Showing 297001 words to 300000 words out of 456519 words

Chapter 100 - MAYRAAH

31 Oct 2024

70584

dawo kano, a gidan Alhaji Habibu aka salwantar da hoton nan nake ji da duk an nuna ma kowa" Hajiya Ramatu tace "Kwarai Kuwa" Ceo dai sai kallon MD take don bata taba sanin daga wannan familyn ya fito ba, da tasan Uncle dinsa ne Alhaji Kabir Saminu da ko aiki bazata daukesa asibitinta ba balle har ta basa matsayinsa na yanzu, Halima ta dafe kanta tace "Kaico.. Mun ci mutuncin er mu da kan mu, dama ance rashin sanin yafi dare duhu" Shi dai Abdallah kallon Mayraah dake jikin Mom dinsa kawai yake babu ko kiftawa, A Karo na farko Alhaji Kabir Saminu wanda shi ma tun shigowar Mayraah ya ga kamannin Mahaifiyarsa da ta rasu tun yana shekara sha hudu, a hankali ya fara magana don zuwa sannan kirjinsa yayi masa nauyi, cike da karfin hali yana kallon Abba yace "Da farko Alhaji bamu da abinda za mu ce maka sai dai mu baka hakuri akan abinda ya faru, ku yi hakuri, ku yi hakuri, rashin sani kam yafi dare duhu, shi yasa ake son mutum ya dinga daga kafa akan abubuwa da dama na rayuwa saboda bayansa, gashi dai a karshe ita wannan yarinya daga tsattson mu ta fito bayan duk cin mutuncin da muka yi maku.... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya hanamu jin kunyan duniya da na kiyama, ban taba jin kunya na abinda na aika irin wannan ba a rayuwata" Kallon Ceo yayi still speaking calmly yace "Kiyi hakuri mun zalunce ki kwarai da gaske, mun zalunce ki mun zalunce kanwarki, bani da abinda zan ce da ya wuce kuyi hakuri, i felt so ashame of my act a yau din nan, i am deeply sorry for making u and ur sister pass through a lot many years ago, duk laifina ne ni na ja komai da naki basa goyon bayan auren da ya so yi, duk da matata tayi iya kokarinta na ganin na hakura na bar sa da auren yarinyar bayan da yaje wani waje aka daura, amma saboda wani dalili na da bai da tushe na lalata auren" Shiru ya sake yi na wani lokaci yana sauke numfashi a hankali, sai kuma ya kalli Abdallah yace "Baza a tashi a nan ba sai da auren wannan baiwar Allahn a kan ka matukar ta amince, ni kuma zan bada sadakinta, i don't mind if she is a Christian or a Muslim" Da sauri Ceo ta kalli Alhaji Kabir dake kallon Aaria yace "Kin amince a mayar da aurenku da shi?" Mikewa Abdallah yayi ya isa gaban Aaria ya durkusa a hankali yace "Pls do not say no Maryam, all this years baki taba fita a zuciyata ba, ba da son raina na guje ki ba umarnin iyayena na bi, don Allah kar ki ce Aa, I never knew you conceived" Kallonsa kawai Aaria take hawaye na sauka idonta, Halima ta dawo kusa da su tace "Don Allan kar ki ce Aa Maryam do this for the sake of ur beautiful daughter" Aaria ta jinginar da kanta saman shoulder din yayarta wasu hawayen na sauka idonta, Ceo dai ta kasa cewa komai ita ma tana hawayen, cikin sanyin murya Aaria tace "I will do it for my daughter" Abdallah ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, Alhaji Kabir ya kalli Musharraf calmly yace "In sha Allah kai ma baza ka tashi a nan ba sai da auren er uwarka wanda kai din kawunta ne" Daga MD, Maheer har Usman daga kai suka yi suna kallon Alhaji Kabir Saminu......
[9/2, 12:01 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Musharraf da kansa ke saman shoulder din Maminsa ya bude ido da sauri amma ya kasa dagowa bayan yaji abinda Uncle din nasa yace, Daga Abba har Ammi kallon Alhaji Saminu kawai suke babu wanda yace komai cikinsu, ita dai Mayraah dake rungume jikin Hajiya Ramatu a hankali ta bude idonta jin abinda kakan nata yace, the parlor was silent for a while, bayan wasu yan dakikai Ceo dake kallon Alhaji Saminu ta girgiza kanta tana kallonsa directly in the eyes speaking calmly tace "Decisions ain't just made that way, Probably an samu wasu changes din da kai baka sani ba, this is something that happened months back not few days ago, so you are suppose to ask her rightful parent ko bayan nan sun mata wani mijin ne kafin ka yanke wannan shawaran, what if da baikon wani a kanta? You ought to have reason that Sir" Hajiya Ramatu ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana shafa kan Mayraah dake jikinta tace "Wannan gaskiya ne Alhaji, haka ya kamata ka fara tambaya tunda bamu san ko da wani abu daban dake zuciyar iyayen nata ba ko ita kanta, or may be her parent may have a different plan for her now" Alhaji Saminu ya jinjina kai, letting out a sigh at the same time looking so weary yace "Tunanin hakan bai zo min ba, wannan kam haka yake, duk da shi ma Musharraf din da wata maganar a kasa, amma domin gyara ɓarakar baya shi yasa nayi kokarin zartar da wannan hukuncin kai tsaye amma ba don nuna isa da er su ba, don maganar Musharraf dake kasa magana ce da zan iya shunning considering abinda ya faru a baya" Sai kuma ya juya ya kalli Abba yace "Ku gafarceni Alhaji nayi kokarin yanke hukunci babu neman shawaranku ko opinion din ku, so now Is there anything you want to say akan decision din nan nawa?" Abba ya sauke ajiyar zuciya bai dai ce komai ba, can ya juya yana kallon Ammi da ta sauke idonta kasa, a hankali yace "Hajiya is there anything?" Ammi ta ɗan kalli Maheer, kawai ta girgiza kai tace "Mayraah za a tambaya, abinda yake ranta shi za ayi mata" Alhaji Saminu ya juya ya kalli direction din Mayraah, Calmly yace "Mayraah" Mayraah ta dago kanta daga jikin Hajiya Ramatu ta kallesa, ya nuna mata gefensa calmly yace "Come over my dear" Mikewa tayi suka hada ido da MD dake kallonta ta sunkuyar da kai ta nufi kakan nata ta zauna inda ya nuna mata, duk kowa na parlon kallonta yake barin Babanta da ya kasa dauke idonsa a kanta, Alhaji Saminu na kallonta kafin yace komai Ceo ta dakatar da shi tace "I think tana bukatar a bata lokaci ta kara samun nutsuwar yin nazari kafin aji komai daga gareta Alhaji, beside she just recovered daga rashin lafiya" Ammi ta gyada kai da sauri tace "Wannan gaskiya ne, ba lafiya isasshe gareta ba, we were just discharged from the hospital not long ago" Tana magana ne amma har hawaye ya cika idonta, Alhaji Saminu yayi ma Mayraah side hug a hankali ya kwantar da murya yace "She should take her time, duk yanda ake ciki next week za mu shigo Abujan gaba daya" Shi dai Musharraf har sannan bai dago kansa ba, Mami dai sai kallon Ceo take haka ma MD.... Hajiya Ramatu ta mike ta tafi gun mai gidan nata ta dago Mayraah dake kusa da shi sannan ta juya tana kallon Ammi da su Ceo tace "Ku mu je can bangare na, ko ruwa baku sha ba...." Mami da Aunty Halima duk suka mike gaba daya suka bar parlon tare da Ammi, Ceo dake bayansu na rike da hannun kanwarta, duk da Hajiya Ramatu na rike da Mayraah amma gaba daya hankalinta na gun Amminta to be sure tana biye da su..... Kamar yanda Alhaji Saminu ya fada bayan barin su Ammi parlon ya maida auren Aaria da Mahaifin Mayraah akan Sadaki dubu dari biyu wanda shi ya bada, Abba kuma ya zama waliyin Maryam. Abinci iri iri aka yi serving din su Ammi a part din Hajiya Ramatu bayan ta kai su can, gidan Alhaji Saminu gida ne me girman gaske don Hajiya Ramatu ma parlor biyu gareta manya, Mayraah dai na gefen Ammi tana cin abincin gabanta, Aaria sai kallonta take babu ko kiftawa haka ma Hajiya Ramatu that couldn't take her eyes off her, Mayraah ko sanin suna yi ma bata yi ba, can ta daga kai ta kalli Ammi for the 4th time, tayi kasa da murya tace "Wai Ammi an kai ma su Yaya abinci?" Kamar an ce ta daga kai taga duk kallonta ake a parlon har Mamin Musharraf, rufe fuska tayi jikin Ammi da sauri tana murmushi kamar yanda Ammi ma ke murmushi, Hajiya Ramatu na girgiza kai tace "Sannu er Ammi, kin kira Ammi yayi sau goma yanzu a nan, kin ki barin ta ma ta ci abincin" Aaria ta sauke idonta a hankali tana juya abincin gabanta, Ceo dai Calmly take cin snacks din gabanta don ta ki cin abinci. Bude kofar wani Bedroom Mami tayi bayan ta fito daga ɓangaren Hajiya Ramatu, MD ta gani zaune yana juya coffee din hannunsa da tea spoon, kallo daya yayi mata ya ci gaba da abinda yake, ta karasa cikin dakin bayan ta kulle kofar tana kallonsa tace "Aliyu ina Musharraf?" MD yace "A masallaci na bar sa" Mami zata yi magana aka bude kofar dakin duk suka juya, Musharraf ne ya shigo Mami ta dinga kallonsa har ya karaso cikin dakin, tace "Ka ci abinci?" Kwanciya yayi saman gadon dakin a hankali yace "I am okay" Mami ta zauna gefen gadon tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Ya kake ga za ayi yanxu Musharraf?" MD ya kalleta yace "Na me fa?" Mami tayi kasa da murya tana kallon MD tace "Mamar ka ta Adamawa tace zata hadasa da Jiddah, ko baka da labari ne?" MD that was surprise yace "Jiddah? No bata gaya min ba, may be ta sha'afa ne but mun yi waya yau da safe ai" Mami tace "Na zata ta gaya maka shi sa ban maka maganar ba, har mun gama shirya komai da ita da Hajiya Safiyya, dama ina da niyyar zuwa nan kaduna in sanar ma Baffan ku sai ga rashin lafiya ta samesa, to dazu ma na fara masa maganar tunda jikin da sauki yace satin da za a shiga sai a kai kudi ko ba da shi ba, idan ya so sai a tsayar da sati daya bikin...." MD ya kalli Musharraf dake danna wayarsa, kallon Mami ya sake yi yace "But Mami tunda an dawo da zancen aurensa da ita Mayraan why not ki gaya ma Umman Adamawa abinda ake ciki yanzu, nasan idan taji abinda ke kasa zata janye batun Jiddah" Mami dai sai kallon MD take ta ma rasa me zata ce, MD yace "But in kuma yaga zai iya duk biyun sai ya aure su, it's not bad ai...." Mami ta ɗan buda ido tana kallonsa at the same time speechless don Jiddahn nan er yayarta ce uwa daya uba daya, kuma wajen yayar nan tata MD ya tashi tun daga yaye ta rikesa har zuwa yanzu don ya ma fi sabawa da ita akan Mamin nasa, shi yasa ma ba wani shakuwa tsakaninsa da Musharraf, Mami ta sauke idonta a hankali tace "Sai dai in ma yaya bayani, idan ya so in ma janyewan ne sai ayi kawai a bar zancen Jiddar, don farin cikin Musharraf shi ne nawa, nasan ba shi da wani option ne dama shi yasa ya amince da auren Jiddah, duk da Jiddah lacks nothing too" MD na gyada kai yace "Sai miskilanci" Mami ta hararesa, sai kuma ta kalli Musharraf tace "Ka kwantar da hankalinka zan kira Umman ko zuwa anjima" Mikewa zaune Musharraf dake ta sauraronsu yayi calmly yana kallon Mamin tasa yace "You know what Mami?" Mami dai kallonsa kawai take kamar yanda MD ma ke kallonsa, Musharraf ya ɗan yi murmushi yace "Baza su bani Mayraah ba" A hankali Mami tace "Me yasa kace haka?" Musharraf ya sauke idonsa yace "Za su canza mata ra'ayi, shi yasa Amminta tayi saurin supporting cewar she needs time to think, baza su bani ita ba" MD dai kallonsa kawai yake, Mami da jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai don sarai ita ma ta gano hakan bata dai son ta daga masa hamkali ne, amma daga furucin Ceo da Ammi ta sha jinin jikinta, A hankali Musharraf yace "Don haka ni na cire rai da Mayraah, i know everything happens for a reason in life...." Yana fadin haka ya koma ya kwanta facing the other direction, Mami tayi tagumi duk jikinta yayi sanyi, MD ya ajiye cup din shayin hannunsa ya mike ya fita daga dakin bai taɓa jin tausayin kanin nasa irin yau ba, Mami ta koma daya side din tana kallon Musharraf seeing tears in his eyes immediately broke her down too. MD na barin dakin ya tafi har zuwa daya part din with different thought in mind, Mayraah ya hango rike da tray din drinks da ruwa tana tahowa, tun da ta hangosa ta rage tafiyarta, hakan yasa ya nufeta ta sha kunu ta tsaya seeing he is coming directly toward her, da ido ya bi wajen da kallo bayan ya isa har gabanta sannan ya amshe tray din hannunta ya ajiye a nan wajen, a takaice yace "I want to speak with you" Ta ɗan buda ido kafin tace komai ya fixgo hannunta, buda baki tayi tana kallon sa da mamaki tana biye da shi lkci daya ta hau waige waige a wajen taga babu kowa, bude kofar wani part yayi ya shiga ciki da ita sannan ya kulle kofar, ita dai kallonsa kawai take fuska daure, Ya zagayo gabanta yana kallonta yace "Did you know what heartbreak means?" Mayraah ta gyara tsayuwa tana kallonsa at the same time looking so confuse, as if counting his words MD yace "Do not break my brothers heart! shi ne first love din ki, idan kika ƙi aurensa kin ci amanarsa after all what he went through, duk abubuwan da suka faru lokacin da aka fara saka bikin ku bai guje ki ba, bai ƙi ki ba, bai canza maki ba, he was there for you all through, idan kika ki sa yanzu kin ci amanar sa, kin ci amanar kauna" Mayraah dake ta kallonsa nan da nan hawaye ya cika idonta, cikin sanyin murya tace "Kaga alamar ni zan ce bana son sa ne? I will never do that, i still love him just like he loves me, and he is still my first love nothing can change that" MD dake ta kallonta yace "Better!!" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta zauna saman kujeran Parlon tana goge hawayen dake zuba idonta. Karfe biyu da rabi Abba ya ce ma Alhaji Saminu za su koma kano bayan sun dade suna hira da shi a parlon sa, Alhaji Saminu yace "Amma dai zaka bar iyalinka da er ku zuwa ko gobe ne a yankar masu ticket" Abba yace "Eh to, dama mai dakin nawa tace min zata je wani ziyara nasan za su kai har gobe a garin nan" Alhaji Saminu yace "To madallah, sai kuma magana ta biyu ina ga kai yafi dacewa ka tambayi yayar Maryam kwana nawa za su diba na tarewar kanwarta, in kadunan ne ko Abuja or even kano nasan it will be okay for Abdallah don duk yana harkokinsa a garurrukan nan" Abba yace "Toh zan sameta yanzu mu yi magana in sha Allah" Ceo na zaune a parlon dake downstairs da Abba da ya sa aka kira masa ita, bayan Abba ya sanar mata dalilin kiran nata Ceo ta dan yi murmushi tace "Wannan sai mun koma Abuja za mu yi deciding da ita Alhaji ai ba abun gaggawa bane, bayan nan i am sorry to say akwai tests da ya kamata duk su biyun za su yi a asibitina na Abuja" Abba yace "Eh hakan abu ne me kyau gaskiya, amma kinsan me nake so da ke?" Ceo ta daga kai tana kallonsa tace "Aa" Yace "Alfarma nake nema don Allah, kiyi hakuri duk ma abinda za ayi kar ya wuce sati biyu" Shiru Ceo tayi, bayan few seconds a hankali tace "To shikenan Alhaji" Abba yace "Nagode kwarai, ni yanzu zan koma Abuja da su Maheer don har sun samar mana ticket din jirgin kasa that is heading to Abuja" Ceo tace "Fine, if it's still available zan sa Aliyu yayi purchasing mana ni da Aaria, nasan shi kilan ba yau zai koma ba, to amma Madam dinka da daughter dinku fa?" Abba yace "Akwai ziyaran da za su yi ne cikin gari, sai gobe za su koma Abujan in sha Allah" Ceo tace "To Allah ya kai mu" Karfe uku da rabi Ceo da kanwarta da Abba da su Maheer suka fita compound drivers din Alhaji Saminu za su kai su Train station dake Hayin rigasa don hawa jirgin kasa da zai je Abuja, duk da yanda Abdallah ya so ko sallama ne su yi da Aaria amma Ceo taki bada wannan space din ta saka kanwarta a mota ita ma ta shiga, Mayraah dai na tsaye kusa da Amminta tana daga ma su Ceo hannu duk da su ma ga nasu drivern da zai kai su Asibitin da Badiyyah take, Mayraah ta kalli motar da su Abba da Maheer suka shiga su ma ta daga masu hannu tana murmushi, babu wanda bai fito daga gidan yi masu sallama ba har Alhaji Saminu sai da ya daure ya fito, Aaria dai sai kallon Mayraah dake makale da Ammi take, Bayan fitar motocin su Abba da Ceo, Hajiya Halima ta bude ma su Ammi motar da za su shiga tace "Amma dai nan za ku dawo ku kwana ko Hajiya?" Ammi tayi murmushi tace "Gidan kanwata zan je daga asibitin, amma in sha Allah da safe za mu dawo mu yi sallama" Hajiya Halima tace "To shikenan, don Allah a gaida mana su, kuma ayi ma me jiki sannu" Ammi tace "In sha Allah" Hajiya Ramatu ta kalli Mayraah tace "Baki dauko maku takeaway din ba Mayraah" Ammi tace "Dama nace sai ta manta sa in dai Mayraah ce" Murmushi Mayraah tayi ta juya ta tafi taje ta dauko, Musharraf na zaune balcony don motar su

Join Our Groups
Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login