Showing 333001 words to 336000 words out of 456519 words
bata da lafiya" Maheer dake sauraronta yayi kasa da murya yace "Amma.... ammi ko dai in kira abokina, yana nan area din yanxun nan zan...." Ammi ta katse sa tace "Har sai yaushe muka san zai karaso Maheer? pls kar ka bata min rai ka zo ka duba min yarinyata in magani zaka siyo kaje ka siyo mata sai kuma ka tsaya kana min maganar banza, in baza ka iya ba yanzu in yi ma Abbanku magana ya kai mu asibiti tunda ba kai kadai bane likita...." Kasa ce mata komai Maheer yayi, ta katse wayarta...... Ɗaga kai su Farrah suka yi suna kallon sa bayan ya shigo dakin da sallama murya can kasa, a tare suka gaishesa still looking at him, amsawa yayi sannan ya nufi inda Mayraah ke kwance, duk su Farrah suka zuba masa na mujiya, mikewa Badiyyah tayi tana kallonsu cikin sanyin murya tace "Ko za mu ɗan je wancan dakin tunda dubata zai yi" Duk suka wani juya suka kalleta, da daddaya da daddaya suka mike suka fita daga dakin sannan ita ma ta fita ta kullo kofar, shi dai Maheer na tsaye gaban gadon yana kallon Mayraah dake baccin wahala tana sauke numfashi da kyar, ya duka gaban gadon ya cire duvet din jikinta a hankali yana feeling temperature dinta, buda idanuwanta tayi lokaci daya suka hada ido da shi, hannunsa ta riko ta marairaice masa kamar zata fashe da kuka ta kai hannun nasa wuyanta tace "Yaya kaina ciwo yake min sosai, my temperature is so high, ko zaka min allura" Shi dai kallonta kawai yake, kamar dai yanda take langwabe masa a baya in bata da lafiya, a hankali ta cire hannunsa daga wuyanta ta fara komawa baya slowly kamar warce ta tuna wani abu, lkci daya zuciyarta ya tsananta bugawa, zata koma daya side din gadon da sauri kamar warce aka tsikara yayi saurin fizgota ya dawo da ita, gigicewa tayi tana zare ido, ya hade rai cikin muryar da bata san sa da shi ba yace "Ni dodonki??" Jikinta na rawa taki yarda ta kallesa tace "Wayyoo Ammi, ni dai ka kyaleni kar in gaya ka da Ammi" ƙin saketa yayi ta dinga mutsu mutsun kwace kanta da duk karfinta amma ta kasa, shi dai kallonta kawai yake, da ta ga ba sarki sai Allah ta gatsa masa cizo da karfi, hakan yasa ya cikata ta samu ta sauka daga kan gadon da gudu ta shige bandaki ta kulle kofar da makulli tana zare ido, tunda take da shi bata taɓa jin tsoronsa a zuciyarta ba sai yau.... Barin dakin Maheer yayi ya tafi pharmacy ya siyo mata magunguna, bayan ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Badiyyah ya bata maganin ta kai mata sannan yayi wucewarsa.....
[9/15, 8:55 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Washegari duk da garau Mayraah ta tashi amma sai kara dukunkunewa take cikin duvet tana sauke numfashi a hankali, nan kuma mothers eve din da za ayi ne bata son fita shine take kara narkewa cikin bargo kamar bata da lafiya, haka Ammi tayi ta lallabata bini bini ta shigo dakin dubata hatta shayi da kanta ta bata, wajen karfe goma aka bude kofar dakin, rufe ido tayi duk tunaninta Ammi ce ta kara shigowa dakin, muryar Usman taji yana amsa gaisuwan su Farrah, sai a sannan ta bude ido, ya karasa kusa da gadon ya xaga ta inda take yana kallonta yace "Ya jikin Mimi?" A hankali tace "Alhamdulillah" muryar Hajiya Amina ta ji ita ma tana amsa gaisuwan su Farrah da Badiyyah, Mayraah ta juya, Hajiya Amina ta karasa kusa da ita tana mata murmushi tace "Mimi Amarya, sannu, ya jikin?" Mayraah ta sauke idonta ta mike zaune da kyar, cikin sanyin murya tace "Ina kwana Aunty" Hajiya Amina na murmushi tace "Lafiya lau Mimi, jiya ina barin gidan ku ka iso...." Zaunawa tayi gefen gadon ta dafa goshinta tace "Allah Ubangiji ya sanya alkhairi my dear, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Allah ya kauda duk wata fitina tsakanin ku" Mayraah ta dinga kallonta ta kasa cewa komai nan kuwa wani iri take ji a ranta idan ana cewa Allah ya basu zuri'a, Ammi ce ta shigo dakin da lafiyayyen farfesun da ta sa Aunty Mariya tayi ma Mayraah, tana ganin Hajiya Amina ta juya ta fita daga dakin tun kan Hajiya Aminan ta juyo, Hajiya Amina dai ta ci gaba da kallon Mayraah tace "Tare muke da masu maki kwalliya yanzu..." Sosai gaban Mayraah ya fadi, ta marairaice tace "Aunty jikina babu kwari, sai dinga jin kamar zan fadi saboda jiri" Hajiya Amina tayi murmushi don ita bata ga alamar rashin lafiya a tare da ita ba, ta dai ga ta rame sosai, zata yi magana sai ga Ceo ta shigo dakin, ita ma ta karasa har gun gadon bayan sun gaisa da Hajiya Amina, ta amsa gaisuwan Usman sannan ta kalli Mayraah tace "How are you dear?" Mayraah ta sunkuyar da kai ta gaisheta, Ceo ta kai hannu jikinta tace "Amminki tace min baki da lafiya" Mayraah ta kasa cewa komai, Ceo tace "You look very much okay now" Hajiya Amina tace "Kin yi wanka ma kuwa?" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina tace "Bari in ce masu kwalliyan su shigo" Tare suka fita dakin da Ceo da zuwanta gidan kenan ita ma, Usman dake kallon Mayraah ganin yanda ta rame yace "Baki cin abinci da kika je kadunan ko?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba don kwalliyan da aka ce za ayi mata yayi mugun damunta, so tayi yau ta yini a daki ko parlor kar ta leka, Usman ya juya ya fita daga dakin. Su farrah suka dinga kallon Mayraah bayan an gama yi mata make up don wani bala'in kyau tayi, tsadadden kayan da Hajiya Amina ta kawo mata shi zata sa for the mother's eve, kayan was so unique and attractive kana gani kasan da kudi ba na wasa ba aka yi kayan, Mayraah tayi kyau har ta gaji, duk wanda ya kalleta sau daya sai ya sake kallonta, bayan azahar aka fara mother's eve a gidan, Gayya na musamman surkar Dr Khalil tayi na jama'anta ita ma, kai kace sun yi mugun dadewa da Ammi, Duk da Zainab ta zo Mother's day din amma taki sakin jiki don ko ido hudu bata son yi da Mayraah, Ga kuma matan manya manyan abokan Abba wa enda duk suka sha gwala-gwalai da nasu ankon, danginsu Alhaji Saminu ma ba a bar su a baya ba, ko wannensu yayi shiga ta kece raini, yan uwa da abokan arziki ne kaca kaca a gidan ana ta shagali, abinci ma yafi kala goma kuma duk serve ur self, kamar ance in juya daga special seat din da aka bani nake zaune na hango yan Ahalin Arewa books da yan Mayraah conversation a tsatstsaye bakin gate suna kokarin yi ma manyan securites dake bakin gate din bayanin su suwaye amma an hanasu shigowa gidan, Meenah Parrot da ta ƙwama wani arnen glasses ta mika ma Ummu Abdurrahaman er ta, rai bace take kokarin masu bayanin yanda take da Maheer da irin jajircewar da tayi na ganin an bar masa Mimin sa, Ma'ani don takaici gefe ta koma ta rataye jakarta irin na Mama Ladi tana cewa "Maheer din ne fa ya gayyace mu ba wai haka kawai muka zo ba, ni fa daga Maiduguri nake, haba don Allah ni wallahi duk an ban haushi" Fatima shanono ta zuge zip din jakarta fuska a murtuke ta ciro ID card dinta na lauya tana nuna masu, Security din ya taɓe baki yace "Madam ba ID card zaki nuna mana ba, ina invitation card dinku?" Ummi dake ta hada zufa sai fifita take da gyalenta ganin da gaske securites din suke tace "Naga abinda ya isheni, wallahi Maheer din fa yasan da zuwan mu, kawai mun kasa samunsa a waya ne, don Allah ku rufa mana asiri" Su Suwaiba Sunusi, Nana Aflam, Bint Hayat, Namafs sai yan idanuwa suke zarewa a bakin gate din ko wanne ta cakare cikin ankon da Meenah Parrot ta fiddo masu, wasu ma bashi suka ci, Aysha Bee ta nemi dakali ta zauna ta rafka uban tagumi tana tunanin uban kudin motar da ta kashe gashi ko na komawa bata da shi, Aisha Yuguda tace "To ko dai kun ga mun maku kama da matsiyata ne, kun dai san babu yanda za ayi mu shigo irin wannan anguwa ba tare da an gayyace mu ba, ku ji tsoron Allah fa" Boss Lady ta cire glass dinta ganin zufa ya fara ɓata mata make up, ita babban takaicinta dubu dari biyu da ta canza ta mayar sabbin naira dari dari zata yi liki, ga su Mom twins da Ummu Nabila da Ice da suka ki zuwa sai kiranta suke a waya wai ta turo masu hotuna da video na biki, basu san har yanzu tana bakin gate ba, Aysha S Bayero ta kalli Damsel da takaici yasa ta kasa magana tace "Tirrr dama sai da nace ma Parrot anya kuwa za a bar mu mu shiga taki saurarata, sai fafa take mana da sunan Maheer yau ga irinta nan, da ma Adamawa muka je na Musharraf" Damsel ta gwalo ido bayan ta hango Sadiya Ummu Hanan, Aunty Amzaj, Aunty Zahrah, Ummu Sultan, Mera Garba da Mom Asas, Ant Maryam, Autan palace, Me lamurje, har da coursemate zaune cikin compound sun cakare cikin tsadadden ankonsu sai murmushi suke ga teburinsu cike da abinci iri iri da drinks, nan da nan hawaye ya cika idon Damsel ganin pamilynta a ciki ita kuma ga ta a bakin gate, tsautsayi yasa ta biyo Meenah parrot ashe bata da wani connection da Maheer din ma, Mama Ladi da ta sha gwaggwaro da jan baki ganin yanda aka cika bakin gate ta karasa can da gudu tana makale jakarta a hammata tana cewa "Yau na ga jaraba, ku kuma daga wani kauyen ku ka zo haka? abun nan fa 'yar gayyata ne, babu gayyar sodi sam a taron nan wllhi, in ba a gayyace ka ba ta yaya zaka ce kai lallai sai ka shigo gidan mutane fisabilillahi, doo Allah masu gadi ku korasu ku garkame mana get, mu je ma ayi ta lafta mana sata mu shiga uku..." Nan da nan securites din suka kulle gate din, Ma'ani ta fashe da kuka tana kallon Parrot da idonta yayi jajir. Sai kusan karfe hudu Maheer ya shigo gidan tare da few of his frnds shi ma saboda hotuna da za ayi da shi da aka ishesa da kira amma da bazai ma shigo gidan ba, Farrah da cousin sisters dinta couldn't take their eyes off him, shi kam ko hada ido baya iyawa da iyayen nasa mata da ma duk matan dake cikin gidan, Ita dai Mayraah na zaune kamar marainiya kusa da Hajiya Amina that was by her side all through the occasion, a haka har Aunty Mariya ta taho da Maheer yayi hoto da Hajiya Amina, ya ɗan kalli Mayraah da ta sunkuyar da kanta taki yarda ta kallesa, Hajiya Amina tace "Toh ni ban ga kunyi hoto da amaryan ba ma ae" Aunty Mariya tace "Ai kuwa dai basu yi ba" Ita dai Mayraah kanta na kasa gabanta sai faduwa yake, Aunty Amina ta nuna masa gefen Mayraah tace "Ka zauna a maku hoto" Shi ma kansa a kasa ya zauna inda ta nuna masa, a hankali Mayraah ta ɗan matsa daga kusa da shi saboda kamshin turarensa da ya cika mata hanci, a haka aka yi ta masu hoto, duk kowa kallonsu yake a compound din don ba karamin matching suka yi da juna ba, hancinsu ma iri daya sak, Aunty Mariya ta hade rai tana kallon Mayraah tace "To kiyi murmushi mana Hajiyata" Da kyar tayi murmushin da kiris ya rage ya zame mata kuka, mai hoton yayi ma Maheer alamar ya matsa kusa da ita don da distance tsakaninsu, sanin all eyes where on them ah compound din yasa Maheer ya matsa a hankali har yana goga jikinta, Mayraah ji tayi tsikar jikinta na tashi duk ta takure a wajen tana Allah Allah a gama hoton, Aunty Mariya ta tafi kiran Ammi dake can cikin mutane ta taho su yi hoto da yaran nata, farin cikin Ammi ya kasa boyuwa a fuskarta a wannan rana sai fara'a kawai take, Kamar ance Mayraah ta daga kai suka yi ido hudu da Umar, bata ma san sanda ya zo ba, murmushi ya sakar mata daga inda yake a compound din ya daga mata hannu, nan da nan hawaye ya cika idonta da sauri ta sunkuyar da kai tana kokarin ganin hawayen bai zubo mata ba... Karfe biyar aka fara shirin za a tafi da amarya don su Mami juyawa za su yi a ranan, nan fa hankalin Mayraah yayi mugun tashi banda kuka babu abinda take duk ta rikice kamar ance za a kai ta wuta, a haka aka sa ta shirya sannan aka daura mata tsadadden lapayan da aka turara mata, bayan duk su Mama Ladi da manyan gidan sun mata nasihar da za su mata aka kai ta bangaren Ammi, har bedroom din Ammi aka shiga da ita don tana ciki da 2 of her friends sai Mother in law din Dr Khalil, Mayraah ta rungume Ammi tana rusa kuka cikin tashin hankali, Ammi dai ta kasa cewa komai, can ta dago kanta da kyar tana kallonta, Mayraah tayi kasa da murya cikin kuka tana kara kankame Ammi tace "Ammi bani da lafiya fa, wallahi bani da lafiya har yanzu" Kwantar da ita Ammi tayi saman gadonta, ai ko kamar jira take ta dukunkune waje daya zuciyarta na bugawa, Hajiya Safiya ta saki baki tana kallon Ammi ganin ta kwantar da Mayraah, Ammi ta mike ta karasa gun su a hankali tace "Ina jin kawai sai dai yan Kaduna su yi hakuri su tafi, kun ga tun jiya haka ta yini ba lafiya yau ma karfin hali kawai take, daga baya ko su Mariya sai su rakata...." Aunty Mariya dake tsaye dakin ta buda baki tana kallon Ammi da mamaki, Ummi tace "Aa, Hajiya ni ban taɓa jin inda aka yi haka ba, don Allah ki bari su kai ta dakinta zata warware a can, tun jiya fa ya kamata a kai yarinyar nan muka basu uzirin mu kuma yau ma sai a basu wani story din, gaskiya a ganina hakan bai yi ba" A hankali Ammi tace "Zan yi ma ita Mamin magana, nasan she will understand, ai ita tasan bata da lafiya tun daga kadunan" Daga haka ta fita duk frnds dinta suka bi ta da kallo baki bude, ai ko Ammi ta samu Mami ta sanar mata abinda ta gaya ma su Hajiya Safiyyah, Mami ma rasa abinda zata ce mata tayi da farko, can tayi murmushi tace "Amma da kin bari an kai ta zata warware a can Hajiya, all this is normal ai" Ammi tayi kasa da murya tace "Nafi son ta kara hutawa ne ko zuwa nan da sati daya ko biyu, stress din yayi mata yawa" Mami dai tayi murmushi tace "Toh shikenan Hajiya if you insist, bari in sanar masu bata jin dadi, sai mu tafi kawai....." A haka dangin Alhaji Saminu suka bar gidan basu kai Mayraah ba wanda su kansu hakan bai masu dadi ba tunda dalilin da yasa suka kara kwana kenan, Mama Ladi sai abinda ta manta ne kawai bata gaya ma Ammi ba don bacin rai, tana kallon Yahanasu tana huci tace "Rashin lafiyar karya kawai da na hofi, duk mu ma ai mun yi haka amma ba a fasa kai mu daki ba, barin ita Meran da kowa yasan yanda take shige ma Mashir take makale masa, to wani sabon ne kuma bata yi da shi ba da har baza a kai ta dakinsa ba, ni nake ganin kinibibi da salon munafurci, yanzu me bayin Allahn nan za su dauke mu banda kananun mutane, tun jiya suka so su mikata dakinta aka hanasu aka ce sai anyi casu, yau kuma a zo masu da wannan tsinannen walakanci don anga suna da kawaici, ni ai ban san wainar da ake toyawa ba wallahi da bazan yarda da hakan ba ko ni sai in fixgo Meran daga cikin dakin in turata a mota su je su mika ta" Yahanasu ta girgiza kai tace "Gaskiya Ammi wani lokacin ban san inda take kai tunaninta ba, a ina aka taɓa haka fisabilillahi?" A fusace Mama Ladi tace "Sai a pamilyn mu, dama nan abun kunya ya kare ai" Yahanasu tace "Yanzu kawai ta saka an tafi da mu a baki, ga yan kaduna da kacalcala magana Malam" Mama Ladi ta fice daga dakin a fusace, ita dai Aunty Mariya ta ma rasa abun cewa don ko kadan ita ma abinda Ammi tayi bai mata dadi ba, don son Mayraah ya rufe mata ido sai ta biyeta aki yin abinda ya dacd, ita ma dai bata taɓa jin inda aka yi haka ba sai yau, kuma tasan don Maheer ne mijin yasa Ammi tayi haka, da wani bare ne can ita ma bazata fara ba ai. Bayan Isha Mayraah na kwance dakin Ammi zuwa sannan ta cire Lafayanta ta canza kaya, sosai hankalinta ya kwanta don sai da ta ɗan ci abincin ma da aka kawo mata, Aunty Mariya ta shigo dakin tana kallonta tace "Kinyi Sallah?" Gyada mata kai tayi, Aunty Mariya tace "Toh tashi ki maida lapayan mu je ki gaida Abba yana parlonsa ya dawo" A hankali Mayraah ta mike zaune tana kallonta sannan ta sauko daga kan gadon, Aunty Mariya ta taimaka mata ta maida lapayan nata dake ta baza kamshi, sannan ta kama hannunta suka fita zuwa parlon Abba, har a sannan da mutane a gidan, ita dai Mayraah kanta na sunkuye duk da ta rufe fuskarta da lapayan jikinta suka iso har parlon Abba, Ido hudu suka yi da Maheer dake zaune kasan carpet, ta sunkuyar da kanta da sauri ta zauna kasa kusa da Aunty Mariya, da kyar ta iya