Showing 300001 words to 303000 words out of 456519 words

Chapter 101 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70679

Abba na barin gidan bayan an yi sallama can ya koma ya zauna, tun bata karasa balcony din ba ta gansa zaune, shi kam bai ganta ba sai da ta zo dab da wajen, suna hada ido taga ya mike ya juya ya shiga cikin parlor, bin bayansa tayi walking a little faster amma tana shiga parlon taga babu shi, waige waige ta dinga yi ko zata hangosa a babban parlon amma bata san direction din da ya bi ba cause the house is so big, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi, tana tafiya a hankali ta haura sama ta tafi ta dauko takeaway din da Hajiya Ramatu tayi masu sannan ta dawo kasa tana kalle kallen ko zata ga Musharraf amma still bata gansa ba, bata san dalilin da yasa hawaye ya kawo idonta ba amma tayi saurin gogewa ta nufi kofa ta fita, a haka ta koma parking space tana tafiya a hankali, ita da Ammi suka shiga motar da zai fita da su suka bar gidan ana daga masu hannu, sai da suka yi nisa Ammi ta kalli Mayraah da tayi shiru, ta jawota kusa da ita tace "Lafiya daughter? Why are u quiet?" Mayraah ta kirkiri murmushin yake tace "Kawai na gaji ne Ammi" Ammi tace "Yanzu gidan Hajiya Murya za mu tafi don sai zuwa karfe shidda za mu je asibitin, Mariya ta kirani dazu wai sunyi waya da Hajja ita da Baaba Yahanasu suna can, to kin ga kar mu je mu cika dakin asibitin, ta so mu sauka gidanta amma nace gwara dai mu je gidan Hajiya Murja" Hajiya Murja cousin sis din su Ammi ce. Kamar yanda Ammi ta fada sai wajen karfe shidda suka fita daga gidan Hajiya Murja zuwa asibitin da Badiyyah take, sai dai ko da suka je still din dai Hajja da Baaba Yahansu suna asibitin, Hajja na kallon Mayraah bayan ta amsa gaisuwar Ammi, a hankali tace "Ya jikin Mayraah?" Mayraah na murmushi tace "Na ji sauki Hajja, ya jikin Sis Badiyyah" Hajja ta sauke kanta tace "Toh da sauki Alhamdulillah" Kana ganin yanayin Hajja za ka ga kamar dai kunyan Mayraah take duk taki sakin jiki, Ammi dai na tsaye bakin gadon da Badiyyah take tana mata sannu, can ta kalli Baaba Yahanasu tace "Yanzu ya ake ciki Baaba?" A takaice Baaba Yahanasu tace "Ɗa fa ya mutu a ciki tun jiya, yanzu dai likitocin sun ce mu jira zuwa nan da sati biyu zata fara nakuda da kanta, in kuma baza mu iya jira ba to za su tattago mata nakudan a irin dubarunsu na asibiti, ni dai nace za mu jira sati biyun in muna da rai da lafiya, sun ma ce ba lallai ya kai sati biyun ba" Ammi dai ta kasa cewa komai amma a ranta hamdala tayi da ɓarin cikin nan, Baaba Yahanasu tace "Toh kin dai ji abinda ake ciki, ciki dai kam ya lalace, kar fa kice wani zamewan kirki tayi don bana ma tunanin ta kai kasan bandakin tunda ina zaune tsakar gida a lkcn, ikon Allah kawai, ciki dama ba daga sati daya zuwa sati takwas ake ɓarin sa ba in ma barin ne? Na taɓa jin inda aka yi barin cikin da ya riƙa, to astagfirullah ban dai sani ba tunda ni ba likita bace, cikin dai Badiyyah kam bai da rai maganar da nake maki yanzu" Ammi ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Allah Ubangiji ya bata lafiya, Allah kuma yasa hakan shine mafi Alkhairi gareta da ma mu baki daya" Baaba Yahanasu tace "Ameen, ai kam shine ma alkhairin, ba mu da rabon wahala kawai" Mayraah tayi farin cikin wannan batu na lalacewar cikin Badiyyah sosai kuwa, ta karasa bakin gadon tana kallonta tace "Sannu sis Badiyyah" Kai kawai Badiyyah ta gyada mata, Baaba Yahanasu tace "Yanxu komawa za mu yi can gidan nawa sai Hajja ta zauna da ita kawai...." Ammi tace "Ai yanzu ma daga gidan Hajiya Murja muke Baaba" Baaba Yahanasu ta rike haɓa tace "Kika sauka gidanta? Matar da har yau ko ci kanku bata ce mana a asibiti ba, ku dai wallahi ba ku da zuciya kare ya lashe, babu yanda ban yi da Mariya kan ta fita sabgar murjan nan a garin nan ba amma taki, ke kuma don neman suna ga gidana kika tafi gidan wata Murja tunda ita tana da babban tsakar gida kuma da gas take girki" Ammi ta kwantar da murya tace "Wallahi ba haka bane Baaba naga kuna asibiti ne, mu kuma gobe da safe za mu koma Abuja, Hajiya Murja kuma tana can tana fama da yarinyar nan nata Sickler wallahi bata da lafiya sosai yarinyar shi yasa ba ku ganta a asibitin ba har yanzu" Baaba Yahanasu dai ta kyabe baki ta ki cewa komai, sai kusan karfe tara su Ammi suka bar asibitin da Mayraah. Washegari da safe kamar yanda Ammi ta fada sai da suka koma gidan Alhaji Saminu yi masu sallama, su din ma dai train ticket aka siya masu don babu jirgi, Ammi kuma tace baza su kai har yamma ba, Mayraah dai sai kalle kallen inda zata ga Musharraf a gidan take amma bata gansa ba sai MD, Ko Mami bata gani ba a gidan, a haka dai MD da Babanta suka kai su train station bayan Hajiya Ramatu tayi masu sha tara ta arziki bayan ta jaddada masu next week duk za su shigo Abujan, Alhaji Saminu ma 200k ya ba Ammi, suna isa station din Ammi tayi sallama da MD da Abdallah, ita dai Mayraah mance waye Abdallah take a gareta don ko dazu sai da Ammi tace mata bata gaidasa ba sannan tayi saurin gaida shi, shi kam sai dai yayi ta bin ta da ido, Da ladabi Abdallah da ke kallon Ammi yace "In sha Allah sati me zuwa za mu shigo Abujan da su Abba" Ammi na murmushi tace "Allah Ubangiji ya kai ku mu" A haka suka rabu a tashar, suna isa Abuja Maheer na tasha yana jiransu, Mayraah was so happy to see him.
[9/3, 8:05 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer na parking bayan sun isa gida Ammi ta bude motar suka sauka da Mayraah, Mayraah ta dau ledan takeaway din da yayi masu a hanya tana kallonsa bayan ya sauka daga motar tace "Yaya kai ma zaka ci ne?" Yace "No, na ci abinci" Juyawa tayi ta bi bayan Ammi zuwa cikin gidan, shi dai yana biye da su a baya, Ammi sai da ta fara shiga dakin da su Mama Ladi suke a downstairs don gaishesu, Mayraah ta kai abincin kitchen sannan ta fito ita ma ta shiga wajensu Mama Ladi ta gaishesu, bayan few seconds ta mike zata fita, Mama Ladi ta bi ta da kallo har ta fita, can ta rike haɓa ta kalli Ammi dake zaune gefen gado tace "Yarinyar nan fa tun da ta ci guba take jin sabon tashen rashin kunya a gidan nan, ta ari halin da ba nata ba, Mera da idan ta shigo gaidaka sai ta zauna a tsanake ta gaisheka cikin ladabi da biyayya har ma ta tambayi ko da abinda zata maka amma yanzu sam ba haka bane, ai dai kinga figil figil daga gaisuwa ta mike ta fice kamar ana mintsilinta, to shi dama Guban haka yake in an ci sa" Aunty Mariya dai tayi murmushi tace "Daga tafiya fa suke Mama Ladi, kuma kin ga ai da gajiya" Mama Ladi ta kara kyabe baki tace "Aa gaskiya Meran da na sani ba haka take ba da, yarinya ce nutsattsiya ga sanyin hali" can kuma ta kalli Ammi da ta fasa gayan abinda ke ranta game da bayyanar iyayen Mayraah da Allah yayi cikin ruwan sanyi, taji gwara kawai ta ja Aunty Mariya ta gaya mata, Mama Ladi tace "Nasan sai da Yahanasu tayi da ni a kadunan nan ko? Shegiya rubabbiyar mata gidanta yanda kika san gidan almajiran kana rad, ko ni da nake karaye sai a siya gidana sau dubu ita ba a taya nata ba" Ammi ta hade rai tace "Haba Mama...." Mama Ladi ta dakatar da ita da sauri tace "Kin fi ni sanin halinta ne ko er uwar ki ce? Matar dake bakin ciki da ni tun muna yara, yanzu haka don Mamuda na shiri da ni har mu zauna mu yi shawara gashi kome nace masa yayi yi yake kansa tsaye yana mutunta ni yana girmama ni wallahi haushin hakan Yahanasu take, to ni nace a tara mata jikoki a gaba su hanata rawan gaban hantsi ta kasa zuwa ko ina? Ba don tulin jikokin gabanta ba wllhi wataran sai Mamuda ya rufe ido ya koreta tsabar yanda zata mayar masa gida kasuwar kurmi don zarya, kullum tana hanyar gidansa kinsan ba kai gareta ba, amma ni ai kinga sai da dalili nake zuwa ba haka kawai ba, banda wannan mata da ta ci Guba na taho ba sai ayi shekara biyu ma ba a ji ni ba, gashi in mutum yaje kaduna tace lallai sai ya sauka a kuturun gidanta kuna shakar numfashin juna to a ina aka taɓa haka fisabilillahi, ke ba tsaftace gida kike ba ba komai ba kice sai an sauka gidanki" Mikewa Ammi tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin, Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta bi bayanta, Mama Ladi ta kara kyaba baki tana yagar bredin gabanta tace "Ba dai kwa son gaskiya" A hankali Mayraah ta bude ido jin ana tapping pillow din da take kwance kai, ta daga kai tana kallonsa with sleepy eyes, yace "Baki ci abincin ba Mimi" Ta rufe ido ta maida kanta daya side din tace "Later" ya sauke idonsa yace "Are you not hungry?" Tayi shiru kuma bata bude ido ba, ya duka kusa da gadon yace "Mimi" Juyowa tayi ta ɓata fuska tace "Yaya bacci fa nake ji, ai nace ma Ammi ba yanzu zan ci ba" A hankali yace "Ohk" Daga haka ya mike ya juya zai fita ta bi sa kallo sai kuma tace "Za ka ci ne?" Juyawa yayi ya kalleta yace "Noo, naga it's almost 3pm baki ci abincin ba, kuma Mama Ladi na ta shiga kitchen din tana fitowa tana tambayar na waye, kar taje ta cinye maki...." Mayraah ta lumshe ido tace "Idan ta ci you can buy me another one" Ya ɗan yi murmushi yace "Ohk then" Ya juya ya nufi kofa sai kuma tace "Ko kuma ka ɗan kawo min nan pls" Ya kalleta bai dai ce komai ba ya fita daga dakin ya kullo mata kofar. Ammi na zaune tare da Aunty Mariya bayan ta sanar mata duk abinda ya faru daga shekaranjiya zuwa yau, sosai Aunty Mariya tayi farin ciki, don har sai da tayi hawaye, she was soo happy for Mayraah but deep down ta fi tausayin er uwarta sanin yanda ta kwallafa rai kan Mayraah, iyakacin son da zata ma er cikinta shi tayi ma Mayraah babu algus, gashi kuma yanzu ba ita kadai ke da ita ba ya kuma kamata ta fara koya ma kanta amincewa da hakan a zuciyarta, she have to start adapting to that gradually, bayan wani ɗan lokaci tana kallon Ammi a hankali tace "Yanzu zata je can wajen mamarta ne tayi kwana biyu?" Ammi ta daga kai tana kallonta babu ko kiftawa, Aunty Mariya ta kwantar da murya tace "Ya kamata ne Ammi, tun da kin ce ga halin da uwar ma ke ciki tun bayan rabata da er ta da aka yi, it's high time ki san Mayraah is not ours alone anymore Ammi, iyayenta suna nan da ran su har ma an maida auren su yanzu haka, ko yaya ne za su bukaci er su ta kusantosu don kaddara ce tayi parting dinsu tun asali, kakanninta ma duk suna nan za su so suma su saba da ita ta saki jiki da su, Ammi baza mu hana Mayraah creating bond da iyayenta da relatives dinta ba" Hawaye ta gani idon Ammi, Aunty Mariya da jikinta yayi sanyi don tasan idan ba ita din ba babu wanda zai ganar da Ammi wannan lamari, ta girgiza kai tace "Kiyi hakuri Ammi, amma ina son ki sani Mayraah ba yarinya bace, she knows her left from right, nasan kuma tasan matsayinki a wajenta tasan wacece ke, don haka kar ki wani sa damuwa a ranki, abu daya ne zai kara nisanta ki da Mayraah, nisa kuma na har abada...." Ammi ta daga kai tana kallonta har sannan hawaye na zuba idonta, Aunty Mariya ta dauko mata tissue ta bata, cikin sanyin murya Aunty Mariya tace "Yau ace Mayraah ta auri wannan saurayin nata ni kai na nasan zata mana nisa, and that is just the fact, don kuwa zata koma cikin dangin ubanta ne Automatically and we have nothing to do about it, kuma sai sanda Mijinta ya bata izini zata zo wajenki, may be ma ba gari daya ba, he can decide su zauna kaduna, gata ga kakanninta, ga kuma iyayenta, in kika ga hakan bai faru ba to sai in dai a gidan nan Mayraah zata yi aure" Ammi ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata, bayan few seconds ta girgiza kai cikin rawan murya tace "Mayraah tana son Musharraf, shi ma kuma i believe yana sonta sosai, bazan iya hanata amincewa da aurensa ba saboda nawa interest din, bazan tauyeta ba, after all her happiness is all what i am after, her happiness is my first priority, bayan duk abubuwan nan da ta fuskanta a baya yanzu she deserves to be more than happy, even though i have other plans for her a baya, yanzu kam plan din isn't going to work, my plans are of no use duba da yanda abubuwa suka kasance a kwana biyun nan, i believe Allah ne ya bani Mayraah a sanda ya so sannan zai kuma rabani da ita a yanzu da ya so for other people to play their roles in her life...." Tana kai wa nan ta mike ta nufi kofa Aunty Mariya ta bi ta da kallo cike da tausayinta, Ammi na kokarin bude kofar dakin Usman ya rigata budewa, ta bi gefensa ta fita daga dakin ya bi ta da kallon mamaki ganin kuka take, sai kuma ya kalli Aunty Mariya, karasawa yayi cikin dakin da sauri ya zauna yana facing dinta cikin damuwa yace "Aunty me ya faru kuma? Why is Ammi crying?" Aunty Mariya ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Usman Pls tell me ur opinion akan auren Mayraah da wannan saurayin nata, tell me all what u think about it" Usman yace "Amma dai kukan me Ammi take Aunty? I want to know first pls" A hankali Aunty Mariya tace "She is crying because of how things later turn out, idan Mayraah ta auri yaron nan Musharraf kaga ai tayi nisa da ita ta koma dangin ubanta gaba daya, sai sanda kuma Ammi ta ganta" Usman ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, a hankali yace "Is that why she is worried?" Aunty Mariya tace "Da bata son Mayraah bazata damu ba Usman, kun fi kowa sanin irin son da take ma Mayraah, motherly love take mata, she feel za a rabata da ita ne na har abada" Usman dai bai ce komai ba, Aunty Mariya tace "What do u have to say Usman?" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Ban san me zan ce ba Aunty" Aunty Mariya bata sake cewa komai ba har bayan minti biyar a dakin, Usman dai yayi nisa tunanin da yake. Bayan isha Mayraah na zaune parlon Abba tare da Ammi sai Maheer da Usman, wanda Abba ne duk yayi kiransu parlon nasa, Abba ya daga kai yana kallon Ammi da ta fada duniyar tunani yace "Hajiya...." Ammi ta daga kai da sauri ta kallesa, Yace "Kin dai san abinda ya kamata shi ake yi ko?" Ammi dai kallonsa kawai take, Abba ya jinjina kai yace "Ya kamata Mayraah taje gidan Ceo tayi masu ko kwana uku ne, don ranan Alhamis Alhaji Saminu yace min za su shigo don jin matsayar mu akan maganar aurenta, and today is Saturday, kinga ranan Wednesday da yamma sai either Maheer or Usman wani yaje ya daukota, if they are not available ma Drivernta zai iya zuwa ya dawo da ita, even though nasan CEO din ma zata sa a dawo da ita in lokacin dawowar nata yayi" Sosai gaban Mayraah ya fadi bayan taji abinda Abba yace tana kallonsa, Ammi dai kanta na kasa bata ce komai ba, Abba yace "Kin fahimci abinda nake nufi?" Ammi ta daga kai a hankali tace "Na gane" Abba yace "Hakan ya kamata, don haka Usman ko Maheer za su iya dropping dinta tomorrow in the afternoon" Ammi dai bata sake cewa komai ba, Abba yace "Kiran kenan dama" Mayraah na tsaye kitchen that same night tana dafa ma Ammi shayi ganin bata ci abinci ba taji an bude kofar kitchen din, juyawa tayi tana kallonsa har ya karaso cikin kitchen din yace "Are you making tea for Ammi?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "Ohk, take ur time..." Juyawa yayi zai fita ta bi sa da kallo tace "Me zaka yi yaya?" Ya juyo yace "I want to make coffee" Tace "Okay let me make you" Yace "Thank you..." Kokarin fara making masa coffee din take, shi dai kallonta kawai yake, ta juya ta kallesa ya ɗan buda ido yace "Alas baki ci abincin nan ba dai Mama Ladi ta ci" Ta ɗan ɓata fuska tace "Ba nace ka kawo min daki ba ka ki kawo min" Yayi murmushi yana shafa beard dinsa yace "Bayan masifar da kika min na tashe ki bacci" Buda baki tayi tana kallonsa, ya karasa ya kashe gas din da shayin da take yi ma Ammi yake kai, ta nufesa tace "Yaya yaushe na maka masifa?" Ba tare da ya juyo ba yace "Cikin mafarki, har da murguda min baki" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita kitchen din ya kullo kofar, haka dai ta zuba

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login