Showing 306001 words to 309000 words out of 456519 words

Chapter 103 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70572

da kallo babu ko kiftawa, Mayraah na fitowa taga har ta tashi kan darduman ta koma kan kujera, hakan yasa ta karasa ta tada sallah... Sosai Mayraah ta sake da Mom dinta few hours da zuwanta gidan, don har tambayarta tayi me zata girka mata, tana gaya mata kuwa ta sauka downstairs ta samu masu aikin gidan suka yi leading dinta zuwa babban kitchen din gidan, Ceo kuma na study room dinta, sai da aka yi Magrib sannan Mayraah ta kai ma mahaifiyarta girkin da tayi mata, ta sake dawowa downstairs ta yanka mata fruits ta kai mata, Aaria na kallonta bayan ta ajiye fruits din a hankali tace "Amma a nan zaki ci kema ko?" Mayraah tayi murmushi tace "Ban yi serving din Aunty ba, she is downstairs" Aaria tace "Ohk, i will wait for you" Daga haka Mayraah ta fita ta sauka downstairs don Ceo na can a zaune, ita ma ta kai mata abincin dining area da fruits, ta sanar mata sannan ta tafi sama gun Mahaifiyarta suka ci abincin tare. Karfe takwas da rabi Mayraah ta sauko downstairs bayan mahaifiyarta ta sha drugs dinta ta kwanta don bata wuce time din bata yi bacci ba, kuma tana gefenta har tayi bacci sannan ta fito daga dakin, Ta karaso cikin parlon tana kallon Ceo ta zauna don ita ce tace mata idan Mom dinta tayi bacci ta sameta downstairs, Ceo na kallonta tace "Tayi baccin ko?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh tayi" Ceo tace "Come closer" Mayraah ta mike ta isa kusa da ita ta zauna, Ceo na kallonta tace "Akan maganar aurenki, ki gaya min gaskiyar abinda ke ranki dear, nasan tun bayan da aka yi calling off din aurenki wancan lokacin kin cire ranki da wannan auren, so now tell me the truth are you still interested in that guy after all what that happened? Sannan if i am not mistaken akwai wani magana da naji kawun nasa yayi kan cewar shi ma yana da wata maganar a kasa, i don't know ko ni kadai naji hakan a parlon ranan...." Ceo ta kalli kofar shigowa parlor sannan ta kalli mai aikinta da ta fito daga wani bangare a parlon da sauri ta karasa ta bude kofar, tun da ya shigo Mayraah ke kallonsa kafin ta sunkuyar da kanta, ya karaso cikin parlon da ladabi ya gaida Ceo, tace "How are you Aliyu, why are you coming this late?" Da ladabi yace "Ma'am i just arrived not long ago" Ceo ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk, what is it you want to discuss with me?" Ya ɗan kalli Mayraah suna hada ido tace "Good evening" Yace "Evening how are you" Ceo ta nuna masa kujera tace "Have a sit" Ya karasa ya zauna, tana kallon Mayraah tace "Get him water" Mikewa tayi ta nufi kitchen, Ceo ta cire glasses din idonta ta ajiye, shi dai kansa na kasa, bayan some minutes Mayraah ta fito rike da tray me dauke da ruwa da lemo da glass cup, ta karasa har gabansa ta durkusa ta ajiye masa sannan ta mike zata bar parlon Ceo tace "Ai bamu gama magana ba, zo ki zauna" Mayraah na tafiya a hankali ta karasa inda take zaune da farko ta zauna, Shi dai MD bai dago kansa ba, Ceo tace "I am listening Aliyu" Sai a sannan ya dago kansa yana kallonta cikin nutsuwa yace "Ma'am i think, i can discuss it with you at the second parlor" Ceo na kallonsa tace "Why not here?" Sai kuma ta dafa Mayraah tace "Does she look like a stranger? C'mon Aliyu" Mayraah ta ɗan kallesa suka hada ido, shi ya fara dauke idonsa, a hankali yace "Ma'am, dama ba wani abu bane, kawai na zo in sanar maki zan ajiye aiki ne...." Da sauri Mayraah ta daga kai tana kallonsa kamar yanda Ceo ma ke kallonsa, Shi dai bai dago kansa ba, calmly ya ci gaba yace "I will be going back to Canada to work as a Medical Doctor" A hankali Ceo tace "Why Aliyu?" Sai a sannan MD ya daga kai ya kallesu ya ɗan yi murmushi a hankali yace "I am glad i had the privilege to serve u and ur great hospital, i will forever be grateful, and i will love you to honor Dr Khalil..." Ya sunkuyar da kansa yace "Don ta dalilinsa Mayraah ta fara aiki a asibitin, he did all he can na ganin ta fara aiki, wanda sanadiyar haka yasa tayi reuniting da iyayenta da mu relatives dinta" A hankali Ceo tace "Aliyu" Ya daga kai yana kallonta, tace "Iyayenka suka ce ka ajiye aiki ko?" Girgiza kai yayi murya can kasa yace "Not at all Ma'am, babu wanda yace in ajiye aiki, ra'ayina ne ajiye aiki" Yana kai wa nan ya mike ya isa har gabanta ya ajiye mata letter of resignation dinsa politely, Mayraah dai sai kallonsa take....
[9/5, 9:18 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Ceo tace "Sit down Aliyu" Juyawa yayi ya koma kan kujera ya zauna yana kallonta, Speaking Calmly Ceo tace "Tell me Why u decided to resign?" Ya ɗan yi murmushi yace "I will be going back to Canada Ma, kema kin san i prefer there" Ta girgiza kai tace "There must definitely be something da baka son fada min, but anyway we will discuss about that later, yanzu dai ina son sanin matsayar kaninka akan auren Mary Ann, don a ranan ma da ake magana ban ji yace komai ba sannan if i am not mistaken naji Uncle dinka yace akwai wata maganar a kasa, ya ake ciki yanzu?" MD dai yayi shiru, Mayraah ta kasa daina kallonsa gabanta na faduwa, Ceo tace "I am listening" Sai a sannan ya daga kai ya kalli Mayraah, sannan ya maida dubansa gun Ceo yace "Probably a kai kudin aurensa da cousin sis dinmu a Adamawa" Sosai gaban Mayraah ya fadi ta dinga kallonsa bata ko kiftawa zuciyarta na bugawa da sauri, Ceo dake kallonsa ita ma tace "And why is that? Me yasa su ka yi decision din nan ba tare da sun bari an sake zama ba kamar yanda Abbanta ya bukata?" MD yace "Saboda alamu sun nuna baza a basa auren ta ba, they have other plan that is best known to them, sannan sun ce a bari some other time ne don ayi manipulating dinta because they have a different plan for her, if not tun a ranan she should have spoken for her self, don haka yasa yace ya hakura" Lokaci daya hawaye ya cika idon Mayraah din bata taɓa zaton Musharraf zai ce haka ba, Ceo dake kallon MD tace "Shi da bakinsa yace ya hakura kenan?" MD ya sauke kansa bai dai ce komai ba, Kallonsa kawai Ceo take, mikewa Mayraah tayi ta bar parlon da sauri hawaye na zuba idonta, Ceo ta bi ta da kallo, can ta maida dubanta kan MD, a hankali Ceo tace "Why not try ur luck Aliyu" MD ya daga kai da sauri yana kallonta without blinking, Ceo ta gyada masa kai tace "Zan shige maka gaba" Da mamaki still yake kallonta, can yayi karfin halin cewa "Budurwar kanina ce fa Ma" Ceo tace "So? You just told me yace ya hakura, sannan har za a kai kudin aurensa so i see nothing wrong, ai duk cikakken namiji baya saurin sarewa yanda ya sare, so may be ba rabonsa bace, and what if taka rabon ce" Shi dai kallonta yake ya ma rasa me zai ce, mikewa tayi tace "Bari ta kawo maka abinci, u need not to worry ba masu aiki bane suka yi, she made it herself, in ka gama zaka iya tafiya gobe za mu yi magana i have a call to receive" Daga haka ta bar parlon MD ya bi ta da kallo, dariya ma kawai ta basa don yasan last thing da zai iya on earth kenan dating his brothers once girlfriend balle har aje ga ya aureta, don ko dazu da safe a kaduna babu yanda bai yi da Musharraf kan ya janye maganar cewar ya hakura da Mayraah amma ya ki, Mami kuma na supporting dinsa don bata son a sake breaking heart din ɗan ta for the second time, with the way Ceo reacted a parlon ranan da kuma yanda Ammi tayi saurin backing dinta hakan kawai ya nuna tana da wata manufar daban akan Mayraah shi yasa duk familyn suka ma cire ran za a ba Musharraf Mayraah, wani tunani ne ya fado ma MD, yayi shiru yana nazari, Ceo na tafiya babban dakin da ta sa masu aiki suka kai box Mayraah taga bata cikin dakin, hakan yasa ta fito ta nufi bangaren kanwarta, tana bude kofar dakin ta ganta kwance gefen uwarta dake bacci, karasawa tayi bakin gadon tana kallonta Mayraah dai ta kasa daga kai ta kalleta, Ceo ta mata alamar ta taso don bata son tashin er uwarta, Mayraah ta sauka daga saman gadon a hankali, Ceo ta kama hannunta suka fita daga dakin, bayan ta kullo kofar tana kallon Mayraah soothingly tace "Kukan me kike Daughter? I thought tun wancan lokacin ke da shi kun yi give up akan auren junan ku, har kun hakura ku ka ci gaba da harkokin rayuwarku, so me yasa hakan zai dameki yanzu don yace dama shi ya hakura?" Mayraah ta sunkuyar da kanta trying hard not to cry, Ceo ta jawota jikinta cikin kwantar da murya tace "Cheer up dear, everything happens for a reason, and the excuse he gave wasn't enough yace ya hakura" Ita dai Mayraah ta kasa cewa komai, Ceo ta dago kanta tace "Now go downstairs and serve Aliyu the food u cooked" Ta gyada mata kai, da ido Ceo ta bi ta da kallo har ta fara sauka downstairs, Mayraah na shigowa parlor bata kalli direction din da MD yake ba ta wuce kitchen, cikin minti kadan ta kai masa abincin dining area ta ajiye masa sannan ta tsaya tana kallonsa, Mikewa yayi ya nufi dining area din yana kallon warmer din abincin da plate with cutleries da ta ajiye masa, sae kuma taga ya dau hanyar kitchen ta bi sa da kallo, ba a dau lokaci ba sai gashi ya dawo da wani plate din da cutleries with another cup duk ya wanke, yana zaunawa ya bude warmer din abincin, a takaice tace "To ai har Food warmer din ba a dauraye ba aka zuba abincin, tukunyar da aka yi girkin ma haka" Ya daga kai ya kalleta, ta juya ta bar dining area din... Daren ranan Mayraah kasa bacci tayi abubuwa biyu suka tsaya mata a rai, wanda da ta tuna sai hawaye, na farko maganganun Usman akan wai ta auri Maheer, Maheer fa??? sai kuma na MD da yake gaya ma Ceo wai Musharraf ya hakura da aurenta, daga karshe ta sauka daga gefen Mahaifiyarta ta tafi bandaki ta dauro alwala... Washegari Mayraah na idar da sallan asuba ta sauka downstairs zata girka ma uwarta breakfast, su kansu masu aikin gidan basu fito ba cause it was still early, kallon dining area tayi sai kuma ta karasa can, ta bude warmers din, ga mamakinta taga MD bai ci abincin ba yayi tafiyarsa, ta kalli plate din da ya dauko jiya da cutleries, haka nan sai jikinta yayi sanyi, tana ta tsaye a wajen, bayan wani lokaci ta kwashesu ta kai kitchen. Wajen karfe tara na safe Mayraah ta shigo dakin da akwatinta yake, kulle kofar dakin tayi ta karasa ta zauna gefen gado, bata san ta saka damuwar jiya haka a ranta ba sai da taga ta kasa yin breakfast, gaba daya bata da wani sukuni, ta goge hawayen da ya taru idonta a hankali, lokaci daya tana tunanin when zata gama kuka a rayuwarta, daga wannan issue din sai wannan issue din, yaushe rayuwarta zai koma kamar da, mikewa tayi tana tafiya a hankali ta karasa gaban madubi ta dau wayarta wanda rabonta da shi tun jiya da daddare, tun da abubuwa suka yi ta faruwa a rayuwarta ta rage rike waya, wani lokacin ma mancewa take tana da waya unlike before da take manne da wayarta a ko da yaushe, ta koma ta zauna tana kallon wayar taga miss calls din Ammi kusan biyar, dialing numberta tayi yana fara ring Ammi ta daga, a hankali Mayraah ta gaisheta, Ammi tace "Are you sleeping?" Mayraah ta girgiza kai cikin sanyin murya tace "Aa wayar na daki ne, ya gida Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, ya mutanen gidan?" Mayraah tace "They are all fine" Ammi tace "To maa sha Allah, hope dai kin saki jiki?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Eh Ammi" Har zata tambayi Ya Maheer sai kuma ta kasa, ta sunkuyar da kanta, Ammi tace "Ashe baku yi sallama da Maheer ba kika tafi" Mayraah ta dago kai a hankali tace "Ai baya nan Ammi" Ammi tace "Amma ai ko bai nan ki kan kirasa ki gaya masa ko fita za ki yi Mimi" Mayraah dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Toh zan kirasa Ammi" Ammi tace "Ko fada ku ka yi ne da yayan naki?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Aa Ammi" Ammi tace "Atoh nasan ai bakwa fada" Mayraah dai kawai tayi murmushi, Basu jima suna magana ba Ammi tayi mata sallama, Mayraah ta dinga kallon wayar bayan Ammi ta katse, can tayi dialing number Maheer, bayan few seconds kawai taji ta fasa kiran ta maza ta katse not knowing ya riga ya shiga, bayan ɗan lokaci sai gashi ya kirata, ta ɗan hade rai, sai da ya kusa katsewa ta daga ta kai kunne tayi shiru, Calmly yace "How are you?" Tace "Fine" Yace "Ya gidan?" Tace "Lafiya" Yace "To maa sha Allah" Ta ɗan yi shiru, jin bai ce komai ba tace "Sai anjima" Yace "Ohk, my regards to everyone" Bata ce komai ba ta katse wayar, bayan kusan minti biyar a hankali tayi dialing number Musharraf, wayar bai shiga ba alamar ya sa a Do not disturb ko kuma ya saka ta a busy, lkci daya jikinta yayi sanyi tana ta kallon wayar, a hankali ajiye wayar ta dalilin knocking din kofa da taji ana yi, ta mike ta isa bakin kofar ta bude, daya daga workers din Ceo ce, da ladabi ta sanar mata Ceo na kiranta a kasa, Mayraah ta fita daga dakin ta sauka downstairs, zaune ta ganta a parlon da MD with Dr Khalil, Mayraah na kallon Dr Khalil cike da mamakin ganinsa ta buda ido tace "Dr ina kwana..." Yana kallonta yana murmushi yace "Lafiya lau Mayraah, congratulations Mayraah...." nan da nan hawaye ya cika idonta tana kallonsa ta ma rasa abinda zata ce masa, can ta zauna kan kujera tana goge idonta cikin sanyin murya tace "Thank you Dr, ina yan biyu?" Yace "Suna nan lafiya lau" Ceo ta mike tana kallonta tace "Ki kai masu Breakfast dinning" Dr Khalil wanda wnn shine karonsa na farko da ya zo gidan Ceo ya kalli Ceo da sauri don shi yayi breakfast, amma dai bai iya yace mata komai ba, shi dai MD bai dago kansa ba, Ceo ta bar parlon ta wuce sama, Mayraah na kallon Dr Khalil a hankali tace "Ya Aunty Zainab fa?" Dr Khalil yace "She is fine Alhamdulillah, congratulations once more Mayraah, i am really happy for you with how things turn out" Mayraah ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "I will forever be indebted to you Dr, i will always appreciate you in my life, bazan taɓa mance kulawarka gareni ba da kariyar da ka bani" Tana kai wa nan ta mike ta nufi hanyar da zai kai ta kitchen tana tafiya a hankali nan ko tunanin effort din Dr Khalil a kanta ta dinga yi tun farkon zuwanta Abuja har karshen zamanta ita kadai a Abuja, Dr Khalil ya kalli MD that is pressing his phone, kawai dai yayi murmushi bai ce komai ba, bayan wasu yan mintuna MD ya mike ya nufi hanyar kitchen din Dr Khalil ya ɗan buda ido ya bi sa da kallo.... Juyawa Mayraah tayi jin an bude kofar kitchen din tana ganinsa ta ci gaba da abinda take, ba tare da ya kalleta ba yace "Kar ma ki wahalar da kanki kiyi da nawa, i am not interested...." Ta bi sa da wani kallo ganin ya dau cup yaje yana wankewa zai yi making coffee da kansa, bata san sanda tace "To kai kafi kowa tsafta kake tunani ne?" Juyawa yayi ya kalleta calmly yace "Eh" Ta kyabe baki ta ci gaba da abinda take, ya gama dauraye daurayensa yayi making coffee ya nufi kofa, ta bi sa da wani kallo har ya fita, ta ci gaba da abinda take yi, bayan some minutes ta fita, ta kai ma Dr Khalil Breakfast dinning table, yana zaune area din tare da MD, Ta ajiye masa tana kallonsa tana murmushi tace "Dr ga breakfast, hope dai kai lafiyarka qlau?" Ya ɗan buda ido don bai gane abinda take nufi ba, MD ya ajiye coffee din da yake sha yana kallonta, ko kallonsa bata yi ba zata bar wajen taga wayarsa da ya ajiye yana vibrate, kallon screen din ta dinga yi ganin Dr Musharraf, daukar wayar tayi Dr Khalil ya buda ido yana kallonta da mamaki, bata tsaya wajen ba ta sauka parlor, sannan tayi picking call din kafin ya katse, ta bar parlon gaba daya, MD ya bi ta da kallo, muryar Musharraf taji yace "Good morning" Da kyar tayi gathering courage a hankali tace "Why did u decide to break your promise Musharraf?" Shiru Musharraf yayi bayan yaji muryarta, bata taɓa kiran sunansa ba sai ranan, ta shiga daki ta kulle ta fashe da kuka a hankali tace "I never expect this from you, shi yasa kaki barin mu hadu in maka magana ranan?" Calmly Musharraf yace "Mayraah, we should stop deceiving our self haka" Cikin rawan murya tace "How please?" Yace "Mu yi hakuri, ur parents have better plans for you and you

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login