Showing 414001 words to 417000 words out of 456519 words

Chapter 139 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70642

ya tsare, da asuba in sha Allah zan taho nima" Maheer bai ce komai ba ya bi bayan Abba da Usman suka fita daga parlon, da ya tuna Ta'aziyyar yan biyu ya kawota Abujan sai yaji hankalinsa ya kara tashi, Ammi ma ta bi su har compound, tana tsaye compound din har suka fita gidan a motar Usman, sai a sannan ta juya ta koma cikin gidan, ta dade zaune parlor duk jikinta yayi la'asar, daga karshe ta mike ta wuce sama har sannan ledan maganin Mayraah na hannunta, dakinta ta nufa ta bude kofar a hankali ta shiga, kwance ta ganta ta rufe har kanta da duvet, Ammi ta zauna gefenta ta sauke duvet din daga fuskarta tana kallonta, a hankali Mayraah ta bude ido tana ganin Ammi ta rike duvet din don ba kaya jikinta, Da kyar ta mike zaune har sannan taki sakin Duvet din a hankali tace "Ammi" Ammi tace "Ga maganinki ki sha Mimi" Ammi na fadin haka ta fiddo magungunan a leda ta balla mata each and every one sannan ta mike mata a hannu, ta mike ta dauko ruwan goran da ta gani gaban mirror ta mika mata Mayraah ta amsa ruwan ta sha maganin gaba daya, Ammi na kallonta tace "Sannu" Komawa Mayraah tayi ta kwanta ta lumshe idonta, Ammi na ta zaune a dakin har ta lura ta koma bacci sannan ta mike ta kashe mata wutan dakin ta koma bangaren ta, har sha biyu Ammi ta kasa bacci, she was soo disturb, har a lkcn kuma bata gaya ma su Mama Ladi abinda ke faruwa ba suna can suna bacci da Aunty Mariya, lokaci lokaci Ammi ke kiran Maheer taji ko sun kusa, har daga karshe wajen karfe dayan dare yace mata sun isa kadunan amma basu karasa hospital din ba. ko da su Abba suka isa asibitin ba a bari sun shiga gun Hajiya Amina dake Emergency har a sannan ba saboda she was in a state of coma, haka suka yi ta zama a hospital din har asuba, karfe bakwai saura wani likita ya taho inda su Abba suke zaune yana kallon Abba yace "Kai ne mai gidan nata ko?" Abba yace "Haka ne" Likitan yace "Ohk ka sameni office" Abba ya bi sa har zuwa office dinsa, likitan na kallon Abba yace "The accident left her with a critical traumatic brain injury, no doubt a bugu sosai a kanta, apart from that ko kwarzane bata yi ba, so sai tayi regaining consciousness fully za mu ji ko da wani waje dake mata ciwo, wa enda aka kawosu tare ma duk sun rasu tun a daren jiya, hopefully za ayi mata CT scan yanzu don ganin state din da brain dinta ke ciki domin mu san next move da za mu dauka" Abba da duk jikinsa yayi sanyi yace "Amma ta farfado yanzu?" Likitan yace "Yeah, but not fully gaskiya, tana da yara ne?" Abba yace "Tana da" Likitan na gyada kai yace "Eeman??" Abba yace "Eh, she is our daughter" Likitan yace "Yauwa sunan yan mata biyu dai ta kira sai namiji, so na rike Eeman saboda sunan daughter na kenan, if possible a taho mata da yaran nata ko zuwa anjima, that might help too" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Amma zan iya shiga wajenta yanzu Doctor?" Likitan ya mike yace "Mu je, duk da dai yanzu za a shiga da ita inda za ayi mata CT scan din" Mikewa Abba yayi ya bi bayan likitan suka fita har zuwa inda aka kwantar da Hajiya Amina, har a sannan akwai likitoci biyu a ciki doing one or two things, Abba ya karasa kan gadon yana kallonta, kamar yanda likitan ya fada babu ko kwarzane a jikinta da zai baka tabbacin tayi accident, ya duka ya kira sunanta cikin calmness, tana son bude ido amma da alama it's so difficult for her to do so, kana ganinta kasan she is in so much pain, ta rike hannun Abba gam, da kyar ta iya bude baki tace "Mahmud, my daughters... they lost der father at a very young age, they have no one apart from me, i am all they have..." Abba yayi karfin halin cewa "Be strong Amina, in sha Allah zaki samu lafiya, kiyi ta addu'a" Muryarta na rawa tace "Sure, i will be strong for them, i will act strong for the girls" Likitan yayi kasa da murya yana kallon Abba yace "She is stressing her self, ka ɗan je waje Alhaji" Ba musu Abba ya juya ya fita daga ward din, Abba na fita ya zauna nan walkway din ya tallabi chin dinsa, sosai ya shiga damuwa da halin da ya ganta a ciki, yan biyunta da take ta nanatawa ne suka kara tsaya masa a rai, tun bayan rasuwan mahaifin yan biyun a yanda ta basa labari yan uwansa suka amshe duk dukiyarsa bayan sun cire mata nata tumunin takaban wai za su rike gadon yan biyun har sai sun mallaki hankalinsu, duk wani fadi tashi ita ke yi ma yaran nata biyu da taimakon kanwar mahaifiyarta don duk iyayenta sun rasu kuma ita kadai ta rayu cikin 'ya ya hudu da iyayenta suka haifa a duniya don duk sauran SS ne da girmansu kuma suke rasuwa, ita ce aka haifa a AS, ana haka ita ma kanwar mahaifiyar nata ta rasu few years ago, shkkn ta dawo babu me taimakonta amma da yake tana da zuciyar nema tayi ta fadi tashi domin yan biyunta su samu ingantaccen rayuwa, duk da rashin adalcin dangin marigayin mijinta bata hana yaranta zuwa inda suke ba, dadewa ne dai baza su yi ba don tasan baza a kulan mata da su yanda ya kamata ba tunda ba wani sonta suke ba hakan kuma ya shafi yaran, ko sun je bai fi suyi kwana uku zuwa hudu su dawo ba, in suka tashi dawowa kuma ko tsinke basa hado su da shi amma duk hakan bai dameta ba bata kuma fasa turasu katsina su kai masu ziyara ba don su din ne dai dolensu saboda halin rayuwa, sam bata nisanta su da dangin ubansu ba.... Abba ya dafe kansa yana tunanin ta yanda har ya hadu da Hajiya Amina ya aureta, basu taɓa sanin juna in person ba, wani abokinsa ne yayi connecting dinsa da ita, a lkcn tana yawan kai masu kayan siyarwa a organization din da abokin nasa yake aiki, saboda kamewarta yasa abokin nasa har ya hada sa da ita, at first Hajiya Amina tayi declining ta nuna masa aure baya gabanta yanzu sbda tana son kula da yan biyunta dake boarding school, da yake Allah ya kaddara za su yi auren sai gashi sun yi just a week da aka hadasa da ita, ire iren tunanin nan ne suka yi occupying mind din Abba, a watannin da yayi tare da Hajiya Amina bazai taɓa cewa ga wani laifi da tayi masa ba, Hajiya Amina mace ce da ko wani namiji zai yi fatan mallaka a matsayin matarsa, ta ko ina ta hadu, kuma har yau bai ga flaws dinta ba, ko da kayi mata abinda bata ji dadi ba baza ka taɓa gani a fuskarta ba, a ko da yaushe zaka ganta da fara'a, har mamakinta yake, hakan kuma na tuna masa irin zaman da yayi da Ammi na shekara da shekaru kafin kwatsam abubuwa su sauya lkci daya, kawai banbancin Ammi da Hajiya Amina shine in kayi mata abinda bai mata ba zata nuna kayi mata, Abba na ta zaune a kujeran dake walkway din tunani iri iri na yawo a ransa at the same time yana ma Hajiya Amina addu'an Allah ya tashi kafadunta cikin gaggawa, gani yake kamar likitocin are too slow akan aikinsu, yaji gwara kawai ya fita da ita kasar waje ko da da last penny dinsa ne in dai Hajiya Amina zata samu lafiya he won't mind, yana cikin wannan tunanin likitan da ya kai sa office dinsa ya fito, Abba ya mike da sauri yana kallonsa kamar yanda likitan ke kallonsa shi ma, karasawa gun likitan yayi kafin yace komai likitan yace "We tried our best Sir, but we lost her, Allah ya mata rasuwa...." Yana fadin haka ya bar Abba tsaye a wajen ya wuce, it seems Abba ya kasa assimilating abinda likitan yace masa at once, yana ta tsaye inda likitan ya bar sa ko kiftawa baya yi at the same time he was trying to digest what the Dr just said to him, sai ga sauran likitocin sun fito su ma, Abba ya bi su da ido, daya a cikinsu ya tsaya yana kallon Abba cikin kwantar da murya yace "Kayi hakuri Alhaji, Allah ya gafarta mata, Allah ya baku hakurin rashi" Yana fadin haka ya juya ya bi bayan sauran Drs din da suka yi gaba, sai a sannan Abba ya daga kafa yana tafiya a hankali ya shiga cikin Emergency ward din, ya dinga kallon gadon da take kwance sun rufa mata zanin gado, cike da karfin hali Abba ya karasa don har wani dishi dishi yake gani, a haka dai ya isa gadon, ya bude zanin gadon da aka rufeta da shi yana kallon fuskar ta, Abba ya duka kusa da ita da kyar yayi gathering duk sauran courage dinsa with shaky voice yace "Allah ya ji ƙan ki Amina, Allah ya maki rahama, Allah ya gafarta maki, Annabi ya san da zuwan ki, Allah....." Kasa ci gaba Abba yayi bayan ya ji hawaye na sauka idonsa... Mutuwar Hajiya Amina, mutuwa ce da ta girgiza duk wanda yasan ta ya kuma yi mu'amala da ita, it was soo hard to believe she was gone for ever, A nan Kaduna aka yi jana'izarta aka kai ta makwancinta, duk dauriya da dakiya irin ta Abba ya kasa dena xubda hawaye, Daga Maheer har Usman duk babu wanda ke da kuzari da nutsuwar driving most especially Usman wanda ba karamin abu bane zai sa shi zubda hawaye, da ya tuna su Eeman da yanda za su dauki mutuwar uwarsu wanda duk duniya basu da sama da ita sai yaji hawaye na bin idonsa ashe sign din mutuwar uwarsu suka ji duk suke rashin lafiya, dole sai train suka bi gaba daya zuwa Abuja... Kaf dangin marigayin mijin Hajiya Amina sun yi matukar girgiza da mutuwar ta don baza su ce ga abinda ta taba masu ba, sun santa a mace me hakuri da kauda kai da maida komai ba komai ba, Ammi tayi kuka har taji ba dadi don har sai da jininta ya hau sosai, sallamar da Hajiya Amina ta shigo har parlonta tayi mata na karshe har tana bata hakurin bazata samu zama ayi sadakan ukun yaran Maheer da ita ba ya kasa fita a ran Ammi, kuka wajen Mama Ladi ba a cewa komai kana ganinta kasan mutuwar ta girgizata don ko magana bata yi sai jan carbi da bin kowa da ido, Mayraah na kusa da Aunty Mariya ita ma ta kasa daina kuka, Aunty Mariya da hawaye ke sauka idonta sai addu'a take ma Hajiya Amina da yi mata fatan Allah ya sa ta yafi a sa'a, halinta na gari ya bi ta, Ba a gaya ma twins din Hajiya Amina rasuwar mahaifiyarsu ba sai kawo su Abuja kawai dangin babansu suka yi kamar yanda Abba yace.... Ranan da aka yi sadakan ukun Hajiya Amina ranan dangin mahaifinsu Eeman suka bar gidan Abba suka koma katsina leaving the twins behind, still a ranan Yahanasu da Hajja ma duk suka koma Kaduna tare da Grandma din Mayraah da Aunty Halima da suka zo Abujan a ranan don yin ta'aziyya, da yammacin ranan Ammi na zaune parlon ta daga gefenta Ihsaan ce kwance Maheer na kokarin mayar mata cannula dayan hannunta bayan ya cire daga hannun da ya fara sa mata saboda kumbura da hannun yayi, tun bayan da aka kawosu Abuja suka ji rasuwan mahaifiyarsu duk suke kwance critically ill, sosai yan biyun suka zama abun tausayi sun kasa absorbing uwarsu ta tafi ta bar su, gwara ma Ihsaan tana da dauriya sai dai ka kamata cikin dare tana kuka, amma Eeman abun ba a cewa komai, don haka Ammi ta ba Abba shawaran ya biya masu Umrah su je kilan Allah ya sa masu dangana da rest of mind, haka kuwa aka yi Abba ya fara processing na biya ma yan biyun da Ammi da Mayraah zuwa Saudi, Ammi na kallon Maheer a hankali tace "Ko zaka bari ta huta zuwa anjima ka sa mata" Maheer ya koma ya zauna, kwanciya Ihsaan tayi a gefen Ammi, sosai Maheer yake jin tausayin yan biyun har cikin ransa, daukar wayarsa yayi jin yana ring yana dubawa yaga MD ne ke kiransa ya mike ya fita daga parlon, Mayraah dai kallon Ihsaan kawai take, by mere looking at the teenagers sai zuciyarka ya karaya har ka zubar masu da hawaye, they are too young for the trauma, especially Eeman da ta fi shiga wani hali na rashin uwarta, it might take forever basu yi healing daga trauma din rashin uwarsu ba, Ammi na kallon Mayraah tace "Eeman tana gun Mama Ladin ne?" Mayraah tace "Eh, suna can parlorn kasa" Mikewa Ammi tayi ta fita daga parlon nata ta sauka kasa, Usman ne zaune parlon trying to comfort Eemaan that is crying silently a jikinsa, tsabar kuka ba dare ba rana duk idanuwanta sun kumbura, ya dora kanta saman shoulder dinsa yana mata magana a hankali yana patting bayanta, ita dai kai kawai take gyada masa hawaye na sauka idonta, duk bai lura da Ammi da ta sauko kasa ba, ya debi abincin dake gefensa wanda Mama Ladi ta zubo mata taki ci, ya kai mata spoon din baki, a hankali ta bude bakin ta amshi abincin, sai ga Mama Ladi ta fito daga kitchen da Custard din da ta dama mata a cup tace "In ma bazata ci shinkafar ba ga kwasta nan na dama mata shi ruwa ruwa, sai da na saka mata a firiji ya dan huce yanda zata ji dadin hadiyewa ba zafi" Daga kai Usman yayi yana kallon Mama Ladi, Mama Ladi ta karasa ta mika masa Custard din ya amsa....
[10/22, 9:28 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Few week later....

Usman na tsaye jikin motarsa ya hango su sun fito daga cikin airport din da wani porter dake dauke da luggages dinsu a kan trolley, suna karasowa Usman ya bude booth dinsa for the porter to assemble the boxes, sannan ya zagayo yayi ma Ammi sannu da hanya yana murmushi, Ammi ta amsa tace "Mun same ku lafiya" Yace "Alhamdulillah" Eeman da Ihsaan suka gaishesa a tare ya amsa yace "How was the flight?" Suka ce "Alhamdulillah" Kallon Mayraah yayi, a hankali tace "Ina yini yaya" Yace "Welcome back Mimi, naji sai kamshin Saudi Arabia ku ke gaba daya" Murmushi Mayraah tayi bata ce komai ba don tun da suka fito haraban airport din mood dinta ya ɗan canza, she was expecting to see Maheer too amma sai bata gansa ba, Usman ya bude ma Ammi back seat ta shiga sannan su Ihsaan suka shiga bayan motar su ma, Mayraah ta bude front seat ta shiga, the journey back home was so silent sai karatun qur'ani dake tashi on a low volume a motar, lkci lkci Usman ke kallon Eeman da ta daura kanta a shoulder din Ammi idonta a kasa, ita dai Ihsaan ta jinginar da kanta jikin motar, a haka suka isa gida, bayan Usman yayi parking a space din parking ya bude motar ya sauka sannan su ma duk suka sauka, Usman ya sauko da duk boxes dinsu mai gadi ya karaso da sauri don karasa masu da box din entrance din shiga gidan, Mayraah zata dau box daya Usman yace "Don't worry Mimi, ku shiga ciki za a taho da su" Tuni Ammi ta nufi entrance din shiga gidan tare da su Ihsaan, Bilkisu har tayi girki tana jiran isowarsu, da fara'a ta tarbe su ta dinga kai masu akwatunan da masu gadi ke ajiyewa a bakin kofa zuwa sama parlon Ammi.... Ihsaan na tsaye parlon Ammi rike da handbag din da Eeman ta dawo da shi daga Saudi tana ciro mata duk abubuwanta dake ciki tana ajiyewa kan kujera, Mayraah dai kallonta kawai take, can tayi murmushi tana girgiza kai, Eeman ta ɗan ja tsaki ta duka gaban akwatinta ta bude, few abubuwan Ihsaan dake ciki ta dinga fiddowa tana ajiyesu kasan carpet, Mayraah dai bata ce masu komai ba don zuwa yanzu ta gaji da settling dispute, Ammi ce ta shigo parlon daga bangaren Abba don yana gidan, tana kallonsu tace "Ku je ku gaida Abbanku yana parlon sa" Mikewa Mayraah tayi twins din suka tashi su ma suka bi bayanta, Ammi ta bi su da kallo har suka fita, sosai take jin tausayin yaran nan har ranta, and she is trying all her possible best na ganin they don't lack motherly love. Bayan Isha Mayraah na parlon Ammi tana cin abinci, su Ihsaan na zaune kusa da Ammi dake seperating tsarabar kowa daga akwatin dake gabanta, a yan satittukan da suka yi a Saudiyya Mayraah ta lura jansu jiki da Ammi ke yi ya sa sun ɗan fara sakin jiki damuwarsu kuma ya ragu a kan yanda suka baro Nigeria duk da haka wani lkcn zaka gansu suna kuka barin Eeman, Bude kofar parlon aka yi Maheer ya shigo da sallama, Ammi ta amsa tana ci gaba da abinda take, tun da Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai, har ya karaso cikin parlon idonsa na kanta, ya zauna kasan carpet ya gaida Ammi ta amsa, Su Ihsaan ma duk suka gaishesa ya amsa da murmushi yace "How was the trip?" Duk suka ce "Alhamdulillah" Kallon Mayraah yayi, without looking at him tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau, ya gajiya" tace "Alhamdulillah" After a while Ammi ta kalli Mayraah tace "In za ku tafi gida ga tsarabanki nan Mimi" a hankali Mayraah tace "Ammi sai gobe" ɗaga kai Maheer yayi ya kalleta, Ammi dai bata kalleta ba tana ci

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login