Showing 264001 words to 267000 words out of 456519 words
sir" Dr Balogun ya juya ya koma IC unit din ya shiga, MD na tsaye gaban Breathing machine din yana kallonsa monitoring each and every alarm it's making baya ko kiftawa as if his own life depends on that too, bai taɓa ba Machine din nan Value irin yau ba a kaf shekarunsa na aikin likitanci, juyawa yayi yana kallon Dr Balogun da ya shigo ICU din, Dr Balogun ya karasa gun sa da ladabi yace "Sir, dama akwai wani yayanta ne ke son a bashi izinin shigowa ya ganta, he is also a Medical Doctor a nan Abuja, a Surgeon" MD dake ta kallon Balogun ya dauke kai kawai don shi ko magana ma baya so, sai ga Dr Khalil ya shigo Unit din shi ma ya nufo MD, ya ɗan sauke nosemask dinsa yace "Sir, akwai yayanta shi ma likita ne, pls in ka bada Permission zai shigo ya ganta ya fita immediately...." Juyawa Dr Balogun yayi ya fita, a hankali MD yace "Meye amfanin shigowan Khalil? As u can see ba wani improvement for now, i think it's not necessary..." Yana fadin haka ya koma ya zauna don wani mugun ciwo kansa yake, Dr Khalil yayi kasa da murya yace "But MD ko yaya ne a bar ko mutum daya a yan uwanta su shigo, barin shi da yake likita, saboda rashin barin mahaifiyarta ta shigo yasa tayi collapsing dazu a reception jininta ya hau yanzu haka she is being admitted also, Abbanta ma ba a bashi daman shigowa ba he is so disturbed, don't forget MD Mayraah is between life and death...." MD ya katse sa da sauri ya mike yace "I don't understand?" Dr Khalil ya kwantar da murya da damuwa yace "We shouldn't deceive our self sir, But that is the reality don haka ka bar yayanta ya shigo since he is also our Colleague, bamu san me zai faru ba" Bai jira cewar MD da ya bi sa da kallo zuciyarsa na bugawa ba har ya fita, MD ya juya da sauri ya kalli Ventilator machine din da yayi making wani alarm, ya karasa kusa da Mayraah that is attached to medical devices and tubing ya duka da sauri, Gown Dr Khalil ya ba Maheer da nose mask with gloves sai takalman da zai shiga ciki da su, tun da ya shigo MD ke kallonsa, Maheer na tafiya a hankali ya karasa gun Mayraah ya kamo hannunta ya duka with breaky voice yace "Mimi, pls wake up Mimi...." MD dai kallonsa kawai yake, Maheer ya hade kansa da gadon yana rike da hannunta gam, MD could see the tears coming down from his eyes, sunkuyar da kai shi ma yayi, Kusan a tare MD da Maheer suka dago kai as a result of alarm din da machine din yayi, Maheer ya mike tsaye da sauri looking at the machine zuciyarsa na bugawa yace "Her pressure is dropping" Bayan sun yi kokarin saita BP din nata by administering her with vasopressin, MD ya kalli Maheer zai yi magana sai ga Ceo ta shigo ICU din, karara zaka ga tashin hankalin dake fuskarta direct ta nufi inda Mayraah take, Wani Dr Ba indiye da bature suka shigo ICU din su ma with another Dr duk suka yi kan Mayraah, Maheer ya sauke idonsa kasa a hankali ya juya ya fita daga IC unit din. Maheer na isa reception din asibitin sai ga Usman ya shigo da Aunty Mariya sai Hajja dake biye da su a baya, Aunty Mariya ta fashe da matsanancin kuka ta nufi Maheer da sauri ta kamo hannunsa tace "Maheer ta farfado ko tana ICU din har yanzu?" Maheer ya kasa ce mata komai, hakan yasa Hajja ma ta fashe da kuka, Usman ya nemi kujera a reception din ya zauna ya dafe kansa, juyawa Maheer yayi walking slowly ya tafi can far end of the reception ya zauna ya jinginar da kansa ya runtse ido zuciyarsa na bugawa da karfi, he just can't imagine loosing Mimi, kuka Aunty Mariya take kamar ranta zai fita Hajja na taya ta, bayan wani lokaci Hajja ta mike tana share idonta ta nufi Maheer tace "Ina Ammin take?" Maheer ya sauke idonsa yace "An kwantar da ita, ta samu bacci" Hajja ta zauna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ga mu gare ka, Allah ka tashi kafadun wannan baiwar taka" Suna ta zaune a reception din for almost 3 hours babu me cewa kowa komai, kowa kuma da tunanin dake ransa, Maheer ya ciro wayarsa dake ta vibrate tun dazu ya ki duba me kiran, don duk hankalinsa na kan wanda zai ga ya fito daga hanyar ICU amma shiru shiru har yanzu daga Ceo din har likitocin da suka zo, kallon screen din wayar yayi yaga number Mama Ladi, ya daga ya kai kunne yayi shiru, daga daya bangaren cikin daga murya Mama Ladi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Maheer ga ni a garin Habuja tun dazu ban san inda zan je ba ina ta yawo a tasha" a hankali Maheer yace "Ki nemi me adaidaita sahu sai in gaya masa asibitin" Da sauri Mama Ladi tace "Tohh to" Katse wayar yayi ya ajiye gefensa ya dafe kansa, ba a dau lokaci ba sai ga kiran Mama Ladi Maheer ya gaya ma mai adaidaita sahun asibiti wanda sananne ne sosai, sannan ya katse wayar ya mayar aljihunsa ya mike tsaye, ya tafi can bakin ICU din ya zauna yana kallon kofar... Wani likita ne a ICU yayi saurin riko MD da yayi baya zai fadi, duk sauran likitocin suka juya kallonsa, Ceo tace "Ka je ka huta Aliyu, get some rest, by the grace of God we have hope" Da sauri yace "No Ma'am i am fine...." Dr Hamid ya dafa sa yace "You need rest MD, kuma baka samu ka ci komai ba and this is pass 12...." Bai jira cewarsa ba ya kama hannunsa za su fita daga ICU din MD da kansa ke juya masa bin sa kawai yake, sai da suka isa kofa ya sake juyawa ya kalli Mayraah da Toxicologist din ke bakin kokarinsu a kanta, suna fitowa daga Unit din Maheer ya mike da sauri yana kallonsu.
[8/18, 7:42 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya dau wayarsa dake ta vibrate ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren Mama Ladi tace "Na shiga uku Mashir gani gaban asibitin cikin rana tun dazu, anya za su bari in shiga kuwa? naga masu gadin wasu gaddawa ba fara'a ba annurin musulunci a tattare da su, ko dai ba asibitin bane ɗan sahun ya ajiye ni" A hankali yace "Ki shigo za su bar ki" Mama Ladi ta zuge karamin Ghana must go dinta ta jefa wayar ciki sannan ta dau abunta ta rataya a kafada, bata sake kallon masu gadin ba ta nufi karamin gate zata shiga security din yace "Mama yau ba ranan kawo ziyara bane, sai gobe da yamma...." Mama Ladi ta tsaya tana kallonsa baki bude, can ta fashe da kuka tace "Dama asibiti wajen ziyara ne? daga karaye fa nake an ba jikata guba ta ci a abinci, in kawo ziyara asibiti sai kace wajen yawon bude ido in ba kaddara ba ma me zai kawo ni nan, tun karfe biyar fa na fito gida daga karaye" Komawa yayi ya zauna bai sake ce mata komai ba kuma bai bude gate ba, Mama Ladi ta ajiye Ghana must go dinta tace "Ikon Allah, To asibitin yan iska aka kawo Meran dama? Wallahi idan har ran jikata yayi halinsa bamu gana ba bazan yafe maka ba har karshen duniya" Ganin Security din bai sake kallon direction dinta ba kuma ya kulle gate, ta ciro wayarta ta sake kiran Maheer, bai daga ba kawai ya mike ya fita waje, after persuading the securities suka bar Mama Ladi ta shiga da Ghana must go dinta tana hararansu tace "Kattin banza kawai, ko me asibitin dai bazai ce kar in shiga ba balle ku masu gadi" Mama Ladi ta kalli Maheer cikin tashin hankali tace "Mashir garin yaya haka ya faru? Me ya kai guba sabon gidan har aka ci ni Ladiyo?" Shi dai bai ce mata komai ba yana tafiya yaje parking space ya bude mata Booth ta saka Ghana must go dinta suka shiga cikin asibitin, zaunawa tayi gefen Hajja ta rike kai ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, mu kuma da bala'in da muka wayi gari da shi kenan a pamily yau, duk wata fitina da tashin hankali da abun kunya a pamilyn mu yake karewa, anya ba lefi muka tafka ma ubangijinmu bamu sani ba kuwa? Daga wannan sai wannan kamar masu shan jinin mutane, To ni dai na yanke shawaran yin azumin kwana uku in nema ma Pamilyn nan namu gafara ko za mu dinga ganin dai dai, don gaskiya ban yarda da wannan iftila'in dake fado mana ba kullum, to ita kuma ina taje ta samu guba ta ci kamar dai ana yunwa a sabon gidan, mu fa zamaninmu dabbobi ne ke cin guba garin ciye ciyensu a titi" Daga Aunty Mariya har Hajja babu wanda ya kalli Mama Ladi, Usman ya mike ya bar wajen gaba daya, Maheer dama ya tafi can gaban ICU ya zauna, Mama Ladi tace "Ai shikenan" Dr Khalil na tsaye office din MD dake zaune after taking his bath yana juya rabin cup din shayin gabansa da teaspoon, Dr Khalil na kallonsa yace "Idan ka sha shayin sai in maka allura don ka warware daga stress din nan so it won't weigh you down" MD yace "No, just pain reliever" Juyawa Dr Khalil yayi ya bar gaban table din yace "Injection zai fi sir" Fita yayi daga office din ba a dau lokaci ba ya dawo rike da allura bayan ya hada masa har da na bacci amma dosage ba me yawa ba, bai yarda MD ya lura da kalan alluran ba yayi masa sannan ya fita daga office din. Da yamma Ceo na tsaye tare da Abba da Usman a bakin ICU with 3 Doctors dake bayanta, bayan ta gama yi ma Abba bayani a takaice a kan yanda suke bakin kokarin su, ta kuma kwantar masa da hankali giving him assurance, Abba da ko kadan yaji bai gamsu da bayaninta ba yace "I just want to know if she is responding, is there any improvement? shine kawai damuwata yanzu" Ceo ta sauke idonta tace "She will respond, sure she will, and they will be improvement soon... She is still being monitored for now" Daga haka ta juya zata bar wajen Abba yace "Ina son shiga in ganta, i want to see my daughter" Ceo ta juya ta kallesa tace "Ka bari idan Allah ya kai mu gobe sir, kaga ko 24 hours bai cika ba da kawo ta ai..." Shiru Abba yayi yana kallonta tashin hankali karara a fuskarsa, tuni ta bar wajen likitocin suka bi bayanta, Usman ya zauna a kujeran wajen looking so disordered, Abba na kallonsa yace "Pls Barrister ka kai su Mariya gida, sun yi yawa a asibitin and the staffs are complaining tunda ba visiting day bane" Usman na kallon Abba a hankali yace "But Abba why not a fita da ita waje? Won't that be better?" Abba yace "Haka nima na so, amma kaga ceo din tasu ai daga waje ta zo da wasu likitocin...." Usman ya jinginar da kansa da bango ya rufe ido.... Maheer na zaune ward din da aka kwantar da Ammi, holding on to her hands yace "Ko minti sha biyar ban yi da fitowa daga can ba Ammi, she is getting better pls ki kwantar da hankalin ki" Ammi ta goge hawayen idonta tace "Toh ni me yasa baza su bar ni in shiga in ganta ba?" Maheer ya kwantar da murya yace "Drip ne fa a hannunki Ammi" Ammi tace "To a cire min mana idan na dawo sai a mayar" Maheer yace "Jininki bai sauka ba har yanzu, ki bari idan ruwan ya kare za ki shiga ki ganta, i promise u she is getting better Ammi" Ammi dai kallonsa kawai take hawaye na sauka idonta, duk da shi ma mugun karfin hali yake mata pretending Mayraah is getting better, ya sauke idonsa yace "Bari in je in amso abinci a gida, Aunty Mariya ta gama" Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga ward din, bayan ya kulle kofar ya jingina da bango ya rufe ido, bayan kusan minti biyu ya bar wajen yana tafiya a hankali, ICU ya koma kamar yanda yace ma Ammi 20 mins ago he was allowed inside amma still no progression as at then, Usman na zaune gaban IC unit din, Maheer ya zauna gefensa yana kallonsa yace "Ka shiga?" Usman ya ta gyada masa kai, shiru Maheer yayi bai sake cewa komai ba, bayan kusan minti goma Dr Khalil ya fito daga Unit din, yana kallonsu calmly yace "In sha Allah muna sa ran za a samu advancement nan ba da dadewa ba, her system is gradually trying to respond" Maheer ya mike da sauri yace "Did she make any movement Dr?" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Not yet, but muna sa rai" Maheer yace "Pls can i go in?" Dr Khalil ya dan masa murmushi yace "Ceo dinmu tana ciki ka bari sai ta fita" Maheer ya koma a hankali ya zauna yace "Ohk nagode" Juyawa Dr Khalil yayi ya bar wajen, dai dai second floor ya hadu da MD that was coming down the stairs as if counting each and every step he is making, he was walking very slowly, tun da Dr Khalil yayi masa allura sai yanzu karfe shidda saura ya tashi, yana ganin Dr Khalil ya tsaya, amma sai ya kasa ce masa komai as if he was expecting a news that might ruin him in seconds, kallon Dr Khalil kawai yake babu kiftawa, Dr Khalil ya nufesa yace "How are you feeling Sir?" Wani boyayyen ajiyar zuciya ya sauke, Dr Khalil ya kai hannu forehead dinsa wanting to feel his temperature, MD ya kauda kansa yana masa wani kallo yace "Na ce maka ka min alluran bacci Khalil? Me yasa zaka min alluran bacci?" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai da kayi baccin yanzu baka samu relieve ba Sir?" MD bai ce masa komai ba ya ci gaba da tafiyarsa zai sauka downstairs, Dr Khalil ya bi sa da kallo yana murmushi don yasan in da zai je, da sauri MD ya juyo, Dr Khalil yayi keeping straight face yana kallonsa, MD ya dawo sai kuma ya fasa masa tambayar da zai masa kawai ya juya ya sauka kasa, Dr Khalil ya san tambayarsa zai yi ko akwai progression but probably bai son ya ji otherwise shi yasa ya gwammace ya je da kansa, MD na sauka downstairs ya nufi ICU ba tare da ya ma san Nurses dake reception suna gaishesa ba balle ya amsa, Maheer ne kadai zaune gaban ICU din idonsa a lumshe, Usman ya tafi gida dauko ma Ammi abinci don Maheer yace masa bazai iya driving din ba, MD ya wuce sa ya shiga cikin Unit din, Wata registered nurse ce kadai zaune at the far end of the Unit tana monitoring Machines din, Tana ganin MD ta mike ta gaishesa da ladabi, shi dai idonsa na kan Mayraah baya ko kiftawa, nurse din ta koma ta zauna, bayan few seconds ya juya ya kalleta yace "You can leave" Mikewa tayi tace "Ohk sir" Daga haka ta fita daga Unit din, walking slowly ya karasa kusa da gadon.... Dukawa yayi looking at her face ya kamo hannunta a hankali giving it a gentle Massage, murya can kasa yace "Mayraah... Can you hear me? I know u can...." Though he wasn't expecting an answer, amma haka ya ci gaba da kiran sunanta in a very low voice without stopping, Kamar me rada yace "Hello! sleeping Beau..." Sai kuma yayi shiru bai karasa ba ya sauke idonsa daga kallonta yana ci gaba da murza palm dinta gently, bayan minti biyar ya daga idanuwansa ya kalleta, a hankali yaga ta juya kai, ya mike tsaye da sauri yana kallonta, sake kiran sunanta yayi this time around bata yi making any movement ba, within few seconds yayi placing mata pulse oximeter probe a finger da sauri yana kallon Machine din, dai dai nan Ceo ta shigo Unit din, Ya mike tsaye yana kallonta, Ceo ta karaso kusa da gadon tana kallon Mayraah tace "Akwai advancement Aliyu?" MD ya gyada kai da sauri yace "She just moved her head now, shine nake duba oxygen saturation level...." Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Glory be to God, this is what we've been waiting for, ka je office dina ka sanar ma Dr George...." MD yace "Ohk Ma'am" Juyawa yayi da sauri ya fita daga Unit din, Ceo ta dinga kallon Mayraah babu ko kiftawa, bayan few seconds ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta kalli kofar ICU din sannan ta karasa kusa da ita ta kamo hannunta a hankali tace "Mary Ann, can you hear me?" Pecking hannunta dake ta kamshin turaren MD tayi tace "Quickest recovery dear" MD na fitowa Unit din Maheer ya mike yana kallonsa yace "Doctor is there any progress now? Zuwa yanzu ya kamata a samu wani progress" MD na kallonsa yace "Sure there is, in sha Allah" Daga haka ya bar wajen Maheer ya bi sa da kallo. Ceo na tsaye kan Mayraah har MD ya dawo tare da Dr George, sannan ta juya ta fita daga Unit din. Bayan isha Dr George yayi decreasing degree na ventilator support din so as she won't be depending fully on the machine, MD da Dr Khalil dai na tsaye suna kallon baturen, har ya gama ya fita after checking her for the last time, Dr Khalil ya kalli MD yace "Kai baka jin yunwa ne tun jiya bawan Allah?" MD ya shafa kansa a hankali yace "I took tea da safe ko ka manta" Bai jira cewar Dr