Showing 261001 words to 264000 words out of 456519 words
mutu?" Bilkisu bata tsaya bata amsa ba ta shiga cikin gida da sauri don dauko ma Ammi takalmanta da Hijab ganin har ta fita gate, dama kuma har ta haddace sunan asibitin da ta gani jikin Ambulance din. Maheer na zaune babban reception din asibitin ya dafe kansa da yayi masa nauyi, lokaci lokaci yake dagowa ya kalli Ammi dake reception din ita ma tare da Bilkisu dake ta kokarin kwantar mata da hankali take bata hakuri amma kamar tana kara tunzurata don Ammi tayi kuka har taji ba dadi, gaba daya ta dawo bata da wani kuzari, sun kusa awa biyu reception din a zaune amma babu likitan da suka ga ya fito har sannan, wannan ya kara daga ma Ammi hankali sosai ba kadan ba, wajen karfe sha biyu da rabi Dr Hamid ya fara fitowa, Maheer ya mike da sauri yana kallonsa don yayi recognizing dinsa as one of the doctors that went inside the emergency room with Mayraah, karasawa yayi gun sa, Ammi ma ta mike da sauri ta nufesa gabanta na mugun faduwa, Dr Hamid na kallon Maheer yace "She is been transferred to ICU...." Yana fadin haka ya bar wajen, Maheer ya bi sa da kallo, Ammi ta fashe da matsanancin kuka ta riko Maheer tace "Maheer me hakan ke nufi? ICU naji fa yace" Maheer yayi kokarin calmly dinta yace "Dama za a kai ta can ai, saboda pulse dinta da ya dauke na wani lokaci, in sha Allah she will be fine Ammi" Karfin hali kawai shi ma yake yana kokarin kwantar mata da nata hankalin. Karfe biyu saura na dare Dr Khalil ya shigo reception din daga ICU, Ammi ta mike da sauri tana goge hawayen idonta ta nufesa don taga kamar kusan duk likitocin asibitin sai da suka shiga Emergency room din, muryarta na rawa ta kamo hannunsa tace "Plss tell me how is my daughter? Kar ka boye min komai don girman Allah ka gaya min Dr, just tell me plss, is she alive?" Hawaye na sauka idonta tayi masa tambayar, Maheer da ya mike tsaye shi ma sai kallon Dr Khalil yake ganin expression din fuskarsa, Dr Khalil yayi kasa da murya amma hakan bai boye damuwarsa ba yace "Zata samu lafiya in sha Allah Mama, ki kwantar da hankalin ki" Dr Khalil ya Kalli Maheer da ya nufosa yace "Dr Maheer?" Maheer ya masa nodding, Dr Khalil yace "Mu je office Dr" Ammi ta fashe da wani sabon kuka ta rikosa tace "Ni ma zaka iya gaya min koma menene Dr, mu tafi office din" Tana fadin haka ta fara tafiya kamar tasan office din nasa, Dr Khalil ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya kalli Maheer dake tsaye gabansa yace "How comes Maheer? Waye yayi mata haka?" Damuwa karara a fuskarsa yayi tambayar, Maheer yayi kasa da murya yace "Wani irin poison ne pls? And how is she? Is she responding? can i see her? Plss?" Zuciyar Maheer na bugawa yayi request din, Dr Khalil ya zauna kan kujera cause he was exhausted ya rike kansa, Maheer ya zauna kusa da shi don gaba daya hankalinsa ya gama tashi, Ammi kuwa tayi gaba ba tare da ta waigo ta ga ko Dr Khalil din na biye da ita ba, Dr Khalil yace "Don Allah garin yaya wannan abu ya faru? Su waye da waye a gidan? Ko taje wani waje ne aka bata abincin?" Maheer yace "Yanzu baza a min alfarma in shiga in ganta ba?" Dr Khalil yace "She is in a critical condition now, we've tried our best, her body is failing, she is on life support" Maheer yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Dr Khalil bai iya ya dago kansa ba har bayan kusan minti daya, a hankali yace "We are trying our very best, akwai manyan likitoci biyu ma from another hospital da suka zo" Yana fadin haka ya mike ya bar wajen Maheer ya bi sa da kallo. Maheer bai taɓa shiga kalan tashin hankalin da ya shiga a lokacin ba, he felt like the world is coming to an end, ji yake kamar komai ya tsaya masa cak a duniyar, he wish mafarki yake, he wish shi ne ya ci abincin nan ba Mimi ba, yasan don shi aka yi poisoning abincin not Mimi, fita yayi daga reception din yana ganin building din na juya masa a kai ya jingina jikin bangon asibitin ya runtse ido zuciyarsa na bugawa da karfi, lokaci daya ya bude ido ya nufi outside of the hospital. Wajen karfe hudu Dr Khalil ya shiga ICU for the countless time, tun karfe uku likitocin ciki suka fita MD kadai ya rage a ciki, Dr Khalil na kallonsa don tun dazu yake tsaye a position din da yake, Dr Khalil ya karasa yayi kasa da murya yace "Kana bukatan ka huta MD, I will stay, go get some rest...." MD dai kallonsa kawai yake bai ce komai ba, Dr Khalil could see how confused and disappointed he is, ya juya a hankali yana kallon Mayraah dake kwance on life support feeling so heartbroken, Sunkuyar da kai MD yayi a hankali yace "I wish we could do more than this, i wish..." Sai kuma yayi shiru, Dr Khalil yace "It's not our fault MD, we tried our best, kawai mu ci gaba da addu'a ba mu cire hope ba in sha Allah" Zaunawa MD yayi ya jinginar da kansa jikin wajen ya rufe ido. Karfe hudu na asuba Abba ya shigo asibitin hankali tashe after driving all the way from kano. Kallonsa kawai Ammi dake zaune reception take yi hawaye na sauka idonta, yanda taga rana haka taga daren nan tare da Bilkisu dake gefenta, Abba ya karasa hankali tashe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ina likitocin suke.. where is the Drs office, suyi transferring dinmu outside of the country kawai" Kuka kawai Ammi take kamar ranta zai fita ta kasa cewa komai, Abba ya nufi Nurse dake zaune reception din da sauri yace "I want to speak with any of the doctor in here pls" Nurse din ta zagayo tace "Ohk sir" Office din Dr Khalil ta tafi don ko minti biyu ba ayi ba ya tafi sama bayan ya fito ICU. Bayan Dr Khalil yaji bukatan Abba yayi kasa da murya yace "Sir our hospital is among the best here in Nigeria, kwararrun likitoci gare mu a nan, ko an fita da ita iyakar abinda muke yi a nan din za ayi mata, likitoci turawa biyu where among us today, so kawai addu'a za mu mata Allah ya tashi kafadunta, in sha Allah she will be fine...." Cikin rashin gamsuwa Abba yace "Na fi gane kuyi referring dinmu any best hospital in the world za mu je plss, ku min haka" Shiru Dr Khalil yayi yana kallonsa. ICU Dr Khalil ya samu MD ya sanar masa abinda Abba ke cewa, MD dake ta kallonsa yace "Ceo tana hanya with 2 Dr's"
[8/17, 11:14 AM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mikewa MD yayi ya jingina da bango yana kallon Dr Khalil dake kallonsa, Calmly yace "She is on her way with Medical Toxicologists, try convincing them" Dr Khalil dai yayi shiru yana kallonsa ganin yanda duk ya fara fita hayyacinsa, maganar ma kamar yana forcing kansa ne yake yi, Dr Khalil ya kwantar da murya yace "MD ka je ka huta, i will remain here...m" MD ya koma ya zauna yace "Pls kayi ma Abban nata bayanin da nayi maka yanzu..." After some seconds Dr Khalil ya juya ya fita, mikewa MD yayi yana kallon Mayraah that is on Medical Ventilator, walking slowly ya isa kusa da ita ya duka ya kamo hannunta yana kallonta a hankali yace "I know you are strong, and u are gonna make it in sha Allah, you have many years and a bright future ahead, come back pls" gently yake murza fingers dinta yana kallonta, yayi hakan for almost 5 minutes sai kuma ya daura kansa saman gadon ya lumshe ido. Maheer na isa gida, Haseenah dake kwance dakinta har ta fara bacci amma jin an bude kofa ta farka tana kallon agogo taga karfe hudu da yan mintuna, sauka tayi daga kan gadon ta fito dakin da sauri, a corridor ta hadu da shi zai shiga nasa dakin, da damuwa tace "Wai me ke faruwa ne Maheer? Bilkisu tace min Mayraah ba lafiya an tafi asibiti, kuma kafin inje dauko hijab har sun wuce ita da Ammi basu jirani ba, yanzu ya jikin nata?" Maheer da ya bude kofar dakinsa yace "Da sauki" Daga haka ya shiga dakin ya kulle kofar, Haseenah sai da taji kanta ya wani sara jin yace da sauki, wato da sauki?? ita da take ta jiran a dawo da gawan Mayraah ana koke koke, meye kuma da sauki? nan da nan taji ranta ya wani baci, shkkn wannan poison din da ta samu da kyar da siddin goshi ya tashi a banza a iska kenan, tun a kano take adana poison din nan ta rasa ta yanda zata saka masa a abinci tunda ba cin abinci yake a inda take ba sai can wajensu Ammi, ko shayi baya sha a Chalet shi yasa har suka taho Abuja bata samu daman aiwatar da nufinta a kansa ba, rai bace ta koma dakinta ta zauna gefen gado tayi tagumi, amma matsiyaciya ce yarinyar nan duk ta ɓata mata aiki don ba don ita ta saka poison a abincin ba gashi ta ci kuma ance jiki da sauki, Maheer ya sa ma kofar dakinsa makulli ya dauko laptop dinsa da sauri ya fara danne danne zuciyarsa na bugawa, cikin mintuna kadan ya shiga software din CCtv system din parlor da yayi installing a Laptop dinsa, cikin mintuna kadan yayi fast fowarding har zuwa time frame da yake so, ya dinga kallon footage din a laptop din babu ko kiftawa wasu zufa na keto masa a goshi duk da AC dake kunne a dakin, zaunawa yayi gefen gado ya kama kansa da yayi masa nauyi, a ransa ya dinga furta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da kyar ya iya mikewa daga karshe yana ganin wani jiri ya kashe laptop din ya dau makullin motarsa ya fita daga dakin yana rike da laptop din nasa, Haseenah na jin ya bude kofar dakinsa ya fito ta sake tashi ta fito daga nata dakin da sauri, bai yarda ya kalleta ba ta bi sa a baya da damuwa tana cewa "Don Allah in sa Hijab mu je asibitin Maheer?" Ba tare da ya juya ba yayi calming kansa ya dake yace "Aa, gobe za a sallameta in sha Allah" Haseenah ta kasa cewa komai ga dinga kallonsa har ya nufi kofa, bata taɓa jin tayi aikin banza aikin hofi a rayuwarta ba irin yau, wato har za a sallamota daga asibitin, ko dai shaka kawai tayi bata ci poison din ba, har Maheer ya fita parlon bata ce masa komai ba tsabar bacin rai, can ta ja wani dogon tsakin takaici ta koma dakinta tayi banging kofar tana tunanin what step next, Maheer ya fi minti biyar cikin motarsa ya hade kansa da Steering yana sauke numfashi a hankali zuciyarsa na bugawa, he wish shi ne ya ci abincin nan ba Mimi ba, he can't imagine loosing Mimi a duniyar nan, da kyar ya composing kansa ya fita daga compound din, driving kawai yake as if he is learning don gaba daya hankalinsa baya jikinsa, ikon Allah kawai ya kai sa police station. Abba da ya dafe kansa ya kasa ce wa komai ga Dr Khalil dake ta kokarin convincing dinsa a kan barin Mayraah har Ceo dinsu ta iso, shi bai ki ya sadaukar da every of his wealth wajen ceton ran Mayraah ba, ya dago kansa ya jinginar da kujera, Dr Khalil could see how devastated he is, trying so hard to calm him duk da shi ma yana cikin damuwar nan don he can't imagine Mayraah giving up, ya kwantar da murya ce "In sha Allah da kwararrun Medical Toxicologist zata shigo kasar, kar ka manta Mayraah staff dinmu ce Alhaji, our Ceo will definitely do what ever it takes na ganin mun ceto rayuwarta idan Allah ya amince, Ceo dinmu na aiki a kasashe sun fi hudu as a medical expert a duniya, sannan tana daukan masu PHD da masters a jami'ar Uk" Abba na kokarin controlling kansa yace "Nan da awa nawa zata shigo kasar Dr?" Dr Khalil yace "Daga UK zuwa Nigeria awa shidda ne da rabi or so, muna sa ran nan da karfe takwas na safiya suna kasar nan in sha Allah, ai tun dazu suka taso" Abba ya mike yace "Ina son ganin daughter ta, a bar ni in ganta don Allah" Dr Khalil ya girgiza kai calmly yace "Kayi hakuri Alhaji, bazai yiwu ba a yanzu... Kayi hakuri" Dr Khalil na fadin haka ya juya ya bar wajen Abba ya bi sa da kallo looking so confused. Haseenah na kwance ta fara bacci bayan anyi sallan asuba ta bude ido jin an bude kofa a parlor, taɓe baki tayi ta gyara kwanciyarta don ko fita ma bazata yi ba, ji tayi an kwankwasa kofar dakinta, ta mike zaune cike da mamaki tana kallon kofar, to ko ce mata zai yi su tafi asibitin, ikon Allah wai Maheer ne ke mata knocking yau, yaushe rabo?? Sauka tayi daga kan gadon ta karasa bakin kofar ta bude, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin yan sanda hudu bakin kofar, ta wani gwalo ido tace "Lafiya? Daga ina haka? Wa ku ke nema?" Wani ɗan sanda ya ciro handcuff yana nuna mata yace "You are under arrest" A gigice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ban gane under arrest ba? Me aka yi? Ko dai batan hanya ku ka yi ba gidan nan zaku shigo ba? Matar aure ce fa, gidan mijina ne nan...." Makalewa maganganunta suka yi ganin Maheer dake tsaye yana kallonta cike da takaicin ranan farkon haduwarsa da Haseenah, Ta hadiye abu da kyar tace "Maheer lafiya? Me ke faruwa? Wa su ke nema haka?" Maheer na girgiza kai zuciyarsa na masa zafi yace "I regret the very first day i met you, nayi da na sanin haduwa dake a rayuwata har na aureki, marrying you was the worst mistake i made in this life, poison kuma kamata yayi ace wanda zan shaka kika nemo ba wanda zaki zuba a abinci har kanwata ta ci ba, ni kika yi niyyar kashewa, da cikin sauki wa enda suka baki wannan deadly poison din za su iya baki wanda zaki shaka min, Haseenah u will surely pay for this, all this while Ina zaune da ke ne ba don na yarda dake ba sai don yi ma mahaifiyata biyayya, sannan ita da ta saka in ci gaba da zama dake har zuwa wani lokaci ita ta bani shawaran saka Cctv a parlon nan to be watching ur movement don haka na sake ki saki biyu, there is nothing left between me and you again, i dissolve our marriage this very moment" Haseenah taji kafafuwanta sun kasa daukanta, wasu zufa suka dinga keto mata ta ko ina a jikinta tun da ta ji ya ambaci cctv camera, durkusawa tayi a kasa ba tare da tasan tayi hakan ba ta fashe fa wani matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" Tsawa ɗan sandan ya daka mata ta mike da sauri duk jikinta na rawa, ya saka mata handcuff din a hannu suka kadata zuwa cikin parlor tana rusa kuka, da sauri ta tafi gaban Maheer ta durkusa bakinta na rawa cikin kuka tace "Maheer kar ka manta ɗanka dake cikina...." Ko rufe baki bata yi ba ya hade fist dinsa ya sauke mata dai dai bakinta da duk strength dinsa lkci daya kuma ya wanka mata wani wawan mari da sai da ganinta da jinta ya dauke na wasu dakikai, hakan bai yi ba ya wani haureta da karfi da kafarsa, ji tayi kamar hakorinta ya fado kan harshenta, ta zaro ido ta tofar kasa taga aiko hakorin nata ne kuma na gaba ya cire tsabar kullin da ya kai mata a baki, tuni jini ya fara bulbulowa, wani ɗan sanda ya dafe Maheer trying to calm him down yace "Kar kayi laifi Yallabai... Ka riga ka damka ta ga hukuma, so this is not accepted...." Daga haka suka kada Haseenah da jini ke ta zuba a bakinta suka fitar da ita daga parlon tana rusa ihu tana kiran Maheer, Maheer ya duka nan parlon ya dafe kansa lokaci daya idanuwansa suka kada. Da safe sai da aka yi admitting Ammi a asibitin don collapsing tayi a reception jininta ya hau sosai, bayan an kara mata ruwa Dr Hamid yayi mata alluran bacci sannan ya bar Abba a ward din ya fita, Maheer dake zaune corridor din IC unit ya rike kai, tun dawowarsa asibitin yake wajen a zaune likitocin sun ki bari ya shiga, ya dago da sauri jin an bude kofa, mikewa yayi da sauri ganin Dr Balogun ya karasa gun sa duk da Dr Balogun bai tsaya ba balle ma ya kallesa haka ya dinga bin sa a baya yace "Pls Dr allow me to see her even if it's just for a minute, she is my sister, i am also a Medical Doctor...." Sai da ya fadi shi ma Medical Dr ne Dr Balogun dake tafiya ya juya ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yace "A Medical Doctor?" Da sauri Maheer ya ciro ID card dinsa ya nuna masa yace "Yeah i am also a Dr Sir, here is my Identity card and place of work" Dr Balogun ya amshi ID card din nasa, ganin asibitin da yake aiki da field dinsa as a Medical Doctor ya tsaya yana kallonsa yace "Ohh really" Mayar masa da ID din yayi yace "Alright Dr, let me talk to our MD, yana cikin ICU din... I pray he allows u in" Maheer yace "I will appreciate that plss