakin, kwance saman gadon wata kyakkyawar mace ce da bazata haura shekara 42 ba cikin babban duvet, tsaye a dakin wata registered nurse ce sai maid biyu, Ceo ta karasa kusa da ita ta zauna tana shafa dogon gashinta a hankali tace "Meet Dr Aliyu" Kallonsa kawai matar take babu ko kiftawa, MD ya dan kirkiri murmushi yace "Good Morning ma'am" ta dai kafesa da ido, Ceo ta sauke idonta kasa, bayan few seconds ta kwantar da ita a hankali tana kallonta, Maid din dake tsaye ta karasa da sauri ta gyara mata duvet din da pillow, Ceo na kallon nurse din dakin tace "Ya aka yi bata yi bacci ba har yanzu?" Da ladabi nurse din tace "Farkawa tayi Ma" Ceo ta sauke idonta tace "Sorry i interrupted ur sleep, pls get me a Syringe and Needle" Nurse din ta juya ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da shi, Ceo na kallon MD tace "Come over Aliyu" Ya karasa kusa da gadon, shi ta sa ya debi jinin, matar was calm har ya gama diban jinin, bayan few minutes Ceo tayi pecking forehead dinta sannan ta kwantar da ita, Daga haka ta mike ta nufi kofa tana fita MD ya bi bayanta, tsaye ya sameta a parlor ta fada duniyar tunani, ya sunkuyar da kansa don shi dai at this point he is confuse at what she is up to, ga jinin dake cikin karamin roba inside a ziploc da ke hannunta, to wace mata ce wannan da ta sa ya debi jininta don shi dai duk zuwansa gidan bai san da ita ba, bai kuma taɓa ganinta ba duk da har upstairs ya kan kai ma Ceo sako, ya dai san ma'aikatan gidan kaf dinsu amma banda wannan mata dake kwance wanda ga dukkan alamu she is not even stable, kallon Ceo ya sake yi ya ga ta dan yi murmushi tana goge hawayen da ke taruwa idonta without looking at him tace "We are going back to the hospital now Aliyu" Ya gyada kai yace "Ohk Ma" Shi ya fara nufar kofa cike da mamaki ya fita daga parlon sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali, karfe biyu da rabi suka isa asibitin, Dr Balogun da shigowarsa reception kenan ya karasa yana ma Ceo sannu da zuwa, Ba tare da ta kallesa ba tace "An maida Mary Ann ward ne ko har yanzu tana da Emergency?" Da ladabi yace "An maida ta ward ma, ai numfashin nata is stable yanxu" Tace "Wani ward din take?" Gaya mata yayi ta nufi ward din MD na biye da ita, Aunty Mariya ce zaune ita kadai a ciki sai Mayraah da ta samu bacci, Aunty Mariya tayi ma Ceo din sannu da shigowa ta koma gefe, Ceo ta amsa idonta na kan Mayraah sai kuma ta kalli MD, calmly tace "Get a Syringe and Needle" MD ya juya ya fita ward din wondering abinda zata yi da shi, bayan few minutes sai ga shi ya dawo, Ceo tace "Take her blood sample" MD was stunned jin instruction din da ta basa, haka nan dai ya debi jinin Mayraah sannan suka fita daga ward din Aunty Mariya dai ta bi su da ido, MD ya raka Ceo har office dinta, bayan ta zauna ta basa sample din da ta sa ya diba a gidanta, a hankali tace "Genetic testing for the both samples nake so Asap" Mamaki ne ya cika MD ya dinga kallonta, har mamakin ya kasa boyuwa a fuskarsa, genetic testing kuma? To me hakan ke nufi? What is her aim nayi genetic test for the both samples, ya dai yi karfin halin amsan samples din yana kallonta, can ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo idonta cike da wasu sabbin hawayen.
Washegari da safe bayan Ceo ta shiga ward din da Mayraah take ta dubata ta fito, har bakin motar ta MD ya rakata da laptop dinta, bayan ta shiga bayan motar ya mika mata laptop din ganin yanayinta yace "Ma'am u need rest" Ta gyada masa kai a hankali tace "Sure, pls ku kula da ita yanda ya kamata" Yace "We will do that Ma" kulle mata motar yayi daga haka ya juya ya koma asibitin, a reception ya tadda Musharraf ya fito daga ward din da Mayraah take, MD na kallonsa ganin zai fita yace "Ina zaka?" Musharraf yace "Airport, my flight is in 30mins time" MD yace "Why did u book without telling me?" Musharraf yace "Mami ai ta gaya maka yau zan koma kano" MD yace "Allah ya tsare" Daga nan ya wuce sama, Musharraf kuma ya fita daga reception din. Daga wannan ranan Ceo bata sake shigowa asibitin ba, a kwana hudu Mayraah ta samu sauki sosai har tana iya cin abinci, all through this 4 days Aunty Mariya ce tare da ita a asibitin sai Usman da Ammi dake zuwa dubata kullum, don Abba ya hana Ammi kwana asibitin. Yau da yamma suna haraban asibitin da Aunty Mariya bayan sun yi strolling kamar yanda likitocin suka ce ta dinga yi duk yamma, Mayraah ta kalli Aunty Mariya da damuwa tace "Aunty wai me yaya yaje yi a kasar waje ne har yanzu bai dawo ba?" Aunty Mariya tace "Wani aiki ne ya kai sa mana, amma nasan ya kusa dawowa in sha Allah" Mayraah dai tayi shiru tana nazarin abinda Aunty Mariya tace, can dai ta sake kallon Aunty Mariya tace "Shine zai tafi bayan yasan bani da lafiya?" Aunty Mariya tayi dariya tace "Gaskiya kam, don kamata yayi ya ajiye masu aikin ya zauna kusa da kanwarsa har sai ta samu lafiya" Murmushi Mayraah tayi bata sake cewa komai ba, Aunty Mariya tace "Ta shi mu shiga ciki ai kinyi strolling din da yawa yau" Mikewa Mayraah tayi suka koma cikin asibitin tare da Aunty Mariya, a haka dai har Mayraah suka yi kwanaki bakwai tare da Aunty Mariya a asibitin, all this while MD gaba daya attention dinsa da curiosity na kan Genetic testing din da Ceo ta basa ayi, ya rasa dalilin kaguwan da yayi result din ya fito, sai kirga kwanakin yake, a washegarin ranan kuma Abba ya bukaci ayi discharging dinsu a gaya masa bill in dai babu sauran matsala don kowa yaga Mayraah yasan ta samu lafiya sosai, Bayan azahar Dr Khalil na kallon MD dake zaune kan office chair dinsa bayan ya sanar masa bukatan Abba yace "Amma kai ya ka ga? Ni dai a ganina ya kamata ayi discharging dinsu" MD yayi shiru, shi kansa yasan Mayraah ta samu sauki yanzu, kuma tunda case din nata a hannunsa yake shi ya kamata yayi discharging dinta amma yaki yin hakan beside ita ma Ceo bata ce yayi hakan ba don kullum sai ta kirasa ta tambayi jikinta asibitin ne dai taki shigowa, Dr Khalil yace "Wai tunanin me kake ne sir? Ko baka gaji da ganinta bane har yanzu?" Da murmushi ya kare maganar, Shi dai MD bai tankasa ba, can yace "Ban gane ban gaji da ganinta ba, let me call Ceo first...." Da mamaki Dr Khalil yace "Ceo kuma? Ita da bata kasar, beside naga ba a taɓa sanar mata ba idan za a sallami patient?" MD yace "Tana kasar nan, beside file din a hannunta yake not me...." Dr Khalil yace "Really, naga yau sati daya bata shigo ba, na zata ta koma ne wallahi....." MD yace "Bata da lafiya ne, but she is better now" Dr Khalil yace "Allah ya bata lafiya" MD ya dau wayarsa yayi dialing number Ceo yana fara ring ta daga, bayan ya gaisheta ya sanar mata dalilin kiran, Ceo tayi shiru, bayan few seconds tace "Zaka iya discharging dinsu, as for bill da ya tambaya kuma, tell him basu da bill" a hankali yace "Ohk Ma'am" Tace "Yaushe result din nan zai fito Aliyu?" Yace "Zuwa anjima in sha Allah" cikin sanyin murya tace "No bill for them" Yace "Ohk Ma'am" Mikewa yayi ya nufi kofa Dr Khalil ya bi bayansa. Tun da Mayraah taji an sallamesu take farin ciki don gaba daya ta kagu su bar asibitin ta koma gida, shi dai Usman bai gane dalilin da zai sa MD yace babu maganar bill everything is free ba, Aunty Mariya na kallonsa tace "Aa fa barrister, ni a ganina saboda staff dinsu ce shi yasa suka ce babu zancen Bill" Usman yace "Gaba daya yaushe ta fara aikin har ta zama staff dinsu? Kinsan yau kwananta nawa a asibitin nan kuwa? ko ICU kinsan nawa ake biya a rana daya balle wannan asibitin me tsada, kuma tayi kusan sati daya a ICU, hatta drugs da alluran da aka dinga mata kwanaki masu tsada ne, ga kuma abincin da ake bata sau uku a rana, so i don't understand dalilin da zai sa yace babu Bill" Mayraah dai sai kallon Usman take, Aunty Mariya tace "Mu dai koma menene Allah ya saka masu da alkhairi barrister, kuma don Allah kar ma ka gaya ma Ammi don nasan sai ta kara juye batun nan, amma nafi tunanin kawai don ta fara aiki ne tare da su yasa suka yi duk wannan abun a kyauta, yanzu dai an sallami Maheer din ne?" Da sauri Mayraah ta juya tana kallon Aunty Mariya babu ko kiftawa, lkci daya ta sauka daga saman gadon da take tace "Aunty ba shi da lafiya ne?" Usman dai kallonta kawai yake, Aunty Mariya ta ɗan zare ido don ta mance a gabanta tayi tambayar, nan da nan ta kirkiro murmushi tace "Jiya ya dawo bashi da lafiya shine ya je ganin likita, amma da sauki ai" Mayraah dai ta dinga kallonta babu ko kiftawa, Can ta juya ta kalli Usman da damuwa tace "Ya Usman dama Yaya bashi da lafiya shi ne aka ki gaya min?" Usman yace "Ya samu lafiya yanzu, idan mun je gida za ki gani" Aunty Mariya ta kama hannunta suka fita daga ward din Usman ya bi bayansu, kamar yanda MD ke avoiding eye contacts da Mayraah for the past one week now, ita ma hakan take a wajenta, don tun da ta gane shine yayan Musharraf wanda back then Musharraf ya sha bata labarinsa amma kuma yace mata yana canada ta ma rasa gane ko kunyan abubuwan da ta dinga masa a baya take, ko kuma dana sanin abinda tayi masa take, wani zuciyar sai yace mata ai ita bata taɓa masa komai ba shine ma yayi ta mata walakanci, but all the same ko don saboda Musharraf ta dau alwashin dole zata ce masa yayi hakuri abubuwan da suka faru a baya amma dai ba yanzu ba tukun, suna fitowa Reception tare da Aunty Mariya kawai ta hada ido da shi, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri, Aunty Mariya na kallonsa da murmushi fuskarta tace "Toh Dr mu zamu tafi gida, Allah Ubangiji ya saka da alkhairi, don Allah ayi ma sauran likitocin ma godiya" Ya sauke idonsa yace "Ameen, Allah ya tsare" Kallo daya yayi ma Usman ya juya ya tafi sama, su kuma suka fita daga asibitin, Mayraah na shiga gida bayan ta rungume Ammi dake kitchen tana masu girki don Aunty Mariya ta kirata ta sanar mata an sallamesu, tambayar farko da ta fara yi ma Ammi bayan ta saketa shine "Ammi ina Yaya?" Ammi ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Anjima zai dawo, mu je kiyi wanka" Da damuwa Mayraah tace "Aa Ammi dama ashe bashi da lafiya ne kika ce min ya tafi kasar waje, don Allah ki gaya min inda yake" Ammi ta kama hannunta tace "Kin ga, in dai yaya ne ai dole zaki gansa tunda gida daya za ku kwana, yanzu mu je ki yi wanka ki ci abinci kafin la'asar yayi" Daga haka Ammi ta ja ta suka fita daga kitchen din zuwa sama. Tun da MD ya ga result din DNA test da Ceo ta sa ayi for the past one week ya shiga wani irin rudani da confusion, gaba daya tunaninsa ya kwance, don result din na fitowa kasa hakuri yayi har sai da duba duk da yasan bai kamata ya duba ba, kasa zaune yayi ya kasa tsaye a office dinsa, gashi ko awa daya ba ayi da su Mayraah suka tafi gida ba, does it mean matar nan da ya gani kwance saman gado ita ce mahaifiyar Mayraah? But how? Meye relationship din matar nan da Ceo? Da kansa fa ya debi jinin matar, sannan ya debi na Mayraah, how comes Genetic test din came out Positive, bai san sanda ya dau wayarsa ya kira Ceo da sauri ba, yana fara ring ta daga, ya koma ya zauna cike da confusion yace "Ma result din ya fito yanzu" Shiru Ceo tayi kamar bazata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Nasan ka duba Aliyu, me ka gani?" Cike da confusion yace "Ma'am it came out Positive" Cikin rawan murya Ceo tace "To ita ce mahaifiyarta" MD ya mike tsaye yace "But how Ma? Are you in anyway related to the Woman?" Ceo tayi karfin halin cewa "It's a very long story Aliyu" sai kuma ta fashe da kukan da take ta kokarin dannewa, MD da zuciyarsa ke bugawa yace "To mahaifinta fa?" Nan ma Ceo tayi shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma tayi murmushin takaici cikin rawan murya tace "Yana nan Aliyu, da kuma zan ambaci sunansa kai kanka zaka san sa, don he is well known amma yafi shekara bakwai rabonsa da Nigeria, time to time mu kan hadu da shi a UK" MD ya koma ya zauna ya ma rasa abinda zai ce mata, da kyar daga karshe ya iya cewa "Yanzu taya za a gabatar ma foster parent dinta wannan issue din?" Shiru tayi kamar bazata ce komai ba tana murmushin takaici, sai kuma a hankali tace "I will give them the time, day, date, month and year din da suka ganta, da kuma dai dai inda suka ganta din, da kuma yanayin da suka ganta" zuwa yanzu she was trying so hard to control her self kar ta fashe da kuka sosai, MD ya kara shiga wani confusion din, ya mike tsaye yace "Amma ta yaya kika san duk wannan Ma? Dama kinsan sanda aka yi deserting dinta ne da kuma inda aka yi deserting dinta?" Hawaye ne kawai ke sauka idonta ta kasa ce masa komai, bayan wasu seconds tayi gathering courage tace "I said it's a long story Aliyu, i will get back to you" Daga haka ta katse wayar yanda zata yi kukan dake cin ta sosai.
[8/26, 10:11 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Ammi ta ajiye abincin da ta kawo ma Mayraah har bedroom dinta da farfesun hanta tana kallonta tace "Ko zaki sha shayi?" Mayraah ta girgiza kai tace "A'a abincin ya isa Ammi" Ammi ta nufi kofa, Mayraah dai ta bi ta da kallo har ta fita ta kullo mata kofar, a hankali ta rufe abincin ta matsar gefe daya sannan ta mike ta dau hularta ta saka ta nufi kofar dakin ta bude a hankali tana leka corridor, sai da ta daina hango Ammi sannan ta fito ta kulle kofar dakinta ta sauka downstairs, dakin Maheer ta tafi ta kwankwasa kofar gently sannan ta murda handle din ta bude kofar, a tare suka juya shi da Usman suna kallon kofar, ta ɗan wara ido ta karasa ciki da sauri tana kallon Maheer da damuwa ta durkusa gabansa tace "Yaya baka san na dawo ba ne?" Sai kuma ta kalli Cannula din hannunsa kafin tace komai yace "Yanzu drip din ya kare zan yi sallah sai in je inyi welcoming dinki Mimi" Ta mike tana kallonsa cike da damuwa tace "Me ya sameka yaya? Since when were u sick?" a hankali yace "Naji sauki ai, Alhamdulillah" Ta kai hannu forehead dinsa gently taji temperature dinsa is normal, cikin sanyin murya tace "Allah ya sauwake yaya" Ya sauke idonsa yace "Ameen Mimi, ya naki

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login