Showing 435001 words to 438000 words out of 456519 words
ya isa kowa a gidan nan" Usman na kallonta yace "Wani abinci?" Mama Ladi ta wani taɓe baki tace "Abincin maraice mana, da rana ma duk ba a koshi ba wallahi Usuman" Usman bai kara tanka ta ba, Mama Ladi ta kalli Eeman da ta rufe ido kamar me bacci tace "Ita kuma wannan haka ta yini yau duk jikinta zafi, ga shegen son jiki tun dazu take makale da ni, in na koreta ta dawo, kyau ace ko er gasasshen kaza ne ta samu wai bakinta ba dadi, ko abinci bata iya ci" Usman ya dinga kallon Eeman da idonta ke lumshe, can yace "Me ke damun ta?" Mama Ladi tace "Canjin yanayi mana Usman, kaga yanzu an kare damuna lafiya, ga sanyi kuma ya taho" Tashi yayi after few seconds ya wuce sama, A hankali Eeman ta ɗan bude ido ganin ya haura sama ta mike zaune, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Wai har yau baku shirya bane da abokin turancin naki?" Eeman ta wani hade rai ta kauda kai tace "Ni bazan taɓa shiryawa da shi ba har abada" Mama Ladi tace "Atoh dai, dama kece baki ji kiyi ta shige masa kamar talaka ya ga Me kudi, haka wata jikata na nan muna ce mata Badiyyah, yarinyar nan taci azaba a hannunsa, wallahi jikinta duk shatin dukansa ne daga sama har kasa, ya ci zalinta ba kadan ba, baiwar Allah tana can tayi aure a wani gari kafin Bichi, baki ga babu me shiga sabgarsa a gidan nan ba sai ke me makale masa kamar kudin cizo, kinga Mera kafin ta auri yayansa ko ga maciji bata yi da shi wllh, saboda ta san halinsa, shi yasa har tayi aure bai taɓa kai mata hannu ba to ina yaga fuska" Shiru Mama Ladi tayi ganin Usman na saukowa daga sama, Eeman ta sauke idonta don da basu hada ido da shi ba dama komawa zata yi ta kwanta kafar Mama Ladi da sauri ta rufe ido, Mama Ladi na kallonsa tace "Yo ai na mance ban gaya maka ba Ammin bata nan ta tafi kaduna, mu kadai ne a gidan yau Usuman, facalolin Mariya ke aurar da 'ya yansu mata uku lkci daya kasan duk sun zo bikin Mera da Mashir, shine ta shirya ta tafi bikin, ni dai nace bazan je ba, ana zaune lafiya a gidan ma ya mutum ya kare balle ana biki, Ammi dai ana tafi biki Kaduna" Usman yace "Na sani ai" Eeman ta ɗan kallesa suka hada ido, murya can ciki kamar warce aka yi ma dole tace "Ina wuni" Fitarsa yayi daga parlon, yana kulle kofa Mama Ladi tace "Maganin ki kenan, wa ya aikeki ki gaishesa?" Eeman kamar zata tayi kuka tace "To ba kallona naga yayi ba shi yasa" Mama Ladi tace "Ai ba kallonki ba, ko ta kusa da gabanki ya wuce jan bakinki ya kamata kiyi kiyi shiru, ba a fa abun arziki da Usuman, kece ma naga yana ɗan buda ma hakora kwanaki can" Eeman tace "Ai bazan sake gaishesa ba" Mama Ladi tace "Berry gud, dubo mana ko abincin ya tsotse" Mikewa Eeman tayi ta tafi kitchen. Mayraah na kwance parlon Ammi tana waya da Maheer, tace "Komai sai ta sa ma mutum ido, ni dai kawai gwara in koma gida" Maheer dake ta sauraronta yana murmushi yace "To ai kinga Ammi ta tafi kaduna wife, daga kaduna kuma zata tafi kano wajen Hajja, so kiyi hakuri ki bari ta dawo sai in gaya mata kince zaki dawo gida" Mayraah tace "Ban gane nace zan dawo gida ba, kai komai sai ka wani cire kanka ka bar mutum a ciki, me yasa baza ka ce mata kawai zan koma gida ba without involving me?" Shiru Maheer yayi, don abu kadan ke provoking dinta yanzun nan sai ta dandankara ma mutum magana, sai da tayi shiru don kanta yace "Toh kiyi hakuri Mimi, in ta dawo zan ce mata zan tafi da ke gida" Mayraah dai bata ce masa komai ba tana cin shinkafar dake kafanta, Yace "Let me take my bath i will call u back later" Tace "Aa zan yi bacci kafin nan" a hankali yace "Ohk" Tace "Kawai ni dai gobe ka siyo min kayan shayi ka kawo na gaji da maganarta a gidan nan" Maheer yace "Ohk i will dear, zan maki shopping gobe in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Tace "Sai da safe" Yace "Har mun gama wayar Baby?" Tace "Bacci na fara ji" Yace "Ohk My love, sleep tight, don't forget ki ajiye abinci kusa dake ba sai kin sauka downstairs ba later cikin dare" Tace "Ohk..." Sallama ya kara mata sannan ya katse wayar, Ita da Ihsaan ne kawai a part din Ammi, Eeman na can da Mama Ladi. Eemaan na kitchen tana ta kokarin dafa ma ita da Mami Ladi irin shayin da taga Ihsaan na yi ma Ammi, tafi minti ashirin a kitchen din da ta fara dafa shayin in ta ɗanɗana sai taji yayi daci sosai, ta rasa me take sa wa yake sa shi ɗacin nan, daukan na hudun tayi zata zubar kenan aka bude kofar kitchen din, da sauri ta juya bayan sun hada ido, ta ajiye shayin hannunta ta kashe gas din ya kulle kofar kitchen din ya nufo ta. Ya tsaya dai dai kusa da ita yace "Have i turn to a ghost that you are running away from?" Ƙin dago kanta tayi, yace "Eeman" Ta wani kallesa da manyan idonta, sai kuma ta juya masa baya ta fashe da kuka ba hawaye, jawota yayi kusa da shi yace "To gaya min me na maki?" Bude kofar kitchen din aka yi ya saketa da sauri amma tuni Mama Ladi ta shigo, yi tayi kamar bata gansu ba tace "Usuman awa guda kenan yarinyar nan tace zata dafa mana irin shayin da ake yi ma Ammi, na ji shirun yayi yawa nace to Allah ya sa ba fasa tukunyar tayi ba" Usman bai yarda su hada ido da Mama Ladi ba don sarai yasan ta gansu, ya nufi inda Eeman ta ajiye shayin ya dau cokali ya debi shayin ya kai baki yaji daci kamar ta saka shuwaka, Mama Ladi tace "To bari in dauko kopi in zuba nawa bazan tsaya iskanci ba" Usman ya juya ya ɗan yi murmushi bai dai ce komai ba, Mama Ladi ta dauko cup da cokali ita ma sai da ta fara debo shayin ta kai baki sai kuma ta juya ta kalli Eeman, bayan ta hadiye da kyar tace "Tirr, yanzu uwar meye wannan kika dafa Eemani? Ke yanzu ba a wani abun arziki dake, babu abinda kika iya sai kawo tsegumi, ga er uwarki nan sai tayi girkin mudu biyu lafiya lau, komanta tsaf tsaf cikin nutsuwa gwanin ban sha'awa, aa gaskiya Ammi na da aiki a gabanta don babu shegen namijin da zai zauna dake a haka ki sa masa hawan jini wataran ya nakada maki shegen duka ya koro mana ke mu kuma saboda ƙin Allah muce bai kyauta ba bayan duk mun san halinki, haka dazu da safe nayi da na sanin ce maki ki gyara min daki, to yanzu kina nufin zubda wnn tsadadden shayin za ayi ko me? Ba fa sato kudi Mamuda yake ba, Bamu gama ji da barnatar mana da abinci da Mera ke yi a gidan nan ba kema gashi zaki barnatar da tsadadden shayi, da na sani Ihisani nasa bakina alekum wllhi, dama kar in ga kafarki a dakina na gaji dake kuma haka" Mama Ladi na kai wa nan ta fice daga kitchen din, Usman dai sai kallon Eeman da ta sunkuyar da kai yake, yayi kasa da murya yace "Yaushe za ki iya abun arziki a rayuwar ki Eeman? Just common tea ma baki iya dafawa ba" Ta wani turo baki zata fita daga kitchen din ya rikota ta fashe masa da kuka sosai, lallashinta ya shiga yi yana kallon fuskarta a hankali yace "Kyale Mama Ladi, ita ma tana kamar ki ba abinda ta iya sai hawa bishiya da debo ma mutane masaran da suka shuka a gonarsu" Eeman ta kyalkyale da dariya hawaye na zuba idonta tace "Ta yaya ka sani Yaya?" Usman na murmushi ya goge idonta yace "Yayarta Hajja ke bamu labari, in masu gonan suka biyota gida Hajja ta basu hakuri ta mayar masu da masaran su, ita kuma ta nakada mata duka" Ganin yanda Eeman ke babbaka dariya ya wani hade rai yace "Kee" Ta hadiye dariyar ta marairaice tace "To ba kai ne ka ban dariya ba" Yace "Yanzu ki tafasa min just ordinary water, sai ki saka madara da Milo, banda sugar, kin ji abinda nace?" Eeman na kallonsa tace "Na ji" Sau biyu yana repeating din kansa kafin ya juya ya fita daga kitchen din ya koma parlor ya zauna. 15 mins later Eeman na tsaye parlor da mop a hannunta ta gama goge shayin da ya fadi kasa garin kawo masa, takalmi ne a kafarta duk da ta share pieces din mug din da ya tarwatse a kasa kafin ta goge wajen, tana ta kallon Usman dake danna wayarsa, shi kam ko kallon inda take bai yi ba, a hankali tace "Yaya in hado maka wani shayin?" Wani kallo ya jefa mata, tayi shiru ta sunkuyar da kai, juyawa tayi ta maida mop din hannunta inda sauran suke sannan ta dawo parlon zata wuce sama, yace "Kee" Ta juya ta kallesa, Ledan dake dinning table ya nuna mata, tana tafiya a hankali ta dauko ledan har biyu ko wanne da gasasshen kaza a ciki, zata nufosa yace "Kar ki zo min nan, ki kai ma Mimi daya...." Kamar munafuka tace "Dayan nawa ne?" Hararanta yayi, ta sunkuyar da kanta ta wuce sama tana ɗan murmushi, sai da ta ajiye ledan nata kazan a daki sannan ta kai ma Mayraah nata, ta dawo dakin kenan ta bude kazar ta aka bude kofa, Tuni Eeman ta matsar da ledan zuwa daya side din gado ta kwanta ta lumshe ido kamar me bacci, Mama Ladi ta shigo dakin tana cewa "Eemani nace yau baza ki kwana dakina ba ne, ina ta jiranki tun dazu" Eeman taki bude ido, Mama Ladi sai bin dakin take da kallo jin kamshin kaza, Eeman ta mike zaune tana murza ido Mama Ladi tace "Har na gaji da jiran ki naga shiru baki shigo ba shine nace bari dai in duba ko lafiya" Kallon Ledan kazan Mama Ladi da ta zagayo zuwa daya side din gadon ta tsaya tana yi tace "Wannan fa?" Eeman ta ɗan yatsine fuska tace "Ya Usman ne ya kawo min ni bana so, maida masa zanyi" Mama Ladi tace "Ji banza, ki maida masa a saboda me" zaunawa Mama Ladi tayi ta jawo ledan, Eeman na washe baki ta dau cinyan kaza daya ta fara ci tace "Dama karya nake ba maidawa zan yi ba fa" Mama Ladi ta dau tsoka daya tana gyara zama ta kai baki tace "Atohh dai, ko uwaka ubanka kake da mutum don ya baka kaza ai baka ki amsa ba tunda ba rokonsa kayi ba, kin ma ciri tuta don ban taɓa ganin ya siya ma ko uwarsa kaza ba sai ke, da gani sulhu yake nema, kar ki kuskura ki sake masa fuska har sai ya sake siya maki wani kazar" Tas suka cinye kazar da Mama Ladi, Mama Ladi ta mike tana gwaguyen ƙashin kazan hannunta tace "Bari in dauko mana lemo me sanyi a firiji" Tana fita ko minti biyar ba ayi ba sai gata ta dawo ba lemun, ta jefar da sauran kazan hannunta ta zauna tana kallon kafarta cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, wani shege tsinanne ya fasa kwalba na taka ya shige min kafa" Eeman ta fashe da wani mahaukacin dariya har da kwanciya tana kyakyatawa.
Washegari Saturday karfe goma Maheer ya shigo gidan, Ihsaan da ta gama sharan gidan gaba daya tayi mopping tana goge gogen kayan kallon ta juya tana kallonsa ta gaishesa, ya amsa yace "Sannu da aiki" Tayi murmushi ta ci gaba da abinda take, ya karaso ya zauna parlon yace "Mimi bacci take ko?" Ihsaan tace "Ehh bata tashi ba" Mama Ladi ce ta fito daga kitchen, ganin Maheer tace "Aa, yaushe ka shigo Mashir" Gaisheta yayi ta amsa ta zauna tace "Kai, wallahi Mendi yayi dacen mace, kafin mu tashi bacci fa yarinyar nan har ta mana kumallo, gashi ta gyara ko ina fes ta share sai kamshi ke tashi a gidan, kasan Balki tare suka tafi da Ammi za a ajiyeta garinsu wai uwarta ba lafiya, ina gaya maka Eemani na can cikin bargo, wallahi mijinta ya banu ya lalace kyau a bari sai tayi shekara talatin kafin a aurar da ita don banga zata yi hankali shekaru biyar kusa ba" Maheer dai danna wayarsa kawai yake yana murmushi, Mama Ladi tace "Gwara Mera za mu ce ba ita kadai bace shi sa take baccin asara yanzu, bata tabuka mana komai a gidan nan sai ci da bacci, tunda dai kafin tayi aure duk mun san tana da hazaka bata da son jiki shi sa abun bai dame mu ba, amma lamarin Eemani na ban tsoro, wllh Ammi na da aiki ja a gabanta, da za aji ta nawa ma kar Balki ta dawo gidan nan, Eemani ta amshi duk aikin Balki" Maheer was just pressing his phone bai ce komai ba, Ihsaan kuma tana ta goge gogenta ita ma, sai ga Usman ya shigo parlon, sai da ya fara gaida Maheer sannan ya kalli Ihsaan, gaishesa tayi ya amsa, Mama Ladi dama tun asuba da ta sauko hada shayin farko suka hadu ya gaisheta, yana kallon Ihsaan yace "Ba na hanaki aiki a gidan nan ba Ihsaan? Ina Eeman din" Mama Ladi tayi karaf tace "Bata tashi ba wallahi, tana can cikin bargo" Usman na kallon Ihsaan yace "Je ki taso ta" Ihsaan ta ajiye towel din hannunta ta wuce sama, Mama Ladi ta zauna tace "Ai dai aure Ihsanin zata yi ta bar ta, zan ga a wani gida zata dinga bacci har karfe goma, dama Balki an sallameta ba sai ta dawo mana ba" Tare Ihsaan da Eeman dake kumbure kumbure suka sauko kasa, taki yarda ta hada ido da kowa tana murza ido, Maheer na kallonta yace "Je booth din motata ki shigo da kayan ciki" Sai a sannan ta daga kai ta kalli Maheer ta gaishesa ya amsa sannan ta nufi kofa ta fita, Mama Ladi sai kallon Usman dake mata mugun kallo take tana ɗan murmushi tace "Kyau wataran ka tsutsula mata belet dinka, in ko baka yi haka ba bazata taɓa shiga taitayinta ba a gidan nan, kaga da haka er uwarta take sai muce ai an sangartasu ne dama, kai dai kawai ka bar yaro me son jiki, tsaf zai kunyata ka a idon duniya, to ga dai Eemani shimfidar gado ma bata iya ba" Eeman ta dinga shigo da shopping din da Maheer yayi a safiyar, Mama Ladi dai ba bakin magana, sai satan kallon kayan take, nan ta fara zargin to ko de Eeman ta fada ma Mera abubuwan da ta dinga fada ne jiya, sai da Eeman ta shigo da duk kayan, Maheer yace "Weldone" Ta ɗan yi murmushi zata wuce sama Usman ya mata wani tsawa, juyowa tayi kamar zata yi kuka tana kallonsa, yace "Put this at the back of ur brain, ke zaki yi girkin rana sannan kiyi na dare" Da sauri Mama Ladi ta mike tana girgiza hannu tace "Aa Usuman, gaskiya a'a, kar ma a fara, ba fa iya cin girkinta muke ba a gidan nan, so kake mu wuni da yunwa mu kwana da yunwa, ina laifin kace Ihsani ta yi mana namu girkin, ita Eemanin sai ta girka wanda kai da ita za ku ci, aa wallahi babu me tilasta mana mu ci girkin Eemani a gidan nan, kar ma a fara" Mama Ladi na kai wa nan ta wuce sama, Usman na kallon Eeman da har taji dadi a ranta yace "Ke zaki yi both Lunch and Dinner" Ta fashe da kuka tace "Ammi ce fa tace Ihsaan ta dinga girki ni in dinga sharara da goge goge" Tuni Usman ya fita daga parlon, Maheer dai murmushi kawai yake yana danna wayarsa, Ihsaan kuma ta ci gaba da abinda take, Eeman ta zauna bakin stairs tayi tagumi tana rusa kuka. Ammi na dawowa daga kano da kwana biyu Mayraah ta sa Maheer ya gaya mata zata koma gida, Ammi na zaune parlonta bayan magrib sai kallon Mama Ladi dake ta bayani take, Mama Ladi tace "Aa ba zancen ki dinga kallo na haka ba Ammi, wallahi in aka kuskura aka kai lefen yarinyar nan katsina kwashe mata kaya tsinannun dangin uban za su yi, mutanen da duk mun san ba tsoron Allah garesu ba, da wani idon za mu kalli pamilyn Alhaji Saminu in suka ga an kwashe kayan da suka kai?" Ammi tace "To ya kike so ayi Mama, can din ya kamata akai lefen don ta ko ina sun fi mu iko da yarinyar nan, in ma sun kwashe mata kaya su da Allah, kuma ai dangin MD din sun san inda suka kai lefe da kike cewa da wani idon za mu kallesu" Mama Ladi tayi tagumi tace "Ni dai na shiga uku ni Ladi, komai ace sun fi mu iko da yara, ta ina suka fi mu ikon nan ne wai tukun? shegun da suka kasa rike marayun yaran kuma ayi ta cewa sun fi mu iko" Maheer dake parlon yayi dariya shi dai bai ce komai ba, Mama Ladi ta juya ta kallesa tace "Kai kaji wani shashashan batu Mashir, mutanen da ba tsoron Allah garesu ba ayi ta wani mutunta su ana cewa sun fi mu iko da yara, ni dai wallahi basu fi ni iko da yan biyun nan ba" Maheer yace "To kawai abinda ya kamata ki shirya ki je katsinan a amshi lefen dake kawai Mama" Mama Ladi