Showing 366001 words to 369000 words out of 456519 words
Ammi tace "Ameen nayi ta kiranki ince ki taho mata da kayan sa wa baki dau waya ba" Bilkisu tace "Wallahi Hajiya wayar na daki ai ko dakin ma ban shiga ba ina tafasa ruwan zafi na dauko kayan shayin muka juyo kawai da dreba" Ammi tace "Mayraah fa?" Bilksu tace "Naje har sama nayi mata sallama don in sanar mata da haihuwar amma kamar ina jin tayi bacci ne" Ammi ta hada ma Haseenah shayi me kauri da kanta sannan ta mika mata, after some minutes Ammi ta mike tana kallon Maheer tace "Zaka kwana a nan ko?" Maheer yace "To put an eyes on the babies" Ammi tace "Toh shikenan zan dawo da asuba in sha Allah..." Daga haka ta kalli Bilkisu tace "Mu je Bilkisu" Bilkisu tace "To Hajiya" Daga haka suka nufi kofa suka fita, Sai a sannan Haseenah ta daga kai tana kallon Maheer, a hankali muryarta na rawa tace "Don girman Allah Maheer kayi hakuri ka yafe min for the sake of this babies" Maheer ya dakatar da ita a takaice yace "Look kar ki dameni... Concentrate on ur health ki bar ni da wnn maganar, i am not interested" Shiru tayi tana kallonsa bata sake cewa komai ba.... Ammi na komawa gida tayi knocking kofar dakin Mayraah sannan ta bude ta shiga ciki, kwance ta sameta kan gado, ganin bacci take Ammi ta juya ta fita. Wajen karfe goma da rabi Maheer ya fito daga ward din da Haseenah take bayan tayi bacci ita da yan biyunta, reception ya tafi ya zauna yayi dialing number Mayraah, har ya gama ringing bata daga ba, ya sake kiranta nan ma bata daga ba, mikewa yayi ya koma ward din da ya fito ya zauna. Washegari da asuba Mayraah na zaune dakin Ammi bayan ta gaisheta Ammi ke sanar mata Haseenah ta haihu, Mayraah tace "Maa sha Allah, Allah ya raya baby, ita kuma Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen" Mayraah ta daga kai ganin kallonta Ammi take tace "Ammi Baby boy ne ko Girl?" Ammi tace "Yan biyu ne maza" Mayraah ta sauke kanta tace "Maa sha Allah, Allah ya raya mana su, ya albarkace su" Ammi tace "Ameen" Mikewa Ammi tayi tace "Bari in je in ga ko Bilkisu ta karasa abinda take yi a kitchen, zuwa karfe bakwai za mu je asibitin, ki je ki shirya" a hankali Mayraah tace "Toh" Ammi na fita daga dakin Mayraah ta mike ta bi bayanta ta koma dakinta. Kamar yanda Ammi tace karfe bakwai ta shirya bayan sun gama hada ma Haseenah breakfast da za a kai asibiti, dakin Mayraah ta shigo ganinta kwance tace "Baki shirya bane Mimi" Mayraah ta girgiza mata kai a hankali tace "Cikina ke ciwo Ammi" Ammi tace "Subhanallahi, tun yaushe?" Mayraah tace "Da daddare, amma da sauki" Ammi tace "To kin sha magani?" Ta girgiza kai tace "Aa zan sha idan nayi breakfast" Ammi tace "To sauko ki hada shayin ki sha, sai ki hadiyi magani ki kwanta" Mayraah ta sauko daga kan gadon a hankali suka sauka downstairs da Ammi, tana zaune parlor har Ammi da Bilkisu suka tafi asibiti wajen karfe bakwai da yan mintuna. Karfe daya da rabi Mama Ladi ta iso gidan bayan Ammi ta sanar mata da haihuwan, sama ta tafi da sabon akwatinta, jin gidan tsit ta tafi bangaren Ammi nan ma ba kowa, ta dawo corridor tace "Ikon Allah, to dama babu kowa gidan aka sa na biyo hanya ko kumallon kirki ban yi ba, tarewa pamilyn suka tafi suka yi a asibitin kenan saboda Hasinu ta haihu" Dakin da take sauka ta kai akwatinta sannan ta fito tace "Toh ni yanzu ya zan yi da yunwan cikina ni Ladiyo" Karasawa tayi ta murda kofar dakin Mayraah, Mayraah dake zaune kan darduma ta daga kai ganin Mama Ladi tace "Sannu da zuwa Mama" Mama Ladi tace "Au da kina ji na kika yi shiru Mera?" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Wallahi ban ji ba Mama, sallah ma nake, yanzu na idar...." Mama Ladi tace "Toh ina yan gidan gaba daya?" Mayraah tace "Suna asibiti" Mama Ladi tace "Kaji wani taya bera bari, ita Hasinun matar kirki ce da za su je asibiti su tare saboda ita, banda ma Pamilyn namu akwai zuciyar musulunci in wasu pamilyn ne yaushe ma za a kalleta, ba fa aure tsakaninta da Mashir din amma ki ji yanda ake hidima da ita, Allah dai yasa tagwayen nasa ne" Mayraah dai kallonta kawai take bata ce komai, Mama Ladi tace "Al-qur'an bazan je asibiti ba inyi ta warin izal, zamana zan yi a nan har ranan da za a sallamesu su, tashi ki samar min abinda zan ci" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta linke darduman da tayi sallah ta ajiye, Mama Ladi tace "Ba dai ki da rabon kishi da er iskar, don duk me bin boka da malamai ɗan iska ne, Maheer mijinki ne ke kadai ba wata shegiya" Mayraah ta sunkuyar da kanta ta fita daga dakin ta sauka downstairs, tun safe she was just moody and weak ta rasa dalili don ko breakfast din kirki ta kasa yi, amma words din Mama Ladi na karshe yasa taji strength dinta ya dawo, she felt relieved with those words, sai dai ita kanta bata san me yasa taji hakan a ranta ba. Mama Ladi na biye da ita suka sauka downstairs, dai dai nan Bilkisu ta shigo parlon rike da basket din abinci da wasu kaya a hannunta, Mayraah na ganin haka ta shige kitchen bata tsaya a parlon ba, Mama Ladi na kallon Bilkisu tace "Daga asibitin kike kema" Bilkisu tace "Eh Mama, an ma sallame mu, sannu da zuwa Mama" Sai ga Ammi ta shigo parlon rike da baby daya, Haseenah na biye da ita, sannan Maheer dake rike da second twin din shi ma ya shigo parlon, Mama Ladi ta nufi Ammi da sauri tana kallon jaririn hannunta tace "Barka barka, ashe dai banda rabon wahala don yanzu nake shirin zan je asibitin sai ga ku, sauka ta kenan wllhi ko zama ban yi ba" Sannu da zuwa Ammi tayi mata tana mika mata jaririn, Mama Ladi ta rike haba tace "Allah mai iko, ki ji ɗan kamar uban yayi kaki, ko ke baki ga haka ba Ammi??" Ammi dai mika mata yaron hannunta kawai take, Mama Ladi ta amshesa tana kare masa kallo kawai ta saki kabbara tace "Wallahi Kamar Mashir sanda kika haife sa, iko sai Allah" Da sauri ta karasa gun dayan Babyn dake hannun Maheer tana kallonsa tace "Yau ni naga abun mamaki, yo wannan ai babu zancen wani gwaje gwaje ko makaho ya shafa fuskar yaran nan yasan na Mashir ne, kawai sai dai muyi fatan Allah ubangiji ya raya mana su bisa imani, fargaban mu daya nonon da zata ce zata basu, kun dai san babu abinda yaro bai dauka a nonon uwarsa, don haka hakuri kawai Mashir zai yi ya tanadi kudin madaran gwangwani don mu ba sai ta shayar mana da yaran ba mun yafe" Dakin da Ammi ta sa Bilkisu ta gyara aka shimfida zanin gado ta nuna ma Haseenah, Haseenah dake kallon Mama Ladi a sanyaye, ta juya tana tafiya a hankali ta karasa cikin dakin da aka gyara mata. Duk Wannan abun da ake Mayraah na jin su a kitchen don kofar kitchen din a bude yake, ta gama zuba ma Mama Ladi abinci ta fito parlon, dai dai sanda Maheer ya sauko downstairs bayan ya haura sama zuwa dakinta bai ganta a ciki ba, bata yarda ta kalli direction dinsa ba ta nufi dakin da take jin muryar Mama Ladi fuskarta a daure, ta shiga da sallama ta ajiye mata abincin hannunta, a takaice tayi ma Haseenah barka without looking at her in the eyes, Mama Ladi ta mika mata one of the twin tace "Amsa yaji duminki ku fara sabawa tun yanzu" Mayraah ta amshi cute baby din wanda truly replica din ubansa ne, kallonsa kawai take bata ko kiftawa, Mama Ladi na washe baki ta amshesa ta kwantar sannan ta dauko dayan ta mika ma Mayraah shi ma, Mayraah ta karɓe sa shima tana kallonsa don ba a iya banbanta sa da ɗan uwansa banda shaidan da aka yi using a asibiti to differentiate them, Mama Ladi tace "To gwara tun yanzu ki fara sabawa da su, su ma su saba da duminki, don da kyar in ba ke zaki rike ma Mashir su ba tunda babu aure dai tsakaninsa da tambadaddiyar uwarsu, saki uku yayi mata" Daga kai Haseenah tayi tana kallon Mama Ladi jin abinda take cewa, sai kuma ta kalli Mayraah, har a sannan Haseenah bata san da auren Maheer da Mayraah ba, to tana fitowa prison kwana daya kacal tayi gidan Abba washegari aka kama mata gida aka kai ta can, duk iya bugan cikin da ta ke ma Bilkisu dake zuwa wajenta don ta samun hint din abubuwan dake faruwa a family din Bilkisu taki bata hadin kai, da alama kuma Ammi ce ta kwabeta, hatta Badiyyah sai da ta tambayi Bilkisu inda take, amma Bilkisu tace mata bata ma san ta ba, don haka Haseenah knows nothing na gidan, har tafiyar da Maheer yayi ma bata sani ba duk da babu ranan da zai wuce da bazata tura masa text na ban hakuri ba amma baya responding, kira kuma dama ya sa ta a busy.... Mayraah dai bata ce ma Mama Ladi komai ba, after few more minutes ta mika mata yaron tace "Zan je in karasa aikin da nake yi Mama" Daga haka ta fita daga dakin, Maheer ta gani zaune parlor, ya mike yace "Mimi" Ko kallonsa bata yi ba tayi tafiyarta upstairs ya bi ta da kallon mamaki, bin bayanta yayi har ta shiga dakinta shi ma ya shiga, yayi kasa da murya yace "Mimi is anything wrong pls?" Cike da masifa tace "Pls i want to be left alone" Shiru yayi yana kallonta, can ya nufeta tace "Nace maka i want to be left alone, pls leave" Kallonta ya dinga yi after some seconds ya juya ya fita daga dakin..... Da yamma wajen karfe biyar Mayraah na zaune parlon Ammi tana tayata sorting out din kayan jarirai masu yawa da ta siyo weeks before Haseenah ta haihu, Maheer ya shigo parlon da sallama Ammi ta amsa tana kallonsa tace "Wai ka ma ci abinci kuwa" Yace "Eh na ci, za mu tafi gida ne yanzu..." Ammi ta kalli Mayraah tace "To bar shi kawai Mimi ki tashi ki shirya ku tafi, Bilkisu zata taya ni" Mayraah da lokaci daya mood dinta ya canza ta ajiye kayan hannunta a hankali amma bata tashi ba, Maheer na kallonta yace "Ina jiranki downstairs....." Daga haka ya juya ya fita, Ammi na kallonta tace "Ki tashi, kar kuma ki mance da sakon da Aunty Mariya ta aiko maki" A hankali Mayraah ta mike ta nufi kofa ta fita, dakinta ta tafi bayan ta shirya ta dau ledan da Bilkisu ta bata almost 4 days ago tace mata Aunty Mariya ce ta aiko mata da shi daga kaduna driver ya amso a park, whereas Ammi ce ta siya mata days before dawowan Maheer, Mayraah ta dau hand bag dinta kenan Ammi ta shigo dakin ganin ledan a hannunta tace "Nasan halin ki da mantuwa dama....." Dan murmushi kawai Mayraah tayi tace "Ban manta ba Ammi" downstairs suka sauka tare da Ammi, Maheer na zaune yana jiran ta a parlor, Mayraah ta karasa dakin da Haseenah take don yi ma Mama Ladi sallama, Mama Ladi tace "Ke da na zata kina nan har ayi suna, shi Masheer din ne yace ku tafi gida?" Haseenah ta daga kai da sauri tana kallon Mama Ladi, sai kuma ta kalli Mayraah da tayi shiru, Ammi ta karasa cikin dakin tace "Wa yace za ayi suna Mama, babu suna ai" Mama Ladi ta saki baki tana kallon Ammi, sai kuma a hankali tace "Ba suna kuma?" Ammi tace "Eh babu taron suna" Mayraah ta juya zata fita daga dakin suka kusa karo da Maheer da zai shigo, hade rai tayi ta koma gefe, ya shiga dakin yana kallonta ko kallonsa bata yi ba tayi ficewarta waje, Sallama yayi ma Mama Ladi shi ma, Mama Ladi tace "Yanzu gida za ku koma da Meran, maimakon ka bar ta har dai mu ga ko za a canza shawara ayi taron sunan, ita ma Meran naga yanda take wani lagwai lagwai da ita bata da wani kuzari Allah sa ita ma ba cikin ne da ita ba, ai sai hidimar ta maka yawo kana matashinka da kai" Sosai Haseenah taji gabanta ya fadi ta dinga kallon Mama Ladi jin abinda tace, me hakan ke nufi kenan? Ammi dai ta juya ta fita ganin zancen Mama Ladi ya fi karfinta, Maheer dai bai tanka Mama Ladi ba ya duba babies din dake bacci kan sabon gadonsu sannan ya fita daga dakin, Haseenah ta kasa controlling hawayen dake zuba idonta, juyawa tayi daga kwancen da take ta dau dankwalinta da sauri ta rufe fuskarta da shi hawaye masu zafi na zuba idonta, shkkn zargin da take tayi ya tabbata. Maheer na parking Mayraah ta sauka daga motar, ta nufi entrance din gida, bin bayanta yayi bayan ya kashe motar, ta koma gefe ta rungume hannunta fuskarta babu yabo babu fallasa, har ya bude kofar parlon ya shiga sannan ita ma ta shiga, rikota yayi ta fara kiciniyar kwace kanta amma ta kasa hakan ya sa ta fashe da kuka, ya kulle kofar Parlon, yana kallonta yace "Haba Mimi, ki gaya min laifi na pls" ganin yanda take kuka kuma ta ki basa amsa kawai ya lumshe ido ya rungumeta jikinsa zuciyarsa na bugawa, tun da ta fara nuna masa attitude a gida ya so shareta shi ma amma zuciyarsa ta kasa hakan this time around, baya jin zai iya sake share Mimi ko me zata masa, daga lkcn da tayi ignoring dinsa har zuwa sanda suka fito daga gidan rasa peace of mind dinsa yayi gaba daya, bai yi niyyar za su dawo gida yau ba don akwai alluran da zai ma babies din da ita kanta Haseenah amma sbda damuwar da ya shiga na sharesa da Mayraah take kawai ya gwammace su dawo gida, yana magana a hankali yace "In ma wani laifin na maki don Allah kiyi hakuri soul mate, kiyi hakuri plss" a hankali take kuka a jikinsa, ya karasa cikin parlon still yana rungume da ita ya zaunar da ita kan kujera ya zamo kasa on his knees yace "Don Allah kiyi hakuri Baby Gal" Jingina tayi da kujeran bata ce komai ba, ya mike ya zauna kusa da ita ya dago kanta yana kallon hawayen dake zuba idonta, kwantar da ita yayi kan kirjinsa a hankali yace "I am sorry Wifey" Lamo tayi jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, ya lumshe ido as if whispering yace "I missed you so much wife" He couldn't believe she said she misses him too, ya dago kanta suna kallon juna unlike before da bata iya kallon idonsa, nan da nan yaji ya rasa duk wani kuzarinsa, yayi kasa da murya yace "Sure?" Lumshe ido tayi ta gyada masa kai a hankali, rungumeta yayi so tight a jikinsa, ta lumshe ido tana shakar daddadan kamshinsa, after a while ya kai bakinsa kusa da kunnenta kamar me rada yace "You want your own baby tonight" Jin tayi shiru ya dago kanta yana kallonta, kai ta gyada masa, ya buda idonsa yace "We will definitely make babies today" Rufe fuskarta tayi kirjinsa, dai dai nan wayarta ya fara vibrate, shi ya ciro mata wayar a jaka ganin Aunty Mariya ke kiranta ya mika mata wayar.
[9/30, 9:14 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah na kitchen tana wanke plate din da suka fara cin abinci tare da Maheer tun bayan isha kafin ya fita, sun fara cin abincin kenan aka kirasa a waya ya fita, tunda ya fita kuma take zaune parlor ta kasa ci gaba da cin abincin, ta kusa awa uku zaune parlor da plate din abincin a gabanta bayan tafiyarsa, ita bata ci ba, bata kuma kai kitchen ba, daga karshe ganin it's almost 12 ta tafi da abincin kitchen ta zubar ta fara wanke plate din, shigowar motarsa da taji gidan yasa ta karasa dauraye plate din hannunta da sauri bayan ta ajiye a rack dinsa ta kashe wutan kitchen din sannan ta fita ta tafi dakinta, after entering her room ta kulle kofar ta karasa inda wayarta yake ta duba agogo taga karfe sha biyu saura minti goma, kashe wutan dakinta tayi ta kwanta kan gado ta rufe har kanta da duvet, bayan few minutes taji ya bude kofar dakin nata, kunna wutan dakin yayi yana kallon kan gadon, can ya karasa ya zauna gefenta ya cire duvet din jikinta a hankali yace "Mimi" Bata bude ido ba balle ta amsa masa, shiru yayi yana kallonta, ya kai fuskarsa kusa da nata still bata bude ido ba, after few seconds ya mayar mata da duvet din jikinta, yayi pecking forehead dinta sannan ya mike ya kashe mata wutan dakin ya fita ya kullo mata kofa, tana jin ya fita ta rufe fuskarta da pillow hawaye me zafi na sauka idonta, har kusan karfe dayan dare Mayraah bata iya tayi bacci ba, sosai taji zuciyarta na mata zafi, lkci lkci kuma sai taji hawaye na gangaro mata, daga karshe ta mike zaune a hankali tana goge idonta, sauka tayi daga kan gadon ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito, wajen karfe biyu da rabi ta jinginar da kanta da gado ta lumshe ido bayan ta idar da sallan da take yi, bude kofar dakin aka yi, sosai gabanta ya fadi ta bude ido amma bata juya ba har ya karaso inda take zaune kan darduma, dukawa yayi gabanta yana kallonta yace "Mimi" Ta dake ta kallesa amma bata ce komai ba, zaunawa yayi yana kallonta a hankali yace "Na dawo kin yi bacci" Ta sauke idonta trying hard not to