Showing 312001 words to 315000 words out of 456519 words

Chapter 105 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70575

tayi tana murmushi tace "Thank you" Yace "Ya kika baro yan can gidan?" Tace "Suna gaisheku" Yace "Muna amsawa" Tafiya ta fara yi zuwa main entrance din gidan ta bar masu kayan nata gaba daya, tana isa kofar shiga Parlon ta bude a hankali sannan ta shiga da sallama, Maheer ne kwance 3 seater a parlon yana kallon kwallo, yana jin sallamarta ya kulle ido as if yana bacci, ta gefen ido take kallonsa da ta shigo parlon can ta dauke idonta har ta fara tafi hanyar staircase sai kuma ta juya ta kallesa sake rufe idonsa yayi ruff kamar me bacci, juyawa tayi bayan komai yayi escaping mind dinta, lkci daya ta koma cikin parlon ta zagaya ta inda kansa yake ta sakalo kanta tana kallonsa a hankali tace "Stop pretending Yaya" Still dai bai bude ido ba, dukawa tayi ta kai fuskarta dai dai nasa har yana jiyo saukan numfashinta tace "Allah nasan ba bacci kake ba da yamman nan" A hankali ya bude ido suka yi ido hudu da shi, a gigice suka ji muryar Mama Ladi da ta fito daga kitchen da kwanonta cike da shinkafa da miya tace "Auzubillahi ni Ladi, sumbatar sa kike Mera?" Mayraah ta dago kanta da sauri ta tashi tsaye, shi kuma ya mike zaune, Mama Ladi dai ta saki baki tana kallonsu da idanuwanta kamar za su fito alamar ta gigice, Can tace "Usuman wallahi tallahi abinda na gani kenan, kai in na masu sharri kar Allah ya bani cin gobe da na jibi, ashe kai ma dai kana tsaye jikin kofa kana kallon ikon Allah, ace gubar lafiya Mera ta ci?? Sumbatarsa fa take, Aa ba ruwana wallahi" Mayraah ta juya da sauri ta kalli bakin kofa taga Usman dake dariya har ya juya ya fita daga parlon ya bar mata kayanta a bakin kofar, Mayraah ta maida dubanta kan Mama Ladi da sauri ta marairaice tace "Sumbata kuma Mama? Wallahi kawai...." Mama Ladi taki tsayawa balle ta saurareta irin taga abinda ya fi karfinta din nan tayi hanyar stairs kawai da sauri, Mayraah ta kalli Maheer hankali a tashe kamar zata yi kuka tace "Yaya shine zaka yi shiru?" Ya gyara zama yace "Nima ba farkawa nayi naga kamar kina hakan ba"
[9/8, 2:27 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer yayi murmushi ganin how shock Mayraah was looking at him, ya dan buda idonsa yace "To ke me zai dameki? Ko dai kin yin ne gaya min gaskiya Mimi...." Ko kallonsa bata sake yi ba ta juya ta nufi stairs da sauri, ya bi ta da kallo yace "Mimi" Juyowa tayi tana kallonsa, ganin yanda yanayinta ya canza ya mike yana kallonta da mamaki yace "Kuka za ki yi?" Kawai ta fashe da kuka kamar jira take , ya buda baki sai kuma ya nufeta da sauri yace "C'mon Mimi, wasa fa Mama Ladi ke maki, ke baki san wasa ba" Cikin kuka tace "Wallahi ba wasa take ba she was very serious kuma kayi shiru kana kallonta, yanzu zata je ta dinga ta fada a gidan nan, what if Ya Usman ma ya yarda da abinda tace" Sai ta kara rushewa da kuka, dariya sosai ta basa sai dai bai yi ba ya kamo hannunta yace "To yi hakuri Mimi" Tana goge hawayen idonta tace "Ni dai mu je kace mata ba haka bane" Yace "Me zan ce mata ba haka bane?" Ta masa wani kallo, yayi keeping serious face yace "Tell me mana" kwace hannunta tayi zata bar wajen ya sake rikota yace "Toh mu je in gaya mata kema sai ki sake mata bayani da kanki" Stairs suka nufa tare yana kallonta ganin da gaske ita hankalinta fa ya tashi, murmushi yayi har suka haura sama zuwa dakin da Mama Ladi take, ba a rufe kofar dakin sosai ba Mayraah taji muryar Mama Ladi tana cewa "Wallahi wallahi idan na masu sharri Ammi kar Allah ya ban ikon cin abincin nan lafiya, ni na fito kitchen kenan shi kuma wannan mutumi Usman ya shigo parlon, tsabar yanda shi ma ya gigice wllh sai makalewa yayi jikin kofa ya kasa shigowa, to in son Mashir din take uban me kuma ake jira? Magana ta gaskiya fa tunda Mera ta ci guba ta fara fin karfin mu a gidan nan, dama guban har da iskanci yake sakawa ko dai irin wanda ita ta ci ne hka?" Mayraah da wasu hawayen suka cika idonta ta juya tana kallon Maheer da ya juya mata baya nan kuwa kokarin danne dariyarsa yake, juyawa tayi ta bar wajen ta nufi dakinta da sauri, bin bayanta yayi har zuwa dakin nata, Mama Ladi na fifita da dankwalinta tace "A gaskiya ba ruwana, naga ma kamar kun mayar da ni ban san abinda na gani nake fada ba duk kun min shiru ga Ladi er iska, shi fa Mashir din nan dama can ya taba aure, sarai yasan meye aure, idan ta ci gaba da yi masa haka wataran biyeta zai yi barin an fasa masu kwan cewar ba muharramarsa bace, lamari ne kawai zai lalace daga ni har ku mu shiga uku, mu kuma kenan ace pamilyn mu daga wannan sai wannan, to ko dai iyayen nata da suka jefar da ita cikin kwata sun hada jibi da turawa ne, kunsan su basu dau Sumbata a bakin komai ba da yake kafurai ne" Ammi dai idonta na kan TV dake aiki Aunty Mariya kuwa danna wayarta kawai take kanta a kasa, Mama Ladi tayi kwafa ta jawo abincinta ta fara ci. Maheer ya kulle kofar dakin yana kallon Mayraah da ta zauna gefen gadonta ta hade kai da pillow tana rusa kuka, karasawa yayi ya zauna kusa da ita ya dagota yace "Ke fa bush gal ce Mimi" Cikin kuka sosai tace "Su Ammi fa taje tana gaya ma yaya, wayyo Allahna na shiga uku" Shi dai kallon bakinta kawai yake, can ya sauke idonsa a hankali yace "Kiyi hakuri, zan je in ce masu bayanin ba haka bane" Yana fadin haka ya fara goge mata idonta da hannunsa yace "It's okay lil sis" Ta daura kanta a shoulder dinsa tana sheshekar kuka, yayi kasa da murya yace "Baza ki daina kukan ba?" Cikin rawan murya tace "Yaya sharri fa ta min" patting bayanta yayi yana murmushi yace "Ai duk mun sani" Sai da yaga ta daina kukan gaba daya sannan ya dago kanta yace "Let me go and meet them" Gyada masa kai tayi a hankali, ya mike ya nufi kofa ya fita daga dakin ya kulle mata kofar, downstairs ya sauka yana murmushi ya tafi ya ci gaba da zamansa a parlon. Mayraah dake ta zaune dakinta har wajen karfe shidda saura ta kasa fitowa balle taje ta gaida Ammi, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri, Ammi ce ta shigo dakin Mayraah ta kasa kallonta har ta karaso cikin dakin, bata taba jin kunyan Ammin nata ba irin yau, Ammi ta zauna gefenta ta dafa kanta tace "Dota kin dawo shine kika yi zamanki a daki?" Mayraah dai ta kasa dago kai ta fara kame kame, Ammi dake ta kallonta can kasan ranta kuma sai ta fara tunanin to ko dai abinda Mama Ladi ta fada haka ne don ita ko da wasa bata yarda da zancen Mama Ladi ba amma reaction din Mayraah ya sa ta fara zargin ko dai haka ne, Ammi tace "Ya kika baro yan can gidan?" Mayraah tace "Sun ce in gaishe ku" Ammi ta dan yi murmushi tace "To muna amsawa bari in je kitchen Abbanku na hanya yau" Ita dai Mayraah bata ce komai ba Ammi ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo, sosai Ammi tayi mamakin jin Mayraah bata ce bari ta zo ta taya ta ba as usual, though notice she is so uncomfortable. Maheer ya bi Ammi da kallo bayan ta sauko downstairs, ita dai kallo daya tayi masa tayi hanyar kitchen, yace "Ammi kuyi ignoring din Mama Ladi kema kin san kawai sharrin ta ne fa" Ammi dai ta tabe baki bata kallesa ba balle ta ce komai ta yi shigewarta kitchen. Bayan magrib Maheer yayi mamaki ganin Mayraah bata fito daki ba har sannan, sama ya tafi ya bude kofar dakinta ya ganta zaune saman darduma ya karasa ya zauna gefen gado yace "Baki sakko kin ci abinci ba Mimi" Tace "Aunty Bilkisu ta kawo min ai" Tana fadin haka ta nuna masa abincin, whereas Ammi ce ta sa Bilkisu ta kai mata abincin har dakin ganin taki fitowa, Maheer yace "Ohk then" mikewa yayi ya fita daga dakin. Karfe tara Mayraah tayi plugging wayarta a caji zata kwanta kenan aka yi knocking kofar dakin, ta kalli kofar sannan ta karasa ta bude a hankali, Usman ta gani tsaye ta sunkuyar da kai, yace "Ke baki san Abba ya dawo bane, ko zuwa zai yi ya gaisheki?" Ta daga kai tana kallonsa sai kuma ta marairaice tace "Yaya kaga abinda Mama Ladi ta min ko?" Da mamaki yace "Me ta maki?" Kamar zata yi kuka tace "Kana wajen fa" Ya ɗan buda ido yace "Ohh that? Kin san an taba mata aiki a ido har sau uku, probably it's making her to see things very close to each other" trying hard not to laugh ya karasa maganar keeping a serious face, Mayraah ta zaro ido tace "Da gaske" Yace "Go and greet Abba" Daga haka ya bar bakin kofar, Mayraah ta dau hijab dinta har kasa ta saka sannan ta fita zuwa bangaren Abba... A hankali ta bude kofar bayan tayi sallama ta shiga, Ammi da Abba ne kadai zaune parlon, ta karasa ta zauna saman carpet ta gaida Abba, Abba yace "How are you dear, kin dawo lafiya?" A hankali Mayraah tace "Alhamdulillah Abba, sun ce suna gaishe ku" Abba yace "To maa sha Allah" Ita dai Ammi kallon Mayraah da kanta ke kasa kawai take, Bayan some seconds Abba yace "Gobe yan Kaduna za su iso in sha Allah" Sai da gaban Mayraah ya fadi duk da tasan goben za su zo amma tana ta kauda tunanin hakan a ranta, still dai bata dago kanta ba kuma bata ce komai ba, Calmly Abba yace "Do you have anything u want to discuss with us daughter akan batun aurenki da Musharraf? Feel free ki fadi duk abinda ke ranki kin ji" Mayraah tayi murmushin karfin hali ta girgiza kai a hankali tace "Aa babu komai Abba" Abba yace "Are you sure ba wani abu Mimi?" Ta gyada masa kai, ita dai bazata taɓa cewa ga yanda suka yi da Musharraf a waya ba, he should speak for himself that tomorrow, or his relatives should speak for him, amma ita kam bazata ce komai ba, Abba ya katse mata tunaninta yace "Toh shikenan Daughter, we pray it's the best for you in sha Allah" Ita dai kanta na kasa, Abba yace "You can leave, Allah ya maki albarka" Da kyar tace "Ameen" Daga haka ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ammi ta bi ta da kallo hawaye cike idonta har ta fita, Abba na kallon Ammi bayan Mayraah ta fita yace "Look Madam, bana son kowa yayi kokarin canza mata ra'ayinta in anyway, nasan ki, nafi kowa saninki, nasan this isn't ur wish for Mayraah saboda wani dalilinki na daban a ranki, adalcin da za mu yi ma yarinyar nan bai wuce supporting dinta ta auri heart desire dinta ba bayan duk abinda ta fuskanta a watannin baya, shirun da tayi yanzu yana nuni da she still loves him and want to be with him, beside yaron nan ni dake mun shaida yana sonta, so na tsakani da Allah, wanda duk abubuwan da suka faru a baya shi bai gujeta ba dai dai da rana daya, don haka laifin iyayensa bai kamata ya shafesa ba in anyway, sannan so far so good yaro ne shi nutsattse ga hankali, muna kuma da yakinin zai rike mana ita da amana duba da irin son da yake mata, ina ce wannan shine babban burin ko wasu iyaye a kan er su idan aurenta ya tashi? and beside ga yanda Allah yayi lamarinsa shi Musharraf din ma ɗan uwanta ne na jini, don haka mu yi masu fatan alkhairi kawai, i think that's all" Ammi ta share hawayen dake zuba idonta tace "Amma kuma kayi saurin judging dina Yallabai, ko last week da muka yi magana da Mariya na gaya mata farin cikin Mayraah shi ne nawa, don haka ni bazan tauyeta ba, babu wanda zai canza mata ra'ayi" Abba yace "Better, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu baki daya... Da can ba Musharraf din muka yarje mata ta aura ba banda ƙaddarar da ta gifta, so now also we should support her, yaron nan ba laifinsa bane, Ko ke a shekarun baya kin taɓa tunanin hada auren Mayraah da daya daga cikin yaranki?" Ammi ta ɗan yi murmushin karfin hali ta girgiza masa kai tace "Ban taɓa ba gaskiya, don a sannan they are all same a cikin zuciyata" Abba yace "Ohh yanzu they are not same kenan?" Ta fashe da kuka tana kallonsa tace "This i never bargained for, yanzu ba ni daya ke da Mayraah ba i have to accept that, an riga da an dasa min a rai cewar rikonta kawai nayi ban haifeta ba wanda a baya ban taɓa mata kallon warce nake riko ba, a yanzu ba tawa bace ita ni kadai, Gradually kuma zata koma gun righful owner dinta, ni da ita dama sai dai hange daga nesa" Abba yace "Ke kike ganin haka har ya tsaya maki a rai" Ammi bata sake ce masa komai ba ta mike tana goge idonta ta fita daga parlon Abba ya bi ta da kallo yana jin tausayinta har ransa... Aunty Mariya na zaune dakin Usman tana kallonsa tace "Don girman Allah ka ajiye wannan laptop din magana nake maka Barrister" Ya mayar da laptop din gefe yace "Aunty na fa ce maki let leave Mayraah, i don't want it to look like mu muka canza mata ra'ayi muka sa ta yin abinda bata yi niyya ba a ranta, let just pray this is just the best, Mayraah is not a kid, kuma da Ammi ta saka a rai cewar tana aure zata mata nisa dama ai shi aure babu inda baya kai mutum, ya kai mutum kasar waje ma balle just within Nigeria, i believe Mimi bazata mance halacci ba that is just it, at the end of the day ma ni sai nayi regretting me yasa nayi mata maganar da kika ce, even the Dr da na samesa da maganar maida ni clown yayi a compound" Aunty Mariya tace "Clown as in how?" Usman na kallonta yace "He isn't taking me or the issue serious, kamar it's funny to him wai taya don Mayraah tayi aure far away zata mance Ammi, daga karshe kuma yace min shi bai ma kawo wannan tunanin a rai ba, kinga ni da ke ne kawai muka kawo hakan a rai, shi yasa kawai naga mu bar ta with her choice, mun ma yi magana da Abba shi ma yace min haka...." Aunty Mariya tace "To ai shikenan, Allah ya sa hakan shine mafi Alkhairi gare mu baki daya" Yace "Ameen, ai Musharraf din na sonta har yanzu, ita ma haka, that is the most important of all" Jawo laptop dinsa yayi ya ci gaba da abinda yake, Aunty Mariya ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo masa kofar. Washegari tun sassafe Aunty Mariya da Ammi da Bilkisu suka shiga kitchen domin fara girkin varieties na abincin da za su tari grandparent din Mayraah da shi, Mama Ladi na zaune kan kujeran dinning a bakin kofar kitchen din tace "Ai in kun kula tun jiya wasan er buya take da ni a gidan...." Aunty Mariya ta juya tana kallonta tace "Don girman Allah ki rufa mana asiri da wannan maganar da yaki ci yaki cinyewa tun jiya Mama Ladi, kuma ni wallahi tallahi nasan ba haka bane kece kilan dai kika juya lamarin a haka" Mama Ladi ta saki baki tana kallonta, can tace "Toh ki hutasshe da kanki ki ce min Ladi makaryaciya mana Mariya" Aunty Mariya dai ta ci gaba da abinda take, kilan in ba haka ta ma Mama Ladi ba wannan magana bazai taɓa mutuwa ba har Abba sai ta iya cewa zata gaya masa, don dai babu yanda za su yi da ita ne amma ita wallai bata so ma ace tana gidan Grandparent din Mayraah da iyayenta za su zo ba kar taje ta kunyata mutane kawai, Mama Ladi tace "Mutuniyar banza kawai da na haihu ai 'ya yana baza su zuba maki ido kina min wannan fitsara haka ba, ko da yake kema din dai gashi har yau shiru shekara sha uku da aure, haka nan lokacin bikin Mashir kika ce a koreni ga Ladin kauye ta zo biki...." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta kalli Bilkisu tace "Bilki kije in da wani abu zan kira ki" Bilkisu tace "To Hajiya" Daga haka ta fita daga kitchen din, Ammi ta kalli Mama Ladi cikin kwantar da murya tace "Don Allah kiyi hakuri ki rabu da Mariya Mama Ladi, baki ma tambayi wasu baƙin za mu yi ba yau muke ta girke girke" Mama Ladi tace "Yo shawara ku ke da ni da zan tambayi wasu baƙi za ayi ku gwaleni, kawai don ni Allah bai taɓa bani haihuwa ba sai in zama banza a gidan duniya...." Ammi na ɗan murmushi tace "Haba Mama Ladi, ai ke uwar mu ce halaq malaq, To iyayen Mayraah ne za su zo yau, dama so nayi ki ga hakan a ba zata shi sa nake ta boye maki" Mama Ladi ta saki baki tace "Iyayen Mera kuma? Su waye iyayen Mera da na sani banda ku?" A hankali Ammi tace "Iyayenta na asali da suka haifeta, dalilin tafiyar mu kaduna kenan satin da ya wuce, dama cewa nayi kawai sai dai

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login