Showing 384001 words to 387000 words out of 456519 words
number ne da bai yi saving ba, tana ajiye wayar zata bar wajen taga text ya shigo, ta sake daukar wayar ta bude ta shiga text din, nan taga text sun kusa ashirin from the number, sosai gabanta ya fadi duk da bata kai ga karanta content din text din ba, tayi scrolling zuwa can sama zata fara da message din farko, a hankali ta zauna kan kujera tana fara karanta first message din ta gane Haseenah ce don rokansa take yayi mata rai kar shi da familynsa su rabata da yaranta, su yi hakuri su bar ta ta shayar da su idan yaso daga baya sai su amshe su, yawanci duk ire iren message din da take masa kenan na ban hakuri da magiyan kar ya rabata da yan biyunta she want to breastfeed them, upon yawan messages din Maheer bai taɓa mata reply ba, kuma da alama wani layin ta samu take ta kiransa take masa message da shi, Mayraah ta shiga call log taga bai taɓa daga kiranta ba duk miss calls ne kusan 50, duk da haka sai da Mayraah taji wani kishi a ranta, ta tabe baki ta ajiye wayar, can master bedroom ta tafi ta gansa zaune gefen gado yana duba abu a laptop dinsa, ta jingina kusa da kofa tana kallonsa a hankali tace "Fruit salad din yana can parlor" Ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya ajiye laptop din yace "Wani laifin nayi kuma?" Turo baki tayi ta dauke kai taki ce masa komai, yana jin yanda tayi maganar kawai yasan da wani abu, ya mike ya karasa kusa da ita ya kamo hannunta a hankali yace "Tell me what is it" Ta ɗan yi yake tace "Kawai na gama yin fruits salad din yana can parlor na ajiye maka" Yana rike da hannunta ya kai ta edge din gadon dakin ya zaunar da ita ya zauna kusa da ita yana kallonta yace "Then why the change of mood all of a sudden?" Ta dan yatsina fuska tace "Bacci nake ji" Shiru yayi bai ce komai ba, can yace "Toh kwanta kiyi baccin ki" Tace "Zan je dakina in kwanta" Yace "Aa ki kwanta a nan don in tabbatar baccin za kiyi" Tace "Fruits salad din fa?" Yace "Zan je in dauko" a hankali ta daura fararen kafafuwanta kan gadon ta koma tsakiyan gadon ta kwanta ta juya masa baya, riga da wando na mutunci yau ta saka na bacci, ya ɗan yi murmushi sannan ya ci gaba da abinda yake yi a laptop dinsa, after a while ya kashe laptop din ya ajiye sannan ya fita daga dakin, zaunawa yayi a parlon yana shan fruit salad din, wayarsa da yayi vibrate alamar shigowar message ya juya ya kalla ganin number da ya turo message din ya ci gaba da shan fruits dinsa, sai wajen karfe tara Maheer ya koma master bedroom, har a sannan Mayraah bata yi bacci ba, sosai messages din da taga Haseenah ke turo masa ya tsaya mata a rai, tasan kawai as far as this babies are between she and Maheer babu ta yanda za su yi cutting communication na har abada, no matter what she remains the mother of his boys kuma dole akwai lokacin da zai zama wajibi su yi communicating for one reason or the other akan yan biyun, Mayraah na jin shigowarsa ta rufe ido da sauri kamar me bacci duk da tana backing dinsa, bandaki ya shiga yayi wanka ya fito, tana jin ya fita dakin ta mike ta zauna, haka nan taji zuciyarta ya kasa nutsuwa ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta fita daga bangaren gaba daya ta karasa can main parlor ta makale tana lekansa, wayarsa ta gani kare kunnensa, after some seconds taji yace "Look Haseenah, in kika ci gaba da damuna da kira da text messages i will block this line too, ni na raba ki da yaranki da zaki dinga damuna haka?" Shiru Mayraah taji yayi alamar yana sauraron Haseenah, sai kuma taji yace "Kina da number Ammi, kina da number Abba so why disturb me bayan bani nace a amshe yara a hannunki ba, plss bana son ki ja min issues da matana idan taga kina kirana da turo min text messages, kindly avoid calling me pls, ni bani na raba ki da yaranki ba, in kika ci gaba da damuna i will block you i promise" Daga haka ya katse wayar, mikewa yayi Mayraah na ganin haka ta juya da sauri ta koma can masters bedroom ta hau kan gado ta kwanta, a parlorn dake bangaren ya jona wayarsa a caji sannan ya shiga bedroom din, karasawa yayi kan gadon ya zauna kusa da Mayraah ya duka yana kallon fuskarta murya can kasa yace "Nasan ba bacci kike ba" Ko da wasa Mayraah bata yarda ta bude idonta ba, tickling dinta ya fara yi, ta matsa da sauri daga kusa da shi kamar zata yi kuka tace "Yaya bacci fa nake" Ya kwanta bayanta ya jawota kusa da shi yace "To yi hakuri" lamo tayi taki ce masa komai, ya kashe wutan dakin, they were like that for 5 mins yana shaƙan kamshinta, hade rai tayi jin abinda yake mata, tana cire hannunsa a jikinta a hankali tace "Yaya bacci fa nake ji" Yace "To sai da safe" Juya mata baya taji yayi ya matsa daga kusa da ita, ita dai bata ce komai ba ta rufe idonta, bayan kusan minti goma ta juya a hankali ta matsa kusa da shi, murya can kasa tace "To yi hakuri Yaya" ya juyo yana kallonta yace "Really?" Ta gyada masa kai, kwantar da ita yayi jikinsa tayi lamo, daga karshe dai Mayraah tayi mugun da ta sanin komawa kusa da shi har ta basa hakuri, don da tasan wahalan da zata sha kenan da bazata fara ba, duk tunaninta iya abinda ya saba mata this pass days ne zai mata ya kyaleta in ta marairaice masa tace zafi, he made sure ya sauke duk urge dinsa daren nan, ko tunawa da batun wani lubricant bai yi ba, ba irin lallashin da bai mata ba bayan ya dawo hankalinsa amma taki sauraransa sai kuka take sosai, wajen karfe daya saura ya kyaleta ya shiga bandaki zai yi wanka, ko da ya fito bai ganta a dakin ba, yayi murmushi ya saka Pajamas dinsa sannan ya fita daga bangaren, ya tafi dakinta ya murda kofar dakin a hankali yaji ta sa makulli, komawa daki yayi ya kwanta feeling so refresh, nan da nan bacci ya daukesa.... Maheer na tashi sallan Asuba bayan yayi alwala ya fito parlor ya cire wayarsa a caji yaga miss calls din Ammi har hudu, sosai gabansa ya fadi ya dinga kallon wayar sai kuma ya duba time din da ta kira yaga tun karfe hudu ta kirasa, kasa kiranta yayi, jin za a tada sallah yayi karfin halin ajiye wayar ya tafi masallaci...
[10/7, 9:13 PM] khaleesat Haiydar 📚✍️: Maheer na dawowa masallaci ya dau wayarsa ya kira Ammi, har kiran ya katse bata daga ba, ya sake kiranta nan ma no response, ajiye wayar yayi ya fita daga bangaren ya nufi dakin Mayraah, murda kofar dakin nata yayi yaji still bata bude ba, ya juya kawai ya koma dakinsa. Gari na wayewa Maheer ya fito bayan yayi wanka ya shirya, har a sannan Ammi bata biyo kiransa ba shi ma bai sake kiranta ba, tun da ya ga miss calls dinta da asuba ya rasa nutsuwarsa gaba daya, gashi ya kasa sake kiranta, kawai yayi deciding ya shirya ya tafi can gidan, knocking kofar dakin Mayraah yayi don har a sannan bata bude ba, a hankali yace "Mimi..." Bai wani tsaya bata lokaci a bakin kofar ba sanin baza ta bude ba, ya karasa parlor ya dau makullin motarsa ya fita zuwa parking space, Mayraah na jin ya tada motarsa ta mike zaune daga kwancen da take, a hankali ta tashi ta nufi kofa ta bude ta fita zuwa parlor, tsaye tayi tana kallonsa ta windan parlor bayan ta ɗan bude labulen kadan, yana gama warming motarsa mai gadi ya bude masa gate ya fita, komawa tayi ta zauna kan kujera tana kallon agogo dake nuni da karfe bakwai da rabi, ta san karfe takwas da rabi yake fita gun aiki in dai yana da morning shift, she don't know why he is leaving early today, har ranta bata ji dadin da ya fita bai yi breakfast ba, a hankali ta tashi ta koma dakinta. Maheer na isa gida bai ma shiga da motarsa compound din ba yayi parking a waje, sai da ya shiga compound bayan sun gaisa da securities din bakin gate ya ɗan ji hankalinsa ya kwanta, babu kowa parlon gidan ya haura sama zuwa bangaren Ammi, da sallama ya shiga cikin parlon, zaune ya tadda Ammi tana zipping din babban akwati ga Aymaan goye a bayanta, Bilkisu dake goye da Aryaan ita ma tana kokarin rufe wani akwatin, Zaunawa yayi yace "Ina kwana Ammi?" Ammi na ci gaba da abinda take tace "Lafiya lau" Maheer ya amsa gaisuwan da Bilkisu take masa sannan a hankali yace "Ammi wannan akwatunan fa?" Ammi tace "Ka ga tun kan Abbanka da ɗan uwanka su sa ni a bakin duniya ga kayan yaran nan na hada masu tas, a samu warce zata kai su kano gun uwarsu su huta nima in huta, yanda muka ga rana haka muka ga dare, har yanzu kuma sun ki shan sabon madaran, ruwan ma da suke ɗan sha sun ki amsa yanzu, ga zazzabin jikinsu yaki sauka, to shine yasa na kira ka tun da asuba in ce maka in za a samu jirgin karfe shidda ka siyi ticket kawai a samu wanda zai kai su kano, Allah Ubangiji ya raya su..." Shiru Maheer yayi, Ammi ta karasa rufe zip ɗin akwatin dake dauke da kayan jariran tace "Toh ga kayansu, in ma ba a samu ticket din ba sai a zuba fetur a mota a tafi a kai su" Maheer ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "To wa zai kai su Ammi?" Ammi tace "Oho, ni dai ba na hada masu kayansu ba, sai kaje bangaren Abban naka ku yi shawaran wanda zai kai su, kar a sa ni a bakin duniya" Maheer bai sake cewa komai ba, Ammi ta kalli Bilkisu tace "Ki shiga daki ki dauko sabon pampers din da aka bude" Bilkisu ta shiga dakin, Maheer dai kallon Ammi kawai yake, Ammi tace "Ai na samu labarin matarsa ta shigo Abujan jiya, sai kaje ka samesa a bangarensa in ita zai ba yaran ta koma kano da su sai ku bata, ko kuma a ba Usman ya kai su tunda shi da Abban naka sun fi kowa damuwan a kai su kano gun uwarsu" Bayan few seconds Maheer ya mike ya nufi kofa ya fita, bangaren Abbansa ya tafi yayi sallama, Abba na zaune parlor yana waya, Maheer ya zauna ya jira har Abba ya gama wayar da yake sannan ya gaishesa, Abba ya amsa yace "Ya gida?" Maheer yace "Alhamdulillah" Abba yace "Wato kai a matsayinka na babba baza ka bude baki ka dinga gaya ma uwarka gaskiya ba ko? You act like duk abinda tayi dai dai ne, sai kayi shiru ka koma gefe kana kallonta, wani irin wawan biyayya ne wannan Maheer, ko attempting na saka ta a hanya kai baka yi, her yes is always ur yes, to in baka sani ba you are doing her harm than good, in the case of this little babies kai likita ne kasan consequences din rabasu da baabarsu amma kayi shiru ka koma gefe acting like it's normal, they are so many ways u can talk to ur mother without being rude, beside kai da ita akwai mutual understanding tsakanin ku, in kayi mata magana zata fi fahimtarka akan ɗan uwanka ko ni, amma you prefer to keep mute a cutar da yaran, to alhaki a kanku kai da ita" Maheer ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Abba ai ta shirya kayansu yanzu za a kai su kanon, ban dai san yanda za ayi arranging tafiyar ba" Abba yace "Arranging wani tafiya? Ita da mai aikinta baza su iya kai su Kanon ba?" Maheer ya sauke kansa yace "She said she is not too fine, shine tace in sameka mu yi magana a samu wanda zai kai su can Kanon" Abba yace "Amina is around, yau kuma zata koma Kano, so she can go with the babies" Maheer yace "To shikenan" Bayan few minutes Maheer ya mike ya fita daga parlon, shi kansa ya samu relieve bayan Ammi ta amince a kai twins din gun uwarsu, Maheer na fita Abba ya kira Hajiya Amina don ya sanar mata tunda karfe goma dama tace masa zata bi Flight ta koma Kano tare da yan biyunta da suka shigo Abujan tare, bayan Abba ya sanar mata zata kai su Aymaan kano tace "To dai yafi kam, don za a shiga hakkinsu da yawa, idan ya so tana yayesu sai a amshesu idan hakan mai yiwuwa ne" Maheer na zaune parlon Ammi bayan ya sanar mata yanda suka yi da Abba, Ammi da ko kallonsa bata yi ba tace "Sai a kai yaran airport ta amshesu a can" Kallonta kawai Maheer yake ya ma rasa abun cewa, Ammi tace "Amma zan fi so ayi tafiyar tare da Mimi" Maheer yace "Sai ta dawo ita kadai?" Ammi tace "Aa sai kaje ka daukota tunda yarinya ce ita" Maheer ya lura Ammi a fusace take, hakan yasa kawai ya mike ya fita daga parlon, flight din karfe goma da rabi yayi booking ma Hajiya Amina da Twins dinta mata sai Mayraah da little babies din, karfe tara saura ya bar gidan zai je ya taho da Mayraah a gida, Mayraah na jin shigowar motarsa gidan ta dai ci gaba da wanke wanken da take, kitchen din ya nufa yana kallonta, taki yarda su hada ido ya karasa kusa da ita yace "Mimi" dauraye hanunta tayi don ta gama, yana murmushi yace "Are you still angry at me?" Wani kallo ta masa, ya danne dariyar da ta basa, yace "You know what?" Ta daga manyan idonta ta kallesa, yace "Finally Ammi ta yarda a kai babies din kano" Kallonsa Mayraah ta dinga yi babu ko kiftawa, lokaci daya jikinta yayi sanyi, returning the twins to kano yana nufin Haseenah is still partially part of the family, communication bazai taɓa seizing tsakaninta da either Maheer or his family ba, then why is he even telling her, har ma taga kamar murna yake, Maheer sai kallonta yake ganin yanda gaba daya yanayinta ya canza, ya kamo hannunta a hankali yace "Ko hakan bai yi ba Mimi?" Mayraah ta kirki murmushi ta girgiza masa kai tace "A'a yayi mana, ya kamata dama ayi considering little babies din, Allah yasa hakan yafi alkhairi, Allah kuma ya raya mana su cikin aminci" a hankali Maheer yace "Ameen wife, and you know what?" Ta girgiza masa kai, yace "Har da ke za aje kai babies din kano" Mayraah tace "Ni a wa kuma?" Shiru Maheer yayi yana kallonta, sam bata ji tana sha'awar aje kai yaran kano da ita ba, ita da ko son ganin uwarsu bata yi har cikin ranta, a takaice tace "I don't think zan iya zuwa, don bana ma wani jin dadi" Maheer ya kwantar da murya yace "Nima ba ni na tsara hakan ba Mimi, instruction din Ammi ne, shine ma yasa na dawo in dauke ki in kai ki can gidan" Mayraah ta sake ji mood dinta ya baci sosai, bata dai ce komai ba yace "Mu je ki shirya Flight din karfe goma da rabi ne" Daga haka ya kama hannunta zuwa dakinta, ta zame hannunta daga nasa a hankali tace "To ina son zan je kaduna daga kano" Maheer yace "Kaduna? Me zaki je kiyi a kaduna?" Daga kai Mayraah tayi ta kallesa, he just realized what he just said, yayi murmushi yace "Ohhh, ok, zaki je gun grannies dinki?" Ta gyada masa kai, tana son ce masa har Mom dinta amma ta kasa ce masa haka, don a duniya kam Ammi ya kamata kawai ta bar ma wannan kalmar, a hankali Maheer yace "Har da gun Momy da Dady ko?" Ta gyada masa kai, yace "Toh shkkn, kwana nawa za ki yi?" Tace "Ko 4 days" Yace "Toh Allah ya kai mu" Ki hada kayanki kar kuyi missing flight din yana fadin haka ya kalli wayarsa dake vibrate a hannunsa, Mayraah ta kallesa yace "Ina jiranki Baby Gal, ki hada kayan" Daga haka ya juya ya fita ta bi sa da kallo with different thought running her mind, bayan few minutes kawai taji zuciyarta ya kasa hakuri ta bi bayansa, bata karasa shiga parlon ba ta tsaya jikin bango jin kamar waya yake a parlon in a low tone, sosai ta kasa kunne don jin me yake cewa, ji tayi yace "Idan ma kin cucesu Allahn da ya halicceki na kallonki kuma ki sani bazai bar ki ba, and lastly kar ki kuma kiran line dina ko ki turo min text since they are taking the twins back to you, duk wani abu na bukatarsu idan ya taso you have Ammi's number, ki kirata ki gaya mata ita zata gaya min zan kuma tura koma menene ta wajenta ta tura maki, that is all i have to say" Mayraah taji hawaye ya cika idonta, ita kawai tasan all this he is saying won't work, dole akwai lkcn da dalili zai kawo su yi waya kamar yanzu da yake waya da ita, bata tsaya ta karasa jin wayar tasa ba ta juya ta koma dakinta hawaye na zuba idonta ta hada kayanta kala biyar a akwati, muryarsa taji a bayanta yace "Har yanzu baki gama ba Mimi" Kin ce masa komai tayi, ya zagayo gabanta yana kallonta ganin danshin hawaye a idonta da mamaki yace "What happened Mimi?" Banza tayi masa, bai sake ce mata komai ba alamar ya sha jinin