Showing 453001 words to 456000 words out of 456519 words
Aunty Mariya ma sallama sannan ya fita daga parlon, Ihsaan ta dau abun da suka siya ma Mayraah ta kai gabanta ta durkusa ta ajiye tana kallonta tace "Allah ya baki lafiya Aunty" Mayraah na mata murmushi a hankali tace "Ameen Ihsaan, Allah ya kiyaye hanya" Ihsaan tace "Ameen" Daga haka ta mike tayi ma su Mama Ladi ma sallama sannan ta fita daga parlon ta bi bayansa, Mama Ladi ta fara matsar kwalla tace "Duk sun yi dacen mazaje wallahi, yanzu ki ga yanda yake kula da yarinyar nan ta dawo kamar ba ita ba, ta zama wata er gayu, kuma sanin er yarinya ce kinga ai har yanzu bai yarda tayi ciki ba sai ya gama renonta yanda ya kamata, ita kanta Eemani muna kyautata zaton Usuman zai zame mata uwa da uba a duniya, amma fa zance na gaskiya duk Mera ta fi su dacen miji, don a nan duniya dai kafin a samu me hali sak na Mashir to sai an tona wllhi, Mashir ba sa wa, ba hanawa, ga gudun bacin rai, ga kunya, ga kawaici, ga biyayya, ita kanta Ammin ace yau ta rasa Mashir Al-qur'an sai tayi karamin hauka...." Mayraah ta dinga wa Mama Ladi wani kallo jin furucinta na karshe, ita kanta Aunty Mariya wani kallon take ma Mama Ladi, Mama Ladi ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah dai yayi masa albarka, ya basa 'ya yan da za su masa biyayya yanda yake mana, tun yanzu Aryaan din nan na lura hakuri ke garesa kamar ubansa, da wuya kaga yayi kuka in ba ko bai da lafiya ba, shi yasa yaron ya shiga raina wallahi..." Babu dae wanda ya tanka Mama Ladi a parlon. Mama Ladi ce zaune parlon Ammi tayi kicin kicin da fuska kamar bata taɓa dariya ba, Aunty Mariya na gefenta zaune a parlon, Ammi kuma na goye da Aryaan dake bacci a bayanta, rai bace Mama Ladi tace "Tun a sannan fa nace a bar wannan batu ni babu ruwana, meye kuma yanzu za a sake tado min da wannan zance fisabilillahi idan ba neman magana ba" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Banda abun ki Mama tunda ance yau zai zo ai da kin jira ya iso in bai maki ba sai a san abun yi kuma, ai dama ba ace lallai dole ba" Aunty Mariya tace "Wallahi haka na gaya mata kafin ki shigo Ammi" Mama Ladi tace "To wai akan wani dalili ma zai zo min tukun? In fa yayi gigin zuwa inda nake zan daddana masa ashar wallahi tallahi, Da girmana a kawo min wani batu na aure banda rashin tsoron Allah, da fa na haihu da ina da jika kamar Meran ki yanzu, a bar ganina ina da kyan jiki ayi zaton shekarata hamsin a duniya, shi kuma Alhaji Saminun kaf danginsa ya rasa warce zai hada da abokin nasa sai ni Ladi? Wato ga Ladi er iska ga Ladi er kauye tunda nace masa a karaye nake, In kin bibiya fa irin abokan nan ne tun na kuruciya wa enda aka yi wasan ƙasa tare, shi Alhaji Saminu sai Allah ya daukaka sa a cikinsu yayi kudi su kuma suna nan da talauci amma suna makale da shi suna maula, to fa ina ga shine a cikinsu wani shegen zai ce ai aure yake so amma bashi da halin yi bai da ko sisi, ni kuma gani er kauye sai in fado ran Alhaji Saminu sai yaga bari kawai ya hadani da shi mu karata, banda haka ai kaf abokansa da suke harkokin arziki tare nera ta zauna masu basu ma zaman kasar nan wallahi, shi kansa Alhaji Saminun sai yayi wata biyu bai kasar ai, wani lkcn da Hajiya Ramatun yake tafiya su yi watannin da za su yi su dawo tare, dama Halima ake bari da jiran gida, in mutumin arziki ne ai da Halimar zai fara yi masa tayi tunda kanwarsa ce ba ni da ban hada komai da shi ba" Daga Ammi har Aunty Mariya dai sun kasa cewa komai, Mama Ladi tace "Shi kuma Mamuda da ya dage kan batun nan har yake ce maku mutumin zai zo yau in gajiya yayi dani ba sai ya bani kudin mota inyi komawata karaye ba, don naga kamar shi ma neman kai yake da ni yana kakkabi da ni, duk ya mance halaccin da na masa a rayuwa, ni kenan kullum ina kan titi zuwa sulhu a gidansa, amma daga karshe saboda zaman lafiya ya dawo gidansa sai ya nuna ya gaji da ni" Mama Ladi na kai wa nan ta fara matsar kwalla, Ammi dai ta kalli Aunty Mariya, Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta fita daga parlon. Bayan Magrib da kyar da siɗin goshi Ammi da Aunty Mariya suka lallaba Mama Ladi dake dakinta akan taje parlon downstairs mutumin ya iso gidan, zagi kam sun sha shi kwando kwando a wajenta har da ɗan hawayenta, daga karshe dai ta saka hijab dinta ko gaya masu abinda ta shirya yi ma mutumin da ya zo wajenta bata yi ba ta fice daga dakin, Aunty Mariya ta kalli Ammi dake tsaye tace "Kar kuma taje ta zage bawan Allah fa Ammi mu ji kunya" Ammi tace "Wallahi nima nazarin da nake kenan Mariya, don ba karamin aikinta bane" Aunty Mariya tace "Tun farko da ta nuna bata ra'ayi Ammi da haka kawai kika gaya ma Abban ya gaya ma Alhaji Saminun, kinga da ba a zo gabar nan ba" Ammi ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Mayraah ce kwance dakin Mama Ladi tana ta kallon Aryaan dake zaune yana wasa da toys dinsa, gaba daya yaron ya juye ya koma sak ubansa, unlike farkon haihuwar sa da yake ɗan kama da ita, duk in suka zo gidan gaida Ammi tare da Maheer sai taji kamar a bata yaron su koma gida tare da shi, gashi ko saninta yaron bai yi ba don baya ma yarda da ita ko Maheer din, Ba karamin shakuwa yayi da Ammi da Bilkisu ba sai Usman me siyo masa toys iri iri, sosai Mayraah tayi nauyi kai kace haihuwa yau ko gobe, yanzun ma Mama Ladi suka zo yi ma sallama shine dalilin zuwansu gidan, Bilkisu ta shigo dakin ta dau handbag din Mama Ladi da ya rage a dakin, Aryaan na ganinta ya fara bin ta har da kukansa, Bilkisu ta daukesa tana kallon Mayraah tace "Ke kina nan Maman Aryaan, za mu je can parlon Ammi" A hankali Mayraah tace "Ina tahowa" Bilkisu ta fita tana dauke da Aryaan, Mayraah ta bi sa da kallo, bayan few minutes ta lallaba ta mike ta dau jakarta ta fita daga dakin, har zata tafi bangaren Ammi sai kuma kawai ta tafi downstairs ta zauna, Ammi na zaune parlonta rungume da Eeman dake kwance jikinta idonta a lumshe, Mama Ladi ma na zaune parlon sanye da sabon atamfarta me tsada da sabon mayafi da takalmi, ga akwatuna uku duk na sababbin kayanta, kai baka ce Mama Ladi bace zaune parlon, Ammi kam sai kallonta take tana murmushi, gaba daya ta kasa daina kallonta, Bilkisu ta ajiye Aryaan dake hannunta ta fara fita da sabbin akwatunan Mama Ladi waje don tun daxu driver ya zo daukanta, Mama Ladi ta kalli Ammi tace "Toh ke yanzu Ammi da zaki je bikin Badiyyah nan da kwana biyu ya kenan zaki yi da wannan me shigar sabon cikin da duk ta fita hayyacinta?" Ammi tayi shiru da farko, sai kuma tace "Ai Bilkisu na nan, kuma kwana daya kawai zan yi in dawo, kin ga Aryaan ma barinsa zan yi a gida...." Mama Ladi tace "To dai gwara kwana dayan, ga su nan duk kafarki suka biyo da wannan azababben laulayin, Mera ta gama farfadowa, yanzu kuma ga wannan da tafi Mera son jiki" Bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo yana kallon Mama Ladi yace "Lokaci fa na wucewa Mama, ga driver na ta jira a waje tun daxu" Mama Ladi tace "To shi direban nan aljanna zai tuka ni ya kai ni ne da bazai iya hakuri ba, tun dazu an isheni dreba na jira, ai dai zai bari inyi sallama a tsanake cikin nutsuwa ko" Ammi ta kwantar da Eeman dake jikinta tace "Ae ba daga shi bane Mama, kar jirgin ya tashi shi yasa ya damu...." Mama Ladi tace "To ina ruwansa, in ma jirgin ya tashi sai a daga tafiyar ai" Ammi ta saka Hijab dinta ta dau handbag din Mama Ladi zata rike mata, sai ga Bilkisu ta shigo ta dau Aryaan ta fita, Ammi ta tafi gun Eeman ta duka tana kallonta tace "Za mu je raka Mama Ladi Airport, ko za ki je?" Eeman ta girgiza mata kai da sauri, Ammi tace "Toh sai na dawo, in kina son wani abu Bilkisu na nan, zan ce ta dawo parlon ta zauna" Daga haka ta nufi kofa, Mama Ladi ta karasa gun Eeman ta kama hannunta tace "To ni na tafi Eemani, Allah Ubangiji ya baki lafiya kin ji, ki dinga daurewa kina cin abincin ko kadan ne, in kuma kunu aka baki shima ki daure ki sha, kema za ki fi jin kwarin jikinki" Eeman ta gyada mata kai, a haka Mama Ladi ta nufi kofa tana kallon Usman tace "Hala dai biyanka dreban nan yayi da ka addabemu tun dazu Usuman.... Shaidan fa aka sani da gaggawa" Usman bai tanka ta ba har ta fita daga parlon, karasawa gun Eeman yayi ya duka gabanta yana kallonta ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Baby, u need anything?" Ta girgiza masa kai bata ce komai ba, yayi pecking forehead dinta yace "Za mu je raka Mama Ladi Airport yanzu" Nan ma kai ta gyada masa, yayi pecking din hannunta sannan ya mike ya fita daga parlon. Gaba daya yan gidan suka tafi raka Mama Ladi Airport banda Bilkisu da Eeman, Ammi ta rungume Mama Ladi bayan sun isa airport din cikin sanyin murya tace "Allah ya kai ku lafiya Mama, Allah ya...." lokaci daya hawaye ya cika idon Ammi ta kasa ci gaba, Murya na rawa Mama Ladi tace "Ameen Hajara, Allah Ubangiji ya kaddara saduwar mu, Allah ya maki albarka ya raya maki zuri'ar ki ya albarkace su, ki tayani yi ma Mamuda godiya, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi da dawainiyar da ya dinga yi min, Allah ya hade kan zuri'arsa ya karesa sharrin masu sharri..." Ammi dai ta kasa cewa komai hawaye na zuba idonta, har cikin ranta ta fara jin kewan Mama Ladi tun bata bar kasan ba, Mama Ladi ta tafi ta rungume Mayraah dake jingine da mota tace "Kema Allah ya maki albarka ya sauke ki lafiya Mera, duk silar ki nake cin wannan arzikin, Allah ya baki zaman lafiya na har abada da mijinki ya raya maki zuri'ar ki, duk da bana jin Mashir ko kadan, don duk mun san wanene Mashir, Mashir mutum ne" Mayraah ta sauke idonta ta kasa cewa komai, Mama Ladi ta kama hannun Maheer dake murmushi tayi masa sallama ta sa masa albarka, tayi ma Usman dake rike da Aryaan shima haka, sannan Omar, tace "Kai ma Allah ya baka mace ta gari Umar, yanda ka gama karatun ka lafiya Allah ya kawo maka babban rabo da mace ta gari" Omar na murmushi yace "Ameen Mama" daga nan kanin Alhaji Ahmadu wanda shi ne sabon mijin Mama Ladi yayi leading dinta zuwa cikin airport da akwatunanta don shi ne zai mata rakiya zuwa UK din. Suna hanyar komawa gida Omar dake driving din motar yace "Amma shi Alhaji Ahmad din yana da mata ne Ammi?" Ammi tace "Ta rasu shekara takwas kenan wai" Omar yace "Allah sarki, amma yana da yara?" Ammi tace "Yaransa maza hudu, uku sun yi aure sai karaminsu dake masters dinsa a England, abokin Alhaji Saminu ne na kut da kut, a yanda ma yake gaya ma Mama Ladin Alhaji Saminun ya girmesa da shekara biyar" Omar ya girgiza kai yana murmushi yace "I am so happy for Mama Ladi, she deserves happiness too" A hankali Ammi tace "Haka ne" Daga haka ta amshi Aryaan dake kokarin dawowa gunta daga hannun Usman, Usman yayi dariya yace "Shi fa yaron nan ya zata kece Baabarsa tsakanin sa da Allah" Ammi na murmushi ta dora goshinta kan na Aryaan tace "Wai haka Aryaan?" Dariya ya fara yi mata ta rungumesa jikinta tana jin son yaron har cikin ranta, gaba daya son da take ma ubansa ne ya dawo kansa yanzu....
Bayan tafiyar Mama Ladi UK da wata biyu Mayraah ta haifo santala santalan 'ya yanta Maza biyu wanda aka mayar masu da sunan yan biyun Haseenah da suka rasu, farin ciki gun Ammi ba a cewa komai, wannan karon Mayraah sak ubansu ta haifo su kuma duk kama suke da twins din Haseenah, Ammi farin ciki biyu ne ya hade mata don ana gobe Mayraah zata haihu Aunty Mariya ta kira take sanar mata she is pregnant after 15 years of patient, farin ciki gun Ammi ba a cewa komai don babu sallan da zata yi da baza ta sa kanwarta a addu'a akan Allah ya bata haihuwa ba, Mayraah na gama wankan jego babu wata wata tayi family planning don bata son taking wani risk din kuma, wannan karan dama a gidan Maheer aka yi sunan twins din, wanda duk mutan kaduna sai da suka zo, har Alhaji Saminu sai da ya zo yi ma jikar tasa barka, Hajja ce ta zauna tare da Mayraah sai Bilkisu dake taimaka mata har aka yi 40 days sannan Hajja ta koma kano ta bar Bilkisu a gidan, kafin 40 days sau uku Badiyyah ke zuwa gidan don ita ma a Abujan take aure, kuma atamfa hudu ta kawo sanda aka yi suna tace inji mai gidanta da kishiyarta duk da kishiyar ma ta zo sunan. Ranan da Mayraah da babies dinta suka yi 50 days tana daki Bilkisu ta shigo tana sanar mata tayi baki a parlor, Mayraah ta kwantar da Shuraim dake hannunta tace "Su waye ne?" Bilkisu tace "Wasu mata da miji ne" Mayraah tace "Abban Aryaan ya fita ne?" Bilkisu tace "Aa yana parlon, tare suka shigo da baƙin yace in maki magana" Mayraah ta dau mayafinta ta fita zuwa parlon, ta ɗan yi mamakin ganin visitors din nata, ta karasa cikin parlon tana murmushi ta zauna tace "Sannun ku da zuwa" Jiddah na murmushi suka gaisa da Mayraah, sannan Mayraah ta kalli Musharraf ta gaishesa, ya amsa da fara'a yace "Sannu Maman twins, hope you are doing fine?" Tace "Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Jiddah tace "Ban ga baby ba, baku zo da ita bane?" Jiddah na murmushi tace "Wai Mimi, tana can kano gun Mami" Mayraah tace "Allah sarki" Mikewa tayi ta tafi dauko masu ruwa da drinks a kitchen, sannan ta koma dakinta with the help of Bilkisu ta kai masu twins din dake bacci parlon, ko minti ashirin basu yi a gidan ba Musharraf yace za su tafi, nan ya ajiye ma twins din 100k, Jiddah kuma ta ba Mayraah tsadaddun atamfa biyu, Mayraah was so happy, and she appreciated the gift so much, Maheer yayi masu rakiya har kofar gida yayi ma Musharraf godiya sosai. Within that period Ceo tayi ma Maheer hanyar aiki a US, at first he was reluctant about the offer don kwata kwata bai son nesa da Ammin sa, amma haka nan Ammi da Abba suka karfafa masa gwiwa akan ya karbi offer din, shi dai har a sannan bai gamsu ba cause he is well paid a inda yake aiki, amma bai ma iyayen nasa musu ba, farin ciki gun Mayraah kam ba a cewa komai don ko babu komai zata kara zama close da mahaifiyarta da dad dinta that are in the US, sai dai duk bata nuna ma Maheer haka ba, Ammi was really down ganin favorite Son dinta da family dinsa za su yi nisa da ita sosai amma bata bari damuwar nata ya fito fili ba tunda ita ce ke kara encouraging Maheer din. Maheer ya so a bar mata Aryaan ganin yanda suka shaku sannan bai saba da su ba sai ita da Bilkisu amma tace kawai su tafi da shi ba komai a hankali zai saba da su in ya ga babu ita da Bilkisun, bayan sun gama processing komai ana gobe zasu bar Nigeria Badiyyah ta zo gidan yi masu sallama, Ammi taji dadin yanda ta ganta, tun ma lokacin sunan twins, don kana ganinta kasan tana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, ga dai shi tana da kishiya kuma gida daya suke, Ammi tace "Inji dai kina girmama abokiyar zamanki Badiyyah don naga matar na da hankali" Badiyyah na murmushi tace "Lafiya lau muke zaune Ammi, bata da matsala kwata kwata, na dauketa kamar yayata ne, yaranta ma duk suna girmama ni, duk da ta aurar da biyu, ni ce ma na yaye yaron first daughter dinta sai jiya na maida sa gun Mamansa" Ammi tace "To maa sha Allah, haka ake so ai, Allah ya ci gaba da hada kan ku...." Badiyyah tace "Ameen" nan Badiyyah ke ma Ammi da Mayraah gaisuwan Haseenah, Mayraah kasa cewa komai tayi tana kallon Badiyyah with shock, Ammi da ita ma sai da ta girgiza tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Haseenah ta rasu? a ina kika samu labarin nan Badiyyah?" Badiyyah tace "Cousin sis dinta naga ta dorata a status shekaranjiya, sai kuma naga wata kawarta ma ta dorata a facebook, ai ban san baku sani ba wallahi..." Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shekaranjiya kenan ta rasu, toh Allah Ubangiji ya ji kanta ya gafarta mata, rashin lafiya tayi ne?" Badiyyah tace "Ameen, nima haka na tambayi kawarta sai take ce min ai tunda tayi accident shikenan ta rasa lafiyarta kullum ana hanyar asibiti da ita, har Allah ya mata cikawa shekaranjiya" Ammi ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "To Allah ya gafarta mata, zan kira mahaifiyarta in mata gaisuwa kuwa don ina da numberta, Maheer ma ina