Showing 255001 words to 258000 words out of 456519 words
taga MD har yayi shigewarsa cikin airport din ya bar ta wajen a tsaye, Business class Ceo ta sa MD yayi masu booking, but because he wants to rest kasancewar he wasn't too fine a conference ranan kawai sai ya biya masu ticket din first class. Sune farkon boarding plane din, Mayraah bata taɓa shiga first class ba iyakarta business class, wajen karfe takwas da rabi jirginsu ya tashi, ya kira flight attendants telling them he is taking nothing don bai ma son a zo a tambayesa, bayan Flight attendants din ta bar wajen, after few minutes Mayraah ta juya ta kallesa taga ya kwanta ya lullebe da duvet, two hours into the flight Mayraah tayi bacci. Bayan awa daya ta farka, ta mike zaune tana kallonsa, har sannan a kwance yake idonsa a lumshe sae karamin towel dake forehead dinsa, ta mike tana tafiya a hankali ta nufi inda yake, bude ido yayi da sauri jin motsi kusa da shi, ta ɗan koma baya kamar munafuka tace "Are you okay?" Flight attendant ce ta iso wajen with pain reliever, Mayraah ta bi ta da ido har ta basa maganin sannan ta zuba masa ruwa a daya daga cikin glass cups da aka ajiye masa da goran ruwa uku, bai amshi glass cup din ba ya dau bottle water instead ya kurbi ruwan ya sha maganin, bayan Flight attendants din ta ajiye glass cup din hannunta ta kalli Mayraah don tana son sake masa labulen wajen for his privacy, kafin tace komai Mayraah tace "We are together" Flight attendants din ta mata murmushi tace "Okay Ma" juyawa tayi ta bar wajen, Mayraah ta kai hannu kan karamin towel din forehead dinsa taji a jike yake da ruwa, cire towel din tayi don har a sannan he is running temperature, ta tafi toilet ta kara jika towel din sannan ta dawo, ta duka kusa da shi zata daura a goshinsa ya fixge towel din yace "Don't worry, je ki ci gaba da baccin ki" Ta wani hade rai tace "But i am a nurse" Daga sama har kasa ya kalleta yace "Nurse with no license and working experience, pls go back to ur seat Madam and sleep" Kwace towel din tayi tace "I don't mind what ever u will say, but i am sticking to the ethical obligations of a Nurse to a patient" Daga haka ta fara goge masa forehead dinsa that is hot with the towel din, kallonta kawai yake, sai kuma ta cire duvet din jikinsa tace "You are running temperature so there is no point in covering ur body with a Duvet" Ko minti goma ba ayi ba ya sake komawa bacci. Kafin su isa Nigeria he felt much better saboda painkillers da ya sha a jirgin, karfe biyu da rabi na dare suka sauka airport din Abuja. Bayan ta dauko akwatinta ta kalli inda yake zaune ya jingina da kujera idonsa a lumshe, shi dama bai taho da komai ba, ta karasa wajen da yake zaune tace "Zan kira yayana ya daukeni, u can leave me here" Ya bude ido da sauri yana kallonta yace "Karya kike ba yayanki bane" Tace "To naji ba yayana bane" Ya mata wani shegen kallo ya mike ya fara tafiya, he is just acting he is fine whereas he is sick, ta bi bayansa suka fito haraban Airport din, taxi suka shiga.... Bayan sun fita daga airport din yace "Ni zan gaya masa address din gidanku da kika yi shiru?" Tace "To ai naga kasan gidan tunda ka taɓa bin Dr Khalil" Juyawa yayi ya kalleta da sauri, ta maida hankalinta kan driver tana gaya masa address din gidan da zai kai ta, MD yace "Shi Khalil din ne yace maki ni na bi sa?" Without looking at him tace "Ai ba sai ya gaya min ba i saw it with my eyes" Bai sake tanka ta ba cause ba shi da strength din hakan, 10 mintues into the journey ya fara bacci, ta ɗan juya ta kallesa, da zata matsa ta koma edge din kujeran kuma dai kawai ta basa access to her shoulder, har suka isa gida yana bacci, Mayraah ta juya ta kallesa, after few seconds calmly tace "I am home" A hankali ya bude ido, sai kuma ya gyara zamansa da sauri, ta ɗan kyabe baki ta bude motar tace "Sai da safe" Daga haka ta sauka ya bi ta da kallo, drivern taxi din ya sauka ya dauko mata akwatinta a booth, bayan ta amsa ta kalli MD dake kallonta, sauke ido tayi ta daga masa hannu sannan ta juya da sauri ta nufi gate din gidan ya bi ta da kallo, Kwankwasa gate din tayi taji security na tambayarta waye, bayan ta basa amsa ya bude gate din ta shiga cikin gidan ya kulle gate din, sai a sannan MD ya sa taxi driver din ya ja motar suka bar unguwan. Mayraah ta zauna saman kujeran dake compound ta ciro wayarta tayi dialing number Maheer, sai da ya kusa katsewa ya daga a hankali yace "Mimi" Ta wara ido tace "Sorry i woke u up" Yace "Ya aka yi? Hope ba ciwon cikin bane?" Tana murmushi tace "Aa ba shi bane, ai tun ranan da aka min allura bai kara ciwo ba, yaya na dawo" Maheer ya mike zaune yace "Da gaske?" Tace "Eh" Yace "Yaushe?" Tace "Just now" Yace "In taho airport inyi picking dinki ne?" Tayi dariya tace "Eh ka taho" Yace "Right away" Daga haka ya katse wayar, mayar da wayar tayi cikin handbag dinta, ta daura handbag din kan akwatin sannan ta karasa chalet da sauri ta tsaya bakin stairs yanda bazai ganta ba har sai ya sauka kasa, bayan kusan minti bakwai sai gashi ya fito sanye da jallabiya, yana sauka stairs din tayi er kara saitin fuskarsa, ya juya da sauri yana kallonta da mamaki, ta kyalkyale da dariya tace "Wallahi nasan ka ji tsoro Yaya" Tun da Haseenah taji ya bude kofar dakinsa dama ta farka daga baccin da take a nata dakin, sai ta fito parlor, bai bi ta kanta ba as usual, tana ganin ya fita compound ta taho window tana leka waje, kawai kuma sai taji muryar Mayraah, Maheer dake kallon Mayraah daga sama har kasa yace "Wa yayi dropping din ki?" Mayraah na murmushi tace "MD dinmu, taxi muka shiga a airport din" Yace "Har kin kara haske daga zuwa Uk, are you sure we are not relocating there?" Tayi dariya tace "Wani haske? Bayan sanyi ake a can sosai, har fa mura sai da nayi, ni dai bana son kasar saboda sanyi" Yana murmushi yace "To ina akwatin?" Ta nuna masa inda ta bar akwatin tace "Yaya i bring you so many chocolates irin wanda kake so" Yace "Really" Tace "Wallahi" Gun akwatin ya nufa ta bi bayansa, Haseenah dake jikin window tana jin duk abinda suke cewa ta bi su da ido.
[8/14, 4:15 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah na biye da Maheer dake dauke da akwatin ta suka shiga main building din gidan, ya kunna wutan parlon cause everywhere was dark, ya juya yana kallonta yace "Nasan dai kinyi bacci a jirgi" Tana cire jacket din jikinta tace "Eh nayi bacci amma ai ba da yawa ba, though i am not sleepy now" Ya kalli agogo dake nuna karfe uku da kusan rabi yace "Yunwa fa?" Ta wara ido tace "First class fa muka shiga yayana, kasan me da me na ci?" Da mamaki yace "First class? Ke da wa? Hospital din ne ya biya maku first class?" Tayi murmushi ta zauna tace "Wa enda muka je conference din mana, tare muka dawo da su ai" Ya zauna yana facing dinta yace "So how was the conference like?" Ta langwabar da kai tace "Duk fa ban je ba Yaya" Yace "Baki je conference din ba?" Ta gyada masa kai tace "Kawai a gidanta na tsaya duk 2 days din nan" Shiru Maheer yayi bai ce komai ba amma deep down him yana mamakin amfanin zuwa da ita kasar da aka yi, can yace "Ku nawa ku ka je?" Tace "I think 4, yaya Abba yana nan?" Maheer ya girgiza kai yace "Yana kano" tace "Ohk.... yaya har bana son in tuna cold din kasar" Yayi murmushi yana kallonta, Hira ta dinga yi masa a parlon yana biye ta duk da baccin da yake ji don dama wajen karfe biyu ya kwanta, ya fara bacci ba dadewa ta kirasa, har kusan lokacin da za a tada sallan asuba suna zaune parlon, suka ji ana saukowa downstairs, Maheer ya kalli agogo yaga nan da minti goma za a tada sallah a masallaci, tuni Mayraah taji kamshin turarensa ta gane shi ne, yana saukowa parlor tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai tana ci gaba da yi ma Maheer maganar da take masa, kallo daya shi ma ya mata ya nufi kofa ta bi sa da kallon gefen ido har taga ya bude kofa, tayi kasa da murya tana kallon Maheer tace "Yaya yaushe ya dawo?" Maheer yace "Jiya da rana" Ganin ya ja kofar parlon bayan ya fita ta wani taɓe baki tace "Yaya kasan abinda yayi min ne a UK?" Maheer yace "Me ya ma ki?" Tace "Ai babu ruwana da shi daga yanxu, kawai fa daga...." Mikewa tayi da sauri ganin Usman ya dawo Parlon ashe yana jikin kofar bai tafi ba, tana ganin ya nufota ta ruga sama da gudu tayi bangaren Ammi, ya juya ya fice daga parlon, Maheer dai ya bi sa da kallo, Mayraah na shiga parlon Ammi ta kulle kofar tana turo baki, Ammi da ta fito daga bandaki ta taho parlon jin alamar an shigo, buda baki tayi tana kallonta tace "Mayraah" Dariya Mayraah tayi ta tafi da sauri ta rungumeta tace "Ammi na dawo" Ammi tace "Ikon Allah, yaushe kika dawo?" Mayraah tace "Dazun nan wajen karfe uku" Da mamaki Ammi tace "To wa ya dawo dake gida?" Mayraah tace "MD din mu" Ammi tace "Maa sha Allah, welcome daughter" Mayraab bata yarda ta bar bangaren Ammi ba don tsoron tafiya dakinta take ta hadu da Usman, wajen karfe shidda Ammi ta sauka downstairs don hado mata shayi ta kawo mata da bread, Ammi na ajiye shayin ta tadda ta ta jinginar da kanta da kujera ta fara bacci, Ammi ta dafata tace "Tashi ki sha shayin sai kiyi wanka ki kwanta" Mayraah ta buda ido a hankali tace "Ammi akwatina na downstairs" Ammi tace "Aa babu akwati downstairs, ko Maheer din ya kai maki daki" Mayraah tace "Zanyi brush in fara wanka kafin in sha shayin" Ammi tace "To je kiyi, in kin gama sai ki hado wani shayin bari in sha wannan" Mikewa Mayraah tayi ta fita daga bangaren Ammi da sauri ta tafi dakinta, tana shiga ta kulle da makulli. Wajen karfe takwas tana parlon Ammi ta gama breakfast kenan Usman ya shigo parlon, tun da ta kallesa sau daya taki dago kai Ammi ta amsa gaisuwar da yake mata, yace "Zan je kaduna Ammi" Ammi tace "Kayi breakfast din?" Yace "Nayi" tace "Toh Allah ya tsare hanya, Allah ya kiyaye, yau din zaka dawo?" Yace "Aa sai Monday in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu lafiya, ya tsare hanya, drive safely pls" Yace "In sha Allah" Daga haka ya mike ya nufi kofa, Ammi ta kalli Mayraah tace "Kun gaisa ne da shi?" Mayraah ta gyada kai tace "Tun daxu da na dawo" Mikewa tayi ta dau wasu chocolates da turare daya ta fita daga parlon, dakinsa ta nufa gabanta na faduwa, ta ɗan yi knocking kofar a hankali sannan ta bude, yana rufe karamin box dinsa, taki bari su hada ido ta kulle kofar, a hankali tace "Yaya don Allah kayi hakuri, i am so sorry about what happened" Jin yayi shiru ta daga kai ta kallesa, calmly yace "Wani abu ya faru ne?" Ta ɗan yi murmushi tace "Bayan nasan fushi kake da ni har yanzu, ni dai plss i am sorry yaya, ga tsaraba nan nayi maka" Bata jira cewarsa ba ta tafi ta bude jakar da ya ke rufewa ta zuba masa chocolate din a ciki ta kulle, sannan ta karasa inda turarrukansa suke a dakin ta ajiye turaren hannunta, sauke idonsa yayi daga kallonta, ta karaso kusa da shi tace "Pls ka hakura yaya?" Yace "I will think about it" Murmushi tayi tana kallonsa. Da yamma Maheer na zaune parlon Ammi, Mayraah ma na parlon, Ammi ta girgiza kai not convinced with what Maheer is telling her tace "Ni manufar tafiya da ita nake son sani tun da ba a bar ta taje conference din a kasar ba, why will they insist on going with her? This doesn't sound right Maheer, wallahi ni fa hankalina yaki kwanciya da aikin nan har yanzu" Maheer ya kalli Mayraah dake kallon Ammi, Ammi ta girgiza kai tace "Ni bazan boye maku ba kawai naji ban ma yarda da ceo din ba, ta yaya daga fara aikin yarinya ko wata biyu ba ayi ba ta dage sai anje wata kasar da ita bayan ga tsofaffin ma'aikata a asibitin, kuma tun da Usman ya dawo yace min gidanta ta sauke ta na kasa nutsuwa, a ina aka taɓa yin haka?" A hankali Mayraah tace "But Ammi she is so kind...." Ammi ta mike tace "Ban yarda da kindness din nan nata a kan ki ba, ai ba ke kadai bace worker a asibitin, why is she just being kind to you?" Daga haka ta yi wucewarta daki Mayraah ta bi ta da kallo, can ta daga kai ta kalli Maheer dake kallonta a hankali tace "Ammi zata ce kar in kara aikin ko?" Maheer ya kwantar da murya yace "Bazata ce ba, do not worry i will talk to her" Mikewa Mayraah tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon ta koma dakinta. Da yammacin Washegari da ya kasance Saturday Mayraah ta gama jera kayanta da aka goge mata a press ta fito daga dakin zata sauka downstairs ta hango Maheer zaune Parlon shi kadai yana danna wayarsa, makalewa jikin karfen stairs din tayi tana kallonsa kamar ta samu TV, ta fi minti shidda tsaye a gurin kawai taga ya dago kai, da sauri ta manne da bango yanda bazai ganta ba tana zaro ido, amma tuni ya ganta, mikewa yayi ya nufo stairs din, tana ganin haka ta juya da gudu ta wuce bangaren Ammi, ganin wajen wayam ba kowa kawai ya sauka downstairs ya ci gaba da zaman sa. Da daddare Mayraah ta fito parlon Ammi zata tafi dakinta ta kwanta don har ta fara bacci ta hadu da Maheer a hanya zai je gun Ammi, yana kallonta ganin taki kallonsa zata wuce bayan ta gaishesa yace "Mayraah" Juyowa tayi tana murza idonta a hankali tace "Yaya bacci nake ji" Ya kama hannunta yace "I know... is there anything u are wanting to say?" Bata yarda ta kallesa ba still tace "Something? Like what?" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, ta ɗan yi murmushi murya can kasa tace "Not at all yaya, dazu kawai naga kana ta gyangyadi shine nake kallon ka fa" Ya wara ido kafin yace komai ta marairaice tace "Zan fara baccin fa a tsaye a nan Yaya" A hankali yace "To fara" Jingina tayi da bango ta lumshe ido slowly, kallonta kawai yake babu ko kiftawa, bayan few seconds ita ma ta bude ido tana kallonsa, bude kofa da taji anyi ya sa ta kifta ido da sauri ta janye hannunta daga nasa, juyawa yayi ya nufi downstairs ta bi sa da kallo har ya sauka, Ammi ta karaso tana kallonta da mamaki tace "Me kike a nan? Baki tafi kin kwantan bane?" Kame kame ta fara yi sai kuma ta wuce dakinta da sauri, Ammi ta bi ta da kallo har ta shiga dakin ta kulle. Mayraah na isa daki kwanciya tayi ta lumshe ido, gaba daya ta nemi baccin ta rasa, tayi ta juye juye har daga karshe baccin ya dauketa wajen karfe sha daya da rabi. Da safe tana kitchen tana dafa ma Ammi shayi Maheer ya shigo kitchen din, tana gane shi ne taki dago kanta tana ci gaba da abinda take, Calmly yace "Good morning Mimi" Still not looking at him tace "Good morning yaya" Ya ajiye cup din hannunsa ya juya ya fita, sai a sannan ta bi sa da kallo sannan ta ci gaba da abinda take. Tana daki wajen karfe sha daya wayarta ya fara vibrate ta jawo ganin Dr Khalil ne tayi picking don tun da ta dawo sau daya ya kirata ya mata sannu da zuwa, bayan sun gaisa yace "Hope kin huta enough?" Tana murmushi tace "Sure" Yace "MD yace a gaya maki ki kawo account details dinki today, za kuma ki amshi ID card...." Mayraah tace "But i wrote down my account details the other day, ID card kuma ai gobe monday ba sai in amsa ba goben" Dr Khalil ya ɗan yi murmushi yace "To dai hakuri za kiyi ki zo tunda yace ki zo yau din, shi ma kin ga baya shigowa sundays infact baya ma da lafiya tun da ku ka dawo har drip sai da na sa mashi, but he is around today, ko zuwa karfe daya ne sai driver ya kawo ki, nasan duka duka baza ki wuce minti talatin ba a asibitin, kin ga driver din ma zai iya jiranki" Mayraah da gaba daya mood dinta ya canza don bata son fitan, a hankali tace "Ohk" Bayan ta katse wayar ta mike ta je ta samu Ammi a parlorn ta, bayan ta sanar mata abinda Dr Khalil ya kirata ya gaya mata, a hankali Ammi tace "Mimi, ina ga fa hakura za kiyi da aikin nan" Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi babu ko kiftawa, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Wallahi hankalina yaki kwanciya har yanzu, i am so disturb this past days na rasa dalili, ina ji a jikina kamar akwai abinda zai faru"