Showing 402001 words to 405000 words out of 456519 words
kanki" Ammi dai bata ce komai ba tana share hawayen da ya kawo idonta, Mama Ladi ta juya tana kallon Abba tace "kai kuma Mamuda banda neman magana da rashin son zaman lafiya irin naka ban ga dalilin da zaka ce lallai lallai sai Usman ya auri er Amina ba, kishiyar da kai kanka kasan har yanzu matar ka bata yi na'am da ita ba saboda kishi irin namu mata, amma duk da haka tana dannewa a ranta..." Abba yace "Ta fadi takamaiman abinda Aminar ta mata da taki na'am da ita har yanzu" Mama Ladi tayi karaf tace "Ta aure mata miji mana, akwai laifin da ya wuce wannan..." Mikewa Ammi tayi tana share idonta tace "Mama kawai ya sallameni ya bar min gidan kawai, aure ne nace na gama, kawai ya kama gabansa bana yi kuma" Tana fadin haka ta shige daki, Mama Ladi tayi kasa da murya tana kallon Abba tace "Kayi hakuri Mamuda, da bata sonka ma bazata fara wannan azababben kishin a kanka ba wallahi, kasan mu mata bamu da control wajen kishin abinda muke so, kishiyar ce ka mata ita a bazata shi sa da duk ta zama haka..." Abba yace "Amma ni abinda nake son in fahimta shine menene aibun auren Usman da er wajen Amina?" Mama Ladi tace "Ai duk aibun da take hangowa kai ba lallai ka hango ba, er kishiyar ta fa aka ce, kawai don a zauna lafiya kayi hakuri ka janye batun nan Mamuda, babu inda aka ce sai lallai ka hada ɗan ka aure da er kishiyar uwarsa, Ammi ba abar walakantawa bace a gareka ina me tunasar da kai, duk sanda ta kwafsa maka kayi kokarin dinga yi mata uzuri kana tuna halaccin da tayi maka a baya sai kaji zuciyarka ta wanke" Abba yace "Sannan ni rabuwan da take fadi kanta tsaye ne ke daure min kai, daga anyi magana daya biyu sai tace a sallameta, a sallameta akan me?" Mama Ladi tace "Duk kishi ne ya rufe mata ido, ka yi mata kishiya a sanda bata yi zato ba bata yi tsammani ba, hakan kuma ya doketa sosai, don haka sai kana lallabata kana kauda kai a wasu abubuwan, nan da shekara daya zuwa biyu sai kaga ta hakura gaba daya ta dawo dai dai, shekara da shekaru kana tare da ita da dadi ba dadi sannan kun san halin juna bai kamata kana yin amarya ka dena mata uzuri ba ka dinga nuna gazawarka na yi mata uzuri, ina lura da yanda kake gasa mata duk maganar da ta zo bakin ka yanzu a gaban kowa, kuma sam da ba haka kake ba wllhi Mamuda, wannan auren da kayi ne ya lalata mana kai ya sauya maka tunani akan komai na gidan ka, shi yasa yanzu idan na zo gidan nan bana wuce kwana biyu don duk ka canza kamar ba kai ba, kaga kuwa Ammi dole ta ga kamar baka bukatarta ne yanzu a rayuwarka, gani zata yi a dole kake tare da ita saboda yara don kafi karkata hankalinka kan amaryarka Amina" Abba dai bai ce komai ba duk yana sauraron Mama Ladi, Mama Ladi ta mike tace "Bari in je kuma in sallami yan hanjina, anjima za mu yi magana ta fahimta da kai" Tana fadin haka ta fice daga parlon, Abba ya fi minti uku zaune parlon bayan fitan Mama Ladi, can ya tashi ya nufi dakin Ammi..... Wajen karfe shidda na yamma Mayraah ta fito daga kitchen bayan ta gama girkin da take, har a sannan ruwa ake duk da bai kai na daxu karfi ba, sosai garin yayi sanyi don rigar sanyi ne ma jikinta, ji take kamar zazzabi ne zai rufeta tun dazu bata jin dadin jikinta, bata tadda Maheer a parlon ba, zata wuce dakinta taji anyi knocking kofar parlor, juyawa tayi tana kallon kofar sai kuma ta karasa bakin kofar don tana ji daxu Maheer na aiken mai gadi amma dai bata san me yace ya siyo masa ba, bude kofar parlon tayi lkci daya tayi turus tana kallonta daga sama har kasa babu ko kiftawa, tana goye da yaro daya a bayanta tana jijjigasa saboda kukan da yake, dayan kuma ta daurasa kan kafadarta shi din ma dai jijjigasan take yana kuka, they were all drenched in rain water, Haseenah na kallon Mayraah cike da gadara tace "A bamu hanya" Mayraah da taki barin bakin kofar tace "Ai ba gidan ubanki bane da za a baki hanya...." Er dariya Haseenah tayi tana kallonta da kyau tace "Eh ba gidan ubana bane, kamar yanda kema ba gidan ubanki bane, amma su kuma twins kinga ai gidan ubansu ne don haka babu karamar shegiyar da ta isa ta hanasu shiga gidan ubansu" Mayraah tace "Zan ko nuna maki na wuce karamar shegiya don wallahi wallahi baki isa ki shigo gidan nan ba daga ke har su" Dariya sosai Haseenah tayi tana jijjiga Aryaan dake kuka sosai yana tari, Aymaan dake bayanta ma tarin yake, tana kallon Mayraah da kyau tace "Ni fa na zata da muka hadu a kaduna zan ganki da cikin naki yan biyun haihuwa ko yau ko gobe sai naga ba haka ba, ke baki yi cikin haifa masa yara ba kuma kice zaki nisanta sa da wa enda Allah ya basa? Ke har kin isa ki raba shi da yaransa in ba dodewar kwakwalwa irin taki ba?" Mayraah tace "Kin baro masu dodadden ƙwaƙwalwa a kano, don in ba dodewar kwakwalwa ba baza su bari ki biyo hanya da kananun yara haka ba, sannan tsabar dodewar kwakwalwarsu basu tunatar maki babu aure tsakaninki da shi wanda kika zo garin nan dominsa ba, banza kawai gantalalliya er wahala" Wani dariya Haseenah tayi har da shewa tace "I am promising you this, in kika ga Maheer bai maida ni gidansa a matsayin matarsa ba sannan uwar tagwayensa to mutuwa yayi, ko kuma ke ce kika mutu bakiyi witnessing ya maida aurenmu ba, yan biyu fa na haifa masa ke kuma ko cikin dayan ma kin kasa dauka har yanzu" Da sauri Maheer ya karaso cikin parlor bayan ya fito daga dakinsa jin kamar hayaniya, buda baki yayi yana kallon Haseenah da yaran a jike jagab, fita balcony yayi da sauri yana kokarin amsan Aryaan a hannunta yace "What's wrong with you Haseenah? Are you mad? menene yasa za ki fito min da yarana cikin ruwa?" Haseenah dai bata tankasa ba, yana amsan Aryaan ta sakko da Aymaan dake bayanta ta daurasa saman kafadarta, juyawa Maheer yayi da sauri zai shiga parlor da yaron hannunsa don cire masa jikakkun kayan jikinsa, Haseenah ta ɗan yi murmushi tana ma Mayraah wani kallo tana biye da Maheer ita ma zata shiga parlon, Mayraah ta tare hanya tana kallon Maheer da kyau tace "Ka daukesu kaje duk inda za ku amma baza a shigo min gida ba" Kallonta Maheer ya dinga yi baya ko kiftawa, can yace "Are you kidding me?" Mayraah tace "Abinda ya fi kidding... In kuma kace lallai sai kun shiga to wallahi tallahi sai dai ka ci gaba da zama da ita da yaran a gidan nan" Maheer that was stunned yace "Mayraah"
[10/16, 9:12 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah bata ko kallesa ba zata kulle kofar parlon fuskarta a murtuke ya dakatar da ita yace "Let me get my car key" Yana fadin haka ya ajiye yaron hannunsa dake kuka a nan kasan balcony din ya bi ta gefenta ya shiga cikin parlon, Haseenah tayi wani murmushi tana kallon Mayraah da kyau, cike da gadara tace "Ai in kin san wata baki san wata ba, kuma a banza don kin hanasa shiga gidan da yaransa tunda gashi a kan idonki dai zai kai mu inda ya dace ya kai mu saboda muna da muhimmanci a garesa, ko banza dai ya gwada maki mun fi ki value da matsayi a gunsa, we are far ahead of you...." Fitowar Maheer yasa Haseenah tayi shiru tana jijjiga yaron bayanta dake kuka, ya dau Aryaan dake ta kukan shi ma a kasan tiles din Balcony ya nufi parking space da shi har a sannan ruwan da ake bai tsaya ba, Haseenah na murmushi idonta a kan Mayraah da ta bi Maheer da kallo tace "Sai kuma ayi hakuri sai sanda kika gansa, in kina da hankali da tunani yanzu sai ki gane yaransa sun fi ki value, don kin hanasa shiga ciki da mu to baki isa ki hanasa ya kai mu wani wajen ba, sai a koma ciki ayi zaman jiransa in ma kin gansa kenan yau, banza kawai" Tuni Mayraah ta kulle kofar parlon, ta jingina da kofar lkci daya taji hawaye na zuba idonta numfashinta na yin sama sama, Haseenah ta bi bayan Maheer zuwa parking space, back seat ya bude ya kwantar da Aryaan, ya mika mata hannu yace "Sauko min da shi" Haseenah ta kwance Aymaan dake bayanta Maheer ya amshesa ya bude bayan motar shi ma ya kwantar da shi kusa da ɗan uwansa, Haseenah na kokarin shiga motar strictly yace "Kar ki kuskura ki shigar min mota" Da mamaki take kallonsa baki bude, she wasn't expecting this from him, kawai ji tayi yana kiran security din bakin gate, security din ya taho da sauri, Maheer yace "Bude min gate, ina fita kuma ka tabbatar ka fitar min da wannan matar daga cikin gidan nan, sannan yau ya zama rana ta karshe da ka bude mata gate ta shigo min gidana" Yana fadin haka ya zaga ya bude driver seat ya shiga motar, Haseenah that was speechless har sannan ta sake baki tana kallon Maheer sai kuma ta kalli direction din entrance din shiga gidan don tabbatar da Mayraah bata wajen tana kallon abinda ke faruwa, da sauri ta juya kamar munafuka ta nufi gate ganin Mayraah bata bakin kofar, fita tayi daga gidan ta tsaya a kofar gida tana jiran fitowar motar Maheer, yana fitowa ta marairaice tace "Ban gane kar in shiga motar ka ba Maheer, yara na ne fa cikin motar and they need me the most a halin nan da suke ciki, kamata yayi ka bani listening ears kaji dalilina na zuwa nan kafin...." Tuni Maheer yayi zoom off ya bar ta tsaye wajen ta bi motarsa da kallo baki bude, she was soo shock bata taɓa tunanin zai yi haka ba, to ina za shi kuma da yaranta? Da sauri ta bi bayan motar da har yayi corner. Ammi ta mike da sauri tana kallon Maheer da ya shigo parlonta da yara tace "Maheer daga ina haka da yara cikin ruwan nan? Where did u get them from" Bata jira amsar sa ba ta nufesa da sauri ta amshi Aymaan daga hannunsa, Mama Ladi da ta saki baki tace "An shiga uku, meye haka kuma yara a jike jagab, a ina ka samo su ni Ladi?" Tuni Ammi ta tafi dakinta da Aymaan don parlon ma akwai sanyi, Mama Ladi ta amshi Aryaan tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, garin yaya ruwa ya ma yaran duka haka" Dakin Ammi ta shiga da shi shima, Maheer ya zauna kan kujera ya tallabi chin dinsa with different thought running his mind, babu bata lokaci Ammi da Mama Ladi suka cire ma yaran jikakkun kayan jikinsu, Dama da sabbin kayansu a gidan wanda surkar Dr Khalil ta kawo ma Ammi bayan an kai yaran Kano, Ammi ta shafesu da Rub sannan aka sa masu kayan, Tana rike da daya Mama Ladi na rike da daya, sosai jikin yaran yayi zafi hancinsu har ya toshe, sai bin su Ammi suke da ido ba kuzari tattare da su, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "To ko dai hauka Mashir din ya fara ne da zai taho da su cikin ruwa? Babba ma ya ya kare da dukan ruwan sama balle yan yaran nan da basu da haƙƙin kowa a kansu, a gidan uban wa ma ya samo su ma dai tukun, ba suna gun uwarsu ba a kano?" Kwantar da Aymaan dake tari Ammi tayi ta lullubesa sannan ta mike ta fita daga dakin ta dawo parlor tana kallon Maheer tace "Me yake faruwa ne Maheer? A ina ka samo yaran nan haka?" Sai ga Mama Ladi ta fito ita ma bayan ta kwantar da Aryaan, Maheer ya daga kai ya kalli Ammi, sai kuma ya dauke idonsa, a takaice ya gaya masu abinda ya faru tun daga jiya da Haseenah ta shigo Abuja da su, amma yayi excluding part din abinda Mayraah tayi masa bai gaya masu ba, Mama Ladi ta saki salati tace "Allah ya tsine ma Hasinu albarka, wallahi so kawai take ta kashe yaran ta bar mu da bakin ciki don taga sun shiga ranmu, banda haka tun da garin Allah ya waye ake tsuga ruwa a Abuja balle tace ta fito da su ne ruwan ya tsuge da su a hanya, da gangan ta shiga da su cikin ruwan don ta musguna mana, kuma ma ya aka yi tasan gidanka tukun?" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ban sani ba wallahi" Mama Ladi tace "Toh amma kai da ta kai su can din ba sai ka amshe yaranka ka shiga da su ciki ba Mera ta basu agajin gaggawa tunda ita ma Nas ce amma saboda rashin lissafi irin naka ka sake shigowa cikin ruwa da su ka kawo mana su nan? Ni kaina da ruwa ya dokeni dazu zazzabi nake yanzu haka balle en jariran nan, jikinsu na can yayi zafi ƙau sai tari suke, anya Hasinu zata gama da duniya lafiya kuwa? To kuwa ita da su har abadan abidina, cikin sauki ta dawo mana da su sai kuma ta kama gabanta, Allah ya isa tsakanin mu da ita kawai" Ammi dai gaba daya ta rasa abun cewa tayi shiru tana tsaye bakin kofar dakinta, Mama Ladi tace "Baka ga ta zama ba, sai ka sake fita cikin ruwan ka nemo masu maganin mura da na zazzaɓi, don wllhi ba ruwan wasa ne ya jibgesu ba hatta pampas dinsu a jike yake, Ammi dai ta mulke masu jiki da man zafi" Dai dai nan aka bude kofar parlon Haseenah ta shigo a jike, rabewa tayi jikin kofa ta tsaya kamar munafuka ruwa na diga a jikinta, Mama Ladi ta gwalo ido tace "Kun ga matsiyaciya, to uwarki kika biyosa nan kiyi? Maza fita kar in saka masu gadi su daga min ke sama su yi waje dake er iska, ko ba ke kika haifi yaran na ba baza ki shiga ruwa da su ba balle ke kika haifesu, ban taɓa ganin azzalumar uwa ba sai a kanki tunda uwata ta haifeni" Haseenah ta marairaice tace "Mama wallahi da gangan dai bazan shiga ruwa da yarana ba, ina ta kiransa baya dagawa kuma duk yaran basu da lafiya shine dalilin da yasa na taho da su inda yake..." Maheer da temper dinsa ke rising ya dinga kallonta trying to control himself, Juyawa Ammi tayi ta shiga bedroom dinta, Mama Ladi ta nufi kofa cikin daga murya tana cewa "Fita er iska, uban wa zaki ma bayani kamar an tambayeki, in sha Allahu ke da yaran nan har duniya ta nade makira kawai, fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke, " Haseenah sai matsar kwalla take tana kallon Mama Ladi, Mikewa Maheer yayi da sauri jin Ammi na kwalo masa kira ya nufi dakin, Mama Ladi ta gwalo ido ita ma ta juya da gudu ta bi bayansa, sosai gaban Haseenah ya fadi don daga jin yanda Ammi ta kwalo ma Maheer kira ba lafiya ba, bata san sanda ta nufi dakin da gudu ba ita ma, zaro ido tayi ta dafe kirjinta ganin Aymaan in a convulsive state Maheer na rike da shi trying to give him first aid, wani ihu ta kwala ta shige dakin da gudu a gigice ta daura hannu a ka ta durkusa gabansu tace "Nashiga uku na lalace, don girman Allah Maheer ka rufa min asiri nothing should go wrong with my son" Babu wanda ya lura da ita a wajen don duk hankalin Ammi da Mama Ladi yayi mugun tashi, Mama Ladi sai zaga dakin take tana rafka uban salati, bayan some minutes yaron ya dawo dai dai amma sai tari yake kamar yanda Aryaan dake hannun Ammi ke tarin shi ma, sai a sannan hankalin Mama Ladi ya dawo kan Haseenah dake durkushe kusa da Maheer duk jikinta na rawa, buda baki tayi tace "Uban wa ya shigo mana da ita kuma, yaushe ta shigo mana nan...." Da sauri Mama Ladi ta fizgo zanin Ammi dake kan gado ta dinga shauda ma Haseenah iya karfinta tana cewa "Shegiya tashi ki fita, uban wa ya shigo da ke, fita er iska kawai" Haseenah ta mike tana matsar kwalla ta nufi kofa ta fita daga dakin tana waigen Aymaan, Ammi da har sannan hankalinta a tashe yake tace "Maheer ko dai mu tafi asibiti ne?" A hankali Maheer yace "Zan fita in siyo masu magani yanzu, ko mun je maganin dai za a basu" Mikewa yayi don ana kiran magrib ya nufi kofa ya fita daga dakin, Haseenah dake tsaye parlon sai hawaye take ta nufesa da sauri ta durkusa gabansa tace "Pls Maheer kar komai ya samu yarana plss" Ko kallonta Maheer bai yi ba ya fice daga parlon yana kokarin controlling temper dinsa... Babu bata lokaci Maheer ya dawo gidan bayan ya je pharmacy ya siyo masu magunguna, har a sannan Haseenah na durkushe parlon Ammi idonta har ya kumbura saboda kuka, tana ganinsa muryarta na rawa tace "Don Allah Maheer ku bar ni in kasance kusa da yarana basu da lafiya, let them feel my warmth plss" Maheer bai ko kalleta ba ya karasa cikin dakin, Ammi na sallah, haka ma Mama Ladi, ya ajiye ledan maganin hannunsa da Cerelac da madara da ya siyo masu ya nufi yaran yana kallonsu... Ammi na idar da sallah ta juya tana kallon Maheer, durkushe ta gansa bakin gadon kan kneels dinsa ya rungume Aymaan jikinsa ya runtse ido, mikewa Ammi tayi dai dai lokacin