Showing 273001 words to 276000 words out of 456519 words
tace "Ohk, amma kasan Flight dina na komawa Kano bayan magrib ne zaka yi using motar Daddy kayi dropping dina airport nan da minti talatin" Musharraf yace "Toh" Kallon MD da ke ta kallon kiran ceo yayi, gaba daya he is absentminded don hankalinsa ma baya kan kiran kawai kallon screen din yake babu ko kiftawa tunaninsa na wani wajen daban, Musharraf ya karasa kusa da shi yace "Zan yi amfani da motar ka" Sae a nan MD ya dawo duniyar tunanin da ya tafi ya daga kai da sauri ya kallesa, sai kuma ya daga kiran Ceo kafin ya katse, sanar masa tayi ta shigo asibitin tana office he should meet her, bayan sun gama magana MD ya katse wayar ya dauko makullin motarsa ya mika ma Musharraf ba tare da ya kallesa ba, Musharraf ya amsa ya nufi kofa, Mami dake ta kallon MD tace "Daddy are you sure you're okay?" Ya mike da sauri yana feigning smile yace "Mami na gaji ne fa, bari in je our Ceo is around ita ta kirani yanzu" Mami tace "Ohk" Yana tafiya a hankali ya fita daga office din. Har ya isa Office din Ceo hankalinsa baya jikinsa, ya sameta tana waya, ya sunkuyar da kai ya jira har ta gama, sannan yayi mata sannu da zuwa da ladabi, ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa daga sama har kasa tace "Are you okay?" Ya gyada kai yana kirkiran murmushi yace "Sure Ma'am" Takarda ta dauka kan table dinta tayi rubuce rubuce sannan ta mika amsa tace "Magunguna da alluran da za a canza ma Mary Ann kenan, it should start from tomorrow morning pls" Ya amsa yace "Ok Ma'am" Tana kallonsa, bayan few seconds tace "You said the result will be ready today Aliyu" Yace "Sure Ma'am it's out, yana office dina ma..." Shiru tayi tana kallonsa, shi dai yana tsaye yana jiran next instruction da zata bada, Ajiye pen din hannunta tayi a hankali tace "Bring it to me" Yace "Alright Ma" Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. MD na komawa office dinsa ya zauna with confusion yana kallon Mami, calmly yace "But Mami ita wannan ai da iyayenta fa, har ma da yayyinta maza, warcen kuma ba cewa aka yi bata da iyaye bata da asali ba? Sannan ita wannan a nan Abuja suke zama...." Mami da ta ma rasa abinda zata ce masa tayi shiru tana kallonsa as if wanting to figure out something, ya girgiza kai yace "Gaskiya ina jin ko kamanni ne, ko kuma, kawai dai ba yarinyar bace....." He just realized he sounds stupid and he is not making any sense, ya kara girgiza kai ya mike ya dau envelope din result din genetic testing din da Ceo ta bada ayi, kofa ya nufa Mami ta bi sa da kallon mamaki har ya fita, yana komawa office din Ceo ya ajiye mata envelope din saman table yace "Here is it Ma'am" Kallon envelope din kawai Ceo take, yace "Is there anything again Ma'am?" A hankali tace "Just wait" Yace "Ohk Ma" Gefe ya koma ya tsaya, ta dau envelope din tayi unsealing dinsa gently ta ciro result din ciki, Shi dai MD kallonta kawai yake, Glasses dinta ta dauka ta saka sannan ta warware takardun tana dubawa, MD wondered why she was this nervous checking the result, ko da yake tace family issue ne, mikewa yaga tayi da sauri ta dafe table dinta, MD ya karaso da sauri kusa da table din yace "Is everything okay Ma'am?" Sai kuma yaga hawaye na sauka idonta ta cire glasses din idonta da sauri tace "I need privacy pls Aliyu" Yana kallonta yace "Alright Ma, take care pls" Daga haka ya nufi kofa yana waigota ya ga ta nufi dakin dake office din, shi dai ya fita ya kulle kofar, jingina yayi da bango ya lumshe ido zuciyarsa na wani irin bugawa, da kyar ya iya jan kafa ya bar wajen ya koma office dinsa, yana shiga office din Mami ta mike tace "Kar nayi missing Flight dina Daddy" a hankali yace "Okay Mami, Musharraf din ya dawo ne" Tace "Eh yana waje, mu je in fara masu sallama tukunna" Bai iya yace mata komai ba, suka koma ward din da Mayraah take, Mami ta karasa kusa da gadon Mayraah tace "Allah ya sauke Mayraah" Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, kallonta MD yake babu ko kiftawa, Mami ta ciro 50k a jakarta ta ajiye gefen Mayraah tace "A siya maki fruits" Ammi tace "Har da dawainiya Hajiya, zuwan kadai ma ai ya wadatar wallahi" Mama Ladi ta kalli Ammi da sauri tace "Kul, ba a maida hannun kyauta baya, godiya kawai za kiyi mata kice Allah ya kara arziki haka ake yi" Murmushi kawai Mami ke yi tace "Lallai kam Mama gwara dai da kika gaya mata" Cikin sanyin murya Ammi tace "To Allah ya saka da alkhairi Hajiya, mun gode kwarai da gaske, Allah ya bar zumunci" Mami tace "Ameen ya Allah, ita kuma Allah ya bata lafiya ya tsare gaba" Ammi tace "Ameen" Mayraah ta ɗan daga kai ta kalli MD da bai fasa kallonta ba suka hada ido, kauda kanta tayi da sauri, Ammi da Mama Ladi suka fita raka Mami, Usman dai sai kallon MD dake kallon Mayraah yake.
[8/22, 11:26 AM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Har bakin mota MD ya rako Maminsa, tun da suka fito asibitin Mami ce ke ta magana shi kam yayi shiru kansa a kasa yana biye da ita ba tare da yasan ma me take cewa ba, bayan Mami ta bude back seat tana kallonsa tace "Take care of ur self Daddy" Yayi murmushin karfin hali yace "Sure Mami, Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka ya juya ta bi sa da ido har ya shiga cikin asibitin, gaba daya ta kasa gane dalilin wannan sanyin da jikinsa yayi lokaci daya, let it not be what she is thinking fa, tunanin hakan yasa taji hankalinta ya tashi, a sanyaye ta shiga bayan motar tana kallon Musharraf, sai da suka kusa Airport Mami tace "Where will u be spending the night Musharraf?" Yace "Hotel" Mami tace "Aa, kaje gidan yayanka.... kuma bana son musu" Musharraf ya kalleta ta madubi yace "Kin fa san halinsa Mami baya son sharing komai nasa da kowa, kawai bata min rai zai dinga yi mu samu issues a gidan nan, ni kuma i don't want to have any issues with him, " Mami tace "Baza dai kayi abinda nace ba kenan" Musharraf yace "To na ji" Mami tace "Yaushe zaka dawo?" Idonsa na kan titi yace "Ko gobe da safe in sha Allah" Mami tayi kasa da murya a hankali tace "Plss Musharraf bana son ka kara zura jiki zuwan ka Abujan nan don Allah, kaga u are yet to recover fully, kar kaje ka kara shiga wani damuwar bazan ji dadin hakan ba, you know what u went through da yanda ka fita hayyacin ka for the past few months, banda ma rashin lafiya ne kaga da bazan bari ka taho Abuja ba har ma in biyo ka, infact i will prevent anything da zai sake hada ka da yarinyar, amma rashin lafiya ya wuce komai, kuma dukkanmu musulmai ne..." Musharraf ya ɗan yi murmushin karfin hali a hankali yace "Mami ni yanzu tsakanina da Mayraah ai sai zumunci, i gave up long ago cause babu hope din aure tsakanina da ita, ta riga da ta min nisa, and with the way things are going bana tunanin za a bari outsider ya aureta, sai ki ga kilan daya daga brothers dinta za a hadata aure da tunda da aure tsakaninsu, so i will keep on nurturing my heart to forget about everything, in kuma rabona ce ita baxan ce bazan aureta ba i will gladly get married to her, amma da kamar wuya" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Na ji dadin da ka fahimci haka, Allah Ubangiji yayi maka zabi mafi Alkhairi a rayuwar ka, idan ma ita din ce Allah ya baka ita cikin ruwan sanyi, in ko akasin haka Allah ya baka warce ta fi ta" A hankali Musharraf yace "Ameen" MD na komawa office dinsa ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi duk ya rasa tunanin da zai yi, it was something he never saw coming, bude kofar aka yi ya dago da sauri, Dr Khalil ya shigo ya karaso gaban table dinsa yana kallonsa yace "Are you okay?" MD ya mike yace "Sure... Pls akwai patient ward 5, ka ɗan dubasa zan je office din Ceo ne" Dr Khalil yace "Ohk...." Juyawa yayi ya fita, MD ya dawo kan sofa din office din ya zauna ya tallabi chin dinsa, ya fi minti sha biyar zaune a haka, daga karshe ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa yana tafiya a hankali har ya fita ya kulle office dinsa, yana isa office din Ceo yayi knocking gently, sau uku yayi knocking din jin bata yi responding ba ya juya ya bar wajen kawai... Dab da Magrib Musharraf ya shigo dakin da Mayraah take, ya ajiye fruits da ya siyo mata, Umar kadai ne dakin sai Ammi, Ammi na kallonsa tace "Sannu da kokari Musharraf" Mayraah dai na rungume jikin Ammi tana bin sa da kallo, Ammi tace "Idan anyi sallah sai ku tafi can gida da Omar ka ci abinci" Musharraf da ya koma kusa da window ya tsaya yayi murmushi a hankali yace "I am okay Ammi" Ammi tace "Aa don Allah kaje gida ku ci abinci" Bai sake ce mata komai ba, ana kiran sallah shi da Umar suka fita zuwa masallacin dake cikin asibitin, ana idar da sallah Musharraf ya fita daga masallacin tun kan Umar ya mike, duk don kar yaje gidan cin abinci. Bayan Magrib MD na office dinsa ya daura forehead dinsa saman table ya ji wayar sa na vibrate, a hankali ya dago ya ga Ceo ce ke kiran sa, dagawa yayi tace ya sameta office, yace "Ohk Ma'am" Katse wayar yayi ya ajiye, sannan ya mike ya bar office dinsa, har ya iso office dinta he was absentminded don tafiya kawai yake tunaninsa na wani wajen daban, gently yayi knocking kofar sai da ta masa izini sannan ya shiga, yana isa bakin table din office din ya tsaya, bata yarda ta hada ido da shi ba duk da har sannan glasses na idonta but he could see how swollen her eyes were alamar ta yi kuka sosai, tace "Pls idan dad din Mary Ann ya zo ka kawosa office dina, i want to speak with him" MD yace "Ohk Ma'am" Daga haka ya juya ya fita wondering why she wants to speak to him directly, on a norms in ma wani bayani ne shi zata sanar ma ya gaya masa amma ba wai tace a kawosa office dinta ba, ba kasafai ake zuwa office dinta ba sai in baƙi tayi, downstairs ya tafi zuwa dakin da Mayraah take, bayan yayi sallama ya shiga, Ammi da Usman ne kadai dakin Mayraah na shan fruits din da Musharraf ya siyo mata a hankali don har sannan kirjinta na mata zafi da ciwo, Ammi na kallon MD tace "Hajiya ta isa kanon kuwa Doctor" MD yace "Aa basu sauka ba" Ammi tace "To Allah ya kai su lafiya" Yace "Ameen" Kallon Mayraah yayi, ita dai kanta na kasa tana shan fruits din gabanta, Ammi tace "Kaga jikin Alhamdulillah yau har tana shan kayan marmarin da kanta" MD yace "Haka ne... Sun shigo yi mata alluran?" Ammi tace "Eh nurse din ta shigo da taga tana shan fruits din sai tace zata dawo..." MD yace "Ohk, Alhajin zai shigo yau?" Ammi tace "Yana ma hanya yanxu" MD yace "Ohk, Ceo ke son ganinsa" Ammi tace "To yana shigowa zan gaya masa in sha Allah, dama dazu da safe yake maganar Bill, tun da har yanzu ko deposit ba a ajiye ba...." MD ya ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips, shi dai Usman bai kalli direction dinsu ba danna wayarsa kawai yake, MD ya juya ya fita daga ward din, yana fita ba dadewa Abba ya shigo, bayan ya ajiye ledan hannunsa yana kallon Mayraah yace "Ya jikin?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Da sauki" Abba yace "Maa sha Allah, gashi har ana jin maganar taki ba kamar dazu da safe ba" Mayraah ta ɗan yi murmushi, Abba ya juya ya kalli Ammi yace "Ki sameni waje za mu yi magana" Mikewa tayi ta bi sa suka fita corridor din dakin, Abba na kallonta yace "Wa ya kira yaron nan zuwa asibitin nan?" Ammi tace "Wani yaro?" Yace "Wanda na gani zaune reception" Ammi tayi kasa da murya bayan ta gano wanda yake nufi tace "Wai Musharraf? Dubiya kawai ya zo yi yallabai" Abba ya wani hade rai yace "What for? Sannan wa ya gaya masa bata da lafiya har ya zo Dubiya?" Ammi da jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, a fusace Abba yace "Am asking wa ya gaya masa bata da lafiya har ya zo asibitin" A hankali Ammi tace "Maheer ne ya kirasa saboda hankalinta ya kwanta, dazu da safe ta dinga cewa a kira mata shi ta nemi yafiya, kasan in mutum na jin jiki babu abinda bazai zo ransa ba...." Abba ya dakatar da ita yace "Can u hear ur self speaking? For what reason za ku yanke hukunci ba tare da sanina ba, shi bashi da hankali ne Maheer din da zai kirasa? ko ya manta rashin mutunci da tijaran da suka yi mana a police station ne?" Ammi tace "Aa yallabai ku ka yi ma juna dai, kar ka manta mu fa musulmai ne, meye amfanin keeping grudges, ai ba haka addininmu ya koyar da mu ba, beside don ya zo dubata naga ba laifi bane sannan tare ma da mahaifiyarsa suka zo wallahi har ta ba Mimi 50k, to meye laifinsu? Kar fa ka manta ku kuka fara saka yan sanda suyi arresting yaron, to tunda har suka iya mance hakan su zo har Abuja dubiya daga kano don me mu ma baza mu manta ba?" Cikin fada Abba yace "Ohh haka kike gani ko? To wallahi idan wani abu ya kara billowa ke zan yi blaming, shi kuma Maheer banda bashi da tunani sam ko ita tace a kira mata yaron sai ya kira, inda Usman ya fi sa kenan don nasan da shi ne bazai kirasa ba wallahi, ana ƙoƙarin yarinya ta mance sa completely a rayuwarta shine ku ke kara gayyato mata shi, iyayen yaron nan su ne root din duk abinda ke faruwa da ita a yanzu" Ammi tace "To dai wannan MDn dake tsaye kanta ba dare ba rana yayan Musharraf din ne, uwarsu daya ubansu daya, sai mu yi yaya kenan?" Kallonta Abba ya tsaya yi baya ko kiftawa, bayan few seconds yace "Yayan Musharraf kuma? How?" Ammi tace "Mu ma duk haka muka yi mamaki kamar yanda ka yi, yayansa ne uwarsu daya ubansu daya" Shiru Abba yayi alamar he is completely speechless, Ammi tace "Atoh, kuma kai kanka ka fadi kirkinsa, dubi fa duk da matsayinsa na MD yanda yake mana a asibitin nan, yanzu ma bai dade da fita ba ma ka shigo, wai CEO dinsu na son magana da kai, kilan maganar Bill dinsu ne...." Abba ya sauke ajiyar zuciya bai sake cewa komai ba, Ammi ta juya ta koma cikin ward din, Office din Dr Khalil Abba ya tafi, Dr Khalil dake shirin zai tafi gida don ba shi da night shift ya gaida Abba da ladabi, Bayan Abba ya amsa yace "Pls Dr kayi min magana da MD wai yana nemana" Dr Khalil yace "Ohk to bari in duba ko yana office" Fita Dr Khalil yayi ya tafi office din MD, zaune ya gansa a kan office chair dinsa da cup din coffee a gabansa ya jinginar da kansa da kujeran idonsa a lumshe, yana jin an bude kofa ya bude ido a hankali, Dr Khalil ya karasa yace "Wai lafiyarka kuwa duk na ganka wani iri, in dai Mayraah ce naga fa har magana ta fara bawan Allah" MD yace "Ban gane ba" Dr Khalil yayi wani dariya yace "Dama ina ta son sai ta samu sauki in maka tambayoyin nan dake cunkushe a raina sun hanani sukuni....." MD yace "Tambayar me?" Dr Khalil na murmushi yace "Ko da yake da sauran time, ba yanzu ya kamata in maka tambayar ba" Ko kallonsa MD bai sake yi ba, ya matsar da coffee din gabansa, Dr Khalil yace "Dad dinta ne ya zo office dina wai kace kana nemansa" MD yace "Yea, bari in fara ma Ceo magana, ita ce ke nemansa" Daga haka ya mike yana tafiya a hankali Dr Khalil dai ya bi sa da kallo. Abba na zaune office din Dr Khalil MD ya shigo bayan ya gaishesa yace "Tana office dinta zaka sameta a can Sir" Abba ya mike yace "Ohk then" MD yayi leading dinsa har zuwa office din Ceo, bayan yayi knocking ya bude masa kofa, Abba ya shiga MD ya kullo kofar sannan ya bar wajen, Zaunawa Abba yayi saman kujera yana gaisheta, a hankali ta amsa, Abba yace "Ya kokari kuma? Dazu da safe nake Allah Allah in tambayi Bill dinmu sai kuma wani uzurin ya taso min naje kano, dawowata kenan aka sanar kina nemana" Ceo ta gyada kai, bata bari sun hada ido da shi ba duk da dai glass na idonta speaking calmly tace "Pls birth certificate din daughter din ka nake tambaya da garin da aka haifeta...." Abba yayi shiru yana kallonta ita dai bata bari ta hada ido da shi ba, ta dinga kauda takardun kan table dinta, Abba yace "Ai ranki shi dade wannan sai dai in tambayi me dakina, don na mance ko an mata ko ba ayi ba gaskiya...." Ceo tace "To ko zaka tambayeta sai ka dawo yanzu ina jiran ka" Abba yace "Sure, right away" Mikewa yayi ya nufi kofa ta bi sa