Showing 327001 words to 330000 words out of 456519 words
inda kika samu first class din da kike daga mana shoulder da shi a hospital, haba an gaya maki first class a nursing science child's play ne" Hade rai tayi tana kallonsa tace "Zaka iya tambayarsa, tun da na fara course din nan every semester da first class nake fita tun ma bai san ni ba, ni ba abinda ya min, and it was my first class that attracted him to me, ko dashing mark baya yi ma student shi in gaya maka" MD yayi er dariya yace "Ko duk jikina kunnuwa ne...." Bai jira me zata ce ba yace "Hope you will take all my advice?" A hankali ta gyada masa kai, yace "Good, if there is anything that bothers you ko a wajen Maheer ne you can get my number cause I will be going back to Canada soon" Hade rai tayi don bata wani son ana danganta ta da Maheer har ranta, ita ce masa tayi ta amince zasu zauna da Maheer as husband and wife ne, Kauda zancen tayi tana kallonsa tace "Kai yaushe zaka yi auren" Gyara zama yayi, sai kuma yayi murmushi yace "Tunda kanena da daughter na sun yi auren ai shikenan, Musharraf, Jiddah, and you" Tace "Ni naka auren nake tambaya" Yace "Babu budurwa ae" Ta ɗan buda ido tace "To in maka budurwa?" Yace "In dai bata da rashin kunya da rainin wayo kamar ki" Bata san sanda tayi dariya ba tace "Ai ko i have a new girlfriend for you" Yace "Really?" Tana gyada kai tana murmushi tace "Yea, Maleeha is her name" Yana gyada kai yace "That's sweet.... Maleeha" Da sauri ta jawo wayarta tace "Bari in kirata" Nan da nan ta shiga contact dinta ta nemo number Maleeha ta kira, tasan bata da wnn number nata, yana fara ring Maleeha ta daga cikin calm voice dinta tayi sallama, Mayraah ta amsa tace "Maleeha" Daga daya bangaren Maleeha tace "Mayraah? What happened to ur line pls? Nayi ta kiranki bana samun ki" Mayraah na murmushi tace "Did you ask Yaya Usman about me?" Tayi er dariya tace "Haba ai bama communicating ne da shi shiyasa, but naji yayana yace min ai kun koma Abuja" Mayraah tace "Ehh haka ne, kina kano ne?" Maleeha tace "Wallahi mun zo bikin cousin sister dinmu ne muna kd" Mayraah ta zaro ido tana kallon MD dake sauraron conversation dinsu, tace "Da gaske, wani anguwa?" Maleeha tace "Unguwar Dosa" Mayraah tace "Kai haba nima fa ina kd, bari inji wani anguwa nake i will get back to you" Daga haka ta katse wayar tana kallon MD tana murmushi, ya gyada kai yace "She's got a cute voice" Mayraah tayi dariya tace "Don Allah ina ne unguwan Dosa?" Yace "Nan anguwan take" Mayraah tace "Lahhh da gaske" Sai kuma ta mike ta dau Hijab dinta tace "To don Allah mu je sai in kirata ta turo mana address din gidan da take" Buda baki MD yayi yana kallonta yace "Kamar fa baki da hankali" Tsayawa tayi tana kallonsa, yace "Da auren naki zaki fita gantali? Ko dai kin zata auren wasa aka maki" Nan da nan mood dinta ya canza, yace "Kirata ta turo maki address din, i will get her for you tomorrow kafin in maida ke Malali" Komawa tayi ta zauna a sanyaye, ya ciro wayarsa yace "Give me her number" Sai a sannan ta ɗan yi murmushi tace "Sai ma ka ganta yaya, soo pretty and cute, idonta ma fa ba irin namu bane wllhi" Shi dai kawai yayi murmushi, nan ta fara karanto masa number yana dialing a wayarsa, tace "Kaga kawai sai ka koma Canada da ita...."
*To fatee shanono sai a dau na annabawa, Allah bai kaddara za a canada da MD ba, Parrot ta samar maki wani MDn a kano*😂😂😂😂
[9/13, 9:01 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Mayraah taji ta samu relieve sosai bayan fitar MD daga dakin, ta mike ta koma saman gadon dakin tana danna wayarta, number Usman tayi dialing yana fara ringing ya daga a hankali tace "Yaya ina yini" Yace "Lafiya lau Mimi, how are you?" Tace "I am fine" Shiru tayi, sai kuma tace "Kun je gida lafiya yaya?" Usman yace "Sai yanzu kika tuna ko mun je lafiya ko bamu je lafiya ba Mimi" Ta ɗan buda ido, a nan tayi realizing ashe tun jiya ai ya kamata ta kirasa taji ya hanya, sai ta langwabar da kai cikin sanyin murya tace "To na manta ne" Yace "Good, ni ai ban tafi jiya ba na tsaya yin wani abun ne, i left for Abuja today in the evening...." Shiru tayi jin abinda yace, lokaci daya tace "To shi yaya fa?" Usman yace "I don't know, I can't reach him..." Da mamaki tace "Baka tambayi Ammi ba?" Yace "Ke me ya hanaki tambayarta?" Bata sake cewa komai ba, sai kuma a hankali tace "Sai anjima" Yace "Ohk Mimi" Daga haka ta katse wayar, kwanciya tayi bayan ta ajiye wayar, cikin mintuna kadan bacci ya dauketa, ko awa daya bata yi ba tana baccin ta farka kamar warce aka tada, ta mike zaune sai kuma ta jawo wayarta tana kallon agogo taga karfe goma da yan mintuna, number Ammi tayi dialing, Ammi na dagawa tace "Baki yi bacci ba dota?" Mayraah ta sauke idonta cikin sanyin murya ta gaisheta, Ammi tace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhamdulillah" Ammi tace "Ya su Hajiya?" Mayraah tace "Lafiya lau.... Ammi yaya ya dawo gida ne?" Ammi tace "Eh ya dawo dazu" Rasa abinda zata ce tayi don ita ba Usman take tambaya ba, can dai tayi karfin halin cewa "Ya Maheer?" Ammi tace "Ohk jiya shi ya dawo, you want to speak to him?" Zaro ido Mayraah tayi tana girgiza kai da sauri tace "Aa dama kawai na manta ban kira bane in ji" Ammi tace "Ohk, they are back Mimi" Da sauri tace "To sai da safe Ammi" Ammi tace "Alright dear, kiyi addu'a kafin kiyi bacci...." A hankali Mayraah tace "Toh" Daga haka ta katse wayar ta koma ta kwanta, bayan ta kwanta da kamar minti sha biyar sai ga Jiddah ta shigo dakin, Mayraah tayi kasa da idonta da sauri kamar me bacci, Jiddah ta karaso daya side din gadon ta ajiye wayarta ta cire Hijab din jikinta ta linke, kayan baccinta ta dauko sannan ta shiga bandaki, Mayraah dai bata dago idanuwanta ba balle asan ba bacci take ba, Jiddah na shiga banɗaki wayarta dake gefen gado ya fara ring, sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon wayar, Yaya M... ta gani jikin screen din ta dinga kallon digit din ganin na Musharraf ne, wanda yayi blocking dinta, a hankali ta mayar da kanta daya gefen, bayan wani lokaci Jiddah ta fito tayi shirin bacci ta karaso ta zauna side din gadon ta dau wayarta, duk da kiran nasa da ta gani sai bata kirasa ba, tana kwanciya sai gashi ya kara kira ta daga.... har kusan karfe sha biyu waya suke da Musharraf, Mayraah dake jin duk conversation dinsu kawai ta mike zaune daga karshe cause the phone call is disturbing her ears kuma bacci take so tayi, sauka tayi daga kan gadon, ta nufi kofa ta fita daga dakin, Jiddah ta bi ta da kallo don ta zata bacci take, parlor Mayraah ta tafi duk da babu wani haske ta karasa ta zauna 3 sitter tana kallon direction din da hasken da ya ɗan haska parlon ke fitowa, Mikewa yayi bayan ya ajiye textbook din hannunsa ya shigo parlon ya kunna wuta yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, yace "Ba ki yi bacci ba?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Kilan ta dameki da waya ko?" Gyada masa kai kawai tayi, yace "Mu je ki kwanta a wani dakin" Ta mike ta bi bayansa tana tafiya a hankali, ya kai ta har wani daki ya bude mata kofar dakin ya kunna fitila yace "Good night" Shiga cikin dakin tayi tace "Nagode" Ya kullo kofar ya bar wajen, bin dakin ta dinga yi da kallo wanda da alama nasa ne, ta karasa ciki sae da ta fara rage Ac din dakin sannan ta kashe wutan ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa. Washegari da safe Mayraah na gama breakfast ta dinga baza idon inda zata ga MD ya maida ta gida don ita har ta shirya, ashe jiya da ya koma can gidan kakaninta da magrib sae da Hajiya Ramatu ta basa kayanta a karamin jaka ya tafi mata da shi, da safe tana wanka dama Mami ta kawo mata jakan har dakin da take, Allah Allah kawai take ta bar gidan ba tare da ta sake haduwa da Musharraf ba, don tun da gari ya waye bata gansa ba bata kuma fatan ta gansa. ita babban takaicinta da tuno yanda yayi blocking dinta kawai, wato shi yana ma da babban dalilinsa na blocking dinta at once, sai kuma yanda yayi ta avoiding dinta farkon zuwansu Kaduna gidan Grandparent dinta yaki barin su hadu balle tayi masa magana, kasa daurewa Mayraah tayi ta mike ta tafi bangaren Mami, Mami na kallonta tace "Kinyi breakfast din Mayraah?" Mayraah tace "Na yi" Zaunawa tayi tana kallon Mami a hankali tace "Mami da safen nan za a kai ni can gidan?" Mami ta ɗan buda ido tace "Har kin gaji da nan din Mayraah?" Mayraah sai taji kunya, sai a sannan taga kamar fa bai kamata tayi maganar ba ma, da kyar ta girgiza kai lkci daya ta wayance tace "A'a Mami, dama Yaya zai kai ni gidansu wata kawata ne..." Da mamaki Mami tace "kawarki kuma?" Wani yayan? Ko Aliyu?" Mayraah ta gyada mata kai da sauri, Mami ta ɗan yi murmushi tace "Nan din ma don ya zama dole ne aka kawo ki Mayraah, da aure a kanki fa yanzu, auren da ko tarewa baki yi ba, so it's not possible to go out anyhow now, ita kawar ta zo nan din mana ta sameki" Dai dai nan MD ya shigo parlon, Mami dake kallonsa tace "Sai yanzu ka tashi Daddy" Yace "Yanzu kuma, no... karatu nake" Mami tace "Kai kace zaka kai ta gidan kawarta? Ko dai baka da kai ne?" Ya buda ido yana kallon Mayraah, da sauri ta girgiza kai tace "Aa Mami dama yace min sai dai ta zo nan...." Zai yi magana Musharraf ya shigo parlon, Mami na kallonsa har ya shigo ya zauna, shi dai MD kallon gefen ido yayi masa ya dauke kai, Calmly Musharraf ya kalli Mayraah yace "Good morning Mayraah" Ba tare da ta kallesa ba a takaice tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" Mikewa tayi ta nufi kofa, kafin ta fita taji Mami dake kallon Musharraf tace "Lafiya son? What happened?" Sounding pissed off Musharraf yace "My expensive white Duvet da shekaranjiya na fara amfani da shi Daddy ya sa min a washing machine" Mami ta kalli MD da damuwa tace "Me ya kai ka dakinsa Aliyu?" MD yace "Ni bana repeating duvet sau biyu, kuma ina son kwanciya ne a dakin, me yasa bazan sa a washing machine ba? He should do better in his sanitary practices, why use duvet for 2 days" Daga haka ya fice ya bar masu parlon, Mami tayi shiru wato shi yasa jiya wajen karfe biyun dare ya shigo mata daki ya dau duvet, har cikin ranta take tausaya ma macen da zata auri Aliyu. Bayan azahar MD da Mayraah suka bar gidan zai maidata gidan grandparent dinta, she was so palliate leaving the house at that moment, duk da tun safen nan bata sake haduwa da Musharraf ba, sannan sun yi waya da Maleeha tace mata zata zo da yamma, amma da ta zauna gidan nan har zuwa yamma to gwara kawai kar ta hadu da Maleehan, bayan sun yi nisa Mayraah ta kalli MD a hankali tace "Yanzu baza ka iya kai ni in ga kawar tawa ba, even if it's just for 5 mins, tace min da yamma zata zo kuma kaga ni gida zan koma yanzu" Ya kalleta yace "Toh sai mu koma ki jirata zuwa yamman" Da sauri Mayraah ta girgiza kai tace "Aa pls" Shi dai driving kawai yake, can tace "Amma da ka amshi numberta jiya ai ce min kayi zaka kirata, shi ne ashe baka kirata ba har yanzu...." Yace "Ohh na manta fa, but why not give her my number sai ita ta kirani, don ni mantawa zan dinga yi" Mayraah ta sake baki tana kallonsa, bata sake ce masa komai ba har dai suka isa Malali, bata san jiya kawai don ya kwantar mata da hankali ba ya biye ta da number Maleeha. Ammi na zaune parlon Abba tana ta kallonsa bayan ya gama magana, jin bata ce komai ba ya daga kai ya kalleta yace "Bai maki dadi ba ko Hajiya?" Ajiyar zuciya ta sauke ta girgiza kai tace "Not at all...." Yace "Mayraah is an only child and an only grandchild, it's nothing don an yi bikin a can Hajiya, sai su kawo mana ita Abuja" Ammi ta sunkuyar da kai tace "To gyaran jikin fa? ni nan jira nake ta dawo ai a fara" Abba yace "Sai aka ce maki su din ma can baza su mata abinda ya kamata ba? Hear what u are saying fa" Abba yayi murmushi yace "We can't just hijack both the Bride and Groom a wajenmu Hajiyata, ku nan kuyi naku taron kawai, su ma can su yi, kinga bayan biki sai su kawo mana amarya, in ma dakinta za su kai ta su kai ta, we can't ignore the fact that su ma suna da hakki a kanta" Ammi tace "To wai a ina ku ka zauna ku ka shirya wannan abu ban sani ba?" Abba yace "Alhaji Saminu yaje Kano wani taro dazu, so mun hadu, sai yake tambayata ya mu ka tsara bikin, a Abujan za ayi komai da komai, ni kuma kawai sai naga we are not being fair, wannan ne dalilin da yasa na gaya masa wannan tsarin don mu fita hakkinsu, and he was very happy about it" Ammi tace "Amma baka yi shawara da ni ba Yallabai, kasan irin burin da na ci na bikin Mayraah kuwa? Yanzu shkkn sai dai kawai a kawo min ita?" Abba yace "Gaskiya hakan shine adalci, su yi bikinsu a can su kawo mana amarya, ku ma kuyi naku a nan" Ammi bata sake cewa komai ba tana ta tunanin irin burin da ta ci na bikin Mayraah tun ma ba a fasa aurenta da Musharraf ba, shkkn duk burin nata ya tashi a banza kenan, Abba ya katse mata tunani yace "So now, shi Maheer din me yace maki yake shiryawa, i mean events or anything of such, ko baku yi magana ba" Ammi ta kalli Abba tace "Yace ba abinda za ayi fa, babu yanda ban yi da shi ba wllhi yaki, ko zaka masa magana kai, kaga tunda Kaduna za ayi taron bikin ae za su dinga expecting Dinner ko kuma dai wani program da mu za mu yi daga nan" Abba yace "Tunda yace baya so kawai a kyalesa, ai dama ba wai wani amfani ke gare taron ba, albarkan auren kawai ake nema, so i am in support of him" Ammi dake kallon Abba a hankali tace "A aurensa na farko ma fa babu abinda aka yi lokacin duk muna cikin tashin hankali yallabai, wannan ma sai ayi sa haka fisabilillahi?" Mikewa Abba yayi yace "Za ku iya hada naku program din mana ku yi da yan uwanki da abokan arziki ba lallai sai da shi ba, can din ma za su yi duk abubuwan da suke so ko bai je ba" Ammi bata sake cewa Abba komai ba, kawai ta bar parlon, can bangaren da Hajja da su Yahanasu da Mama Ladi suka sauka ta tafi, don gobe ake son kai lefen Mayraah kaduna, zaunawa tayi cikin sanyin murya ta masu bayanin da Abba yayi mata, Mama Ladi da ta saki baki tace "Naga abinda ya isheni, to mu meye amfanin kwaso jiki da muka yi muka yo nan din? Fisabilillahi me yasa tun wuri ba a sanar min ba inyi zamana a kadunan a amshi lefen da ni a can, to Al-qur'an komawa zanyi, dama babu yanda Hajiya Ramatun bata yi kan cewar in ɗan kara kwanaki ba nace aa bari dai mu koma Abujan mu fara shirye shiryenmu mu ma, ashe ba uwar da za ayi a nan, ranan fa da na bar gidan ranan Mayraah ta sauka gidan ita kuma, to a gaskiya Mamuda ya bamu kudin mota kawai mu koma kadunan tunda can za ayi biki, mu zauna nan mu ci me, ga can inda ake biki" Yahanasu tace "Mu fa nan dangin ango ne Ladi, kuma mu za a kawo ma amarya a damka mana a hannu mu amsheta, idan muka ce za mu je biki kaduna su wa za su tarbi Meran idan sun kawo ta??" Mama Ladi ta mike tana hada akwatinta tace "Sai ku tarbeta in mun kawota...." Hajja dai sai kallon Mama Ladi take cike da takaici, Yahanasu tace "Ke dai Ladi baki son gaskiya, ki koma kiyi masu uban me a kadunan" Mama Ladi ta juya ta kalleta tace "Kar fa ki sa ince inyi ubanki a kaduna Yahanasu, ki fita idona in rufe, a ina aka taɓa ganin biki gidansu amarya babu dangin ango ko daya? In sunce can za ayi biki mu ma nan dangin ango ai sai a cire mutum biyu ace mu je can" Hajja tace "Mariya bata iso ba, don haka sai ita ta xauna kadunan..." Mama Ladi tace "Aa wallahi, sanda ke da 'ya yanki da jikokinki ku ka guje Meran kuka mata koran kare ina ce ni da Mamuda ne kawai muka tsaya mata cikin tsanani cikin wuya? Ai ita Meran ba dabba bace tasan komai duk kallonku take, iyaka ta raga ma Ammi da ta ci kashinta ta ci fitsarinta, to kuma wani burga za a min kan Mera" Ammi ta mike kawai ta fita daga dakin, Hajja dai bata sake