Showing 285001 words to 288000 words out of 456519 words

Chapter 96 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70650

ajiye jaririya a cikin kwali ɗan nesa da wani rijiya kusa da masallaci me koren fenti" Ammi ta daga kai da sauri ta kalli Ceo bata ko kiftawa, sai kuma ta kalli Abba da sauri taga kallonta yake, Mayraah ita ma sai kallon Ceo take babu ko kiftawa, Ita dai Ceo bata yarda ta dago kanta ba ta ci gaba a hankali tace "Zai iya kasancewa ku ba a nan ku ka sameta ba, probably ko an kai ta gidan Marayu ne, or anything of such dai, but nasan dole za ayi keeping wannan record din ko ma ina ku ka sameta" Tana magana ne hawaye na sauke idonta tana gogewa da karamin towel din hannunta kuma har sannan taki daga kai ta kallesu, Abba yayi karfin halin cewa "Dr, amma don Allah ke wacece, kiyi mana bayani yanda za mu fahimta plss, how did u know all this" Ceo ta daga kai a hankali tana kallonsa tace "Ina son in fara sanin a inda ku kuka sameta kafin in ci gaba" Abba ya gyada kai da sauri yana kallon Ammi da idonta ya cika da hawaye ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take zaune tana kallon Ceo, sai kuma ya maida dubansa kan Ceo yace "Dai dai yanda kika fada, haka ne" Ceo na goge idonta muryarta na rawa tace "To Mahaifiyarta na sama" Mikewa Ammi tayi zata bar parlon Abba ya dakatar da ita, har sai da ya mike ya nufota sannan ta koma a hankali ta zauna hawaye na sauka idonta, kamar yanda yake sauka idon Mayraah da jikinta ke bari jin abinda Ceo ke cewa, Abba bai koma kujeran da yake ba ya zauna kusa da Ammi yana share zufar dake keto masa a goshi da handkerchief din hannunsa yace "Don Allah Dr har yanzu a duhu muke, plss we need a better explanation, date da rana da kika ambata da ma exact spot duk haka ne we are not disputing that, ni ne nan na fara ganinta that very early morning" Ceo dai kallonsa kawai take bata ko kiftawa kamar bazata ce komai ba hawaye na sauka idonta, sai kuma ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Labarin me tsayi ne Alhaji" Abba yace "We have all day pls" Usman dai ya sunkuyar da kansa duk yana sauraron abinda take cewa, unlike Maheer da MD dake kallonta all waiting to hear what she have to say eagerly, Cikin sanyin murya Ceo tace "I will make it brief...... My dad was a Muslim, Mahaifiyata kuma came from a Christian home, so she is a christain, my father was a military personnel wanda aiki ya kai sa kudu har ya hadu da Mahaifiyata a can ya aureta without the consent of her parent that were strictly against the marriage because her father was a devoted pastor, infact she came from a reputable Christian family, ta dalilin haka har disowning dinta iyayenta suka yi amma bata damu da hakan ba saboda son da take ma mahaifina da ya rufe mata ido, babu dadewa da aurensu aka ma dad dina transfer zuwa Adamawa wanda nan ne asalin garin sa, sai dai he lost his parent at a very young age amma yana da yayyi mata hudu sannan shi, sai kuma sauran relatives dinsa, a Adamawa aka haifemu ni da kanwata warce na bata tazaran kusan shekara 7, babu tsanar da dangin Mahaifinmu basu nuna ma Mahaifiyarmu ba duk don kasancewar ta Christian, mind you Abbanmu bai taba forcing dinta ta amshi addininsa ba don tana Christianity dinta tana zuwa coci shi kuma yana addininsa na Islam, i have my muslim name that is Aisha as at then, kanwata Aaria kuma Maryam, kawai dai Abbanmu bai yarda ta kai mu church ba don islamiyya muke zuwa ma sannan, babu dama mom din mu ta shiga dangin Abbanmu ko yaya ne sun dinga kyara da tsangwamarta kenan a fili babu boye boye, tsana suke mata me tsanani, wasu suce mata warce bata kallon gabas, wasu su kira ta da kafura, wasu su ce mata arniya, wasu su ce mata karuwa, gashi bata da kowa nata a Adamawa sai Abbanmu wanda shi kuma ake yawan masa transfer gari gari don wataran sai mu yi wata shidda bamu sa shi a ido ba sai dai ya mana aiken kudi da kayan abinci, tsanar da ake ma Mom din mu a familyn Abbanmu ba iya ita kadai ya tsaya ba, har mu hakan ya shafa kiri kiri suke nuna mu ba jininsu bane, ko mun je inda suke sai su kore mu, ko sunanmu basa kira sai dai su kira mu da 'ya yan kafura ko 'ya yan Arniya, don sun ce kaf zuri'arsu wai babu kafuri kuma baza a fara ta kan kaninsu ba, infact basu ma yarda mu din 'ya yan Mahaifinmu bane, his relatives made life a living hell for our mother and us in Adamawa, mun sha wahalansu sosai" Shiru tayi tana goge hawayen dake sauka idonta trying hard to control her self, bayan few seconds ta ci gaba da kyar tace "Ba iya family din Abbanmu ba, hatta anguwan da muke mutanen cikinsa basa wani son hulda da mu saboda Mahaifiyarmu ba musulma bace tana zuwa coci don a sannan ana yawan samun religious crises a arewacin Nigeria, kuma anguwan da muke duk majority musulmai ne unlike now da akwai Christians da yawa a Adamawa with different languages sannan civilization ya bazu ko ina yanzu ana zaune lafiya da juna sai dai abinda baza a rasa ba, all this while mom dinmu bata waiwayi garinsu a kudu ba ko da wasa sanin yanda ta rabu da iyayenta da danginta, i was 12 years old Allah yayi ma Mahaifinmu rasuwa bayan harbesa da aka yi a wani operation da suka fita, our mother was depressed and shattered after receiving this bad devastating news of our fathers death, ya zamana bamu da kowa kuma a garin Adamawa, ana 40 days da rasuwan Abbanmu yayyinsa mata da danginsa suka zo suka dauke duk wani abu da ya bari na dukiya wai basu yarda cewar mu 'Ya yansa bane dama, kawai ya dauko Mahaifiyarmu ne a kudu suna zaune ba tare da aure ba don haka bamu da gadonsa islamically, we were left with nothing sai gidan haya da muke ciki wanda Abbanmu bai jima da biyan rent din ba ya rasu sai foodstuffs da shima bai dade da aiko mana ba" Ceo na goge hawayen dake zuba idonta ta ci gaba tace "Ina jss3 a lokacin a wani private school Aaria kuma tana primary school, tun bayan rasuwan Abbanmu mom dinmu ta rasa lafiyar ta saboda shock din da ta shiga, yau ciwo gobe lafiya duk ta fita hayyacinta, a haka cikin ruwa cikin zafin rana zata fita duk inda zata samu aikatau tayi duk don ta kula da mu, wani lokacin ma haka zata dawo bata samu aiki ba sai dai mu kwana da yunwa, I have my class mate then a makarantar da Abbanmu ya saka mu kafin ya rasu duk da mun daina zuwa makarantar saboda babu halin biya don ta abincin da za mu ci ma Mom din mu take, amma haka wani lokacin classmate din nan tawa zata debo mana kayan abincin gidansu a boye ta kawo mana mu girka" Ceo tayi shiru staring at the big plasma in the parlor, sai kuma tayi murmushin takaici tace "The mistake we made ni da kanwata was that, bamu yi wayon ce ma Mom dinmu ta kai mu gun relatives dinta a South ba, nasan kilan su da baza su guje mu ba, bayan rasuwan Abbanmu da wata sha daya Mahaifiyar mu ma ta rasu, leaving us with nobody to look unto as family members or relatives, leaving us in this harsh world all alone, just i and my little sister" kuka take sosai tana kallon Abba dake kallonta da ma duk occupant din parlon, ita dai Mayraah na jikin Ammi ta rufe idanuwanta zuciyarta na bugawa, Ceo tayi kukanta me isarta, cike da karfin hali tace "Life took another horrible dimension for us, we have nobody to look unto, we were too young and naive, bamu da me ba mu abinci sai wannan classmate din tawa duk da iyayenta ba wai wasu masu kudi bane kawai rufin asiri gare su, gashi ko bin ta kanmu dangin Abbanmu basu yi ba duk da ganin mahaifiyarmu ta mutu, ga kudin hayanmu ya kare, amma mai gidan duba da halin da muke ciki na rashin gata da rashin iyaye sai ya maida mu wani gidan hayansa na masu karamin karfi wato daki daya, as i am talking to you now jikokinsa biyu na aiki hospital din, Dr Hamid here in Abuja, sai Dr Misbahu in my lagos branch, babu batun boko ko islamiyya a lokacin sai dai mu jira Classmate dita ta samo mana ɗan abinda za mu dafa daga gidansu kuma duk a boye take debo abincin ta kawo mana, kwatsam sai yayan babanta ya kai ta boarding da cousin sister dinta for her Ss school, wannan dalili yasa na fara jan kanwata zuwa kasuwa inyi dako don mu samu abinda za mu ci, da daddare mu dawo gida mu kwanta, dama tun bayan rasuwan Abbanmu muka bar zuwa islamiyya sai mom dinmu ta tafi da mu coci, to cocin ma tunda ta rasu muka daina zuwa don unguwan da mai gidan ya maida mu da nisa sosai daga cocin bamu da kudin motar zuwa, but i do read the bible together with my little sis sannan in koya mata karatun boko. Bayan wani lokaci sai wani mutumi a kasuwa ya bani aikin tsare masa babban shagonsa don kullum yana ganina cikin kasuwa da kanwata ina dako, duk ranan duniya yake sallamata bayan da na basa labarin bamu da iyaye, to da wnn kudin na hada na saka kanwata a makaranta mara tsada, ni kuma na ci gaba da zuwa kasuwa, a kwana a tashi har Aaria ta gama primary school, ita kuma classmate din nan tawa tayi candy ta dawo gida ta tafi tsohon gidanmu aka mata kwatancen inda muka koma, with her assistant na biya ma Aaria secondary school me kyau tana zuwa, ni kuma ta ban shawara tunda ina da kokari don kafin in zama drop out ni ke leading a ajinmu tace min in siya science textbooks na senior secondary school in dinga karatu kawai sanda za a fara registration na waec nima inyi registration in zana waec, hakan nayi amma fa sai da nayi shekara ina karatu a gida kafin in zana waec din wanda ita classmate din tawa ce ta biya min, Ita kuma ta samu admission a jami'a, duk kudin da nake samu a kasuwa tarawa kawai nake don ina son inyi sponsoring kanwata ko da ace ni ban samu wani karatu me zurfi ba ita ina son tayi karatu sosai don tana da kokari ita ma, tana gama junior secondary school nayi deciding ta tafi boarding school saboda yanda naga she is growing into a beautiful girl kuma maza sun fara bibiyanta at her very young age, beside Aaria is too naive sannan bata da wayo gata matsoraciya, she is just intelligent but not smart or brave, still a haka dai sai da wannan classmate din tawa ta tallafa mana don kudaden wajena basu isa na kai ta boarding din ba, bayan Aaria ta tafi boarding school iyayen classmate dita suka yi relocating back to kano, sunyi kokarin su nema mata transfer a University din da take amma bai yiwu ba, to hakan yasa sai dai ta je kano hutu, a sannan kuma bawan Allahn da nake jire ma shago ya koma Gombe da family dinsa, da ɗan kudin wajena nayi jari ina siyar da pure water a kasuwa ko gaya ma wannan classmate din tawa banyi ba don karatunta na bukatar nutsuwa sosai, she was studying medicine sai a jima bata fito daga cikin makaranta ba ma, duk don in dinga providing needs din kanwata dake boarding school nake sana'ar da nake" Shiru Ceo tayi tana murmushin takaici, duk occupant din parlon kallonta suke, i trust my little sis, a ɗan tarbiyyar da nayi mata tun bayan rasuwan iyayenmu nasan abinda zata aikata da wanda bazata aikata ba, ko a sanda nake jire shago a kasuwa da sun tashi boko kasuwa take zuwa ta sameni immediately kuma sai karfe shidda na yamma muke komawa gida tare, har dai ta tafi boarding school, bayan sun zana jarabawarsu na waec, ina kwance ni kuma bani da lafiya tun bayan da mota ta bugeni wajen siyar da pure water sai ban je na taho da ita ba tunda bata da kudin motar dawowa gashi waya bai yi yawa ba a sannan, ko yayi yawa ma we can't afford it, duk classmates dinta suka tafi gida sai ya kasance ba su da yawa da suka rage a makarantar don school was on vacation su kuma suna waec, ana haka sai wata classmate dinta taga ita ma zata tafi ta bar ta, hakan yasa ta samu Aaria tace Babanta zai zo daukanta su je sai a ajiyeta don su ma Adamawa za su, bayan an zo daukarta sai ta sanar ma Aaria ba babanta bane ɗan uwanta ne, a haka dai ya daukesu su biyu....." Ceo ta share sabon hawayen da ya taru idonta tace "Da na daure a sannan duk tsananin rashin lafiyar da nake naje na dauko kanwata da duk abinda ya faru bazai taɓa faruwa ba, i still blame my self for everything till date, the useless man took advantage of my poor sister, he assault her, don sai ya yi dubara ya fara dropping din cousin sis din tasa a gida, i don't even know if they are cousin, sai washegari ya dawo da Aaria gida, she never told me anything that happened, na dai ga gaba daya yanayinta ya canza and her eyes were swollen, na tambayeta menene ke damunta haka, sai tace min ai last paper dinsu ne take ganin kamar bata yi kokari ba, na dai kwantar mata da hankali nace zata yi passing duk papers din, for one week nayi ta rarrashinta don taki walwala tunda nasan ta da saka abu a rai... that wasn't enough for the useless man, haka ya ci gaba da bibiyar kanwata duk bata gaya min ba saboda tsoro don bayan dawowar ta da yan kwanaki na koma kasuwancina, all my wish was for her to write jamb ita ma ta tafi University, few months later na fara ganin some changes tare da ita tana ta rashin lafiya a tsatstsaye, bata iya cin abinci, ban kawo komai a raina ba don har Chemist na kai ta nace Malaria ke damunta muka siya magani, ana haka Classmate dita Hajiya Amina that turned family ta zo bayan sun yi mid semester break, nan fa ta ankarar da ni Aaria is pregnant" Ceo na girgiza kanta hawaye na sauka idonta ta kasa ci gaba har sai bayan wani lokaci ta dake cikin rawan murya tace "Because we were nobody, ba mu da kowa, ba mu da wanda zai tsaya mana... kawai don nayi kokarin kwatar ma er uwata 'yan cinta akan assaulting dinta da aka yi shine mahaifin wannan mugun mutumi ya sa aka kulleni a prison for good 7 months" Kuka Ceo take sosai, cikin karfin hali tace "Da ba don Hajiya Amina ba, kilan da Aaria mutuwa zata yi, don there is nobody to take care of her, bata da kowa ga rashin lafiya na ciki da take yi, bata zuwa ko ina tana one room din da aka bamu a kwance 24/7, duk da wahalan karatu haka kullum Hajiya Amina ke fitowa daga makarantarsu ta je wajen Aaria kai mata abincin da ko iya ci bata yi, sannan sai tayi mata duk abinda ya kamata kafin ta bar gidan, ga magunguna da take siya mata, she was there for her all through the hard time, tayi bakin kokarinta a kanta sosai wanda iyakaci nima abinda zan mata kenan, my sister was depressed.... A haka na fito daga prison bayan 7 months, nayi bakin cikin ganin Hajiya Amina bata sa Aaria ta zubda cikin nan ba, satina hudu da fitowa daga prison Aaria ta haihu, ta haifi ya mace daga ni sai ita a daki wajen karfe sha dayan dare, ko kuka jaririyar bata yi ba bayan ta haifota, nayi dubara na kai mata ruwan zafi bandakinmu dake cikin dakin sannan na zazzage taliyar mu dake cikin kwali na dauki jaririyar da ko goge mata jiki ban yi ba na nannadeta cikin zani na sakata cikin kwalin, na dau leda na rufeta da shi sannan na kulle kwalin na fita da ita cikin daren, nayi tafiyar da tafi ta minti arba'in ina ratsa unguwanni da lungunan talakawa da ban taɓa sanin da su ba a Adamawa, har daga karshe na iso wannan exact spot din kusa da rijiya, na tabbatar babu wanda ke kallona na ajiyeta sannan na juya da sauri na kama hanyar gida, wanda da kyar na iya gane hanyar gida tsabar lungunan anguwannin" Cikin rawan murya ceo ta nuna Mayraah tace "Genetic testing showed ita ce jaririyar nan da na ajiye shekaru ashirin da biyu da suka wuce......"
[8/28, 9:37 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: A hankali Ammi ta kara jan Mayraah jikinta hawaye na sauka idonta, Abba was speechless, haka ma su Maheer da duk jikinsu yayi sanyi don duk ba haka suka so jin labarin ba, shi dai MD sunkuyar da kansa kawai yayi wishing it was never like this too, Ceo na goge idonta a hankali tace "Tun da na raba Aaria da jaririyarta ta hadu da post traumatic stress disorder, Hajiya Amina was mad at what i did to the innocent Baby, kuma babu yanda bata yi da ni akan mu koma inda nayi deserting jaririyar ba nace mata nima ban san unguwan ba don tafiya kawai nake cikin duhu bazan gane inda na dinga bi ba, ban taɓa tunanin trauma da kanwata ta shiga

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login