Showing 405001 words to 408000 words out of 456519 words

Chapter 136 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70664

da Mama Ladi ta idar da sallahn ita ma, Ammi ta nufi Maheer da ya bude idonsa da ya kada sosai, kasa karasawa Ammi tayi kusa da shi, a hankali ya zauna kan carpet har sannan yana rungume da yaran yana kallon Ammi, da kyar Ammi ta iya cewa "Ka basa maganin ne?" Ya girgiza mata kai cikin karfin hali yace "Ya rasu" karaf a kunnen Mama Ladi da ta jefar da darduman hannunta ta kwala wani ihu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, ya rasu fa kace Mashir?" A gigice Haseenah ta shigo dakin jin Mama Ladi na furta rasuwa, daura hannu tayi a ka ta kwala wani uban ihu jikinta na rawa ta nufi Maheer da gudu ta durkusa gabansa tana kokarin amsan Aymaan dake hannunsa, turata yayi daga kusa da shi yana kallonta da idanuwansa da suka yi ja, A hankali Ammi ta zauna gefen gado hawaye na sauka idonta tana kallon Aymaan dake jikin Maheer ya rungumesa har sannan. Duk da kukan da Mama Ladi ke rusawa hakan bai hanata yi ma Haseenah koran kare daga dakin Ammi ba don Charger wayar Ammi ta dauka ta dinga tsula mata tana cewa "Fita ki bamu waje kin kashe daya hankalinki ya kwanta" Haseenah dawowa tayi kamar warce aka kwance ma nut daya a kai ko jin dukan da Mama Ladi ke mata bata yi, Bilkisu ta shigo dakin a gigice jin ihun Haseenah da muryar Mama Ladi dake rusa kuka, Mama Ladi na ganin Bilkisu tace "Ja ta ki yi mana waje da ita Balkisu ta kashe mana yaro daya saura daya, ja ta ku fita ta bamu waje mu yi kukan mu cikin nutsuwa...." A haka Bilkisu ta kama Haseenah da ta dawo kamar mahaukaciya ta fitar da ita daga dakin, Ammi na kallon Maheer da kansa ke a kasa, hawaye na zuba idonta a hankali tace "Kayi hakuri, Allah ya sa me ceto ne, Allah ya raya mana ɗan uwansa" Shi dai Maheer bai dago kansa ba har sannan gawar Aymaan na rungume jikinsa, Ammi ta dauko Aryaan ta rungumesa tana bude ledan magungunan da Maheer ya shigo da shi zata basa, Usman ne ya shigo dakin da sauri ya nufi gun Maheer, Mama Ladi ta kara rushewa da kuka tace "Mun rasa daya daga yan biyun Usuman, ta kashe mana daya sauranmu daya, ba don ba don ba sai ince kai da Mamuda ne ku ka ja mana" Usman ya duka gaban Maheer yana kallon yaron hannunsa, shi dai Maheer bai dago kansa ba....
Wajen karfe goma Ammi na parlonta ta goya Aryaan, Abba bai dade da barin parlon ba ya koma bangaren sa, Mama Ladi dai na zaune kan carpet ta rafka uban tagumi sai gyangyadi take zubawa, hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar Usman ya kori Haseenah daga gidan, da kanta kuma ta jaddada ma masu gadi kar su bari ta shigo gidan, hakan yasa Haseenah ta makale a gate din gidan tana kuka kamar ranta zai fita, Maheer na zaune kan kujera ya jinginar da kansa da kujeran, Usman dake ta tsaye parlon ya juya kawai ya fita, Ammi ta juya ta kalli Maheer a hankali tace "Maheer ka tashi ka tafi gida dare yayi ga Mayraah ita kadai a gidan" Mama Ladi ta daga kai ta kalli Ammi da sauri tace "Ya tafi wani gidan? ba gwara ya tsaya ya sa ma dayan da ya rage mana ido ba, kina gani shi ma sai da yayi tafiyar ruwan nan a hannun Mamuda dazu" Ammi na kallon Mama Ladi tace "Naga jikin nasa ba zafi yanzu, kuma ai har abinci ya sha, gashi kuma yana bacci" Mama Ladi tace "Duk da haka ni dai ba ruwana, kamata yayi yaje gidan ya dauko Meran su dawo nan tare mu yi zaman makokin mu cikin kwanciyar hankali" Mama Ladi ta kalli Maheer tace "Ka gaya mata rasuwan ma kuwa?" Maheer ya girgiza mata kai, Mama Ladi tace "Gwara haka, kar ka gaya mata ka daga mata hankali ita daya a gida, ke kuma Ammi da kike cewa an bar ta ita kadai a gida in yana da aikin dare a asibiti ba ita kadai take kwana gidan ba dama" Ammi bata sake cewa komai ba, Mikewa Maheer yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon Ammi ta bi sa da kallo cike da tausayinsa, Maheer na shiga dakinsa ya dau wayarsa yayi dialing number Mayraah, har ya katse bata daga ba, ya ajiye wayar a hankali gefensa ya jingina da pillow, yana ta zaune a haka wajen karfe sha daya Ammi ta shigo dakin, har sannan Aryaan na goye a bayanta, tana kallonsa tace "Maheer baka samu ka ci abinci ba fa, bari in kawo maka shayi" Tana fadin haka ta fita daga dakin ta tafi kitchen ta hado masa shayi ta kawo masa, ya amsa yana kallonta yace "Nagode" Ammi ta zauna edge din gadon, shayin ya fara sha, Ammi na kallonsa tayi kasa da murya tace "Duk hakuri za mu yi Maheer, haka Allah ya kaddara mana sai dai muce Alhamdulillah ala kulli haal, haka Allah ya tsara shi ba me tsawon kwana bane, Allah ya sa me ceto ne" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Haka ne, Ameen ya Allah..." Ammi tace "Amma kar ka gaya ma Mayraah, ka bari sai da safe" Ya gyada ma Ammi kai yace "In sha Allah" Ammi na ta zaune dakin bayan kusan minti ashirin ta mike ta nufi kofa ta fita, throughout half of the night Maheer yaje sama parlon Ammi to check on Aryaan yafi sau biyar haka ma Abba da Usman, duk in Maheer ya shiga parlon zai tadda Ammi idonta biyu tana goye da yaron a bayanta, Mama Ladi kuma tayi shimfida a kasa da carbi a hannunta tana ta bacci, da taji an bude kofa sai ta bude ido da sauri tana jan carbin hannunta, wajen karfe uku da rabi Maheer ya shigo dakin yaga Ammi na kokarin goya Aryaan bayan ta bashi madara sannan ta basa paracetamol don jikinsa yayi zafi sosai, Ya karasa kusa da Ammi yace "Ammi ko zaki kawo sa kema ki kwanta ki huta, you need to rest too" Mama Ladi da ta mike zaune bayan Maheer ya shigo parlon tana jan carbin hannunta tace "Tun tuni nake son in amshesa ta huta amma sai ya fara kuka, yafi gane ma bayan ne..." Ammi ta gama goya Aryaan tace "Ka bari kawai, Ya fi son goyon ne" Maheer dai bai ce komai ba yana kallon Ammi, Mama Ladi tace "Kai ma ka samu kaje ka kwanta Mashir" Juyawa Maheer yayi ya fita daga parlon.... Wajen karfe hudu da rabi Maheer ya dawo parlon Ammi, Ammi na zaune da yaron a bayanta tana bacci a haka, Mama Ladi kuwa har da guntun minsharinta ga carbinta ya fadi daga hannunta, Maheer ya karasa kusa da Ammi ya kirata a hankali, Bude ido tayi da sauri, ya kwantar da murya yace "Ammi ki bani shi plss ki huta haka" Ammi tace "Alwala ma nake son inyi...." Kwance yaron tayi daga bayanta ta dawo da shi kafarta, Maheer ya dinga kallon yaron kamar yanda Ammi ma ke kallonsa, sai kuma ta daga kai da sauri ta kalli Maheer, daukan yaron yayi daga kafarta ya sauka kasan carpet yana kallonsa, da kyar Ammi tace "Ko za a kara basa maganin muran don dazu paracetamol kawai na basa" Maheer bai dago kansa ba bai kuma ce ma Ammi komai ba, Ammi ta sauka kasan carpet din ita ma ta zauna tana kallonsa, sai a sannan ya daga kai yana kallonta da idanuwansa da suka sauya launi, da kyar ya iya bude baki yace "He is gone too" Ammi ta mike tsaye da sauri tana girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da sauri Mama Ladi ta bude ido ta mike zaune tace "Lafiya??" Hawaye na zuba idon Ammi ta kalli Mama Ladi tace "Shi ma ya rasu" Mama Ladi tayi wani ihu ta dau carbinta ta tashi da sauri ta fita daga parlon tana rusa kuka.....
[10/17, 8:47 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Yanda Haseenah taga rana haka ta ga dare a cikin flowers din kofar gidan Abba da ta rakube, tayi kuka har ta gode Allah, ga insect dake ta cizon ta a jiki, har a sannan ta kasa yarda wai yaronta daya ya mutu, ta yaya ma zai mutu yaran da ta taho Abuja da su hale and hearty, so full of life, bazai taɓa yiwuwa ba ace daya ya mutu, gani take kamar mafarki take kuma zata farka daga mugun mafarkin, a haka aka fara yayyafi wajen karfe hudun asuba, kawai abubuwan da suka faru a gidan Maheer ne ya dinga dawo mata daya bayan daya, har da yanda Mayraah ta hanasa shiga da su cikin gidan, ta fashe da matsanancin kuka zuciyarta na tafarfasa tace "Wallahi ita ta kashe min yarona, ita ce sanadi, ita ce silar mutuwarsa, don da mun shiga gidan duk haka bazai faru ba, dole in dau revenge din kashe min yaro da kika yi" Har aka kira sallan asuba tunaninta na kan abinda zata ma Mayraah as revenge, ta zo Abuja da mission iri iri amma ko daya bata yi achieving ba sai ma mutuwa da ɗan ta daya yayi, ji tayi gaba daya zuciyarta ya kekashe, har ranta taji zata iya yin komai don ganin Mayraah ta dawo mara amfani a doron kasa, she can go to any extent into making Mayraah useless in life, ita yanzu ko tsoron a maida ta prison din ma bata yi, kawai Allah Allah take gari ya fara haske ta bar unguwan, jakarta ta bude ta ciro wayarta ta tafi contact ta lalubo wani number ta kira, har ya katse ba a daga ba, ta maida wayar jakarta, tana jin an kira sallah ta fito daga shukokin tana rike da jakarta ta bar gun. Karfe goma saura na safe Maheer ya shigo parlor bayan sun dawo daga makabarta, tunda ya shigo parlon Ammi ke kallonsa, daga kusa da ita Aunty Mariya ce da jama'an da suka shigo yi masu gaisuwa, Daga gefen Ammi Mama Ladi ce sanye da zumbulelen hijab da carbi a hannunta tana ja, mikewa Ammi tayi ta bi sa zuwa dakinsa tace "Wai ka sanar ma Mayraah kuwa, nayi ta kiran wayarta bata dagawa" Yace "Eh makullin mota na shigo in dauka zan tafi can gida" Ammi tace "Ko zaka fara yin breakfast?" Yace "Aa idan naje gida zan yi" Ammi ta bi sa da kallo har ya dau car key din sa, sai da ya fita sannan ta dawo ta zauna cikin jama'an dake parlor... Maheer na isa gida bayan yayi parking mai gadi ya rufe gate sannan ya nufosa da sauri yana kara gaishesa, Amsawa Maheer yayi ya kulle motarsa, Mai gadin yace "Yallabai wannan matar ta jiya fa ta sake zuwa nan" Maheer ya juya yana kallonsa yace "Yaushe kenan?" Mai gadin yace "Wajen karfe bakwai na safe" Maheer yace "Sai aka yi yaya?" Mai gadin yace "Aa ban bari ta shigo ba kamar yanda kace Yallabai, don har sai da muka yi hayaniya da ita, mai gadin wancan gidan ya fito da shi muka hadu muka korata" Maheer yace "Shikenan...." Entrance din shiga parlor ya nufa yana tunanin zuwa police station ayi setting masa boundary between Haseenah and his family in all. Yana shiga parlon ya dinga bin ko ina da kallo ganin everything was the way it was yesterday evening, walking slowly ya nufi dakinta ya bude kofar ya shiga ciki, karasawa yayi kan gadonta ya zauna yana kallonta, after few seconds ya yaye duvet da ta rufe har kanta dashi a hankali, ta bude idanuwanta da suka yi ja tana ganinsa zata juya ya rikota da sauri yayi kasa da murya yace "I am sorry Mimi" Da kyar tace "I don't understand, you are sorry for what?" Ya sauke idonsa kasa, after few seconds yace "For what happened yesterday" Ta girgiza kai tace "They are ur family also so there is nothing to be sorry about, just create time for them too" Tana fadin haka ta juya masa baya lkci daya hawaye ya cika idonta yana gangaro mata, Maheer dai ya kasa ce mata komai kansa a kasa, he wasn't expecting this reaction from her, he was expecting her to be mad at him, tun da ya baro can gida yake zullumin yanda za su kwashe da ita in ya iso, but her reaction now made him so weak, sai yaji gwara ma ta zama mad at him da wannan reaction din nata, a hankali yace "We lost the kids Mimi...." Mikewa zaune Mayraah tayi ba tare da ta shirya hakan ba ta juya tana kallonsa bata ko kiftawa, shi dai bai bari sun hada ido da ita ba, da alama she was shock and speechless, after few seconds Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Ki shirya za mu tafi can gidan...." Her voice was trembling ta matso kusa da shi da sauri ta kamo hannunsa tace "Ban gane ba Yaya" Yana gyada mata kai cikin karfin hali yace "Yea, Allah ya masu rasuwa gaba daya tun jiya..." Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin Mayraah ta bi sa da kallo zuciyarta na wani irin bugawa ta koma ta jingina da gado, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba ta sauka daga kan gadon da sauri. Maheer na komawa parlor da few seconds sai gata ta fito parlon, ya daga kai daga inda yake zaune yana kallonta, kanta a kasa ta nufo inda yake zaune tana tafiya a hankali hawaye na zuba idonta, dukawa tayi kan kneels dinta a gabansa tana girgiza kai cikin rawan murya tace "I don't mean to be mean to dem, just that the mother...." Kasa ci gaba tayi ta hade kanta da kujeran da yake zaune tana kuka sosai, dagota yayi yace "It's not and will never be ur fault Mimi, mahaifiyarsu ce tayi ajalinsu because of her evil mind and selfish interest, she caused their death, dama kuma Allah ya kaddara ba masu tsawon rai bane, don haka kar ki zargi kanki, the least i will do is to blame you wife, i know you have a heart of gold, u have ur reasons which are on point, Alhamdulillah abinda ya hadamu da ita ya raba, and i will now have peace of mind, i know u will bore me many many beautiful kids just like you in sha Allah" Mayraah dai ta kasa daina kukan da take, sosai tayi regretting act dinta, gani take kamar kawai yana kokarin kwantar mata da hankali ne amma ba haka bane a ransa, ta dade bata ji ta shiga wannan tashin hankalin da ta shiga ba, kawai ganin kyawawan yaran take suna mata gizo a vision dinta, Maheer ya dagota ya rungumeta jikinsa trying to calm her down ya kwantar da kanta saman kirjinsa, har a sannan ta kasa daina kuka, abinda ya faru jiya ne kawai ya dinga dawo mata, ita kanta in ance zata yi acting yanda tayi jiya bazata taɓa yarda ba, but maganganun Haseenah was so harsh ba kowa ne zai iya kai zuciyarsa nesa ba, muryarta na rawa ta daga kai tana kallonsa tace "I hate my self for this, i was mean" Maheer yayi murmushi yana girgiza mata kai yace "Noo Baby gal, ke kika shiga cikin ruwa da su? Kinsan tun daga ina ta taho da su a cikin ruwa?" Mayraah dai bata ce komai ba hawaye na sauka idonta, Yayi kasa da murya yana goge mata fuskarta yace "Ki tafi ki shirya mu je can gidan, Ammi is asking of you, blame ur self not wife, it's already written that baza su yi tsawon rai ba, and we all should accept that with good faith" Da kyar Mayraah ta iya mikewa duk jikinta a sanyaye ta nufi dakin ta. Da yammacin ranan wajen karfe bakwai Mayraah ta shigo parlon Ammi rike da plate din abinci da ta zubo ma Mama Ladi, har a sannan bata da kuzari ga wani zazzabi da take ji, Aunty Mariya na kallonta bayan ta ajiye ma Mama Ladi abincin tace "Kin kai ma Maheer ne" Mayraah ta girgiza kai tace "Ya fita zai siyo magani ne" Mama Ladi ta hadiye abincin bakinta tace "Ji jaraba, waye kuma bai da lafiya?" Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Kaina ke ciwo" Mama Ladi tace "Yo ba dole ba wannan uban kuka da kika ci yau ko kece uwar yan biyun nan sai haka, duk mun hakura muna ta cin abinci amma ke ko ruwa kin ki kai wa baki, in an bibiya ma uwar tasu tana can ko dar, dama don ta muzanta mu ta kashe yaran da ruwan sama, da kyar in Hasinu zata ga annabi S.A.W, mu dai Alhamdulillahi tunda Allah ya dubi Maheer ba shi da rabon wahala a duniya, don hada iri da Hasinu ai bala'i ne, Allah mun gode maka da wannan ni'imar da ka mana na daukan ran yaran nan tun ba aje ko ina ba" Daga Ammi har Aunty Mariya wani kallo suke ma Mama Ladi, Yahanasu ta rike haɓa tace "Ke dai Ladi baki da kai sai na daukan kaya, mutuwar ce ni'ima ko kuwa dai baki da hankali ne?" Mama Ladi ta juya ta kalli su Ammi tace "Ku fa yi min iyaka da tsohuwar can, ku min iyaka da ita fa, tun dazu take shigar min hanci da kundundune, wallahi kar mu raba hali a gidan mutuwa a tafi da mu a baki, haka dazu na zubo abinci ta dinga yi da ni, uwar me na tsare mata, to a gaskiya na gaji kada in mata rashin kirki a gidan Mamuda a sa ni a bakin duniya" Shigowar Usman parlon ne yasa Mama Ladi tayi shiru, ya karasa cikin parlon ya nufi Ammi da wayarsa ya mika mata yace "Ammi duba ki ga wacece wannan?" Ammi ta amshi wayar tana duba abinda yake nuna mata, kallonsa tayi da

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login