Showing 363001 words to 366000 words out of 456519 words

Chapter 122 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70608

Maheer bai ce mata komai da farko ba, can yace "Ba ga driver ba Ammi, sai mai aikinki ta rakata su je asibitin kawai, zan bata number na if there is anything idan sun je ta kirani" Ammi dai tayi shiru tana kallonsa, Mayraah dai kanta na kasa tana jin conversation din nasu, Ammi tace "To it's better su tafi da wuri" Mikewa Mayraah tayi, Ammi ta kalleta tace "Za ki je ki kwanta ne Mimi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Eh" Ammi tace "Toh kiyi kwanciyar ki a nan mana" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Zan je dakina" Ammi tace "To je ki" Ta nufi kofa Maheer ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita. Tuni Ammi ta sauko downstairs don sanar ma Bilkisu ta shirya ta raka Haseenah asibiti, don tun wajen karfe ukun dare Haseenah ke fama da ciwon ciki har asuba kuma bata yi bacci ba, Ammi na kallon Haseenah da ta samu bacci a parlon, sannan ta tafi kitchen... Bilkisu dake aiki a kitchen din ta juya ta gaisheta da ladabi, Ammi ta amsa tace "Yaushe tayi baccin?" Bilkisu tace "Tun da ya bata magani bayan wani dan lokaci bacci ya dauketa" Ammi tace "To idan ta tashi driver zai kai ku asibiti, zan baki number Maheer din idan da wani abu sai ki kirasa" Bilkisu tace "Toh Hajiya" Juyawa Ammi tayi ta bar kitchen din Bilkisu ta ci gaba da abinda take. Har gari ya waye Mayraah na kwance dakinta, ɗan baccin safen da take yi ma ta kasa yin sa ta rasa dalili, tashi tayi daga karshe ganin karfe tara saura ta shiga bandaki don yin wanka, ta fito daga wanka tana shiryawa Ammi ta bude kofar tana kallonta tace "Mimi kin yi breakfast ne?" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Ban yi ba" Ammi tace "Toh ki je sai ki hada har na yayanki ki kai masa" a hankali Mayraah tace "Toh" Juyawa Ammi tayi ta fita daga dakin, Mayraah ta gama shiryawa ta fita zuwa downstairs, Haseenah ce zaune a Parlon da shayi a gabanta ta jinginar da kanta da kujera, da alama tayi nisa tunanin da take don bata ma san Mayraah ta sauko downstairs ba, Mayraah tayi wucewarta kitchen ta fara hada ma Maheer breakfast, tana gama hada masa breakfast din ta dauka ta fito daga kitchen din ta nufi dakinsa, har a sannan Haseenah da ta jinginar da kanta da kujera bata sani ba, bayan kusan 10mins Bilkisu ta shigo parlon daga dakinta tana kallon Haseenah tace "Aunty baki gama shan shayin ba har yanzu? Dreba na ta jiran mu a waje" Haseenah ta sauke numfashi a hankali tace "Ciwon cikin ma ai ya lafa min bilkisu, kawai ruwan lipton zaki taimaka ki kawo min na kasa shan shayin...." Bilkisu ta juya ta tafi kitchen ta bude flask ta tsiyaya mata ruwan lipton sannan ta kai mata, kadan Haseenah ta sha ta jawo maganin da Maheer ya bata jiya tana dubawa, sai kuma ta kalli Bilkisu tace "Ya ma yace zan sha maganin nan?" Bilkisu tace "Biyu yace ki sha ai" Haseenah tace "Anya, kinga fa uku ne babu a jiki, gwara dai in tambayesa" Bilkisu dai bata ce mata komai ba tana kallonta, da kyar Haseenah ta dafa kujera ta mike tsaye ta fara tafiya shi ma da kyar don kafafuwanta sun mata nauyi sun kumbura, dakin Maheer ta nufa, Bilkisu ta bi ta da kallo kawai ta tafi ta ci gaba da abinda take, Haseenah na isa kofar dakin nasa kafin ta bude taga an riga ta bude kofar, komawa gefe tayi ganin Mayraah, daga sama har kasa Mayraah ta kalleta sannan ta bar wajen, Haseenah ta kalli cikin dakin, Lkci daya Maheer ya murtuke fuska ganinta yace "Ke wai baki da hankali ne ko kuma kin fara hauka ne? That was how u barge into my room earlier this morning, are you alright?" Haseenah ta sukunyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds ta juya ta bar bakin kofar dakin.... Mayraah na zaune parlon Ammi Maheer ya shigo da sallama, Ammi na kallonsa tace "Bilkisun ta kira ka?" Yace "Aa" Zaunawa yayi, Ammi dai kallonsa kawai take ganin he is moody, amma tayi tunanin kawai saboda Haseenah ce da yake tunanin ta karfi da yaji ana cusa masa ita, Mayraah dai idonta na kan TV, mikewa yayi Ammi tace "Ko da wani abu ne?" Ya girgiza mata kai yace "Aa babu" Kofa ya nufa Ammi ta bi sa da kallo tace "Night shift gareka ne yau?" Yace "Eh" Daga haka ya fita, Bayan fitarsa da some minutes Ammi ta mike ta fita daga parlon ita ma. downstairs ta sauka ta gansa zaune a parlor shi kadai, Ammi ta zauna tana kallonsa tace "Me yasa kake son saka ma kanka damuwa ne Maheer? Nobody is trying to bring Haseenah back to ur life in haka kake ganin" Maheer ya ɗan yi murmushi yace "Abinda babu aure tsakanina da ita Ammi, ni Haseenah is not and will never be my problem now, don nasan babu komai tsakanina da ita, kawai daxu ne aka turo min wani email daga wajen aiki" Ammi dake ta kallonsa tace "Wai me?" Ya sauke idonsa yace "I think some weeks ago na ce maki an bude wani branch na hospital dinmu a lagos, and the grand opening is tomorrow, though anyi employing likitoci da nurses but still they selected 6 old staffs, 3 from kano, and 3 from Abuja, ana son su dan yi aiki na ɗan lokaci a hospital din sannan a saka ma Sababbin staffs ido...." Shiru yayi yana kallon Ammi dake kallonsa, Ammi tace "And u are among the ones selected here in Abuja" Bai ce mata komai ba, tace "Hakuri zaka yi kawai, dama shi aiki ya gaji haka, yanzu kenan transfer za su maka zuwa Lagos din?" Yace "Aa kawai wata daya za mu yi a can" Ammi tace "To ai da sauki, zaka ga wata daya kamar gobe ne in muna da rai da lafiya, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" Yace "Ameen" Ammi tace "Yanzu yaushe ne tafiyar?" Maheer yace "Flight din karfe shidda da rabi na yamma ne" Ammi tace "Yau kenan, Toh Allah ya kai mu, Mayraah will remain here har ka dawo" Shi dai bai ce komai ba, wayarsa ne ya fara ring ya daga ganin Bilkisu ce ke kiransa... Bayan sun gama magana yayi mata transfer din kudin da tace, Ammi tace "To ita wannan ya batun kama gidan da Abbanka yace ka kama mata" Maheer ya mike yace "Nayi ma wasu agents magana, ina jiran feedback dinsu zuwa anjima" Ammi tace "Allah ya kai mu, gwara ta je can ita kadai, in ma da wani abu Bilkisu zata dinga zuwa gidan ta mata, we are not taking second risk" Karfe biyar Maheer ya dawo gida tun da ya fita bayan conversation dinsa da Ammi, Haseenah dake kwance a parlon, ta bi sa da kallo shi kam yayi kamar bai ganta ba, yana haurawa sama ya bude dakin Mayraah ya ga bata ciki, hakan yasa ya karasa bangaren Ammi, babu kowa a parlon ya karasa cikin Bedroom dinta, gogaggun kayan Ammi take gyara mata, ta juya ganinsa, ya karasa har kusa da ita yace "Aiki kike Mimi?" Ta sauke idonta ta gyada masa kai, ya amshi kayan hannunta yace "Toh bari in taya ki" Tace "Aa zan iya" Jera kayan suka fara yi a tare cikin press din dakin, lkci lkci take kallonsa ta gefen ido, bayan ya ajiye kayan hannunsa wanda shine na karshe ya juyo da ita yana rike da 2 of her hands, a hankali yace "You know what Mimi?" Ita dai bata daga kanta ba, yace "Anyi Transferring dina zuwa Lagos...." Mayraah bata san sanda ta daga kai tana kallonsa ba, ya gyada mata kai a hankali yace "Yea, i just received the mail this morning" Bata san sanda tace "Lagos kuma?" Ya gyada mata kai, sunkuyar da kanta tayi, ya jawota jikinsa a hankali giving her a warm hug, kafin yace komai yaji an bude kofa can parlor, saketa yayi, ita ma ta juya da sauri ta bar wajen. Karfe shidda saura Maheer ya gama hada box din kayansa a dakinsa, Ammi na dakin nasa ita ma, Tun da ya gaya ma Mayraah batun tafiyar gaba daya ta dawo wani iri, tana zaune parlor a downstairs ita da bata wani cika son zaman kasa ba, lkci lkci take kallon kofar dakinsa ko Ammi zata fito amma bata fito ba, Bilkisu ce ta shigo parlon tare da Haseenah, bayan sun je can chalet ta taya Haseenah hada kayanta, dai dai nan Ammi ta fito daga dakin Maheer da ke rike da boxes dinsa, Ammi na kallon Bilkisu tace "Inji dai kin dau duk Abinda zata bukata?" Bilkisu tace "Eh Hajiya ba a manta komai ba, akwati biyu ne, suna parking space na bar su a can" Haseenah dai ta karaso da kyar ta zauna kan kujera tana maida numfashi, Maheer idonsa na kan Mayraah da ta tsiri danna waya, Ammi ta dau wani seal envelope ta mika ma Maheer tace "Takardan da aka basu a asibiti ne, ina jin ko na scan ne" Maheer yace "Kawai ta ajiye a wajenta, i have nothing to do with it...." Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta ajiye envelope din kan kujera tana kallon Bilkisu tace "Ku je mota ku jira" Bilkisu tace "To Hajiya" Kofa ta nufa Haseenah ta tashi ta bi bayanta, Maheer dai duk hankalinsa na kan Mayraah, Ammi ta kalleta tace "Mimi kun yi sallama da yayan naki" Ɗan murmushi tayi tace "Eh Ammi" Mikewa tayi ta amshi hand luggage dinsa ta nufi kofa ta fita, tana tsaye a parking space din taki yarda ta kalli Haseenah dake zaune back seat, Bilkisu kuma tana jikin motar a tsaye, Maheer da Ammi na isowa parking space din Mayraah ta sa hand luggage dinsa a booth, ta ɗan kallesa tace "Allah ya kiyaye hanya" Yace "Ameen" Ammi na kallon Bilkisu tace "To ki shiga bayan motar ke ma, zai fara kai ku gidan ne, kafin driver ya kai sa Airport" Bilkisu tace "To Hajiya" Bude back seat tayi ta shiga ta zauna gefen Haseenah, Juyawa Mayraah tayi ta bar wajen, Maheer ya bi ta da kallo, har ta shiga cikin gidan, zagawa yayi kamar zai shiga front seat sai kuma ya dawo yace "I think ban dauko power bank dina ba" Daga haka ya bar wajen da sauri ya nufi entrance din shiga gidan, direct sama ya tafi zuwa dakin Mayraah, ya ganta zaune gefen gado ta daura fuskarta kan pillow, tana jin an bude kofa ta dago kanta da sauri tana goge hawayen idonta, karasawa yayi ya zauna kusa da ita da damuwa yace "Mimi" ta sauke kanta wasu hawayen na zuba idonta, rungumeta yayi jikinsa, kamar jira take ta fashe da kuka, kasa ce mata komai yayi yana jin kukan nata har cikin ransa, cikin sanyin murya yace "I am spending just 4 weeks in Lagos Mimi, 4 weeks is just like tomorrow" Ita dai gyada masa kai kawai tayi hawaye na zuba idonta, a hankali yace "I will miss you so much" Ya dago kanta yana goge mata hawayen fuskarta da hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, yayi kasa da murya yace "Ko dai mu tafi tare ne?" lumshe ido yayi giving her a deep snog..... Tun da Maheer ya tafi Mayraah ta fara kirga kwanakin da yace mata zai yi a Lagos, ita kanta ta kasa fahimtar irin kewarsa da take duk da a rana ya kan kira ta sau uku, sai dai sbda yanayin aiki basa dadewa a wayar, gaba daya gani take kamar kwanakin basa gudu, duk da Ammi tayi vowing ko inda Haseenah take bazata je ba amma saboda zuciyar musulunci kasa yin hakan tayi, don kuwa duk bayan kwana uku ta kan bi Bilkisu su je gidan da aka kama mata ta dubata, Mayraah bata taɓa cewa zata je gidan ba, Ammi ma bata taɓa ce mata ta shirya su je ba, daga karshe Ammi kawai ce ma Bilkisu tayi ta debi kayanta a akwati ta koma gidan gaba daya ganin yanda Haseenah bata iya yin komai sbda nauyin ciki, kayan babies kuwa babu wanda Ammi bata siya ba, har abubuwan da ake bukata na haihuwa ta siya..... Mayraah na zaune parlorn Ammi bayan isha tana kallo, Ammi kuma tana can bangaren Abba, wajen karfe tara Ammi ta dawo bangarenta, ganin fruits din da ta bar ma Mayraah bata sha ba tace "Me yasa baki sha fruits din ba Mimi?" Mayraah tace "Na koshi ne Ammi" Ammi ta zauna tace "Dazu wai hiran me Usman ke maki a parlor daga ganina yayi shiru?" Mayraah tayi er dariya tace "Ammi wannan ai secret ne between us" Murmushi Ammi tayi tace "To in ke da shi baku gaya min ba ai Abbanku ya gaya min yanzu" Dariya Mayraah tayi tace "To me Abba yace maki?" Ammi tace "Oho" Murmushi kawai Mayraah ke yi ta kuma ki gaya ma Ammi maganar da suka yi da Usman. Washegari friday Bilkisu ta bugo ma Ammi waya kan cewar Haseenah bata da lafiya tun jiya, Ammi tace "Ko dai nakuda take?" Bilkisu tace "Ina kyautata zaton haka" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh zan taho yanzu, in haihuwan ne sai mu tafi asibiti" Babu bata lokaci Ammi ta sa driver ya kai ta gidan da Haseenah take, ko da taje taga ba labor bane amma ganin condition dinta haka ta sa driver ya maido su gida gaba daya..... Mayraah da Ammi suna kitchen ranan lahadi da yamma, Mayraah na assisting din Ammi dake ma Abba girki, Bilkisu ta shigo kitchen din tana kallon Ammi tace "Hajiya ina jin fa nakuda take" Ammi ta fito daga kitchen din ta karasa kusa da Haseenah dake duke a parlor tana yarfe hannu don azaba, Ammi ta kamata tana kallon bilkisu tace "Maza ki kira Driver mu tafi asibiti" Mayraah dai na tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, da azaba yayi ma Haseenah yawo bata san lokacin da ta kwala wani ƙara ba ta kankame Ammi, Bilkisu ta tafi dakinta da sauri ta dauko wayarta don kiran driver, Ammi dai sai sannu take ma Haseenah, dai dai nan Maheer ya shigo parlon, da Mayraah ya fara hada ido a parlon, amma ganin condition din da Haseenah ke ciki kawai sai ya nufesu, Ammi ta kallesa tace "Ka dauko Makullin motarka mu tafi asibiti labor ne" Dakinsa ya nufa da sauri, Mayraah ta bi sa da kallo cikin few seconds ya dawo parlon da car key dinsa ya fita don starting motarsa, Ammi ta daga Haseenah da taimakon Bilkisu suka tafi parking space da ita, Ammi na kallon Bilkisu bayan sun taimaka ma Haseenah ta shiga mota tace "Ki dauko akwatin kayan haihuwan nata" Babu bata lokaci Bilkisu taje ta dauko sannan suka dau hanyar asibiti, Suna isa asibiti ko 30 mins ba ayi ba Haseenah ta haihu.
[9/30, 9:14 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer na tsaye bayan isha yana kallon yaran dake kwance kan gadon jarirai a wani ward, it took some times kafin aka samu yaran suka yi kuka bayan an haifo su, kallon babies din yake daya bayan daya baya ko kiftawa, sai ga wata nurse ta shigo tare da Ammi dake biye da ita, Ammi ta karasa kusa da gadon jariran, ta fi minti daya tana kallon yaran, tun da aka haifosu kusan awa daya kenan sai yanzu aka bari Ammi ta shigo inda suke bayan likitoci sun tabbatar they are fine, ita duk tunaninta ma ko sun mutu ne jin shirun yayi yawa, Ammi ta kalli Maheer sai kuma ta sake kallon yaran sannan ta duka ta dau daya daga jariran tana gyara baby blanket da aka yi wrapping dinsa da shi tana murmushi tace "Maa sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana ku bisa tafarkin addinin musulunci, Allah yayi maku albarka" Mika ma Maheer yaron tayi tana kallonsa har sannan murmushin fuskarta bai gushe ba, sauke idonsa yayi ya amshi yaron daga hannunta, Ammi ta duka ta dau daya jaririn shi ma ta masa addu'a.... Haseenah na kwance ita kadai a ward din da aka kwantar da ita hawaye na sauka idonta, ita ma ba a dade da kawo ta ward din ba don tun da ta haihu ta shiga unconscious state, bayan ta dawo hayyacinta aka maido ta ward, sai kuma taga shiru shiru ba a shigo mata da babynta ba gashi Ammi dake kusa da ita bata ce mata komai akan babyn ba, sai sannu kawai take mata, hakan yasa ta fara tunanin ko ya mutu ne yaron, daga karshe ma Ammi barin ward din tayi wannan yasa ta dinga kuka ita kadai babu me rarrashinta. Bude kofar ward din da aka yi yasa ta juya da sauri, Ammi ta shigo rike da one of the baby, ta karasa har kusa da Haseenah dake kallonsu, Ammi ta kwantar mata da shi a gefenta tana kallonta tace "Sannu Haseenah, Allah ubangiji ya raya, ke kuma Allah ya baki lafiya" Haseenah dai goge hawayen idonta kawai take tana kallon yaron, dai dai nan Maheer ya shigo ward din ta daga kai tana kallon second baby dake hannunsa, ya karasa ciki ya kwantar da shi kusa da dan uwansa, Haseenah ta dinga kallon Babies din that are so identical, sai kuma ta ɗaga kai ta kalli Maheer dake kallonsu shi ma, a takaice yace mata "How are you feeling?" Ta gyada masa kai a hankali tace "I am okay" Abba ne ya shigo ward din da sallama tare da Usman, ko wannensu ya dau each of the babies Abba yayi ma Haseenah barka tare da addu'an samun lafiya..... Bayan tafiyar Abba da Usman da kusan minti sha biyar Bilkisu ta shigo rike da basket din kayan shayi ta ajiye tana kallon kyawawan jariran tana washe baki tace "Alhamdulillah, Allah ubangiji ya raya su, yayi ma rayuwarsu albarka, ke kuma Allah ya baki lafiyar shayar da su"

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login