Showing 417001 words to 420000 words out of 456519 words
gaba da abinda take, bayan few seconds tace "Haka yace maki" Shi dai Maheer kallon Mayraah yake, Mayraah tace "Ehh sai gobe" Ammi bata sake cewa komai ba, Usman ya shigo parlon da sallama Ammi na kallonsa tace "Ka ci abincin?" Usman ya zauna kan kujera yana kallonsu Ihsaan yace "Na ci" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga parlon da plate din da ta ci abinci, tana fita ko 3 minutes ba ayi ba Maheer ya mike kansa a kasa ya fita daga parlon, downstairs ya sauka ya nufi kitchen yana shiga ciki ya ganta tana dafa ruwan shayi, karasawa yayi, yayi hugging dinta ta baya yace "Did you know how much i miss you wife" Kashe gas din tayi da sauri tace "Yaya idan wani ya shigo fa, don Allah ka sakeni" juyo da ita yayi yana kallon kwayar idonta a hankali yace "Billah i miss u so much wife, baki ga har ramewa nayi ba" Ɗan murmushi tayi ta kwantar da kanta kirjinsa ta lumshe ido murya can kasa tace "I miss you more yayana" Ya dago kanta yace "Really?" Hade rai tayi tace "Amma shine baka zo daukan mu a airport ba?" Yayi murmushi yace "Ina hospital then, baby gal, amma kiyi hakuri" Ta juya masa ido tace "Toh na hakura" Yace "Mu tafi gida?" Tace "Ai na riga nace ma Ammi sai gobe" yace "Toh meye a ciki in kin canza mind dinki?" Bai jira cewarta ba ya kama hannunta tana zaro ido ya fita da ita daga kitchen din suka haura sama, kwace hannunta tayi ganin ya nufi bangaren Ammi da ita, ya juya yana kallonta yace "Oh baza ki mata sallama ba" Ta marairaice tace "Ni dai plss ka bari gobe yaya, na riga fa nace mata sai gobe" Bai tsaya ya ci gaba da sauraronta ba ya tafi parlon Ammi yayi masu sallama sannan ya fito, duk magiyan da Mayraah ke masa ya bari gobe bai saurareta ba, haka nan ta sa Hijab dinta ya kama hannunta suka fita daga dakin, tun ma basu bar gidan ba ta fara jin kunya, a haka suka fita kofar gida ya bude mata front seat ta hade rai ta shiga ya kulle sannan ya zaga ya bude driver seat ya shiga. Wajen karfe goma Ammi na zaune parlon Abba tana kallonsa a hankali tace "Yanzu goben za su tafi katsinan kenan?" Abba da idonsa ke kan Tv yace "In sha Allahu" Shiru Ammi tayi, bayan few seconds tayi kasa da murya tace "Kana ganin baza su bari mu rike su ba yallabai?" Abba ya girgiza kai calmly yace "Gaskiya da kamar wuya, a sanda ku ke Saudiyya Yayan baban nasu ya kirani yafi sau uku, so nace masa kuna sauka yau washegari za a kai masu su" Ammi bata san sanda hawaye ya cika idonta ba, har cikin ranta take tausayin marayun taji kuma tana son a bar mata rikonsu da hakan zai yiwu but basu da wani say akansu sai yanda dangin mahaifinsu da mahaifiyarsu suka yi, ta so ta rikesu ta yanda ko da za su yi kukan marairaici bai wuce in sun tuno mahaifiyarsu ba amma ba don sunyi lacking motherly love and care ba, shi dai Abba bai sake cewa komai ba har a sannan idonsa na kan TV, Ammi ta share hawayen da yaki tsayuwa a idonta cike da karfin hali tace "Toh karatunsu fa, they told me they just wrote jamb not long ago" A hankali Abba yace "Na masa maganar yace min kar in damu they will take care of that, kawai dai a kawo masu su katsinan" Ammi ta dinga kallon Abba, can tace "Kamar nisanta su da mu suke son su yi" Abba ya ɗan yi murmushi ya girgiza kai yace "Eh kusan haka, don gani suke za mu ce za mu rikesu" Ammi ta kasa cewa komai har sannan hawaye na zuba idonta, after a while tace "Bana son su yi kukan marairaici ne, ka dai san halina kasan abinda zan iya aikatawa da wanda bazan aikata ba, amma da zan rike yaran nan iyakan rikon da Marigayiya xata masu zan masu" Abba na kallon Ammi yayi murmushi yace "Ae ba sai kin fada ba Hajara i trust you, tunda kika reni Mayraah to ko wa ma za ki rike da amana" Ammi ta goge idonta tace "Kasan wani abu yallabai?" Abba ya kalleta yace "Sai kin fada" Tayi kasa da murya tace "Wallahil azeem tun a ranar da mahaifiyarsu ta zo gaisuwan yaran Maheer naji na janye kalaman da nayi na kan cewar Usman bazai auri er ta ba, why because mun yi magana ta fahimta da kai a ranan da ka kira Mama Ladi ta taho daga kaduna, nauyin baki kawai nayi ban sanar maka ko shi Usman din ba, na sha gaya ma Mariya ni bani da matsala da Hajiya Amina kuma ba abinda ya taba hadamu da ita hasali ma bata taɓa min komai ba, da kai ne nake da issue don ina ganin kamar bani da sauran wani value a wajenka tunda sai ka yanke decision dinka kake sanar min ko yayi min dadi ko kar ya min, wallahil azeem dalilin da yasa nayi reacting haka kenan a parlonka ranan gani nake kamar iyakata kake nuna min ka mayar da ni bora a gidanka, sai gashi daga baya mun yi magana ta fahimta da kai ana ranan da yan biyun Maheer za su rasu, nayi nauyin baki ban sanar da abinda ke raina ba har Hajiya Amina ta rasu, yanzu gani za ayi don naga bata da rai yasa na amince" Abba dake ta sauraronta ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah ya sa mu dace, in mun je katsinan zan ma yayan Mahaifin nasu magana mu ji ya za su ce, don da kaina nake son in mika masu yaran, Usman zai mana booking flight zuwa kano, daga can kanon yayi driving dinmu zuwa katsina" A hankali Ammi tace "Allah ya kai mu" Washegari throughout haka Ammi ta yini babu walwala bayan Abba da Usman sun tafi kai su Eeman katsina, ta rasa dalilin da yasa take jinta cikin damuwa haka, sai taji da ma Mama Ladi na gidan ko ba komai zaka yi dariya ko baka yi niyya ba, wajen karfe hudu na yamma ta kira Maheer bayan sun gaisa tace "Kana gida ne Maheer?" Maheer yace "Aa ina wajen aiki" a hankali tace "Toh shikenan, na zata kana gida ne ince ka taho min da Mayraah" Maheer yace "Is everything alright Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, girki da nake son tayi min ne" Maheer yace "Toh bari in kirata tayi ordering bolt ya kawo ta" Ammi tace "Aa kar ka damu, zan sa Bilkisu tayi, sai anjima" Daga haka ta katse wayar... Bayan magrib Ammi na zaune kan darduma sai ga Mayraah ta shigo tare da Maheer dake biye da ita a baya, Ammi ta dinga kallonsu, Mayraah ta karasa ta ajiye food warmer din hannunta, Maheer ya ajiye warmer din miya dake hannunsa, Mayraah ta karasa gun Ammi ta zauna da murmushi tace "Ina yini Ammi" Ammi ta sauke ajiyar zuciya sosai taji ta samu relieve na damuwar da ya cunkushe mata a zuciya tace "Lafiya lau Mimi, yanzu sai da yasa kika yi girkin" Mayraah na murmushi tace "I cooked ur favorite" Zaunawa Maheer yayi ya gaida Ammi, Ammi ta amsa tace "Ya aiki?" Yace "Alhamdulillah" Mikewa Mayraah tayi ta sauka downstairs don dauko plate da spoon, Maheer na kallon Ammi a hankali yace "Ammi kamar kina da damuwa" Ammi ta sauke idonta jin hawaye ya kawo idonta, cike da karfin hali tace "Maheer baza ka gane yanda mutuwar baiwar Allahn nan ya tsaya min a rai ba, i am feeling guilt da bansan dalilinsa ba, bani da rest of mind kwata kwata" Maheer ya dawo kusa da ita ya zauna cikin kwantar da murya yace "Ammi addu'a kawai take bukata a garemu sai kuma kyautata ma marayun da ta bari, mu ma nan duk lokaci muke jira, sai dai Allah ya sa mu cika da imani" Hawaye na sauka idon Ammi tace "Ameen, but i am really disturbed, i never gave her a chance while she was alive, i am feeling guilty" Maheer ya sauke idonsa, Ammi na share idonta tace "Ina jin zan je wajen Hajja ko sati daya inyi, i need to rest" Maheer ya daga kai yana kallonta, can ya kwantar da murya yace "But Ammi ba yanzu ya kamata ki je ba, just yesterday ku ka dawo daga Saudiya, ki bari in an kwana biyu" Shiru Ammi tayi bata ce komai ba, Maheer yace "Ko Mimi ta dawo nan tayi 2 days so that she can keep u company" Ammi ta girgiza kai tace "Aa, ba komai ai Bilkisu tana nan Maheer" Maheer dai ya dinga kallonta, Ammi ta goge idonta tace "Dama Mama Ladi zata zo ne, ba komai yasa na kara jin kaina cikin damuwa ba sai tafiya da yan biyun nan, tausayinsu nake sosai i am just hoping dangin uban nasu baza su bari su yi kukan marairaici ba, they are too young for that" Mayraah ta shigo parlon da sallama ta tafi ta fara debar ma Ammi abincin da ta girka mata, Kawo abincin tayi ta ajiye ma Ammi a gabanta, Ammi tayi murmushi tace "Thanks daughter" Mayraah ta zauna gefen Maheer tana kallon Ammi, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo da sallama, Ammi ta daga kai da sauri tana kallonsa tace "Kun dawo Usman?" Ya karaso ya zauna a hankali ya gaisheta, Ammi ta amsa tace "Ya ku ka baro su Ihsaan din?" Usman ya sauke idonsa don har sannan he is still heartbroken at the way the twins were crying da za su baro su gidan yayan babansu, without looking at Ammi yace "Lafiya lau" Ammi tace "Abbanku ya shigo ne?" Usman yace "Ehh ya shigo" Mikewa Ammi tayi tana kallon Mayraah tace "Mimi rufe abincin barin inje in dawo" Daga haka ta fita daga parlonta, Mayraah ta juya ta gaida Usman ya amsa, tace "In zubo maka abincin yaya?" Yace "Sallah zan yi Mimi" Daga haka ya mike ya fita daga parlon, Ammi na isa parlon Abba bayan tayi masa sannu da dawowa Abba ya sanar mata yanda suka yi da dangin uban yan biyun Hajiya Amina, Ammi was speechless, can tace "Toh sai yaushe suke ganin za su isa auren?" Abba ya ɗan yi murmushi yace "Baza su bada auren bane ba fa, from the look of things so suke in cire hannu a lamarin yaran gaba daya, they were emphasizing on abinda ya hada ya raba, ko makarantar da yake cewa zai nema masu ba haka bane, from my observation gadon da uwarsu ta bari suke hari, they were even asking me of her Atm cards" Ammi ta kasa rufe baki don mamaki tana kallon Abba, can tace "To yan uwanta fa?" Abba yace "Ita kadai ce ai, duk siblings dinta died of sickle cell, her parent are late, sai distance relatives" Ammi ta kasa cewa komai, after few seconds Abba yace "Yara dai nasu ne, we have no say akan su, kawai iyaka namu mu bi su da addu'a" Abba na kaiwa nan ya mike ya shiga bedroom dinsa. Ammi na zaune parlonta tare da Bilkisu dake ta mata hira Usman ya shigo parlon da sallama, mikewa Bilkisu tayi ta fita daga parlon, Usman ya zauna yana kallon Ammi, sai kuma yayi kasa da kai yace "Ammi dama za a zo gaishe ki ne gobe" Ammi dake kallonsa tace "Wa zai zo gaisheni kuma?" Usman ya daga kai yace "Sunan ta Maryam" Ammi ta kasa daina kallonsa, a hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Mikewa yayi, Ammi tace "Amma..." Usman ya tsaya yana kallonta, a hankali tace "Eeman din kuma fa Usman?" Usman ya ɗan yi murmushi yace "Aa, ai ba wannan zancen kuma Ammi, tunda kika nuna a'a tun a lkcn na bar maganar" Ammi ta girgiza kai tace "Aa Usman, baza ka bar maganar ba yanzu...." Zaunawa Usman yayi yace "Kiyi hakuri Ammi, na bar maganar nan tuntuni, Eeman da Ihsaan a matsayin wa nake garesu yanzu" Ammi was speechless, after a while Usman ya mike yace "Zan je in ci abinci" Da ido Ammi ta bi sa har ya fita daga parlon, Yana dakinsa Ammi ta bi sa, tana daga tsaye bakin kofa tace "Amma zan fita gobe Usman, sai dai wani lkcn ka kawota" Usman dake kallonta yace "To Allah ya kai mu"
Wajen karfe biyun dare Maheer ya farka bai ga Mayraah kusa da shi ba, mikewa zaune yayi after a while don at first yayi tunanin tana bandaki ne, ya sauka daga kan gadon ya fita, dakinta ya nufa yana bude kofar ya ganta zaune kan darduma ta hade kanta da gwiwa tana jin an bude kofa ta daga kai da sauri tana goge idonta, ya karasa kusa da ita yana mata kallon mamaki ya duka gabanta yace "Mimi" Bata yarda sun hada ido ba tace "Sallah nake ne" Cike da damuwa yace "Why are you crying Mimi? Did i offend you in anyway?" Daga kai tayi ta kallesa nan da nan hawaye ya cika idonta, sosai hankalinsa ya tashi ya dagota ya zaunar da ita gefen gado ya zauna gefenta cike da damuwa yace "Don Allah ki gaya min me ya faru wife?" Ta rufe fuskarta a shoulder dinsa tana shesshekan kuka, sosai ta rikita sa ya dinga lallashinta, da kyar ya samu ta daina kukan yana rungume da ita, bayan wani lkci yayi kasa da murya yace "Tell me what the problem is Mimi?" Ta lumshe idonta tana jin wani sabon kukan na taho mata, a hankali yace "Wife" Muryarta na rawa tace "I will write it down tomorrow" Shiru Maheer yayi, yana patting bayanta a hankali yace "Why not now wife?" Ta girgiza masa kai tace "I will tomorrow" Ɗagata yayi suka fita daga dakin nata ya koma nasa da ita, tana rungume jikinsa bacci ya ɗauketa, ya dinga shafa bayanta yana shakan daddadan kamshin da gashinta ke yi ya lumshe ido, a haka shima bacci ya daukesa.... Da asuba Maheer na dawowa masallaci yaga Mayraah bata dakinsa, ya dinga kallon takardan da ta ajiye masa kan gado, ya karasa ya dau takardan ya warware yana karanta content din, zaunawa yayi gefen gado bayan ya gama karanta abinda takardan ya kunsa, after few minutes ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya linke takardan ya ajiye, yana tafiya slowly ya fita daga dakin nasa ya tafi nata, yana bude kofar ya ganta zaune kan darduma, ita dai bata daga kai ba har ya karasa inda take ya duka gabanta yana kallonta.
[10/23, 9:45 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer ya dagota ya zaunar da ita gefen gado, ya zauna kusa da ita yana kallonta, ita dai taki yarda ta hada ido da shi, a hankali yace "Mimi" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, ya kamo hannunta cikin kwantar da murya yace "Saboda haka kike sa ma kanki damuwa? Kin mance komai lokaci ne? Beside we are not in a haste Mimi, and i believe God's time is the best, duka duka yaushe har ma muka zama husband and wife din, C'mon baby girl...." Jawota yayi jikinsa yana murza hannunta yace "Pls bana son in sake ganin kina kuka akan haka on a serious note wife" Ita dai bata ce komai ba, yayi murmushi ya dago kanta yace "Ni da nake son sai mun yi like 2 years showing you how much i love you without any form of barrier" Ta wani kallesa, Kashe mata ido yayi yace "Abin da so nake mu tafi Honeymoon a Maldives, Bora, Santorini, Iceland to witness the beautiful northern light ( aurora borealis) shine zaki dinga kira mana babies tun ba mu je Honeymoon ba, plss the babies should hold on till i take my beautiful princess round the world" Ita dai ta lumshe ido tayi shiru duk tana sauraron sa, yace "Buh Wait, ke yanzu if i should impregnate you da wani idon zaki kalli wa enda kika ce ma aurenmu abomination ne? Ko kin mance yanda kika rike Abba kina ihu ranan da ya kawo ki?" Bata san sanda ta rufe fuskarta a chest dinsa ba da sauri, Yana murmushi yace "Kuma nima dai kunya zan ji aga nayi putting Lil sis dina in a family way, bayan kuma Allah yana kallonmu" Mayraah ta dinga cusa kanta a kirjinsa tana murmushi, Kwaikwayon muryarta yayi yace "Yaya wallahi Allah yana kallonmu fa...." Da sauri ta tashi zata bar masa dakin yayi hanzarin jawota yana dariya ya cire mata hijab din jikinta.... Ammi na zaune parlonta da yamma Maheer ya shigo da sallama ta dalilin kiran da tayi masa tun yana wajen aiki da rana, ya zauna kan kujera yana kallonta yace "Ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ka tashi aikin kenan" Yace "Eh yanzu na tashi" Ammi tayi kasa da murya tace "Dama magana ce akan Usman yasa nace ka zo" Maheer dai kallonta yake hoping ba wani laifin Usman din ya mata ba, Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta koro masa duk yanda suka yi da Usman a jiya da ta kawo masa maganar auren Eeman, Maheer dai yayi shiru, Ammi tace "I don't know ko zaka masa magana ya bar zancen yarinyar da yace zai kawo ta gaisheni, Eeman marainiya ce yanzu, tun mahaifiyarta na da rai ya so ta da aure ni ce nace ban amince ba, yanzu ma dai ba don ni zai yi ba, maraicinta kawai zai duba...." Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Zan masa magana in sha Allah" Ammi tace "Shi sa ma da yace zai kawo budurwar tasa ta gaisheni nace masa bana nan yau" Maheer yace "Ba damuwa, in sha Allah zan yi masa magana" Sai dab da magrib Maheer ya bar gidan bayan Ammi ta basa food warmer din Mayraah ya tafi mata da su gida. Tun da Maheer ya kwantar ma da Mayraah hankali bata sake saka damuwar rashin haihuwa