Showing 258001 words to 261000 words out of 456519 words

Chapter 87 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70647

Mayraah da jikinta yayi sanyi tayi shiru tana kallon Ammi, can ta sunkuyar da kai, Ammi ta mike ta koma kusa da ita ta jawota jikinta, nan da nan hawaye ya kawo idonta amma bata bari Mayraah taga hakan ba ta goge idon da sauri tace "I don't know why i am afraid Daughter, duk kwanan nan wasu irin mafarkai nake da ban gane kansu ba" Mayraah tayi karfin halin cewa "In sha Allah Ammi na bar aikin since you are not comfortable with it" Ammi dai tayi shiru tana rungume da ita wasu hawayen na taruwa idonta. Bayan azahar Mayraah na kwance dakinta taji wayarta na vibrate, mikewa zaune tayi sanin bazai wuce Dr Khalil ba, to me ma zata ce masa, kai tsaye dai bazata ce masa Ammi tace ta bar aikin ba, a hankali ta jawo wayar bayan ta gama tunanin abinda zata ce masa, amma sai taga wani layi with special digits ne ke kiranta, ta dinga kallon screen din babu ko kiftawa, babu wanda ya fado mata sai Musharraf, lkci daya taji jikinta yayi sanyi and she just believe shine ke kiran nata tunda babu wanda ke da layin bayan yan gidan da Dr Khalil, picking call din tayi kafin ya katse ta sa hands free gabanta na faduwa tana jiran jin muryarsa, "Didn't Khalil pass my message to you?" Mayraah tayi shiru, ko kadan bata yi wani mamakin inda ya samu numberta ba bayan da ta ji muryarsa, after some seconds ta langwabar da kai tace "A gidanmu ance sai gobe zan je tunda kowa yasan yau ai bana zuwa aiki" Jin yayi shiru tace "Hello" Yace "No bari nayi ki gama rashin kunyan" Ta dan tabe baki tace "Abinda aka ce a gidanmu fa nake gaya maka ai ba rashin kunya bane" Yace "Za ki sani" Daga haka ta ji ya katse wayar, ta ajiye a hankali ta koma ta kwanta maganganun Ammi na dawowa kanta, lkci daya hawaye ya cika idonta. Bayan la'asar Mayraah ta je kai bowl din da tayi ma Ammi fruit salad a ciki taga Maheer zaune parlor yana kallo, throughout yau bata gansa ba, bayan ta gaishesa ta tafi kitchen da bowl din ya bi ta da kallo, ba a dau lokaci ba ta fito ta xauna kujeran dake facing dinsa tace "In maka girki yaya?" Ya dan buda ido yace "In baxan takura Mimi ba" Murmushi tayi ta mike ta wuce kitchen.... Kafin karfe shidda Mayraah ta gama girka masa favorite dinsa, bayan magrib ganin bai shigo gidan ba ta dau wayarta tayi dialing numbersa yana fara ring ya daga a hankali yace "Mimi" Tace "Yaya na gama kuma naga baka shigo ba" Yace "I am having headache Mimi ki kawo min nan" Da damuwa tace "To bari in kawo maka yaya, Allah ya sauwake" Daga haka ta katse wayar ta dau hijab din da tayi sallah ta mayar jikinta sannan ta fita, downstairs ta sauka zuwa kitchen bayan ta dau abincin iya wanda zai iya ci ta fita ta kai masa chalet, dukawa gabansa tayi ta ajiye masa abincin tace "Idan ka ci sai ka sha magani" Yace "Yes dear" Mikewa tayi ta fita daga parlon, Haseenah da ta shigo kitchen take tsaye tun farkon da Mayraah ta kirasa yace mata ta kawo abincin, tana jin alamar Mayraah ta fita ta kwala wani kara me karfi, Maheer dake kwance ya mike zaune yana kallon kitchen din, banda zuciyar musulunci babu abinda zai kai sa kusa da kitchen din nan, but because of the kind of heart he have haka nan ya tashi ya tafi kitchen din, ƙasa ya ganta a kitchen din tana sauke numfashi, ya karasa yana kallonta ta dinga nuna masa kirjinta, tun dawowarsu gidan sai ranan yayi mata magana yace "Me ya faru" Da kyar tace "It's paining me" Nan da nan hawaye ya fara sauka idonta tana girgiza kai, sai da ya kai zuciyarsa nesa ya daga ta yana jin wani mugun tsanar ta har cikin zuciyarsa, suka fito daga kitchen din da kyar tana numfarfashi taki zama parlor tace "Daki zan je" Haka nan suka tafi dakin nata, hawaye na sauka idonta ta dinga juye juye tace "Wallahi mutuwa zan yi ciwo yake min sosai" Shi dai yana tsaye yana kallonta as if trying to diagnose what she said is wrong with her, muryarta na rawa tace "Kilan Ulcer ne ranan na bar maganin a kitchen din Ammi da ya tasar min" After few minutes ya juya ya fita daga dakin tana jin ya bude kofar parlor sannan ya rufe ta taso da gudu ta leka parlon ganin ya fita ta koma dakinta da sauri ta jawo karamin ledan dake karkashin gadonta ta fito parlor a guje ta nufi inda Mayraah ta ajiye masa abinci hannunta na rawa ta bude warmer din miyan ta juye abinda ke cikin kwalban gaba daya a miyan, ko ina na jikinta rawa yake, da yatsanta ta jujjuya miyan sannan ta kulle da gudu ta koma daki ta tura ledan da kwalban karkashin gado ta shiga bandaki ta wanke hannunta da handwash ta fito ta kulle kofar bayan ta goggoge hannunta ta koma inda ya bar ta ta kwanta ta kulle ido, bayan few seconds ta ji ya bude kofar parlon ta dinga sauke numfashi a wahale idonta a kulle har ya shigo dakin..... Tablet ya ciro a pack din hannunsa ya mika mata da goran ruwan, ta mike zaune da kyar tana yarfe hannu hawaye na sauka idonta ta amshi maganin da ruwa, ya ajiye sauran maganin sannan ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo, yana fita ta tura maganin karkashin carpet ta ajiye ruwan ta mike ta koma gefen gado ta zauna tana murmushi duk da yanda gabanta ke faduwa, alas gwara duk kowa ya rasa shi, da dai tayi witnessing ya auri Mayraah ko kuma wata mace a doron kasa bayan ita to gwara duk a rasa shi gaba daya, ta goge hawayen idonta tana murmushi. Maheer na komawa parlon ya zauna ya bude abincin da Mayraah ta ajiye masa, rufewa yayi ya koma ya kwanta don gaba daya bai jin appetite din cin abinci, throughout ranan haka ya yini da fever, yana ta kwance har bacci ya daukesa, Haseenah dai na gefen gado a dakinta har sannan ta ma kasa fitowa parlon, ta san wani lokacin sai ya bari abinci ya huce yake ci, tasan yanzun ma jira yake abincin ya huce kafin ya ci. Bude ido Maheer yayi ta dalilin wayarsa dake ring, ganin Mayraah ce ke kiransa ya daga a hankali yace "Mimi" Tace "Yaya ka sha maganin?" Yace "Zan sha" jin yanayin muryarsa da damuwa tace "To sai yaushe?" A hankali yace "Zan sha Mimi, am not too fine, ko zaki kawo min tea?" Ta sauka daga kan gado tace "To bari in kawo maka" Duk Haseenah na jin wayar da yake don kofar dakinta a bude yake, ta yi wani murmushi ta mike a hankali ta kulle kofar dakinta wato baya jin dadi alamar har ya ji a jikinsa yau ne ranarsa na karshe a duniya, tasan dai babu ta yanda Mayraah zata yi girki ko kadan ne ace bai ci ba, dole zai ci abincin, bayan kusan minti sha biyar Mayraah ta shigo parlon da sallama, ta ajiye shayin hannunta ta duba abincin ganin bai ci ba da damuwa ta koma gefensa ta zauna tana taɓa forehead dinsa, jin he is running temperature tace "Yaya ka ci abincin ko kadan ne sai in maka allura" Yace "Bari in fara shan shayin" Daga haka ya mike zaune, ta dau shayin ta mika masa ya amsa, kadan ya iya sha, tayi tayi da shi ya kara yace ya ishesa, ta ajiye shayin yace "Pls go to my bedroom zaki ga maganin da na sha dazu a bedside drawer ki dauko min" Tace "Wanne ne Bedroom din naka?" Ya nuna mata direction din ta mike ta tafi cikin dakin, ta dauko ledan maganin ta dawo parlon ta bude masa su ta basa ya sha ya koma ya kwanta, tana kallonsa tace "Dama baka da lafiya ne yaya?" Yace "I was feeling feverish tun da safe" Tace "Toh Allah ya sauwake, in zuba maka abincin ko kadan ne ka ci?" Ya girgiza mata kai yace "Bazan iya ci ba Mimi" Tayi shiru tana kallonsa, dama in har yana rashin lafiya komin kankantarsa baya iya cin abinci sai tea, a hankali tace "Toh shikenan bari in tafi da shi" Yace "Hope u are not angry?" Tayi murmushi tace "Aa yaya, ai nasan baza ka iya ci ba ko na bar sa nan, but plss ka kara shan shayin ko kadan ne" Ya mike ta dau shayin ta mika masa ya sha kusan rabi sannan ya ajiye ya kwanta yace "Thank you" Tace "Ko zaka shiga daki ka kwanta?" Yace "Aa nan nake kwanciya wani lokacin" Da damuwa tace "Kilan ma sauro ne ya cijeka ka samu malaria" Murmushi kawai yayi ya lumshe ido, tace "Anjima zan kira inji if u are better, in kuma baka ji sauki ba sai in sa driver ya kai ni pharmacy in siyo alluran da zan maka, yace "Ohk Mimi" Mikewa tayi ta dau abincin da cup din shayin ta fita ya bi ta da kallo sannan ya lumshe ido. Mayraah na komawa can cikin gida ta kai abincin kitchen, bayan ta wanke cup din da ya sha shayi, ta dau plate ta bude abincin ta debi shinkafa kadan ta sa miya, ko naman bata saka ba, ta bar sauran abincin a nan kitchen ta wuce sama zuwa dakinta, ajiye abincin tayi ta cire hijab dinta sannan ta dau wayarta zata jona a charge taga tana da miss call daya, dubawa tayi taga number da ya kirata dazu, mamaki ne ya cikata ta zauna gefen gado tana kallon number, to me yasa ya sake kiranta? Ko dai mistake yayi? Kawai a ranta ta sa mistake ne ma ba ita zai kira ba, kallon agogon wayar tayi taga karfe tara har da minti biyar, ta ajiye wayar gefenta sannan ta dau bowl din abincin da ta zuba ta dau cokalin ta fara cin abincin.... Cokali uku Mayraah tayi ta ajiye spoon din a hankali jin wani abu tun daga throat har zuwa cikinta, lokaci daya taji cikinta ya ƙulle, makogwaronta taji kamar ana yanka mata, ta fara jan numfashi da kyar tana zaro ido, ihu take son bude baki tayi amma ta kasa, hannunta na rawa ta jawo wayarta dake gefenta da last strength dinta ta iya danna call log dinta tayi sending call din number da hannunta ya taɓa, ko fitowa maganarta bai yi sosai ta dinga cewa zata mutu not knowing ko kiran ya shiga ko bai shiga ba, an daga ko ba a daga ba, mikewa MD yayi after hearing her almost inaudible voice kamar warce ake strangling tana cewa zata mutu, yace "Hello... Hello" amma kalmar da take ta maimaitawa kenan, Katse wayar yayi da sauri ya sake dialing amma har ya gama ringing ba a daga ba, ya sake kira no response, sau hudu yana kiran layin nata, zan mutu da ta dinga cewa ne kawai ke rotating a kansa, and she sounds as if they are strangling her, wannan yasa ya fara dialing number Dr Khalil da sauri, har ya gama ringing bai daga ba, Kallon agogo dake nuna karfe tara da minti sha biyar yayi, ya koma ya zauna yana kallon textbook din gabansa, kasa kwanciya hankalinsa yayi ya mike tsaye, in few minutes ya canza daga pajamas din jikinsa zuwa sweat pant with shirt, makullin motarsa ya dauka ya fita daga gidan, har bayan da mai gadi ya bude masa gate ya fita daga gidan kiran layin Mayraah yake but no response, ya sake kiran number Dr Khalil don yasan bazai rasa number kowa a gidan ba amma shi ma no response, though yasan yana asibiti suna operation as at that time, cikin minti sha biyar MD ya isa gidansu Mayraah after driving with speed, parking yayi kofar gida ya nufi gate din gidan sai a sannan ya fara tunanin me zai ce ya ma kai sa gidan, bai ko kalli fuskar security guy din da ya bude masa gate din ba zai shiga cikin gidan security din ya ki basa hanya yace wa yake nema, MD ya kallesa yace "Baka taɓa ganin motata kofar gidan bane?" Daga haka ya bi gefensa ya shiga ciki walking in a haste, Babban Chalet din building din ya fara kalla, sai kuma ya karasa main building din gidan, standing at the main entrance yayi knocking kofar, komawa baya yayi thinking if he isn't going to look stupid? Bude kofar aka yi, mai aikin Ammi na kallonsa daga sama har kasa ta gaishesa da ladabi, sai da ya fara tunanin sunan Mayraah sannan yace "Mayraah... Ita za ki kira min" Da ladabi tace "Yallabai ai ta hau sama ta kwanta" Yace "Tafi saman ki kirata yanzu" Juyawa tayi ta bar wajen ta wuce sama, kwankwasa kofar dakin Mayraah tayi taji shiru, sai da ta kwankwasa ya kai sau biyar bata ji an amsa ba, hakan yasa ta juya ta sauka kasa don komawa tace masa bata bude mata kofar ba, Ammi ta fito daga bangarenta jin ana knocking kofa, bata ga kowa corridor din ba, kawai ta karasa dakin Mayraah don bata ga ta zo yi mata sai da safe ba gashi har goma ya kusa, murda kofar dakin tayi ta bude, ganinta kwance a kasa Ammi ta karasa cikin dakin tace "Meye haka kika kwanta kasa Mimi?" Wani ƙara Ammi ta kwala da karfi ba tare da ta san tayi hakan ba, lokaci daya ta zube gabanta ta fizgota ganinta kwance with foam coming out from her mouth, jijjigata ta dinga yi jikinta na rawa tana kiran sunanta, kawai ta saketa ta fito dakin da gudu ta kara kwala wani ƙaran, gaba daya tayi rikicewar da bata taɓa yi ba a rayuwarta, bilkisu dake kokarin gaya ma MD Mayraah bata bude kofar ba kilan tayi bacci, ta zaro ido jin ihun Ammi ta juya da sauri, tuni MD ya shiga parlon bayan shi ma ya ji ihun da Ammi ta kwala, har ya fara tafiya ganin girman gidan bai kuma san exactly inda zai bi ba, ya fixgo Bilkisu yace "Where is her room?" Bilkisu ta nuna masa hanyar stairs din gidan, ya nufi can da sauri yana danna emergency line dinsu na asibiti a wayarsa for Ambulance, cikin few seconds aka daga kiran, Bilkisu dai sai bin sa take a baya jiki na rawa don duk ta tsorata, har sannan Ammi bata daina ihun da take ba don she was soo shocked, daga karshe taji kamar an zare mata duk kuzarinta ta fara ganin jiri ta dafe karfen stairs din ta durkusa inda take tsaye tana maida numfashi, dai dai nan MD ya hauro saman Bilkisu da jikinta ke rawa na biye da shi da gudu, kallo daya yayi ma Ammi dake maida numfashi da kyar, kawai ya shige dakin da ya gani a bude, Bilkisu na leka dakin ita ma ta kwala kara ta koma baya tana zaro ido, Ammi na kallon Bilkisu bakinta na rawa tace "Maheer" Bilkisu na jin abinda Ammi tace ta sauka kasa a guje zuwa chalet. MD na shiga dakin ya jefar da wayarsa ya durkusa gaban Mayraah ya dagota da sauri, yana ganin yanayin da take da kuma abincin dake gefenta cikin second biyu yayi diagnosing hakan as poisoning, ganin she has no sign of pulse, ya saita kansa don da farko rikicewa yayi, ya kwantar da ita da sauri ya fara mata CPR a kirjinta with every of his strength dan bai san for how long pulse dinta ya tsaya ba, dai dai nan Maheer ya shigo dakin after running all the way from the chalet, zuciyarsa na bugawa ya karaso kusa da su ya durkusa ya dafe kansa yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" MD was doing all his possible best to revive her pulse....
[8/15, 9:31 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Haseenah na makale jikin window taki fitowa sai zare ido take tun bayan da Bilkisu ta zo tana kuka ta kira Maheer, she doesn't even know weda she should be happy or otherwise, duk da ba haka ta so ba, har kasan ranta tayi bakin ciki da ba Maheer bane ya ci abincin nan, amma Mayraan ma dai da ta ci Allah Ubangiji ya sa ta mutu kawai, addu'ar da ta dinga yi kenan feeling no epitome of remorse akan abinda ta aikata, tana cikin wannan tunanin taga Ambulance ya shigo gidan, duk iya leken da take bata ga wanda ya saka Mayraah a Ambulance din ba, amma tana ta jiyo kukan Ammi, sai kuma ta juya da sauri ta koma dakinta tana tunanin inda zata yi discarding kwalban poison din don tasan ko hauka take bazata saka a bola ba.... MD har zai shiga Ambulance din bayan paramedic da suke ciki sun saka ma Mayraah oxygen with Maheer by her side, sai kuma ya juya ya kalli Ammi dake biye da shi a gigice tana kuka kamar ranta zai fita ita ma tana kokarin shiga Ambulance din, speaking calmly yace "In sha Allah she will be fine, bazai yiwu ki shiga Ambulance ba..." Bai jira cewarta ba ya shiga Ambulance din suka bar gidan, Ammi na kara rusa kuka, Sai da Haseenah ta ji fitar Ambulance din ta fito compound a rikice ta nufo Ammi da gudu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa Ammi, na fara bacci naji kamar siren, meye ke faruwa?" Hankali tashe take tambayar tana zaro ido, Ammi ko kallonta bata yi ba ta bi bayan Ambulance da sauri ko takalmi babu, Haseenah ta koma gun Bilkisu da ke kuka tace "Wai me ke faruwa Bilkisu? Me ke faruwa a gidan nan" Cikin kuka Bilkisu tace "Wallahi Mayraah ce babu lafiya har kumfa na fitowa bakin ta" Haseenah ta dafe kirji tana gwalo ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kuma ta

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login