Showing 444001 words to 447000 words out of 456519 words

Chapter 149 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70600

dinta da Dad suka koma US, Washegari Sunday Aunty Halima da Cousin sis dinsu suka raka Mayraah Abuja, tun ana saura kwana biyu su maida ta aka sanar ma Ammi. Bayan tafiyar su Aunty Halima don ko awa daya basu yi gidan ba suka juya don drivern Alhaji Saminu ne ya kawosu, Ammi da Mama Ladi na zaune parlorn downstairs, Ammi na rike da Aryaan dake ta mata dariya kamar ya san ta, duk inda Mayraah tayi idon Mama Ladi na kanta, yanzun ma da ido ta bi ta har ta nufi kitchen zata je dauko ruwan babynta, Mama Ladi ta kalli Ammi ta rike haɓa tace "Ke kiji yarinya ta zama mace, kamar dai ba Mera figaggiya ba, iko sai Allah, mata ta cicciko abunta tayi bul bul sai juya mana baya take, kana ganinta kasan dadi kan dadi akayi ta loda mata gidan kakannin nata, shi kan sa yaron dubesa tabarakallah ya zama bukeke, gaskiya nononta me kyau ne" Mama Ladi ta kyabe baki ta mike ganin Ammi ba tanka ta zata yi ba ta wuce sama, dakin Eeman ta tafi ta sameta kwance idonta a rufe, Mama Ladi tace "Kin hakura da kukan kenan, to tsoro nake kar in tofa nawa cibi ya zama ƙari" Juyawa tayi ta fita ta kullo mata dakin tayi kasa da murya tana tafiya tana cewa "To ina dadi er uwarta na Canada ita ace tana Najeriya, ba sai a rabu da ita ba, har dae ita ma Allah ya bayyana mata wani dake rayuwa ƙasar waje tunda ba mummuna bace ita har ta ma so tafi er uwar kyau, kawai ana nema ayi ma yarinya dole, ni dai ba ruwana...." Bayan Isha Maheer ya zo gidan, yana zaune parlon Ammi bayan ya gaishesu ita da Mama Ladi, Ammi ta kira Mayraah dake dakinta, Mayraah ta fito ganin Maheer ta gaishesa ya amsa, Ammi tace "Dare yayi ki daukosa ku tafi gida" Mayraah tayi shiru tana kallon Ammi don ta zata a gidan za su kwana, Mama Ladi tace "Jiya Balki da Eemani suka je suka kalkale maki gidan suka goge ko ina suka wanke maki bandakunan gidan, har zanin gado sun shimfida maki a daki, babu abinda zaki yi idan kun je" Juyawa Mayraah tayi a hankali ta koma dakin Ammi ta dauko Aryaan dake bacci ta fito, Bilkisu ce ta kai masu kayansu booth din motar Maheer, Ammi na kallon Mayraah tace "Baya tashin dare ai ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Baya tashi" Mama Ladi tace "To sun dai koya maki yanda zaki masa wanka dai ko, kar ki je ki halaka ɗan mutane da sabulu" Ammi ta kalli Mama Ladi tace "Sai kace ba nurse ba Mama" Mama Ladi tace "Atoh, gwara dai mu ji tun wuri" Ammi ta kalli Mayraah tace "Ko baza ki iya masa wanka ba?" Mayraah na murmushi a hankali tace "Zan iya" Mama Ladi tace "To gwara dai haka" karfe tara suka bar gidan bayan Mama Ladi da Bilkisu sun raka su har bakin mota. Suna isa gida Mayraah ta tafi dakinta ta sake kakkaba bed spread din kan gado ta kwantar da Babynta dake bacci, sannan ta cire hijab dinta ta linke ta fita daga dakin, zaune ta tarda Maheer a parlor tace "Baka shigo da kayan ba?" Yace "I will bring them in tomorrow, ko da abinda zaki bukata a cikin kayan ne in shigo da su ynxu?" Ta girgiza masa kai, yace "Ohk... Bacci babynki yake?" Tace "Ban gane Babyna ba? Kai ba naka bane?" Yace "Aa wannan naki nr wife since you named him, our next baby will be mine cause i will be the one to name him" Yana murmushi ya kare maganar, ita dai kallonsa kawai take don she didn't fine what he was saying funny, ya mike ya kamo hannunta still smiling ya dawo da ita kan kujeran da yake zaune ya zaunar da ita shima ya zauna yace "C'mon Baby gal, ko ni baza a bani privilege din naming next baby ba?" Tace "Wannan ma kai ne kace ka bar min naming din ai, bani nace ka bar min ba, i never tot zaka ce i should name the baby" Ya mata side hug yace "Haka ne Sweetheart, i pray our next baby should be a beautiful girl just like you" At the mention of giving birth to another Baby sai da Mayraah taji zuciyarta ya tsinke, a hankali tace "Ni nace maka zan kara haihuwa ne?" Murmushi yayi yace "Za ki kara mana wife, amma ba yanzu ba don nima ban mance wahalan da kika sha ba baby, kin sha wahala sosai, shi sa na baki zabin sunan babyn, but our next baby which i pray should be a girl zanyi naming dinta after Haseenah in sha Allah" Mayraah bata san sanda ta daga kai tana kallonsa ba babu ko kiftawa, yayi kasa da murya yace "Kinsan a rayuwar nan komin lalacewan mutum zaka ga definitely yana da good side dinsa, so wani lokacin idan na tuna good side din Haseenah i just feel...." Shiru yayi bai ci gaba ba, Mayraah dai kallonsa take still not blinking, ya sauke wani bayanannen ajiyar zuciya a hankali yace "Just that her bad side over shadowed the good side of her, bazan mance wani abu daya da Haeeenah ta min na kyautatawa ba, akwai wani lokaci....." Shiru ya kuma yi kamar me nazari, sai kuma ya girgiza kai yace "Ko da yake, let just leave this discussion for another day" Mayraah ta mike daga kusa da shi ta koma baya tana kallonsa tace "You are looking into my face kake gaya min zaka yi naming yarinyar da ban ma kai ga haifa ba with Haseenah? Are you for real?" Maheer yayi kasa da murya with surprise written all over his face yace "Wait Mimi... Is there anything wrong with that? Do you actually find this not okay?" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah, tana girgiza kai muryarta na rawa tace "I know why you are saying all this, amma tsakanin ka da Allah Yaya why did you have to pretend u are okay with my decision concerning the naming of this baby? Why do u have to pretend plsss" Maheer ya mike yana kallonta yayi murmushi yace "So that to please you Mimi, dole in so abinda Mimina ke so, But kinsan wani abu?" Mayraah ta dinga kallonsa with shock all over her face, A hankali yace "Ita mace in dai namiji ya taɓa rungumar ta, ko yayi kissing dinta, ohk... Stuffs like that dai, to baya taɓa fita completely daga ranta ko shekara nawa zata yi a duniya, those memories will be ringing in her brain once in a while...." Da kyar Mayraah ta iya bude baki tace "Ban gane ba yaya" Yace "Look into my eyes and tell me baku taɓa rungumar juna da shi ba Mimi, tell me bai taɓa tabaki ba sanda ku ke dating, infact har bayan kun rabu a sanda kike zuwa office ki samesa daga gidana, that not being enough har gidansa kin sha bin sa...." Mayraah taji kafafuwanta sun kasa daukanta ta dinga kallonsa kamar ranan ta fara ganinsa, Yace "Ina ga kin manta sanda kika dawo gidana wataran Hijab dinki na kamshin turarensa, sbda guilty conscience ban ce maki komai ba kika maza kika yi soaking hijab din a bandaki, ko kin manta?"
[11/6, 7:25 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah ta dinga kallon Maheer with shock ta kasa ce masa komai hawaye na sauka idonta, sosai kanta yayi mata nauyi ta dinga jin kamar parlon na juya mata tsabar yanda maganganunsa suka daketa, Maheer ya juya yana backing dinta calmly yace "And i am sorry to tell u that, ni ba sunan tsohon saurayinki na saka ma yarona ba Mimi, i named my son after your father, though ban san ko ke kin sanar ma su Ammi da yan kaduna sunan Ex dinki aka sa ma babyn ba, and still ke zaki iya bari a ranki cewar sunan da kika zaba aka sa ma yaronki cause u are entitle to ur thinking, but reverse is the case in my own thinking.... i never named my son after ur Ex, ke dai ki ci gaba da kallon yaron as ur Ex namesake, ni kuma zan ci gaba da kallonsa as ur dad's name sake.. na sa a raina that you are taking me for granted because i am just an alternative to you Mimi, I wasn't ur choice and i will never be ur choice, kawai dai kinyi biyayya ne kike zaune da ni, but you forgot that both i and u never bargained for this Mimi, kamar yanda baki taɓa tunanin akwai randa zaki wayi gari ki gan ni a matsayin mijinki ba nima ban taɓa tunanin za a wayi gari mu yi rayuwa irin ta mata da miji dake a gida daya ba, we all never saw this coming, wannan ne yasa har yanzu kika kasa cire first love din ki a zuciyar ki, you look into my face baki min kara ba kika ce sunan tsohon saurayinki za a sa ma babynki meaning he still have a special place in ur heart, someone that ko mun hadu dauke min kai yake and u expect me to name my child after him? Kin maida ni ma ban san me nake ba because i chose peace over everything in life, I am so hurt for 2 months now.... na kuma kara tabbatar ma kaina da cewa zama kawai kike dani saboda biyayya sannan u cherish me just as an elder brother amma ba don soyayya ba..." Shiru yayi bai sake cewa komai ba yana kallon kofar parlon ko kiftawa babu, Da kyar Mayraah ta juya har sannan hawaye masu zafi na zuba idonta tana tafiya a hankali ta nufi dakinta, sai a sannan Maheer ya juyo ya bi ta da kallo, tana shiga dakinta ta dafa gado sbda yanda kanta yayi mata nauyi, zaunawa tayi kan carpet ta hade kanta da gwiwa har sannan hawaye masu zafi na zuba idonta, maganganunsa ne suka dinga dawo mata daya bayan daya a kanta, har kusan karfe daya na dare Mayraah bata tashi daga inda take zaune ba, tayi kukan har taji ba dadi, she can't even explain exactly what she is feeling a ranta, wajen karfe daya da rabi Aryaan ya farka, a hankali ta daga kanta da yayi mata nauyi tana kallonsa amma bata tashi daga inda take zaune ba, sai da aka dau lokaci da tashinsa ya fara kuka, ko kadan bashi da rigima, yaro ne mai hakuri sosai, tasan yunwa yake ji shine ma yasa har yake kuka, kasa tashi tayi don attending ma babyn, a hankali ta jinginar da kanta da ke mata ciwo jikin gado, after a while aka bude kofar dakin, ita dai bata daga kanta ba, ya shigo cikin dakin ya karasa inda Aryaan ke kwance yana ta kuka, ya daukesa ya nufi kofa Mayraah ta bi sa da kallo har ya fita, bayan minti sha biyar tayi karfin halin tashi da kyar ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta dau dardumanta ta shimfida ta fara sallah... After almost an hour Mayraah ta mike daga kan darduman bayan ta idar da sallahn ta linke ta ajiye, sai a sannan ta ɗan ji sanyi abinda take ji a ranta, sai dai ciwo sosai kanta yake mata, tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta bude ta fita daga dakin, kwance ta gansa a parlorn idonsa biyu, ya daura Aryaan da ya koma bacci a kirjinsa, suna hada ido ta sauke kanta, after few seconds ta nufi inda yake kwance walking slowly, dukawa tayi kan carpet din ta kusa da inda yake kwance tana kallonsa, after some seconds ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Dama Yaya all this while zargina kake?" Shiru yayi da farko kamar bazai ce komai ba, can kuma yace "I don't get you" Lokaci daya hawaye ya cika idonta ta kasa ce masa komai, rufe fuskarta tayi jikin kujeran tana kuka a hankali, Maheer ya lumshe ido shi dai bai ce mata komai ba, Bayan tayi kukan me isarta ta dago kanta muryarta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri ni, ban san ta perspective din da zaka kalli abun ba kenan" Shi dai bai bude idonsa ba balle yace mata komai, hawaye na sauka idonta tace "I had no intention of hurting you, but i am very sorry" Bayan few seconds jin bai tanka ta ba, hawaye na sauka idonta ta mike ta dau Aryaan dake kirjinsa, sai a sannan ya bude ido, bata bari ta hada ido da shi ba tace "Abincin zan basa" Bai ce mata komai ba ta nufi daki da Baby, bayan ta gama breastfeeding dinsa ya koma bacci ta kwantar da shi, har kusan asuba Mayraah bata iya tayi bacci ba, sosai taji ta shiga damuwa zuciyarta ya rasa sukuni, bayan sallan asuba tana ta zaune kan darduma tana azkar dinta, tana idarwa ta mike ta dauke darduman duk da jirin da take ji haka ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta fita daga dakin, zaune ta gansa a parlor da counter a hannunsa, tunda suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ta isa har inda yake ta duka without looking at him ta gaishesa, ya amsa yace "How was ur night" Tace "Alhamdulillah" Mikewa tayi ta koma dakinta ta zauna kan carpet ta jinginar da kanta da gado, har bacci ya fara daukanta ta tashi ganin karfe bakwai da rabi, ta cire hijab dinta ta linke a hankali ta ajiye sannan ta fita zata kitchen, bata gansa zaune a parlon ba ta karasa kitchen din... Wajen karfe takwas da rabi Mayraah ta gama ajiye breakfast din da ta girka kan dinning table, Dai dai nan ya fito parlon yayi shirin fita office, ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta sauke idonta a hankali tace "Ga breakfast din na gama" Yace "Ohk" ta bar dinning area din ta tafi dakinta, Aryaan na kwance idonsa biyu ta samesa, yana ganinta ya fara mata dariya, ta karasa kan gadon ta duka ta daukesa with smile on her face ta fara cire masa kaya zata yi masa wanka, ta fito bathroom da Aryaan kenan bayan tayi masa wanka taji fitar motar Maheer daga gidan, a hankali ta kwantar da Aryaan ta fita zuwa parlor, shayi kawai taga ya sha a breakfast din da ta ajiye masa, ta juya ta koma dakinta, sosai tayi kokarin ganin ta yakice damuwar da ya cika mata zuciya, ta shirya Aryaan ta basa abinci ta kwantar da shi tsakiyar gado, sannan ta shiga wanka. Bayan Azahar Mayraah na zaune kan carpet ta daura kanta saman kujera idonta a lumshe bacci ya ɗauketa a hakan, Aryaan na zaune cikin keken yara yana wasa da kayan wasan dake jikin stroller din, da sauri ta bude ido jin ƙaran faduwan abu a cikin baccinta, stroller din gabanta ta dinga kallo babu ko kiftawa, sai kuma ta sake rufe idonta ta bude don gani take kamar mafarki take ganin Aryaan baya cikin stroller dinsa, ai bata san sanda ta mike tsaye da sauri ba tana kalle kallen parlon zuciyarta na bugawa, bakin kofar parlon ta tafi da sauri taga kofar a kulle ba kuma takalmi da zai nuna alamar mutum ya shigo parlon, wani tashin hankalin da ta dade bata ji irinsa ba ta shiga lokaci daya, lekawa compound tayi taga babu motar Maheer, jikinta na rawa ta dawo cikin parlon da sauri tana bin ko ina da kallo cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da sauri ta nufi dakinta zata dauko hijab dinta ta tafi gun mai gadi ta kusa cin karo da shi a corridor yana rungume da Aryaan yana murmushi, Aryaan na ganinta ya fara dariya kamar ya san abinda ke faruwa, nan da nan hawaye ya cika idonta ta jingina da bango saboda yanda zuciyarta ke bugawa kamar zai fito daga kirjinta, kana ganinta kasan ta tsorata sosai, Maheer na murmushi ya duka ya dau makullin da yayi using ya tasheta sannan ya jawota jikinsa yayi kasa da murya yana kallonta yace "Haka kike son sa dama?" Ita dai bata ce masa komai ba tana goge hawayen da yaki tsaya mata, yana rungume da ita suka koma parlor, letting her sit on the chair ya mika mata Aryaan yace "Zan koma aiki, just came back to check on you two, hope you've eaten?" Kai kawai ta gyada masa duk da bata ci ba, ruwan shayi kawai ta iya sha don gaba daya taji bata da appetite, yace "Shikenan sai na dawo later" Sai a sannan ta daga ido ta kallesa tace "Me zan dafa?" Yace "No don't worry, zan mana take away while coming back" Bata kuma cewa komai ba ya duka yayi kissing forehead din Aryaan dake hannunta, sannan ya mike yace "Till later" A hankali tace "Allah ya tsare" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle kofar. Bayan Isha Mayraah ta gama dafa ma Maheer shayi ta zuba a cup ta fito daga kitchen din ta tafi bangarensa, gaba daya hankalinta na kan Aryaan da ta bari shi kadai a dakinta yana bacci, ta shiga bedroom dinsa da sallama ta karasa har inda yake zaune yana duba wani littafi ta duka ta ajiye masa shayin, sannan ta mike zata ce masa zata koma dakinta sbda Aryaan ta ga shi ma ya mike tsaye yana kallonta, sauke idonta kasa tayi, ya kamo hannunta a hankali yace "I am sorry Mimi, i am sorry about yesterday, i think i overreacted, they are things i shouldn't have said yesterday...." Mayraah bata yarda ta hada ido da shi ba tana kokarin ganin hawaye bai taru idonta ba, ya jawota jikinsa ya rungumeta apologetically yace "Kiyi hakuri don Allah, may be is because of the love i have for you yasa nayi reacting haka, you were talking about ina zargin ki jiya, me zai kawo zargi tsakanina

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login