Showing 24001 words to 27000 words out of 210919 words

Chapter 9 - CIWON SO

10 Oct 2024

4235

balle kuma aki miliyoya ina zamu samu? Idan kuma ba mu samu ba fa, haka zan zuba ido ina kallon rayuwar mijina uban ??a ko ??iyar da zan haifa?

%??mm... Malam Zaharadeen dan zo dan Allah%???

Likitan ya fada a lokacin da muke daf da ficewa daga office din, kusan a tare muka waigo sai yayi alama da na tafi da hannu yana furtawa.

%??mo ke zaki iya tafiya akwai abun da nake son na tambaye shi ne, wata kila a gaban ki ba zai iya amsa min ba you can go%???

Na saki hannunsa na juya na fice sai na samu su Mama da Hajiya tsaye dukansu fuska dauke da hawaye, Jinginawa na yi kusa da kofar ta kai hannu na dafe zuciyata da nake jinta a wani kalar yanayi marar misaltuwa, can kuma hannuna ya sauka a kan cikina, taya zan raini cikin da Deen ya dade yana kwallafawa rai ni kadai? Hannu Mama na ji a kafadata ashe wai kuka nake yi ban sani ba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?.

%??mahra karki saka damuwa a ranki, ciwo ba mutuwa ba ne kuma be zama lallai dan kana ciwo zaka mutu ba, ki kwantar da hankalinki babu abun da zai faru da yardar Allah%???

Na daga mata kai ina kokarin danne kukan dake kokarin fito min.

%?~ia ina zamu fara neman kudin maganin?%???

Shi ne abun da ya fado min a rai, miliyan bakwai fa ba daya ba, ba biyu ba, wana aje? Me muke da shi?

%??mhikenan Mama rasa mijina zan yi miliyan bakwai wa zai ba mu su a duniyar nan?%???

Na fada ina fashewa da kuka domin zuciyata ta karaya matuka, sai Mama ta kwantar da ni jikinta.

%??mnshallah babu abun da zai faru, ki karfafawa mijinki guiwa karki saka shi ma ya fara jin wani iri%???

Tana rufe baki Deen na bude kofar ya fito, yanayin idonsa da fuskarsa kadai sun isa su karantar da ni irin tashin hankali da damuwar dake cikin zuciyar mijina.

%??miya faru?%???

Ya tambaya kamar be san damuwata ba, sai na yi saurin dagawa daga jikin Mama na share hawayena.

%??ma komai%???

Na furta ina kallonsa hawayen dake sauko min sun ki su tsaya, ciki da karfi hali irin na namiji mai karfin zuciya ya sakar min murmushi.

%??mu tafi%???

Ba musu na fara takawa Mama na rike da hannuna shi kuma yana tsaye gefena ina ta kallon yadda yake dauke kowace kafa yana taka dayar har muka isa inda ababen hawa suke. Sai da muka fara saka Mama da Hajiya a wata napep dabam da zimmar ya fara sauke Mama kasancewar ita ce kusa sannan ya wuce da Hajiya. Mu kuma muka shiga wata napep din, kwantowa na yi jikinsa sai na ji kamar ban taba jindadin kwanciya a jikinsa ba a irin yau, haka nan kawai na ke jin kewarsa. Hannunansa ya saka ya kama nawa hannun ya rike yana kallon titi, ni kuwa hawaye suna ta yi min zirya a tsakanin idanuwana da kumatunta kamin mu isa gida na jika Hijab dina har gefen rigar Deen ya samu.

%??ma na san haka zaki yi ta kuka da ban bari an shiga dake ba, wannan halin da kike ciki shi zai karasar da ni Zahra, wata kila da kina cikin farinciki nima zan iya saka ran samu farinciki, amman damuwarki ita ce matsalata a yanzu, ji yadda kika jika hijabinki idonki har ya kumbura%???

Ya fada yana kallon fuskata, Mai Napep din ma kallona yayi sai dai be ce komai ba har Deen ya ciro kudinsa ya bashi, sannan ya rika hannuna muka nufi gida, duk yadda na so dakatarda kuka Wallahi, to wai wace macen ce za a fada mata kusancin mijinta da mutuwa ba ta yi kuka ba? Haka muka ratsa mutanen dake zaman kashe wando a unguwarmu muka bude gida. Muna shiga cikin gidan ya rumgume ni sai na lumshe ido ina maida numfashi a hankali can kuma na mika hannu ina taba fuskarsa, sai na ji hawaye na sauko masa, saurin dagowa na yi na kalleshi.

%??mamu samu kudin Inshallah%???

%??miliyan bakwai Zahra? Ina?%???

%??mllah zai mana hanya, kuma zamu samu%???

%??mamuwata yanzu ba na samun kudin ba ne, na halin da zaki shiga ne, be zama lallai dan an samu kudin an yi maganin na warke ba, kuma be sama lallai dan ba a samu maganin na mutu ba, amman ke yanzu na san kin riga da kin yi damuwa muhalli a zuciyarki, damuwarki ita ce damuwata a yanzu, idan na mutu a wane hali zan barki? Idan kuma na rayu a wane hali zaki rayu? Kina kallona da wannan ciwon kullum, Zahra bana son na rasa farinciki da murmushin da na saba gani a fuskarsa, ina son ki Zahra soyayya irin wanda bata da magani so mai rufe ido ya saka mutum aikata komai, taya ni zan samu kwarin guiwa idan kina a cikin damuwa?%???

Kamar an yi ruwa an dauke haka na ji hawayen idona sun tsaya cak, me nake nema a yanzu da ya fi farincikin mijina?

%??meen zo mu zauna%???

Na fada kamar ba ni ba ina kama hannunsa mu nufi kofar falo, sai ya saka makullin hannunsa ya bude kofar muka shiga, a kujera daya muka zauna sai ya cire min hijab din jikina ya gyara min fuskata, sannan ya jani jikinsa ya rumgume.

%?mina zamu samu wannan kudin?%???

Shine abun da ya fara zuwa min a rai, kamar ya san abun da nake tunani kenan sai na ji ya shafa kaina yana fadin.

%??mina nan kina tunanin inda zamu samu kudi ko?%???

Ya dago na kalleshi ina murmushin karfin hali.

%??mkwai gidan da Baban ya bar mana ni da Yaya Maryam, zan ce a raba a bamu nawa sai na saida, kuma yan'uwana mahaifina suna da rufin asiri na san za su iya taimaka mana%???

%??muk kudin da zamu samu ba zai kudin da ake bukatara ba, and bari na fada miki ba zaki sai da gidanku na gado saboda ni ba, i won't allow that, and please promise me duk halin rayuwa da matsin da zamu shiga ba zaki taba zuwa gurin Abiey neman taimako ba%???

Na girgiza masa kai.

%??mo na rasa kowa a duniya bayan ba zan taba zuwa gurin Abiey neman taimako ba, ba zan sake yin arba da fuskar maketacin mutum kamar Abiey ba, balle har na nemi taimakonsa har abada Deen har ta abada%???

Na fada da kakkausar murya, ajiyar zuciya na ga ya sauke sannan ya sake rumgume ni. Mun dade a haka kamin ya sake ni ya dago da ni jikinsa.

%??mari na je na yi cefa ne, na girka mana wani abu mu ci me kike so?%???

%??mai na ke so Deen kai na ke so%???

Na furta ina masa wani irin kallo na kauna da ni kaina ban san ta ina soyayyarsa take karuwa a zuciyata ba. Murmushi yayi ya rika hannuna ya sumbata

%??mi ai gani a kusa da ke, i love you%???

Kana ya saki hannun nawa bayan ya furta, ya shiga bedroom be dade ba ya fito ya fice zuwa yi mana cefane. Fitarsa da minti biyar Yaya Maryam ta shigo gidan tana sallama, ni kuma na unkura da cikina na mike tsaye da zimmar fita na tarota sai gata ta shigo falon da kuzarinta. Ina kallonta hawaye suka sauko mata ni kuma na yi murmushin karfin hali na koma na zauna.

%??maya Maryam%???

%??ma'am Zahra%???

Ta amsa min da muryar kuka tana kallona cike da tausawa kamin ta kalli cikina.

%??ma kike ji yanzu?%???

%??mana jin komai%???

Na amsa ina kokarin tare hawayen da suke son taruwa a idona, ta so ta yi ta dawo kusa da ni ta zauna.

%??ma kira Mama zan je asibiti sai ta fada min kin dawo gida kuma ta fada min abun da likita ya ce%???

%??mani lokacin jarabawa takan zowa bawa ta fuskar da bai yi tsammani ba, zan yi zaton bayan bakinciki da Abiey ya saka min zan sake fuskarta wani ba, Yaya Maryam bana son na rasa mijina, shi ne rayuwata na saba komai Deen yake min ban san dadin zama da namiji ba sai da na auri Deen, rasa miji a gurin mai shekara ma akwai damuwa balle ni, cikin farin nake dauke da shi Yaya Maryam kudin hidima ma muna nema balle kuma samun kudi mai yawa haka yana da wahala na san rasa Deen zan yi%???

Na fashe da kuka, sai ta rike hannuna tana kuka.

%??manwana... Kin tuna ranar da za a daura aurenki da Abiey%???

Na daga mata kai.

%??ma so ya kunyata ya kunyata mutanen da aka tara da sunan aurenki, sai Allah ya kawo miki Deen kin tsammaci haka?%???

Na girgiza mata kai alamar aa.

%??mita ce Allah ya kawo miki ba tare da kin sani ba, kuma daya kawo miki sai ya zabo miki wanda yake sonki tsakani da Allah fiye da Abiey, wanda yake gudun bacin ranki yake kaunar farincikinki%???

Na daga mata kai cike da gamsuwa.

%??moh a nan ma shi zai kawo mana mafita, karki saka kanki a damuwa kina da dauke da ciki, zamu samu mafita da yardar Allah%???

%??mnty Miliyan Bakwai fa... Ina zamu samu wannan kudin?%???

%??mi yi ta addu'a Allah zai kawo mana mafita, gidan da Baba ya bar mana zamu saka shi kasuwa na san zai yi miliyan uku ko sama da haka ma kin ga sauran sai mu nema gurin Allah%???

%??mar da na ki ka son?%???

%??miye amfanin duk wani abu da zan mallaka a duniyar idan ban taimaki yar'uwata ba? Haba Zahra%???

Ban san lokacin da na kwantar da jikina a jikinta ba ina jin wani irin kaunarta na shiga raina, daman mun saba ni da ita idan matsalar wani ta taso a tare muka haduwa mu magance, wani lokacin kuma idan ka ga muna fada sai ka rantse da Allah zamu iya dabawa junanmu wuka, musamman lokacin da bata yi aure ba, sai mu kwashe sati daya muna gaba da juna, amman da zarar wani ya taba ta ko ya taba ni daga ranar gaba ta yanke.
10/1/22, 22:01 - Buhainat: *B??0? ?]Mq?? CIWON - SO B??0? ?]Mq??*

By Khadeeja Candy


9??_/Q

Yana dawowa daga cefane, Yaya Maryam ta karba ta girma mana shimkafa da miya da dan kifin daya siyo mana.
Muna tsakar gidan ni da Yaya Maryam Baba ya sallamo ya shigo fuskarsa dauke da damuwa, ni da Yaya Maryam muka gaishe shi ya amsa mana yana kara tambayar bayanin abun da likitocin suka ce, Deen na jin haka ya fito ya tarbi mahaifinsa da far'ar suka shiga cikin falo, be wuce awa daya da yan mintuna ba ya fito cikin yanayin damuwa yayi mana sallama ya fice, duk yadda na so ya tsaya har Yaya Maryam ta karasa girkin ya ci be tsaya ba, sai addu'a yake ta mana yana saka mana albarka.

Bayan Yaya Maryam ta gama ta zubo mana ni da Deen ita kuma ta zuba a plate dabam ta ci, ni kam kasa ci na yi ga mamakina shi kam sai ya ci abincin sosai kamar ma be taba ci abinci mai yawa irin na ranar ba, aka'ida idan ban ci abinci ba baya ci amman a yau sai ya manta da duk wannan ya zauna ya ci abincin sosai kamar shi ne abincinsa na karshe.

%??mari na fita na samo miki wani abu da zaki ci%???

Ya fada bayan ya kwashe kayan da muka ci abincin, yana fitowa waje Yaya Maryam ta tsayar da shi ta kira ni.

%??mahra...%???

%??ma'am%???

Na amsa ina yunkuwa da cikin na tashi abu ga mai son jiki. Daker na karaso falon na zauna kusa da mijina, sai ta kalleni ta ce.

%??mamata yayi ku koma asibiti abaku takardun da ake bukata so that ko zamu nunawa wani muna da hujja amman idan babu takardun aikin da kudin aikin yake rubuce rubuce wani zai yi zaton kamar karya ne, abu na biyu kuma Deen ka yi magana da Hajiya idan tana da wata hanya can da zamu iya samun taimako sai a kara, nima kuma zan yi duk abun da ya dace da yardar Allah%???

Shiru Deen yayi kamar ba zai ce komai ba, har sai da na kai hannu na taba shi.

%??meen%???

Ya juyo ya kalleni da murmushi a fuskarsa.

%??ma dai mun dan jira mu ga abun da Allah zai yi, akwai wani magani na sauka da nake son na gwada, kuma idan muka dage da addu'a wata kila komai zai zo da sauki%???

Daga ni har Yaya Maryam mamaki muke masa.

%??mane irin maganin hausa kuma? A garin neman gira a sai a rasa ido, abun da aka ce ya kai stage din da ba a so sai kuma ka ce zaka sha wani maganin hausa?%???

Yaya Maryam ta fada, sai yayi murmushi.

%??miliyan bakwai? Haba samunsu ai ba mai yiyuwa ba ga talaka, da ma ace ina da wata kaddarar ne da na aje shago ne nake tsoro fa shagon ma kuma ba nawa ba, Hajiya kuma bata da komai Wallahi yan'uwanta kuma ba wasu masu son zumunci bane balle mu saka ran su taimaka mana, mai son Zumunci yayanta ne kuma Allah ya karbi abun sa, Baba Kuma danginsa ba wasu masu karfi ba ne daga shi har su babu mai tada wani%???

%??mllah zai ba mu Deen%???

Na fada a sanyaye.

%??moh Allah ya kawo mana mafita%???

Duk muka amsa da Ameen sannan ya tashi ya fice, be dade da fita ba Yaya Maryam ta saka hijab dinta ta fice bayan ta yi min nasiha ta kwantar da hankali, be dade ba ya dawo da lemun kwalba marar gas da gasashen naman ragon da nake kyautata zaton zai kai dubu uku a yadda rayuwar nan take da tsada. Sai da ya zauna ya bude naman sannan ya riko hannuna na dawo kasa na zauna.

%??mllah yasa ba kudin da kace kana ajiya ka taba ba%???

%??moh idan ban taba na siya miki abun da kike so ba, mi zan yi da su%???

%??mmman kasan abun da yake gabanmu%???

%??mannan dabam yanzu kika gama fadin Allah zai kawo mana mafita ai, so kawai ki yi shiru da bakinki ki ci kawai%???

Murmushi na yi na kai hannu na taba fuskarsa, sai ya saka hannunsa yana daukar naman yana saka min a baki.

Washe garin ranar muka koma asibiti duk wani abu daya kamata mu yi sai da muka yi suka hada mu da likita da ya kamata ya duba shi aka kara ba mu wasu gwajen gwajen da zai kai dubu dari biyu da ashiri har da yan canji sama, sannan kuma suka ba mu takardar aikin dabam dake dauke da kudi kusan miliyan shida da dubu dari da sittin, a lokacin ne hankalina da na Hajiya ya kara tashi sai dai shi kadan ban ga wata damuwa a tare da shi ba, har kara ma jiya da aka fada mana yanayin ciwonsa ya nuna damuwa a tare da shi tsabanin yau da kamar ma murna yake da abun.
Nikam gaba daya na gama tsinkewa duk kuwa da irin kokarin da yake na kwantar min da hankali, Mama ma ko wane dare sai ta kira ta ji lafiyata sannan take iya bachi, sa safe kuma Mijinta zai kira wato mahaifin Deen ya tambayi lafiyar dansa da kuma ni. Ina cin abinci amman hakan be hana rama samun muhallin a jikina ba, daman ance kwanciyar hankali ke kawo kiba ba yawan cin abinci ba, wata kila kuma har da cikin nan dake kara girma kamar yana zanje ni, daman can ni ba wata mai kibar bace, balle kuma yanzu da abubuwa biyu suka hade min gurin daya.
}?}? Ina ganin tausayin mijina a idona, nima kuma zuciyata cike take da tausayinsa ga wata kalar shakuwa da soyayyarsa dake kara rabata wacce ta dara ta da. Ba a dauki lokaci ba aka saka gidanmu na gado kasuwa, duk wanda ya zo ya duba sai yayi masa tayin wulakancin abun da muke zaton zai kai miliyan biyu da wani abu sai ayi masa tayin miliyan daya da yan kai, sai dau daga karshe aka fada mana cewar dilali ake kira yayi masa kudi gida uku sai a dauki na tsakiya. Haka kuwa aka yi sai muka kira dilallin unguwarmu ya duba gidan yayi masa kudi miliyan daya da budu dari takwas sai kuma miliyan biyu da rabi sai kuma miliyan biyu da dubu dari tara. Wasa wasa aka kwashe sati biyu ba siye gida ba wasu idan suka zo suka yi ciniki ba abari ba ba za su dawo ba, wasu kuma idan suka siya sai suce zabi zasu bada mu kuma sai mu ki aminta da hakan saboda muna bukatar kudin ne, sai dai na lura da wani abu daya kwanaki suna ja, lafiyar Deen tana karuwa har wani fresh yake kumatunsa na tasowa kamar wanda lafiya tayi masa yawa. Duk lokacin da yake na ya kwantar min da hankali ne, idan ya dawo daga aikin tsaron shagon da yake sai ya fito da ni tsakar gidan mu zauna mu yi ta hira, daman kuma ya saba baya shigo min hannu rabbana sai ya riko min wani abu ko da minti ne domin ya san ni sarkin kwadayi.
Yau ma bayan mun magana cin abinci muna zaune waje muna hirar gidan da har yanzu ba a samu mai siya ba, ya kwaso kayan wankina ya fita ya siyo sabulu da omo da zimmar zai wanke min tufafin kamar yadda ya saba idan kayana suka yi datti shi yake wanke min ya goge ya jera min a wardrobe. Sai yau wannan karon bana jin zan iya barinsa na saka hannunsa cikin ruwan ma balle har ya wanke, sanin ciwon dake damunsa ko a da da ace na san ba lafiya yake ba ba zan taba yarda yayi min wanki ba, girki dan kam zan bari domin ban iya girka komai ba ban da ruwan zafi, indomie ma idan aka yi wasa koneta nake, domin na girma da kiriniyar da bata bar ni na iya komai ba. Ina ganin ya dauko bokiti na tashi na fara kwashe kayana

%??me zaka yi wanki saboda na maida ni mahaukaci%???

Tsayawa yayi yana kallona kamin ya kyalkyale da dariya.

%??mhikenan zauna ki wanke daga yau ba zan sake saka hannuna na wanke ba%???

Ya fada saboda ya san babu abun da na tsana a duniyar nan sama da wanki.

%??mi ban ce zan yi ba, amman kai ma ba zaka yi ba%???

Kayan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login