Showing 324001 words to 327000 words out of 456519 words
tunanin a rayuwarta akwai sanda zata ga wata a matsayin kakarta ba Hajja ba, ta taso tana ma Hajja kallon kakarta ne duk tsawon rayuwarta, a ranan kusan duk matan yan uwan kakanta Alhaji Saminu dake nan cikin garin kaduna suka zo yi ma Mayraah sannu da zuwa tare da yaransu, wasu sa'anninta wasu sun girmeta, wasu ta girmesu ga dai su nan, babban family ne sosai me cike da yara da jikoki, kowa kuma Mayraah yake zuwa gani, ba su suka bar gidan ba kuma sai bayan Magrib. Washegari sai kusan da rana Mayraah ta sauko downstairs don bacci kawai take ta yi tun dazu, Hajiya Halima dake zawarci a gidan tana gyara dankwalin kanta tace "Kin sakko kenan Mayraah" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta karasa ta zauna tace "Eh" Kakarta dai sai kallonta take with love, Hajiya Halima ta mike ta dau handbag dinta tace "Dazu Abba ke tambayarki nace ai kina bacci" Sallama aka yi a parlon duk suka daga kai, Mayraah dai kallonsa take har ya shigo parlon kansa a kasa, Hajiya Ramatu tace "Har ka dawo kenan Daddy" Yace "Eh daxu da safe na dawo" Zaunawa yayi yana kallonta yace "Ina wuni Mama" Tace "Lafiya lau Dr, ya su Mami? Ya jikin nata? Ko da yake mun ma yi magana da ita ai dazu, tace min tana da bakuwa ko" Yace "Haka ne" kallon Aunty Halima yayi ya gaisheta ita ma, ta amsa tace "Baka koma aiki ba kenan Daddy?" Yace "Ina hutu, za ki fita ne" Tace "Wallahi kawata ce ke aurar da 'ya, har an gama biki jiya ban je ba, shine zan je in mata Allah ya sanya alkhairi" Yace "Ohk" Sallama tayi ma Hajiya Ramatu, sannan ta kalli Mayraah tace "Mayraah sai na dawo" Mayraah tace "Allah ya tsare" Sai a sannan ya kalli Mayraah, tana ganin haka ta sunkuyar da kanta, yace "Sannu Amarya" Ta sake daga kai ta kallesa duk yanda ta so kar ta hade rai kasawa tayi, saboda me zai ce mata amarya, amarya kuma kamar yaya, da kyar ta bude baki tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau" Ya maida dubansa kan Hajiya Ramatu yace "Mama Baffa yana nan kuwa?" Tace "Bai jima da fita ba, yace min dai zaka kawo masa magunguna" Yace "Ehh na so in dubasa ne in ga ko there is need in canza maganin" Tace "Ai kam sai can magariba zai dawo" Yace "Toh Allah ya kai mu, ni zan koma, zan dawo bayan magrib din" Tace "Toh shikenan, kana ji Daddy, nayi waya da can iyayen Mayraah nace za a kai ta gidan yaron nan taje ta gaishesu, duk da ya zo dazu tana bacci, to amma dai ta je ta gaishesu, idan ya so daga can sai ku tafi gidanku ta gaida Mami, in zaka dawo da magrib ka taho da ita, bana son hadata da driver, na so Halima duk ta kai ta to jiya ni na tsayar da ita bata je bikin er kawarta ba zata je mata Allah sanya alkhairi yau, ita kuma Mayraah ban san kwanaki nawa iyayen suka deban mata tayi ba" MD yace "Toh shikenan Mama" Hajiya Ramatu ta kalli Mayraah tace "Baby je ki shirya kawunki ya ajiyeki gidan ɗan uwansa kin ji" Mayraah bata ce komai ba ta mike ta wuce sama ita ba fitan ne ma ya tsaya mata a rai ba gidansu MD din da aka ce har can a kai ta ne ya dameta, taje tayi me kuma a gidan nasu, zaunawa tayi gefen gado tasan kilan in aka ji shiru bata sauko ba kakarta zata biyota saman sai ta gaya mata ita dai bazata gidansu Musharraf ba, ai kam bayan kusan minti talatin sai ga Hajiya Ramatu ta shigo dakin, da mamaki take kallonta tace "Baby baki shirya ba?" Mayraah ta sauke idonta a hankali tace "Umma ni bana son inje can gidan nasu" Hajiya Ramatu ta karaso gefenta ta zauna tace "Wani gidan kenan? Ko gidansu Aliyu?" Mayraah ta gyada kai, Hajiya Ramatu ta dafata cikin kwantar da murya tace "Kin ga Mamin bata da lafiya, kuma tasan kin zo, ko da muka je Abuja ranan alhamis din nan da ya wuce kawai karfin hali tayi amma bata jin dadi, bayan mun dawo sai da aka mata ƙarin ruwa, banda zuwan da za muyi Abujan da ta koma kano tun last week sai ana sauran kwanaki biki zata dawo, kiyi hakuri kije sai ki mata ya jiki kin ji Baby, zan ce masa kina gaisheta ya dawo da ke gida" Mayraah dai jikinta yayi sanyi sosai, babban tashin hankalinta kar ma taje gidan su hadu da Musharraf, Hajiya Ramatu dake kallonta cikin lallami tace "Yi hakuri" Mayraah ta mike a hankali ta tafi zata dauko kayan da zata saka, Hajiya Ramatu ta bi ta da kallo tana murmushi, ta lura kamar an shagwabata kawai fitowa fili ne shagwabar bai yi ba, a tare suka sauko downstairs tana rike da hannunta bayan ta shirya, MD ya mike yana kallon Hajiya Ramatu yace "Ta dai gaya ma mijin nata ko?" Hajiya Ramatu tayi murmushi tace "Haba ai sai da muka nemi izini Daddy bazata fita haka ba babu izini" Mayraah ta dinga kallonsa a ranta tana ji kamar ta fashe da matsanancin kuka, ita har a zuciyarta bata yarda ita matar aure bace har yanxu, a haka dai suka bar gidan Hajiya Ramatu ta rakasu har parking space, bayan sun bar gidan sai da suka yi nisa MD dake driving idonsa a kan titin gabansa cikin calm voice yace "I wish you a happy married life Mayraah, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a masu albarka" Ta juya ta kallesa, nan da nan hawaye ya cika idonta amma bata ce masa komai ba, ita Allah ya gani da duk abinda Usman ya gaya mata shekaranjiya take aiki a zuciyarta, to yace mata everyone is against the marriage and she should continue seeing her self as Miss, to me yasa za a dinga ce mata happy married life, happy married life with who? To shine har yanzu dai bata gane ba.... Har suka isa gidan Babanta MD bai sake cewa komai a motar ba, Mayraah was flabbergasted ganin Mom dinta a gidan baban nata, she was soo happy ta rungumeta bayan ta bude masu kofa, ashe ita bata san tun ran juma'a Mahaifiyarta ta dawo gidan babanta ba bayan Abba ya shawo kan Ceo da tace sai bayan sati biyu, Aaria ma ta ji dadin ganin er tata sosai duk da tasan ta zo kadunan don Abdallah ya gaya mata, Mayraah ko ta kan baban nata bata bi ba duk hankalinta na kan uwarta da ta ja ta suka shiga ciki. Suna gidan har bayan la'asar sannan MD ya sanar ma Abdallah zai kai ta wajen Mami ne don da magrib Umma tace ya maidota gida, Abdallah yace "Toh shikenan Aliyu, nima zan shigo gidan da magrib din" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi bayan da Abbanta ya shigo ya samesu da Aaria a daki yace ta fito Aliyu na jiranta, duk zaton ta za a barta ta kwana gidan, ita kanta Aaria felt somehow don da an bar mata ita ta kwana amma dai bata ce komai ba suka fito parlor tare da Mayraah da mood dinta ya canza gaba daya, A haka Mayraah ta bar gidan tare da MD kana kallon fuskarta kasan ranta bai so ba, yayi driving dinta zuwa gidansu na kaduna, Mayraah dai na biye da MD har ya bude kofar Parlon sai da ya bari ta fara shiga sannan shi ma ya shiga, sai sinne kai take kamar munafuka har ya kai ta parlon Maminsa, shi ya nuna mata kujera sannan ta zauna, Mami ta fito daga Bedroom dinta jin an bude kofa, ganinta tace "Aa Mayraah sannu da zuwa, ashe ku ne tafe" Mayraah ta sauka kasan carpet ta zauna sannan ta gaisheta cikin sanyin murya, tayi mata ya jiki.... Mami na murmushi tace "Koma saman kujera kiyi zaman ki" Mayraah bata koma kan kujeran ba, MD na kallon Mami yace "Wani maganin Musharraf ya kawo maki da yace kar ki sha wancan din?" Mami ta kalli kofar dakinta tace "Jiddah kawo magungunan nan Daddy ya gani" Bayan few seconds wata doguwar yarinya da bazata wuce 23 years ba ta fito daga dakin, Mayraah ta daga kai tana kallonta bata ko kiftawa, fara ce sosai kamar ka taɓa ta jini ya fito, her lips where soo pink, kyau kuwa kamar ita tayi kanta, duk da dankwalin dake kanta kana iya hango tulin baƙin gashinta da tayi parking, bata da wani jiki but shape dinta is breathe taking, Yarinyar ta karaso cikin parlon tana kallon Mayraah, tayi ɗan yi murmushi har dimple dinta ya nuna tace "Sannu da zuwa" Mayraah ta sauke kanta ta amsa mata, Ledan maganin hannunta ta tafi ta mika ma MD ya amsa yana duba magungunan ciki, sai kuma ya kalli Mami yace "To meye wnn din ya siyo maki?" A takaice Mami tace "Ya dai fi min wannan da ka ban nake ta wahala" dariya Jiddah tayi MD ya jefa mata wani kallo, ya ajiye ledan maganin a kasa ya mike ya fita daga parlon, Mami tace "Atoh, ka ban magani yana ta wujijjiga ni tun shekaranjiya, wnn kuma gashi tun safe da na sha lafiya lau" Jiddah ta mike tana murmushi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai gata ta dawo rike da tray din ruwa da lemo ta ajiye ma Mayraah, ita dai Mayraah bata sake yarda ta kalleta ba, Jiddah ta koma kan kujera ta zauna, Mami na kallon Mayraah tace "Ya su Amminki da Abba?" A hankali Mayraah tace "Duk suna lafiya, suna gaisheku" Mami tace "To maa sha Allah" Haka Mayraah tayi ta zuba ido taga MD ya zo ya maidata gidan kakanninta amma shiru har six, kana ganinta kasan a takure take a parlon, abincin da aka kawo mata ma bata ci ba, tana ganin Magrib ya gabato taji hankalinta ya tashi, gashi ta kasa ce ma Mamin ai ance ta dawo gida kafin magrib, a haka dai taje tayi alwala tayi sallah a Parlon, tana zaune kan darduma aka bude kofar parlon ta daga kai da sauri ya shigo da sallama, Mami tace "Wai fita kayi dama" Yace "Aa ina Chalet" Kallon Mayraah yayi sannan ya kalli Mami yace "Mami zan maida ta gida" Mami tace "Da Magariban nan zaka maidata gida? Ina laifin gobe da safe" Mayraah taji gabanta ya fadi, MD yace "Umma cewa tayi in maidata da magrib" Mami tace "Aa bai kamata ba, tomorrow is another day in sha Allah, zan kira Maman" Mayraah ji tayi kamar ta rusa ihu a parlon hankalinta yayi mummunan tashi, MD yace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga parlon, sai ga Jiddah ta shigo, Mami na kallonta tace "Jiddah ki bata kananun kaya ta canza na jikinta" Jiddah ta kalli Mayraah tace "Ohk" Mami tace "Bi ta ku je Mayraah" Mikewa Mayraah tayi tana tafiya da kyar tabi bayanta suka fita daga parlon Mami. Har isha Mayraah na makale a dakin, abinci ma sai kawo mata daki aka yi, bata taba shiga takura irin haka ba a rayuwarta, ji take kamar a ƙaya take, Jiddah dai sai harkar gabanta kawai take alamar dai ita ma bata sakewa da stranger, Mayraah sai dai tayi ta satan kallonta, wajen karfe tara Mayraah dake zaune dakin ita kadai ta mike da kyar ta dau tray din abincin da aka kawo mata zata fitar da shi kar abun nata yayi yawa, don Jiddan ce ma ta kawo mata abincin, kar ta ga kamar jira take ta fitar da tray din, gidan kuma da alama babu me aiki, a hankali ta bude kofar dakin ta fito corridor, walking slowly ta nufi hanyar da zai kai ta main parlor din gidan, sosai gabanta ya fadi jin dariyar Musharraf tun kan ta karasa cikin parlon, ita tama taba ganin yana dariya haka kuwa? Ai sai dai murmushi, zaune yake tare da Jiddah a parlon, giving her a look that can melt heart, ita kuwa Jiddah taki yarda ta kallesa sai danna wayarta kawai take duk da ba waje daya suke zaune ba amma basu da wani nisa da juna, a hankali ya matso da kansa kusa da ita ko me yake ce mata oho, ta ɗan matsa daga wajen ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da danna wayarta tana ɗan murmushi, gaba dayansu babu wanda ya lura da Mayraah, a hankali ta juya zata koma inda ta fito taga MD ya fito daga Parlon Mami, yace "You want something?" Bata yarda ta kallesa ba ta girgiza kai da sauri tace "Aa zan kai kitchen ne" Ya amshi tray din a hannunta, sai ya ga hawaye idonta, shiru yayi yana kallonta, can ya fita parlon ita kuma ta wuce daki da sauri, nan tsakiyar parlon ya ajiye tray din yana kallon Jiddah yace "Take it to the kitchen" Jiddah ta daga kai tana kallonsa, yace "Sai kuma ki bar bakuwa ita kadai a daki?" Jiddah ta ɗan buda manyan idanuwanta tace "Yaya nima fa jiya na zo, am i not also a stranger?" Musharraf dake kallon MD yace "Do we have visitor?" MD yace "Kaje ka tambayi Maminka" Daga haka ya bar parlon, Ya kalli Jiddah yace "Bakuwa Mami tayi ne?" Jiddah ta daga kai ta kallesa a karo na farko tun shigowarsa parlon, kasa daina kallonta yayi baya ko kiftawa, don tun dazu yake fama da ita ta dago kai taki, cikin sanyin muryarta tace "Eh, dazu ta zo, naji Mami na ce mata Mayraah...." Musharraf yace "Oh Mayraah, ta zo kenan, she is my cousin's daughter" Jiddah tace "Eh haka Mami tace min" Yayi kasa da murya yace "Toh kin ci abincin Baby?" Sauke idonta tayi tace "Eh" Yace "Wait for me kar ki shiga ciki pls, bari in je mu gaisa da ita" Daga haka ya mike ya bar parlon ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, don bata iya kallonsa sai dai a sace, Musharraf na shiga wajen Maminsa yaga Mayraah bata nan, hakan ya sa ya dawo dakin da take yayi sallama, tana zaune kasan carpet, MD kuma na tsaye jikin kofar yana mata magana ganin Musharraf yayi shiru, komawa gefe yayi ya basa hanya ya shigo, Musharraf na shiga dakin da fara'arsa yace "Amarya ya kike, ashe kin zo gidan mu, i just got to know now, ya kika baro yan Abuja" Ta ki kallonsa da kyar tace "Lafiya" da murmushi yace "Toh you are welcome amarya" Daga haka ya juya ya fita daga dakin, duk yanda Mayraah ta so controlling kanta ta kasa ta fashe da kukan da bata shirya ba wanda kuma bata san dalilinsa ba, MD ya zauna kan kujeran dake dakin yana kallonta yace "What's ur problem Mayraah? Meye na kuka" Girgiza masa kai tayi cikin kuka tace "Sir amma Umma fa tace ka dawo dani gida da Magrib" Yace "Ke ni babanki ne ba Sir ba, don't sir me again" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yace "Kamar yanda nake gaya maki yanzu you can see for ur self ya nuna maki he has moved on, to ke meye damuwarki? Beside in ma auren ne kin rigasa ai, don ranan da za ayi bikinki shi za a daura nasa auren, accept this is the best for you Mayraah, i promise you it's the best, ke matar aure ce yanzu" Tace "Ni ka daina ce min matar aure" Ya ɗan buda ido yace "To matar me zance maki" Tana Girgiza masa kai cikin rawan murya tace "Yayana fa ake cewa an aura min, how will i cope with this plss, ta yaya zan iya zama da shi as my husband, isn't it weird? wallahi ina masa kallon wanda muka fito ciki daya ne, all my life a haka muka taso da shi, why all of a sudden zai zama mijina kuma" Kuka take sosai, MD ya ɗan yi murmushi yace "Ba dai wannan Calm gently Dr din ba da na sani? To u are very lucky Mayraah, just our few encounters together in hospital when u were sick na lura shi mutum ne me kirki da saukin kai da sanin ya kamata, bai dauki kansa komai ba, imagine he was also a Dr but he was patient har sai sanda aka basa izinin shiga wajenki a ICU yake shiga, unlike that other one, har number Maheer ina da shi yanzu haka kuma muna magana, i was a bit relieved da naji shi ne mijinki, but i know it will be hard for u kasancewar kun taso gida daya kina masa kallon wanki as you've said, kinga Jiddan nan few years back an so in aureta but i decline don ina mata kallon warce muka fito ciki daya tunda a gidansu na tashi since when i was a toddler, ina gidan aka haifeta ta girma as my lil sis shi sa ni kallon jinina sosai nake mata, but in ur on issue ga yanda situation ya juya at the end, amma i am assuring you u will be proud of this one day one time, Allah ya riga ya rubuto mijinki ne shi din, nothing can change that Mayraah, kiyi hakuri" Ita dai hawaye kawai take tana kallonsa, yace "Don haka ina baki shawaran ki cire duk wani abu dake ranki, ke matar aurece ko tunanin Musharraf kika kawo ranki sai Allah ya tsine maki, nima kawai don babanki ne yasa na zauna nan ina maki magana if not bazan ma fara zama dake ba, kin dai ga shi harkan gabansa ma kawai yake yana jiran ranan aurensa eagerly, ke kuma da naki auren a kai kin zauna kina masa kuka, to kukan me? Kukan kina sonsa har yanzu ko me?" A hankali ta girgiza masa kai, yace "Toh kiyi hakuri and say Alhamdulillah in every situation" Goge idonta tayi a hankali bata ce komai ba, ya ɗan yi murmushi yace "I now see ta