Showing 426001 words to 429000 words out of 456519 words

Chapter 143 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70704

da su Eeman ke mata, Mama Ladi ta nemi kujera ta zauna tana bin ko ina da kallo tace "To ina Mashir din?" Mayraah tace "Bai dawo aiki ba" Mama Ladi tace "Bawan Allah, to xuwa nayi in sanar maku an saka bikin Ihsaan da Mendi wata biyu kacal..." Mayraah na murmushi tace "Ammi ta gaya ma Yaya jiya da ya kirata ai, dama cewa yayi in ya dawo aiki sai mu je can gidan anjima" Mama Ladi tace "Ni na zata ma bakwa garin ne ai..." Mayraah dai sai murmushi take ta tafi kitchen zata kawo masu ruwa, gashi yau kwana biyu rabon da tayi girki, kawai taji girkin ya fice a kanta gaba daya ta rasa me ke damunta a ranta, she is so tensed ga dai shi babu inda ke mata ciwo, wannan yasa da ya dawo aiki jiya ya duba Bp dinta yaga yayi kasa sosai, a daren ya fita ya siyo mata fruits iri iri ta zuba a fridge, haka nan Mayraah ta kawo masu ruwa da lemo, sai fruits sannan ta koma kitchen tana tunanin abinda zata dafa masu, tun bata fara girkin ba taji baza ta iya ba, kawai ta tuna akwai cup cake da tayi order jiya, ta dauka ta kai masu kawai. Har karfe biyar da wani abu su Mama Ladi na gidan, Maheer na dawowa aiki da takeaway din abinci da Mayraah tace ya yi masu a hanya Mama Ladi ta fara tattara cake dinta da bata ci ba da kwalin katon lemo duk ta saka cikin jakarta tace "Dama kai nake jira maza maida ni inda na fi wayo, cikina sai kugi yake, ta hadamu da kayan marmari kamar wasu marasa lafiya" Mayraah ta buda baki tana kallon Mama Ladi, Maheer yayi dariya yace "Ai ga abincin na taho maku da shi gas din girkin ya kare ne" Mama Ladi ta amshi ledan hannunsa ta cire takeaway daya ta saka a jakarta tace "Mu je ka ajiye ni gida" A hankali Mayraah tace "Don Allah ku kwana mana Mama sai mu je can gidan gobe gaba daya" Mama Ladi tace "Haram, in kwana inyi me a gidan yara, gashi wai ba gas, o'o ban saba kwana gidan mutane ba gaskiya, gwara kawai ya tafi ya ajiyeni gidan 'ya ta, in su Eemani za su kwana to su kwana tunda gidan yayyinsu ne dama" Haka nan Maheer ya tafi kai Mama Ladi gidan Ammi leaving the twins behind... Washegari da yamma wajen karfe biyar Mayraah ta fito parlor ta sa su Ihsaan su shirya don Maheer zai yi dropping dinsu gidan matar Dr Khalil ta haihu, sosai taji dadin kwanan da yan biyun suka yi a gidan don throughout bacci ta yini take yi, duk su suka yi komai a gidan har girki, iyaka da ta farka ta ɗan ci apple ta koma bacci, in lkcn sllh yayi ta tashi tayi, bayan Magrib Maheer ya kai su gidan, Mayraah ta juya tana kallonsa bayan yayi parking a waje, a hankali tace "Zaka shiga ne Dear?" Yace "Aa kawai ku shiga in kun gama ki kirani" Tace "Ina zaka?" Yace "Fueling station" Mayraah tace "Ohk Dear" Sauka tayi daga motar su Eeman ma suka sauka rike da ledan atamfa biyu da kayan baby da Mayraah ta siya ma babyn da Zainab ta haifa, A cikin jakarta dubu ashirin ne da Maheer ya bata ta ba Zainab din... Mayraah ta shiga compound din tare da su Ihsaan dake biye da ita, a bude suka tar da kofar parlon Mayraah ta shiga da sallama suna biye da ita, Zaune taga MD a parlon da Dr Hamid, sai shi kansa Dr Khalil din, tun da suka shigo parlon idon MD ke kan Ihsaan da taki yarda ta hada ido da kowa na parlon, Dr Hamid kam sai kallon Eemaan dake murmushi tana gaishesu yake da kyar Mayraah ke jan kafa jin cikin ta ya hautsine lkci daya saboda aroma din girki da ya cika mata hanci, ji tayi amai na neman taho mata ta nufi hanyar bandaki dake cikin parlon da sauri tana rufe bakinta, MD da Dr Khalil suka mike tsaye suka bi ta da kallo, Cousin sis din Zainab da ta fito daga kitchen ta bi bayan Mayraah zuwa bakin bandakin tana mata sannu, sosai Mayraah ta galabaita don babu abinda ta ci tun safe sai apple, Cousin sis din Zainab ta rikota ganin ta kasa tsayuwa suka fita daga bandakin tana mata sannu....



Ur evidence via 07087865788




[10/28, 9:22 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah bata tsaya gaida su MD da suka bi ta da kallo a parlon ba ta wuce dakin Zainab, after almost 10 minutes Dr Khalil ya shigo dakin da sallama ya zauna kan kujera yana kallon Mayraah da ta Kwanta gefen gadon Zainab, a hankali Mayraah ta gaishesa, ya amsa yace "Dama baki da lafiya ne?" Tace "Eh bana jin dadi, amma am getting better" yace "Allah ya sauwake, ina Dakta?" Ta sauke idonta tace "Shi yayi dropping din mu" Yace "Ohk, shine bai shigo ba kuma" Ɗan murmushi kawai Mayraah tayi bata ce komai ba, Dr Khalil yace "Allah ya sauwake Mayraah" Tace "Ameen" Ya mike ya fita daga dakin, Mayraah na kallon Zainab tace "Ina yan biyu?" Zainab tayi murmushi tace "Suna can gida wajen Ummi, sai kallon wa ennan twins din nake tun dazu wishing to see mine grow like this one day" Mayraah ta kalli su Ihsaan da Eeman dake dakin tace "In sha Allah kamar gobe ne" Zainab na murmushi tace "In sha Allah" Cousin sis din Zainab me suna Hafsat ta shigo dakin tana kallon Mayraah tace "Sannu ya jikin yanzu?" Mayraah tace "Alhmdlh" Hafsat tace "Za ki iya cin abincin ma kuwa?" Da sauri Mayraah ta girgiza kai don kawai at the mention of abinci taji wani aman na kokarin zuwa mata, ta mike zaune, Zainab dake kallonta tace "Ko a kawo maki tea ko Lipton?" Mayraah tace "Am okay" Cousin sis din Zainab na kallon Eeman dake rungume da baby din Zainab da Ihsaan dake kusa da ita tace "To ku muje dinning ku ci abinci tunda bata son aroma din abincin...." Ihsaan ta girgiza kai tace "Mun ci abinci a gida" Zainab tace "Aa don Allah ku ci ko kadan ne, kawo Babyn ku je ku ci abincin, ko a kai maku wani dakin in baza ku je parlor ba" Ihsaan ta girgiza kai tace "Sai dai ko Eeman" Eeman ta wani kalleta, sai kuma ta kalli Hafsat tace "Aunty mun ci abinci a gida, thank you so much" Hafsat tace "Toh shikenan" Juyawa tayi ta fita daga dakin, ko minti uku bata yi da fita ba sai ga ta ta dawo dakin tana kallon both Eeman da Ihsaan tace "Ana kiran Ihsaan a cikin ku" Ihsaan ta daga kai tana kallon Hafsat, sai kuma ta kalli Mayraah dake kwance, Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Tashi ki je mana, kina zare ido kamar baki san me kiran ki ba" Ihsaan dai bata ce komai ba, after few seconds ta ajiye wayarta da handbag a hankali ta mike ta fita daga dakin, Eemaan tana kallon Mayraah ta wani taɓe baki tayi kasa da murya tace "Aunty she is pretending she doesn't know who is calling her" Ihsaan ce ta dawo dakin Eeman tayi maza tayi shiru tana gyara hulan babyn dake hannunta, Sosai ta ba Mayraah dariya, Mayraah ta gama lura shegen tsokana ne da Eeman ga shiga sabgar da ba a sa ta ba shi yasa tasu ta zo daya da Mama Ladi sosai, unlike Ihsaan that is always on her own and minding her business, ko magana sai ya kama take yi, ko kuma ta kalleka ma taki cewa komai, shi sa ba su cika shiri da er uwar tata ba kullum cikin fada suke, Ihsaan ta nufi inda Mayraah ke kwance ta duka kusa da ita tana kallonta tayi kasa da murya tana murmushi tace "Aunty ko za ki ara min hijab dinki plsss" Mayraah tace "Me ya samu gyalen naki?" Ihsaan ta sauke idonta tace "It's not big" Mayraah tace "Da baki san bai da girma ba kika fito da shi" Murmushi kawai Ihsaan tayi bata ce komai ba, Eemaan har ta gaji da mika wuya duk don taji maganar me Ihsaan ke yi amma bata jin komai, Zainab sai kallon Eeman take don ba karamin dariya ta bata ba, Mayraah na kallon Ihsaan tace "Ki je da gyalen ai dare ne Ihsaan" Ihsaan dai tayi shiru, sai kuma ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita, shegen kunya gareta kamar amaren zamaninsu Mama Ladi, Eeman na kallon Mayraah tana murmushi tace "Aunty nasan me take gaya maki" Mayraah ta kalleta tace "Ba dai ruwanki" Dariya Zainab tayi tana kallon Eeman.... Har Mayraah ta fara bacci Zainab ta tasheta jin wayarta na ta vibrating a jaka, Mayraah ta mike zaune da kyar ta bude jakar ta ciro wayar tana kallon Screen din, ganin Maheer ne ta daga ta kai kunne daga daya bangaren yace "Baki kusa da wayar ne baby gal?" Mayraah tace "Are you back?" Yace "Yeah ina kofar gida ku fito mu tafi" Mayraah tayi kasa da murya tace "Ka shigo kaga baby mana" Yace "Ai na ma Dr Khalil barka ta waya Mimi, kawai ku fito mu tafi it's late" Tace "Ohk" Katse wayar tayi ta mayar jikin jaka, Zainab tace "Kar dai tafiya za ku yi?" Mayraah ta kalli agogon dake dakin tana ɗan murmushi tace "Ai mun dade Mom twins" Har parlor Zainab ta rako Mayraah da Eeman, da kyar Mayraah ke tafi don duk jikinta is so weak, ganin babu kowa a parlon sai cousin sis din Zainab ta ji dadin hakan a ranta, a haka suka yi sallama Hafsat nayi mata fatan samun lafiya, Mayraah tace "Ina Ihsaan din?" Hafsat tace "Ina jin tana waje" Mayraah tace "Dr ya fita ne" Hafsat tace "Yes, he left with the other Dr not too long" Mayraah ta gyada mata kai tayi mata sai da safe ta fita daga parlon, Eeman dake rike da handbag dinta tana biye da ita a baya. A bayan motar Maheer suka tadda Ihsaan, Eeman ta shiga bayan motar, Mayraah dai bata ce mata komai ba duk da tayi mamakin ganinta amma maganar taji wahala yake mata, ta shiga front seat tana kallon Maheer yayi reverse suka bar layin. Har suka isa gida Mayraah bacci take, tun a hanya Maheer ke juyawa ya kalleta lkci lkci don it's so unusual of her, har dai suka iso gida, Su Eeman suka sauka bude motar suka sauka bayan Maheer ya mika ma Ihsaan makullin kofar parlor, suna kulle motar suka nufi entrance din gidan a tare, Maheer ya sauko daga driver seat ya zagayo ya bude door din inda Mayraah take ya dafa Forehead dinta a hankali yace "Wife..." Ta bude ido da sauri, sai kuma ta gyara zama tana kalle kalle tace "Yaushe muka iso gida" Yace "Kina ta bacci a hanya" Tayi murmushi, a hankali tace "I am so exhausted dear" Yace "Wani aiki kika yi yau har kika zama exhausted Baby?" Bata ce masa komai ba ta sauko daga cikin motar, ji tayi wani jiri ya debeta, Maheer yayi saurin rikota yana kallonta yace "Are you okay?" Kasa cewa komai tayi, ya rungumota jikinsa yace "Your body is warm" Da kyar tace "Na gaji ne, i need to rest" Maheer wish su kadai ne a gidan da kawai daukar abarsa zai yi ya tafi cikin gida da ita, ya dafa shoulder dinta making her rest on him suka nufi entrance din gidan yana kallonta har suka isa parlor, basu tadda su Ihsaan a parlon ba haka ya sa ta dauketa ta zaro ido murya can kasa tace "Meye haka yaya, we are not alone fa" Bai saurareta ba ya nufi Masters Bedroom da ita, ya direta saman gado ta mike ya kara hasken dakin sannan ya dawo kan gadon ya zauna yana kallonta, lumshe ido tayi tace "Bacci zan yi" Shi dai bai ce komai ba, after some minutes ya kai hannunsa goshinta, firgit ta bude ido wai har ta fara bacci, ya sakar mata murmushi kamar bazai ce komai ba sai kuma yace "Me za ki ci?" Ta girgiza masa kai da sauri tace "I am full" Yana shafa cikinta yace "No dear, ko in kawo maki apple din ki?" Ta gyada masa kai, yace "Right away baby gal" Hijab dinta ya fara kokarin cire mata yana cewa "Cire hijab din so that you will be comfortable" Da sauri ta rike tace "Noo, ina jin sanyi" Yace "Ga duvet baby" Ta girgiza masa kai tace "Na fi son hijab din ni dai" Yace "Ohk my love" Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin ya tafi kitchen, Bayan ya gama wanke mata apples din ya ajiye bowl din kan center table, ya tafi dakin da su Eeman suke yayi knocking, Eeman ce ta bude kofar yace "Kun ci abinci kuwa?" Eeman tace "Eh mun ci yaya" Maheer yace "Ohk then, sai da safe" Juyawa yayi ya bar wajen Eeman ta kulle kofar, bangaren da Mayraah take ya tafi bayan ya dau mata apples din, ajiye bowl din yayi kan beside drawer yana kallonta ganin yanda ta takure waje daya alamar tana jin sanyi amma taki lulluba da duvet din, jawo duvet din yayi trying to cover her with it ta bude ido da sauri yace "You are shivering baby" Bata ce komai ba ya lullubeta da duvet din yace "Ga apple din na kawo maki" Ta girgiza masa kai tace "Sai gobe zan ci" Bai ce mata komai ba ta lumshe ido, ya fi minti goma zaune gefen gadon yana kallonta, daga karshe ya mike ya maida apples din kitchen ya dawo shiga wanka, bayan ya fito ya saka Pajamas dinsa ya kashe wutan dakin ya kwanta a gefenta, har ya fara bacci wajen karfe daya yaji tana tashinsa, mikewa zaune yayi ya kunna wuta yana kallonta yace "You need something dear?" A hankali tace "Ina son zan ci apple din" Yace "Ohk My love" Sauka yayi daga kan gadon ya fita daga dakin, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo da bowl din apples da ya wanke, ya karaso kusa da ita ya zauna ta dau apple daya ya ajiye sauran kan beside drawer, ta jinginar da kanta kan shoulders dinsa ta fara cin apple din a hankali, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawan kirki bai yi, ko rabin apple din bata ci ba ta mika masa, ya karba yace "Ya isheki ne?" Kasa ce masa komai tayi, ya dinga kallonta yace "You want to throw up?" Da sauri ta gyada masa kai, ya dagata suka tafi bandaki, sosai Maheer ya tausaya mata bayan tayi aman, ya wanke mata fuska ya dawo dakin da ita yana kallonta, she was so weak and worn out, kuka take yi a hankali ya rungumeta jikinsa yana patting bayanta slowly, after a while ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Shi ne kika ki jira mu je Honeymoon din da nace za mu je wife?" Mayraah ta daga idanunta ta kallesa, murmushi ya sakar mata, ta sauke idonta bata ce masa komai ba, a haka bacci ya dauke. Washegari tun da sassafe Ammi ta dinga kiran Maheer a maido mata da su Eeman gida, yana son ce mata Mayraah bata da lafiya ko za ta barsu su ɗan kwana biyu amma ya kasa ce mata hakan, daga karshe babu yanda ya iya haka ya sa yan biyun su shirya Mayraah na bacci ya tafi dropping dinsu a gida, tun daga wannan rana Mayraah tayi sallama da lafiya, she gradually became so sick, babu abinda take iya ci, ko ruwa ne ta sha sai amai, gaba daya taji duniyar ta mata zafi tsabar yanda take jin jiki, hatta Maheer din bata son gani a kusa da ita, lkci daya duk ta rame ta fita hayyacinta, gashi shi dai Maheer har sannan bai fada ma su Ammi bata da lafiya ba, duk sanda suka yi waya in ta tambayi Mayraah sai yace tana nan lafiya, 3 hours kawai yake yi a hospital ya dawo gida saboda ita, ranan wani friday yana zaune parlor kiran Mama Ladi ya shigo wayar sa, ya daga ya gaisheta, ko amsawa bata yi ba tace "Yanzu dai abinda kai da matarka Mera ke nufi da mu na kira in ji, Yau sati nawa rabonku da gidan nan, ko dai kun bar garin ne bamu sani ba, sannan ga bikin marayun yaran nan ana ta shirye shirye ku ko a jikinku, ko don kaga uwarka na kawaici ka zata hakan na mata dadi ne, in ita Meran bata da hankali kai ma hankalin ka rasa ne? yara biyu duk ku fita harkar uwarku ko ɗar baku ji a ranku ba, to wallahi ku ji tsoron Allah, yau sati nawa rabon ita Meran ta kirata ta gaisheta sai dai kai ka kira, ni dai nace wllhi bazan yi shiru ba sai na amayar da abinda ke rai na, wannan ai walakanci ne, ko dai barin Habujan ku ka yi bamu sani ba" Maheer dake ta sauraron Mama Ladi, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "Mama Mayraah bata da lafiya ne fa" Mama Ladi tace "Innalillahi, Bata da lafiya kuma? Tun yaushe?" A hankali yace "Tun su Eeman na nan" Mama Ladi ta rafka salati ta katse wayar ta tafi dakin Ammi tace "Kin ji wai Mera bata da lafiya yau kusan sati hudu, da ban kira na masa soso da sabulu ba dama bazai gaya mana" Ammi da ta juya tana kallon Mama Ladi tace "Bata da lafiya? me ya sameta" Mama Ladi ta zauna kan kujera cikin jimami tace "Ni dai fargabana Allah ya sa ba guban da taci bane ya fara mata illa tunda har anyi shekara daya yanzu, to in ba guban ba wani rashin lafiyar arziki ne yau har sati hudu gantalallen yayi shiru yaki gaya mana?" Ammi ta dau wayarta ta

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login