Showing 390001 words to 393000 words out of 456519 words
ne, a ina ku ka samo ta ke da Usuman din??" Mayraah tace "Kano za su koma ne tare" Mama Ladi tace "Toh me ya hadasa da ita har za su koma kano tare? Kun ji neman bala'i ko" Bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo, Mayraah ta juya ta fita daga parlon, Usman ya zauna kan kujera ya gaishesu gaba daya, Aunty Mariya ta amsa tace "Ashe kana Kadunan Ussy" Yace "Dazu da safe na shigo" Mama Ladi tace "Yanzu Mera ke bamu labari wai zaka koma kano da er wajen Hajiya Amina" Usman bai tanka ta ba ya ciro wayarsa, Aunty Mariya tace "A zuba maka abinci Usman?" Usman yace "Na ci abinci" Mama Ladi tace "Ai ko yarinyar kyakyawa da ita ga fara'a" Shi dai Usman idonsa na kan wayarsa, Text din Aunty Mariya ne ya shigo wayar tasa ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya bude text din, bayan ya karanta content din, after some minutes ya mike ya tafi dakin baƙi, Mama Ladi ta bi sa da kallo, Aunty Mariya ta tafi kitchen ta dauko mata plate da spoon ta kawo ta ajiye mata, Mama Ladi tace "Ko er lemon ma yau basu hado min da shi ba kilan bai isa bane" Aunty Mariya ta nufi dakin da Usman ya shiga, tana shiga dakin ta kulle kofa tana kallon Usman tace "Kai kuma Usman a ina ka dauko yarinyar nan za ku tafi kano?" Usman yace "Tare suka zo da Mimi from kano yesterday" Aunty Mariya tace "Toh tun wuri ka san yanda zaka canza zancen nan a kunnen Mama Ladi kar ta kai ka gaba" Usman yace "Kamar ya kenan?" Aunty Mariya tace "Tsaf zata iya kiran Ammi tace mata gashi gashi ko baka san halinta bane" Usman yace "To ai ba komai ko ta kira Ammin" Aunty Mariya tace "Ko dai baka da kai ne??" Usman yace "No, but like seriously is there anything wrong don mun tafi kano tare da ita Aunty?" Bude kofar dakin aka yi duk suka juya, Mama Ladi na tsaye bakin kofar tace "Wannan ai walakanci ne a kawo min abinci babu ruwa kamar wata doki, saura kadan in kware, kin wani shigo daki da shi kuna zantawa ga Ladi bare na zaune a parlor" Mikewa Usman yayi ya fita daga dakin ya koma parlor, Mama Ladi ta bi bayansa, zaunawa tayi gaban abincin nata tana kallon Usman tace "In ba lalura ba me zai kawo ni gidanta da har zata dinga walakanta ni haka Usuman, ai kamata yayi ni ta dinga min nawa girkin daban a kitchen dinta tunda ba zaman dindindin na zo yi gidan ba, kaga fa ranan kawai wani ikon Allah naje gaida Ramatu kakar Mera sai muka hadu da Alhaji Saminu muka gaisa a mutunce shine yake tambayata ko in da passpo don yaga ya dace ya biya min Umrah, to ina na ga passpo, ai ko nace masa akwai 'ya ta a garin nan zan je ta rakani mu je inyi, shine ya hadani da uban kudade na taho Mariya ta rakani muje ayi min, kaji dalilin zuwana gidanta har na kwana biyu" Usman ya ɗan yi murmushi yace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Amma fa na kwabeta nace kar ta gaya ma Ammi, kai ma ka ja bakinka kayi shiru sai komai ya kankama" Usman yace "Toh shikenan" Mama Ladi tace "To ita er wajen Hajiya Aminar da za ku kano tare ya sunanta?" Usman yace "Sunan Ammi gareta" Mama Ladi ta toshe bakinta da hannunta, can tace "Wallahi yarinyar kyakkyawa ce ga nutsuwa, ko kan kujera taki zama tsabar kunya, gata er yarinya karama, zata yi shekara nawa yanzu?" Usman yace "Ina jin 18" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Wallahi da ma kawai ka nemeta, don ni shaida ce uwarta mutuniyar kirki ce wayayyiya, ga haɓa haɓa da mutane, tasan kan zaman duniya matar" Usman dai murmushi kawai yayi yana danna wayarsa, Mama Ladi tace "Allah kuwa, ko ni da kaina sai in ma Mamuda magana, matsalar dai uwarka, tunda kasan wani lokacin ba nutsuwa gareta ba, ta dau azababben kishi ta kuntsa a ranta ya hanata sukuni" Shigowar Aunty Mariya parlon yasa Mama Ladi tayi shiru ta ci gaba da cin abincinta, Mayraah ce ta fara shigowa parlon Eeman na biye da ita, Mama Ladi na washe baki tana kallon Eeman tace "Kun ci abincin Yan mata?" Eeman ta gyada mata kai tace "Mun ci" Mama Ladi tace "Ko zaki kara da nawa?" Eeman na murmushi ta girgiza kai tace "Aa na koshi Mama" Mikewa Usman yayi ya bi Aunty Mariya kitchen yayi mata sallama ya fito, sannan yana kallon Mama Ladi yace "Za mu tafi Mama" Mama Ladi tace "Kanon za ku tafi yanzu?" Yace "Ehh" Mama Ladi ta jawo jakarta ta bude, yan dari biyar biyar sababbi ƙal sai kamshi suke ta ciro har guda goma ta mika ma Eeman tana murmushi tace "Amma ya sunanki" Eeman ta sunkuyar da kanta tace "Eeman" Mama Ladi tace "Toh gashi Eeman ki saka kati ba yawa kin ji" Eeman bata amshi kudin ba, Usman ya amsa ya mika mata, bayan few seconds ta amsa tayi ma Mama Ladi godiya, Mama Ladi ta kwalo ma Aunty Mariya kira tace "Ki fito Eeman za su tafi kano" Aunty Mariya ta fito tace "Har za ku tafi Usman" Daki ta tafi ta dauko sabon turare a kwali ta saka a leda sannan ta hada da 2k, ta ba Eeman, wnn din ma Usman ne ya amsar mata, Mayraah ta dau handbag dinta tace "Aunty za su ajiye ni a gida ne su wuce" Aunty Mariya tace "Ke da na zata zaki kai yamma, ki bari kawai da yamma mai napep dina ya maida ke gidan" Mayraah tace "To" Har mota ta rakasu sannan ta dawo cikin gidan, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Don Allah Mera basu dace ba? Ni dai wallahi ta kwanta min a rai, da zai ji shawarata kawai ya neme ta ya aureta" Ita dai Mayraah Murmushi kawai take, Mama Ladi tace "Allah kuwa" Mayraah na kallonta tace "Mama Hajja tana nan Kaduna ne?" Mama Ladi tace "Wacce Hajja, Hajja ai tana Adamawa" Mayraah tace "Aunty Badiyyah fa?" Mama Ladi tace "Badiyyah tana can wajen dangin ubanta a Bichi, nima jiya Mariya ke gaya min wai za a kai kudin aurenta ranan juma'a, ta samu wani dattijo a wani kauye kafin a karasa Bichi, matansa biyu zai rufa mata asiri ya aureta, taɓon cikin shege dai bazai taɓa goguwa a rayuwarta ba har duniya ta nade" Mayraah dai tayi shiru, duk jikinta a sanyaye tana kallon Mama Ladi. Mayraah na dakin Aunty Mariya dake kallonta tace "Kinyi amfani da kayan nan da na tura maki kuwa Mimi?" Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "Aa" Aunty Mariya tace "Toh saboda me?" Shiru Mayraah tayi, Aunty Mariya tace "Yanzu yaushe za ki koma Abuja?" Mayraah tace "Gobe in sha Allah" Aunty Mariya tace "To goben da safe ki dawo nan, ki gaya ma Grandma din taki ko driver sai ya kawo ki" Mayraah tace "Toh" Da yamma me napep din Aunty Mariya ya maida Mayraah can gidan Grandparent dinta. Mayraah na zaune part din Aunty Halima tana danna wayarta bayan Isha, Aunty Halima ta shigo parlon tana kallon cup din gabanta tace "Baki shanye ba Mayraah? Shi kenan fa" Mayraah ta ajiye wayar hannunta ta dau cup din, da kyar ta tilasta kanta ta shanye content din cikin cup din, magungunan gyara masu inganci Aunty Halima ta siya ma Mayraah kafin ta dawo daga gidan Aunty Mariya, shine ta kirata parlonta duk ta bata su ta sha.... Washegari da sassafe warce zata yi ma Mayraah kitso ta zo gidan, Mayraah ba ta kitso saboda tsayin gashinta amma ta kasa gaya ma Grandma dinta, haka nan ta hakura aka fara mata kitson, kafin karfe goma aka gama zanzara mata kitso da yayi mugun mata kyau, sai kallon kitson take ta madubi, ita kanta tayi mamakin yanda kitson yayi mata kyau sosai, still haka nan ta sake zama don me lalle na jiranta, sai kusan azahar aka gama lallin, sosai lallin ya haskata ta dawo kamar wata sabuwar amarya, wanka tayi ta dauro alwala, bayan tayi sallah ta ci abinci sannan ta shirya don driver zai kai ta gidan Aunty Mariya....
[10/11, 5:46 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Har karfe biyar na yamma Mayraah na gidan Aunty Mariya don ko da ta kira Maheer bata samesa a waya ba ta cire ran tafiya ranan, tana zaune parlon surkar Aunty Mariya bayan ta kai mata pack din sabulu da Omo da Aunty Mariya tace ta kai mata inji Ammi, sosai surkarta da suke ce ma Hajiya Mama tayi farin ciki da sabulun da Omon da Mayraah ta kawo mata, Hajiya Mama na kallonta tace "Yanzu yashe za ki koma Abujan?" Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Gobe in sha Allah" Hajiya Mama tace "Amma nan zaki kwana de ko" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa anjima zan tafi" Hajiya Mama tace "Toh Allah ya kai mu" Tashi Hajiya Mama tayi ta tafi daki sai ga ta ta fito da turmin atamfa a leda ta ba Mayraah, Mayraah ta kasa amsan atamfar, sai da Hajiya Mama tayi da gaske da ita tace "Ke fa na ba ki dinka, dama Allah bai bani ikon zuwa bikinki ba, amma wasu daga matan gidan duk sun je, ke dai ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya, kuma ayi ta hakuri" Godiya Mayraah tayi mata kanta a kasa bayan ta amshi atamfar, daga karshe ta mike ta mata sallama ta bar parlon, tana isa part din Aunty Mariya ta cire takalminta tana kallon takalmin dake bakin kofar parlon sannan ta shiga ciki ta kulle kofar, ɗaga kai yayi ya kalleta, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, kawai gani tayi ya mike ya nufota ya rungumeta jikinsa, ta lumshe ido tana shakar kamshin turarensa da ya cikata, ya zame mayafin kanta yana kallon kitsonta, underneath his breathe yace "Waow it's so beautiful" Ta daga kai ta ɗan kallesa tana murmushi, a hankali yace "I missed you so much Baby" Kawai ji tayi ya fara kissing lips dinta, Dai dai nan Aunty Mariya ta fito parlorn, saketa yayi da sauri, Mayraah da duk ta daburce ta bar wajen, Aunty Mariya tayi kamar bata gansu ba, ta kullo kofar dakin baƙi dake a bude, sannan ta karasa cikin parlon tana kallon Maheer da mamaki tace "Aa, dama kana anguwan ka kirani?" Bai yarda sun hada ido ba ya zauna kan kujera yace "Ina wuni Aunty" Tace "Lallai Maheer ce min fa kayi ka kusa baka shigo kadunan ba" Murmushi yayi kansa a kasa, tace "To ya hanya?" Yace "Alhamdulillah" Tace "Ya ka baro su Ammi" Yace "Duk lafiya lau" Ta kalli Mayraah da ta kasa dago kai kamar munafuka, tace "Mimi duba fridge a kitchen akwai table water ki dauko masa" Mayraah ta ajiye ledan hannunta ba tare da ta yarda sun hada ido da Aunty Mariya ba ta wuce kitchen, Shi ma dai har a lkcn ya kasa kallon idon Aunty Mariya, definitely yasan ta gansu, Mayraah ta fito rike da ruwan gora a tray da cup ta ajiye masa, sannan ta tafi ta dau ledan atamfar da Hajiya Mama ta bata tace "Aunty, Mama ta ban wannan" Aunty Mariya ta buda baki tana kallon atamfar dake cikin ledan tace "Ni fa ba don ta baki komai na bada sabulu da Omo ki kai mata ba, gani nayi Mama Ladi ta zo bata yi dubaran kawo mata komai ba, kema kin zo kuma nace daga Abuja kike shi sa na baki nace kawai ki kai mata in ji Ammi" Mayraah dai bata ce komai ba, Aunty Mariya tace "Toh ai shikenan, Allah ya saka da alkhairi, mun gode kwarai" Kallon Mayraah kawai Maheer yake as if ranan ya fara ganinta, sosai yaga kitson da aka mata yayi ya mata kyau da lallin hannunta da kafarta, Aunty Mariya ta dawo da shi daga shagalan da yayi yana kallon Mayraah, tace "Amma sai gobe za ku koma Abujan ko?" Yace "Aunty kawai zan bar motar gidan Usman sai mu bi train" Aunty Mariya tace "Toh ai naga lokaci na wucewa, gashi har after 5" Yace "Eh yanzu za mu tafi in sha Allah" Aunty Mariya ta kalli Mayraah tace "Mu je in baki sakon Ammi Mimi" Mikewa Mayraah tayi ta bi baya Aunty Mariya zuwa Bedroom dinta Maheer ya bi ta da kallo, Aunty Mariya na kallonta bayan sun shiga dakin tace "Ai dai kinga duk yanda kika yi amfani da abubuwan da na baki ko?" Mayraah dai ta gyada mata kai avoiding eye contact with her, Aunty Mariya tace "To wanda ke can gidanki ma duk haka zaki yi using dinsu bayan 2 weeks kin ji?" A hankali Mayraah tace "Toh" Aunty Mariya tace "Kar fa ki ki amfani da su Mimi" Mayraah bata dago kanta ba tace "Zan yi Aunty" Aunty Mariya ta bata Humra da ta saka mata a leda, Mayraah ta risina ta amsa tace "Nagode Aunty" Tare suka fito parlon, tana kallon Maheer tace "To in dai kun isa Abujan za mu yi magana Maheer" Maheer yace "Toh Aunty" Aunty Mariya tace "Yanzu fa sai kun je Malali kun dau box din kayanta sannan tayi masu sallama kafin kuje train station din" Maheer yace "Eh can za mu je" Aunty Mariya tace "Toh Allah ya tsare hanya, a gaida min da Ammi" Har bakin gate ta rakasu, sai bayan da taga tafiyarsu ta juya ta koma cikin gida.... Maheer sai da ya shiga har cikin gidan Alhaji Saminu don gaida Grandma din Mayraah bayan sun isa gidan, da fara'a Hajiya Ramatu ta tarbesa tana tambayarsa su Ammi, har yan biyu sai da ta tambayesa yace "Suna lafiya Umma" Mayraah ta bar su nan parlon ta tafi sama zuwa daki ta ajiye mayafin jikinta gefen gado tana tunanin ko period dinta ne ya zo don last period dinta ko kadan bata yi cramps ba kawai ganinsa tayi, fitowa tayi daga bathroom din ganin she is not seeing her period, jin ana knocking ta karasa ta bude kofar dakin, Daya daga masu aikin gidan ce tace mata Aunty Halima na kiranta a dakinta, Mayraah na isa dakin Aunty Halima ta dauko mata sauran magungun da suka rage ta bata tana kallonta tace "Kar dai kije ki ajiyesu kina kallo a gida Mayraah" Mayraah ta ɗan yi murmushi kanta a kasa tace "Zan sha Aunty" Aunty Halima tace "Yauwa to, ki gaida su Amminki da kyau, Allah ya tsare" Mai aiki ce ta kai box din kayan Mayraah zuwa motar Maheer, bayan sun bar layin Maheer yayi wrapping hannun Mayraah a nasa a hankali yace "I miss you soo much Baby gal" Mayraah ta kasa ce masa komai tana jin wani iri with just him holding her hands, yace "There is no train going to Abuja this evening fa" Mayraah ta kallesa a hankali tace "Yaya driving din dare zaka yi kenan?" Calmly yace "No, za mu yi lodging hotel gobe sai mu tafi Abujan da safe" Ta ɗan buda ido tace "Hotel kuma Yaya?" Ya kalleta ya kashe mata ido yace "Allah na kallonmu ko?" Ta wani kallesa sai kuma ta turo baki ta kauda kai tana murmushi, ya matsa hannunta, ta zaro ido tayi er kara... Hotel me tsada Maheer ya biya masu, yana gaba tana biye da shi har zuwa dakin hotel din da aka basu makulli, bayan ya ajiye wayoyinsa yace "Zan je sallah, close the door" Yana fita ta kulle kofar dakin. Mayraah ta dau sabulunta ta shiga bandaki, sai da tayi wanka ta dauro alwala ta fito dakin, bayan ta idar da sallah ta gama addu'o'inta ta mike ta linke hijab dinta ta ajiye, ta bude box dinta ta fiddo kayan baccinta riga da wando, sai da ta gama shafa turarrukanta ta saka kayan baccin, tana zaune gefen gado tana chatting ta WhatsApp da Mom dinta Maheer yayi knocking, ajiye wayar tayi ta mike ta bude kofar, ya shigo ciki yana kallonta yace "I met with an old time frnd, after many years, shine muke ta labari" Mayraah dake kallonsa tace "Mace ko namiji?" Murmushi yayi ya ajiye abincin hannunsa yace "Kinsan dai bazan maki karya ba, Namiji ne...." Zaunawa Mayraah tayi gefen gado, shi kuma ya bude abincin da aka basu na hotel din, a hankali tace "I am not hungry, kawai drink din zan sha" Ko don abubuwan da Aunty Mariya ta dinga bata ne yasa taji bata jin yunwa ita kanta bata sani ba, Maheer na kallonta yace "Me kika ci?" Tace "Da gaske bana jin yunwa" Yace "Ohk, let me take my bath" Yana shiga bandaki Mayraah ta bude abincin tana kallo, naman ciki ta dauka ta fara ci tana sha da drink din... Bayan ya fito daga wanka yace "Kiyi alwala mu yi isha" Ta tashi ta shiga bandaki, wani alwalan tayi ta fito, suna idar da sallah Maheer ya cire jallabiyarsa ya dawo kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Did you miss me Baby gal?" Ita dai bata ce komai ba ta daura kanta jikin gado tana kallonsa bata ko kiftawa, hijab din jikinta ya cire yana kallon riga da wandon jikinta yace "Bana son wannan kayan baccin gaskiya" Ta ɗan buda ido ta kallesa, duk da dariyan da ya bata kawai tayi murmushi tace "Ban gane ba?" Ya matso kusa da ita kamar zai shige jikinta underneath his breathe yace "Change it pls Baby, change it to a more sexy one" Mayraah ta kasa ce masa komai, lkci daya taji duk jikinta was very weak, ya kafeta da ido as if waiting for an answer to his request, da kyar ta iya bude baki tace "Irinsu kadai na taho da fa" Ya kai bakinsa kunnenta yace "Ohk just take 'em off" Mayraah ta zaro ido, sai kuma murya can kasa tace "Sai in sa me?" a hankali yace "U are refusing me my Halal