Showing 438001 words to 441000 words out of 456519 words

Chapter 147 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70681

ta gyara zama tace "Haka kuma ya kamata ayi fa, ai dama ya kamata ace mutum daya yaje daga nan tunda wajenmu yaran nan suke, to a ina za ayi daurin aure da taron biki?" Ammi tace "Can katsina za ayi daurin auren, su yi taron su muyi namu a nan" Mama Ladi tace "Kuma mu dai ke da amarya a nan, yaushe naji Mamuda na cewa zata je katsinan?" Ammi tace "Cewa suka yi ba sai ta zo ba da ya sanar masu, wai sun ce hanya ba kyau" Mama Ladi ta saki salati tace "Ɗan abinda za su mata na aure fa suke gudu, yo Allah na tuba ko ni bazan mata kayan daki ba balle Mamuda, kai amma gaskiya ban taɓa ganin tsinannun mutane irin dangin uban yaran nan, wato basu da niyyar mata komai, to ni dai na hakura ma da zuwa amsan lefen, kada inje su bar ni da yunwa ni ba kowa gareni a katsina ba in shiga uku" Ammi tayi dariyar da bata yi niyya ba Maheer na taya ta, Mama Ladi ta mike ta nufi kofa tana cewa "Shi kuma Usuman ko budurwar gano mugayen halayyansa da yake ta boye mata tayi ne tace ta fasa auren, to ni dai har yau ban ji an sake zancen kai kudi ba, to dama ko alhakin Eemani ai ya isa yasa asirinsa ya tonu gun budurwar tasa, mutumi duk ya bi ya takura er mutane kullum sai ta zubda hawaye a gidan nan, in an bi ta a sannu in dai aiki ne ai duk zata iya wataran ba sai an dinga matsa mata ba, dama masu suna Hajara Allah na tuba ai duk an san halinsu ne wnn, sam basu da kwanturol" Maheer ya daga kai da sauri yana kallon Mama Ladi, ita dai Ammi murmushi kawai tayi, Mama Ladi dai ta fice ta bar masu parlon, bayan fitar Mama Ladi Ammi ta kalli Maheer don dazu taga yana ta kame kame yana son mata magana sai kuma Mama Ladi ta shigo, Ammi tace "Ko gida za ku koma tare da Mimin ne?" Ya daga kai ya kalli Ammi, yayi kasa da murya yace "Cewa tayi in maki magana zata koma gida saboda Mama Ladi" Ammi tayi murmushi don duk kwanan Drama suke da Mama Ladi don ma Mayraahn bata wani tanka ta, Ammi tace "Toh shikenan, yau din za ku tafi?" Yace "Eh" Ammi tace "To kayi mata magana ta fito ku tafi tana cikin daki" Mikewa yayi ya shiga dakin Ammi, Mayraah ta mike zaune tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Nayi ma Ammi magana" A hankali Mayraah tace "Ka ce mata za mu tafi da Ihsaan?" Ya zauna gefenta yace "Aa ban gaya mata ba, ke dai ki gaya mata" Tare suka fito parlon, Mayraah ta zauna tana kallon Ammi a hankali tace "Ammi don Allah za mu je da Ihsaan" Ammi tace "Gyaran jiki za a fara yi mata ai Mimi, ko ku je da Eeman" Da sauri Mayraah tace "Aa Ammi" Ammi tayi dariya tace "Wai ya ake min kakkabi da 'ya ta ne" Mayraah ta marairaice tace "Ammi ai ko daga can za a dinga zuwa yi mata gyaran jikin" Ammi tayi murmushi tace "To ai ko ta bi ku ba dadewa fa zata yi ba Mimi, ko a samar maku me aiki?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa" Ammi tace "Toh shikenan, kiyi mata magana ta shirya sai ku tafi" Murmushi Mayraah tayi ta mike ta fita daga parlon don sanar ma Ihsaan ta hada kayanta, Mama Ladi ce ta shigo parlon Ammi da sauri tace "Ammi ke kika ce Ihsaani ta hada kaya ta bi Mera?" Ammi tace "Eh" Mama Ladi tace "To a gaskiya ki buga ma Balki waya duk inda take ma ta dawo, ubanwa zai dinga mana girki a gidan nan, ba dai Eemani ba dai ko? Yarinyar da ko shayi bata iya dafawa ba, shinkafan nan ɗan banza in ta dafa sai ya caɓe, To wallahi Buga ma Balki waya ta dawo babu me iyawa da girkin Eemani a gidan nan in dai ba zaman yunwa ake son mu fara a gidan Mamuda ba" Ammi dai bata ce ma Mama Ladi komai ba har ta fita daga parlon, a haka Mayraah suka bar gidan tare da Ihsaan....
Tun da Mayraah ta koma gidanta da Ihsaan ta lura gaba daya bata da walwala ko abincin kirki bata ci, tun ma daga gidan Ammi Mayraah ta lura da hakan, amma yanzu hakan yafi worst, it's just 2 weeks away from her wedding, ranan da daddare bayan Maheer yayi bacci Mayraah ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta saka a kan kayan baccin jikinta sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, dakin da Ihsaan take ta tafi, zaune ta ganta saman gado ta hade kanta da gwiwa, tana jin an bude kofa ta dago kanta da sauri tana goge idonta, Mayraah ta karasa har kan gadon ta zauna tana kallonta, Ihsaan dai ta kasa kallonta, Mayraah tayi kasa da murya tace "Few days back na tambayeki meke damunki kika ce min ba komai Ihsaan, ko kina son komawa gidan Ammi ne?" Ihsaan ta girgiza kai hawaye na sauka idonta, Mayraah ta kamo hannunta tace "Then tell me what ur problem is, kwana biyu na lura kun dena waya da MD ko?" Ihsaan ta fashe mata da kuka, Mayraah tace "Did u have issue with him?" Girgiza mata kai Ihsaan tayi hawaye na sauka idonta, Mayraah tace "To me yasa ku ka dena waya?" Cikin rawan murya tace "Na kashe wayan" Mayraah ta jawota jikinta tana patting bayanta cikin kwantar da murya tace "Tell me what the problem is Ihsaan, take me as your big sis, in kuma baza ki gaya min ba gobe sai in sa Yaya ya kai mu gidan Ammi sai ki gaya mata ita" Ihsaan ta girgiza mata kai da sauri, Mayraah tace "Then tell me what is it" hawaye na sauka idonta a hankali tace "Ni tsoro nake ji" Mayraah tayi shiru jin abinda tace, can tayi murmushi ta dago kanta tace "Tsoron MD din?" Ihsaan ta fashe mata da sabon kuka ta gyada mata kai, sosai ta ba Mayraah dariya amma ta dake bata yi ba, ta rungumeta tana patting din bayanta tana murmushi, gaba daya ta ma rasa me zata ce mata.
[11/3, 7:05 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya bude kofar ward din a hankali ya shiga ciki ya kulle, yana tafiya slowly ya nufi inda take kwance bayan ta bude idonta dake rufe tana kallonsa, dukawa yayi ya kamo hannunta yana kallon idonta da suka kumbura, gently ya goge mata hawayen da ya gangaro gefen idonta ya hada goshinsa da nata, yayi kasa da murya yace "Weldone Wife, may Allah S.W.T bless you" Ita dai kallonsa kawai take har sannan hawaye na bin gefen idonta, ya lumshe ido yayi kissing dinta, yace "Hope you are fine?" Da kyar ta gyada masa kai har sannan hawaye bai dena bin gefen idonta ba, ya sake kissing dinta yana share mata hawayen idonta yace "Billah i love you so much Mayraah, thank you for making me a father, today is one of my happiest day in life, Allah ya maki albarka wife" Mikewa yayi ta dalilin bude kofa da aka yi, wata nurse ta shigo ward din ta karaso har inda suke, Maheer ya amshi babyn hannunta yana kallon fuskar babyn, Nurse din ta kalli Mayraah da murmushi fuskarta tace "Congratulations Madam, Allah ubangiji ya raya, Allah ya baki lafiyar shayarwa" Daga haka ta juya ta fita daga ward din, Maheer ya duka ya dora ma Mayraah babyn a jikinta ta sauke idonta tana kallon kyakkyawan Babyn dake ta mutsu mutsu da baki, ganin taki rungume babyn yayi kasa da murya yace "Common Mimi, hold ur bundle of joy, let him feel ur warmth" Rungume Babyn tayi a jikinta ta lumshe ido wasu hawayen suka zubo idonta, shi dai kallonta kawai yake yana murmushi, bude ward din aka sake yi Mama Ladi ta shigo Ammi na biye da ita a baya rike da basket na kayan shayi da flask da cup, Mama Ladi ta saki salati tace "Kai jama'a... yanzu salon ma'aikatan asibitin su yi mata kallon bata da kowa yasa ka kawota asibiti tun jiya tana nakuda ita kadai baka sanar mana ba Mashir? Yaushe zaka fara yin abu irin na magidanta ne fisabilillahi gashi har an haifa maka yara uku biyu suna lahira, kai kanka kasan nas nas da gulman jaraba kamar don su aka halitto gulma, yanzu haka nasan duk asibitin ya dauka an kawota tun jiya da safe gashi har yau da maraice ba a ga kowa nata a tare da ita ba, wannan tozarci har ina Mashir" Shi dai Maheer bai ma kalleta ba balle ta sa ran zai tanka ta, Tuni Ammi ta karasa kusa da gadon da Mayraah take ta duka tana kallonta da babyn kusa da ita, she couldn't hide the joy on her face, tana girgiza kai trying not to shed tears amma hakan bai yiwu ba don sai da hawayen ya zuba idonta tace "Sannu Mimi, sannu daughter..." Mayraah ta ɗan yi murmushi kawai tana kallonta, Ammi ta dau Babyn jikinta tana kallo babu ko kiftawa, he was soo cute kamar ɗan larabawa jazir da shi, shi din ma dai yanayi yake da Maheer, Mama Ladi tayi maza ta amshesa jaririn daga hannun Ammi tace "Allahuuu Akbarrr, Allah mun gode maka da wannan ni'imar da ka mana, mace ce ko namiji?" Maheer yace "Namiji" Mama Ladi tace "Iko sai Allah, wannan balarabe kuma daga ina ni Ladidi, dama jarirai na da mikakken hanci? Iko sai Allah, ku ga ɗa kamar ɗan larabawan gaske, gashi sai da ya riƙa yayi bul bul a ciki aka haifosa tabarakallah maa sha Allah, kuma da kanta ta haifosa, Lalle Mera jaruma ce, ga dai rabin fuskar na uwar, rabi kuma sak na uban" Sai da Maheer ya kalleta, sai kace wani alien wai rabin fuska na uwa rabi kuma na uba, wannan wace irin mata ce, Ammi dai ta duka kusa da Mayraah ta kamo hannunta tana mata sannu, Duk ƙara da kawaici irin na Maheer haka ya nufi inda Ammi ta ajiye basket din da ta shigo da, ya bude flask din zai fara hada ma Mayraah shayi, Ammi na ganin haka ta mike amshi cup din a hannunsa, tsabar farin ciki da murna ta mance da batun kayan shayin, tana hada ma Mayraah shayin tayi masa barka, yayi kasa da kai yace "Ameen" Mama Ladi dai sai kallon jaririn take tsabar kyau kamar shi ya halitto kansa, anya ta taɓa ganin jariri me kyau haka ma kuwa, can tace "Ashe dai kwanaki jagwal aka haifo mana muke ta rawan jiki kamar tarwada, Ga dai jariri kamar daga tsatson larabawa ni ko sai kallonsa nake kamar na samu hoto, to uwa kyau uba kyau, kakanninsu ta wajen uwa da uba su ma kyau kamar su suka yo kansa, kunga kuwa ai dole a haiho balarabe, Allah sarki Badiyyah mijin dai na can kamar gwaggwon biri, ko me zata haifo" Sai da Ammi tayi stiff jin abinda Mama Ladi tace, can dai jiki a sanyaye ta gama hada ma Mayraah shayin yana tiriri ta mika mata, Mayraah ta amsa a hankali, Maheer ya fita daga ward din ganin Abba na kiransa yasan ya karaso asibitin ne.
Bayan isha Ammi ta kamo hannun Mayraah ta sauko daga kan gado a hankali ta saka takalmanta, Ammi ta mika mata hijab din da zata saka don an sallamesu, Abba ya nufi kofar ward din yana rungume da jaririn ya fita looking so happy, the happiness he felt holding Maheer as a new born was exactly how he is feeling today holding Maheer's son, tun da suka shigo dazu tare da Usman har aka yi discharging Mayraah suna nan asibitin, Maheer ya dau basket din kayan shayi zai fita Mama Ladi tace "Ai kyau ace duk inda mutum zai je kar ya kuskura ya bar abun magana ko abun kunya, don wannan abun magana ne Mashir ya bar ma Mera a asibitin nan, tana fara nakuda zai kawota asibiti sai yayi sauri ya bugo min waya, in ma bai bugo min ba ya bugo ma uwarsa ya sanar mata mu bar duk abinda muke mu gudo asibitin, amma sam Mashir bai yi haka ba, ya kawo er mutane kawai ita kadai tun jiya da rana har yau da maraice" Usman dake kallonta don tayi maganar nan yafi sau biyar tun shigowansa ward din da Abba, zata ci gaba da magana ya katse ta yace "To wai ko an kira an gaya maki me za ki zo kiyi a asibitin banda labari kamar yanda kike yi yanzu Mama? ai ba ko wani asibiti bane suke yarda ai masu gayya a zo a cika masu waje da surutu, ba asibitin gwamnati bane nan din, sannan duk wani me kula da ita naga ai a bayan mijinta yake, da ba don nan yake aiki ba ma baza a bari ki shigo ba...." Ammi dai gyara ma Mayraah Hijab dinta kawai take, Usman ya mike ya bi bayan Maheer ya fice daga ward din, Mama Ladi da ta kasa tashi daga kan kujeran da take zaune ta kalli Ammi a hankali tace "Kin ga dai ban yi da yaron nan Usuman ba amma babu abinda ya mance bai gaya min ba a nan" Sai kuma ta fara matsar kwalla tana gogewa da gyalenta tace "Yau da dashi nake abun bazai min ciwo ba, shi Mashir din bai da baki ne? Da yake yaron arziki ne yaron kirki me ladabi da biyayya da girmama manya kinga ai tun dazu da nake ta mitata bai tanka ni ba tsabar yanda ya koshi da tarbiya, me nayi ma Usuman ya zage ni haka? Daga dai na nuna bakin cikina ba a kira mu mun zo asibiti mu taya Mera da addu'a ba tana nakuda" Ammi ta kalleta tace "Don Allah ki taso mu tafi Mama kiyi hakuri ki rabu da Usman..." Mikewa Mama Ladi tayi tana share hawaye ta bi su suka fita daga ward din.
Gata kam babu irin wanda Mayraah bata gani ba ta ko wani Angle, washegarin ranan da ta haihu Grandma dinta ta kamo hanyar Abuja, Aunty Mariya ma haka, she felt soo love ta ko ina, ranan da Grandma dinta ta iso tana zaune daki da yamma Ummin Zainab na shirya Baby bayan ta gama masa wanka Bilkisu ta shigo dakin da sallama tana rike da wayar Maheer ta mika mata tace "Wai gashi za ayi maki magana Maman Baby" Mayraah ta amshi wayar tana duba screen din, bude ido tayi ganin video call ne, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi, muryar Ihsaan taji tana cewa "Aunty Mimi Congratulations" Mayraah ta daga ido tana kallon Screen din wayar hannunta, taga Ihsaan a bayan kujeran da MD ke zaune tana waving mata hannu tana murmushi, sosai tayi wani kyau ta cicciko kamar ba ita ba, Mayraah na murmushi tace "Hi Ihsaan ya kike" Ihsaan na murmushin ita ma tace "Lafiya lau Aunty, ya baby?" Mayraah ta haska mata babyn don Ummin Zainab ta gama shirya sa ta kwantar da shi, Ihsaan tace "Waow, he is so cute Aunty, plss peck him on the lips for me" Ita dai Mayraah murmushi kawai take, kuma ko da wasa taki yarda ta hada ido da MD dake kallonta yana murmushi, mikewa yayi ya bar kusa da Ihsaan da ta cika masa kunne lamenting how handsome the baby was, yana kallon Mayraah yace "Congratulations matar Yaya" Mayraah ta ɗan kallesa ta rufe ido da hannunta still smiling, yace "Hope you are doing fine?" Ta zame hannunta ta gyada masa kai a hankali tace "Alhamdulillah, how is Canada?" Yace "Cool Mimi, in sha Allah in few days time za mu shigo Nigeria" Mayraah tace "Toh Allah ya kai mu" Yayi er dariya yace "Sai ga Mimi da Babyn Yaya... Mimi gave birth to Lil Maheer" Mayraah ta wani turo baki tana masa wani kallo, yana dariya yace "Bye Dear, take good care of ur self, Allah ya kara lafiyar shayarwa" A hankali tace "Ameen Nagode sosai, Allah ya dawo da ku lafiya" Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar, Mayraah ta juya ta kalli little Baby dinta dake bacci, har ranta take jin babyn, ko gajiya da kallonsa bata yi, ganin su biyu ne kawai a dakin ta duka giving him a kiss on his soft cheek, bude kofar dakin aka yi ta mike zaune da sauri, Maheer ne ya shigo dakin, tun safe rabon da ta gansa, ta dinga kallonsa har ya karaso cikin dakin, ya isa har gabanta ya duka, kissing her forehead yace "How are you wife?" Ta gyada masa kai tana murmushi tace "I'm fine...." Ya duka ya dau babyn yana kallonsa, sai kuma ya kalleta yace "I'm still yet to figure out wanda babyn ke kama da" Mayraah ta nuna masa kanta, Yana murmushi ya zauna kan kujera yana facing dinta, tun dazu yake son magana da ita amma sbda mutane bai samu daman hakan ba, a hankali yace "Na baki zabin sunan babyn, wani suna kike son ayi masa huduba da?" Mayraah tayi shiru tana kallonsa, lkci daya wasu memory suka dinga dawo mata, after some seconds ta sunkuyar da kanta, cikin sanyin murya tace "Are.... you, okay with Musharraf?" Maheer ya dinga kallonta, bata iya ta hada ido da shi ba, after a while yayi kasa da murya yace "Why not Mimi, in har haka kike so, so be it in sha Allah" Ta daga kai ta kallesa, hawaye ya gani idonta, ya mike ya dawo inda take ya kwantar da Babyn hannunsa sannan ya zauna kusa da ita da damuwa yace "Is there any other thing apart from this Wife?" Ta girgiza masa kai, yayi mata side hug yana goge mata hawayen idonta a hankali. Ana saura kwana biyu suna Mom din Mayraah da Dad

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login