Showing 3001 words to 6000 words out of 210919 words

Chapter 2 - CIWON SO

10 Oct 2024

4239

da kasaita ya kalleta sai ta mike tsaye tare da idanuwansa.

%??mou're Pretty...%???

A tsakanin furucin da kuma ganinsa sai ta rasa wane ya fi bata mamaki.

%??mhank You Abiey%???

Ya gyara zaman idanuwansa a fuskarta.

%??mo you know me%???

%??mou're famous waye be sanka ba?%???

Sauban ya amsa masa, juyawa ya yi ya kalli Sauban kamin ya juyo ya sake kallon yarinyar form head to toe.

%??mhat if i told you i like you%???

Murmushi ta yi ta juya ta fice daga falon. Sauban kallonsa kawai yake da mamaki.

%??mhat if i say i like her?%???

Abiey ya fada ba tare da ya Kalli inda Sauban yake zaune ba.

%??mn mata engaged%???

Sai a lokacin ya kalleshi.

%??mai ba san yadda zaka yi convinced dinta ta so ni ba?%???

%??ma son ka ne matsalar ba, I'm sure tana son ka, rusa engagement din ne matsala%???

%??mhat's the difference da Zahra ce da sai ta zata sama min yarinyar%???

%??moint of correction, that's the problem, baka da magana sai ta Zahra%???

%??meah she's me, I'm her%???

%??mo she's her, you're her stop fooling yourself%???

Abiey ya dora kafarsa daya saman daya.

%??mna tuna wata rana zamu yi wasa, kuma tana son gani sai tace min, Abiey ka tafi da ni i told her gidanku ba za su bari ba, sai ta ce ka sace ni, zan baka number Mama na ka kirata kace ta baka miliyan goma, sai ka dauke ni mu tafi, idan muka dawo sai ka ce ka rage mata ta bada dubu goma, idan ta baka sai ka sake ni%???

%??mnd you did?%???

Sauban ya tambaya, sai ya girgiza masa kai yana murmushin takaici.

%??mo amman da na san wannan ranar zata so da zan rayu babu Zahra a kusa da ni, da na sace ta na aureta%???


%??ma ci abincin please...%???

Sauban ya fada yana kallon abokinsa, ko kadan baya son Abiey na tunawa da rashin Zahra, saboda ya san abun zai yi effecting dinsa sosai.
10/1/22, 21:58 - Buhainat: https://arewabooks.com/chapter?id=6302bd0285b828fd38495813

*B??0? ?]Mq?? CIWON - SO B??0? ?]Mq??*

By Khadeeja Candy


2??_/Q


Karfe daya daidai aka daura auren Sauban, a Tahir Guest Palace aka yi liyafa. Duk wani kai da kawo da ango ke yi Abiey na zaune guri daya ya natsu kallonsu ma sai ya ga dama yake. Daman can Abiey wani murdadden mutum ne da ba komai yake burgeshi ba, abun da kuma kake ganinsa ba a bakin komai ba, shi za iya daukarsa mai muhimmanci.
}? Sauban ya masa uzuri ne, saboda ya san halin da yake ciki, kuma ya san abokinsa ba mai yawan son surutu da hayaniya ba ne, tun bayan tafiyar Zahra. A gidansu Sauban Abiey ya karasa wuninsa, duk kasancewar Sauban din baya tare da shi yana can tare da sauran abokansa, shi kuma yana dakin Sauban din doing nothing, ya kwanta sai dai ba bachi yake ba, kansa kuma yana jin kamar babu komai a ciki, domin kokarin tunani yake tunanin komai ya ki zuwa masa. Tashi ya yi zaune ya nufi bathroom sai da ya shiga sannan ya cire tufafin jikinsa ya kunna shower ya sakarwa kansa ruwa, ya rufe ido jikinsa na amsa each and every drop of water da ke sauka a fatarsa. Haka nan kawai ya ji yana bukatar bata lokaci a tsaye ruwan na zubar masa.
}? Ya kusan awa a tsaye sannan ya kashe shower ya nufi inda tawul yake ya dauka ya daura, ya sake daukar karami ya soma goge jikinsa. Zuwa ya yi gaban madubi ya tsaya yana kallon yadda Allah ya tsara halittar kirjinsa. A nan ma ya bata lokaci sannan ya bawa jikinsa hakkinsa na kamshi kana ya nufi wardrobe din Sauban ya bude dayan bangaren da ya san sabin kaya yake ajewa, ya cire hanger ya saka tufafin sannan ya nufo wayarsa ta dauka tare da key din motar ya nufi kofa kamin ya karasa kofar Anty ta bude ta shigo fuskarta dauke da murmushi.

%??mnty...%???

Ya furta with confused.

%??me kake yi a daki Abiey?%???

Ya dan yi baya kadan kamar mai tunanin abun da zai fada. Anty kuma ta tsare shi da ido.

%??mhm.. Talk%???

Ya yi murmushi.

%??mnty bana jin sakewa cikin mutane, so i decided na zauna a nan%???

%??manzu da ka tashi ina zaka je?%???

%??mida...%???

Ya fada da kamar tunanin gurin zuwa, domin ba da niyar zuwa gida zai fita daga dakin ba, kuma idan ba gidan ba be san inda zai je ba.

%??mbiey haka kake son zama kamar ba mutum ba, yau ranar daurin auren babban abokinka amman ace kana nan daki kamar mai tsoron mutane? Ka bar shi can by himself ka kyauta kenan? And now you're talking me gida zaka je? Ba kai za a je kai ango ba?%???

%??ma ni mana, kawai dai zan je na dawo ne%???

%??maya fada miki ina dakin nan?%???

%??ma tambayi Ammy tace bata ganka ba, na kira wayarka baka daga ba, sai na kira Sauban ya fada min kana dakinsa saboda ka karbi makullin dakin%???

%??manzu zan ba wani keys din sai na same shi a inda yake%???

%??ma'ayi Dinner Anjima%???

%??m don't think zan iya zuwa, amman zan gwada%???

%??mou have to, Dr ma ta tafi tare da Ammy gida yanzu, saboda su samu shiryawa anjima su zo dinner, sai dai ni ba zan samu dawowa ba yanzu zan wuce%???

Ta fada a sanyaye sannan ta juya kamar zata tafi sai kuma ta juyo ta kalleshi.

%??mbiey....%???

Sai kuma ta yi shiru ta kasa karasawa.

%??ma... Sai.. Kaje gida ba yau.. Zaka iya kwana a gurin Ammy if you like%???

Abiey ya yi murmushin da be shirya ba ya shafa kansa ya juya ya juyo.

%??mai Martaba yace kar na kwanar masa a gida?%???

%??mo akwai inda zan je ne yau, maybe can zan kwana bana son ka kwana gidan bana nan%???

Wani murmushin ya sake yi na miskilanci.

%??maba Anty I'm not a child, I'm old enough to know what is right and wrong for me, I'm enough to know who loves me and who don't, Anty just go straight to the point ki ce Mai Martaba yace kar na kwanar masa a masarauta yau, ai daman na san ya tsane ni kuma na karbi hakan%???

%??mbiey ba son ka ne ba ya yi ba, kai da shi kun kasa fahimtar juna ne%???

Anty ta fada try to convince him, sai ya sassauta muryarsa ta yardar zata fahimta.

%??mnty ki daina damun kanki, Mai Martaba ba zai taba son na ba, Mai Martaba be taba tsanar wani mutum kamar yadda ya tsane ni ba, sai dai hakan ba zai saka ni na tsane shi ba, he is still my father no matter what happen and i still proud of him, ba zan taba tsanarsa ba%???

Ya karasa idonsa na cika da kwalla, Anty ma idonta ya cika da hawayen tausayinsa saboda ta san irin yadda Abiey ya rasa gata da soyayyar mahaifi tun yana jariri har zuwa yanzu da ya girma.

%??mbiey%???

Ta juyo tana kiransa, be juyo ba be kuma fasa fitar da yake kokarin yi ba. Sai da ya shiga motarsa dake fake harabar gidansu Sauban sannan ya samu sukunin sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa yayi ma motar key.
}? Tafiyar minti talatin ta kai shi gidansu gurin Ammy, tun daga waje ya gane Dr Zainab tana gidan kamar yadda Anty Amarya ta fada masa saboda motarta da ya gani a waje. Karasawa ya yi ya murda kofar falon a hankali ya shiga try to make himself calm kamar babu damuwa a tare da shi, kamar bako haka ya bi ko'ina na katon falon da kallon sannan ya zauna saman kujera ya lumshe ido yana sauraren bugun zuciyarsa. Kamar an jefo Zainab haka ta fito ta sauko downstairs daman ta hango shigowarsa ta windows Ammy.

%??mbiey miyasa da zaka taka jirgi ka bar kasar nan ba tare da ka fadawa Mai Martaba ba? Yanzu kuma ka dawo ka sauka a gidansa har ka shirya ka fito baka shiga ka gaisa da Mai Martaba ba?%???

Maganar da Dr Zainab ta yi bata saka shi bude ido ba, dan baya jin zai iya amsa mata ma, yayarsa ce ta uku da Ammy ta haifa sai dai uwa kawai suka hada uba kowa da na shi, shekara uku ta ba shi haihuwa, sai dai gurin Abiey age it's just a number, musamman ita da suka zama kamar twins a wani lokaci can baya saboda shakuwa.

%??mmmy....%???

Ta kwala ma Ammy kira ganin ba shi da lokacin amsa mata, sai kuma ta juyo ta cigaba daga inda ta tsaya.

%??mbun da kake yi be dace ba Abiey, no matter how Mai Martaba zai tsane ka, mahaifinka ne, kuma dole ka bi shi idan kana son samun albarka%???

Ya bude idon ya kalli tsayen da ta yi a kansa.

%??mnd....?%???

%??mike and...?%???

Ta tambaya cikin rashin fahimtar furucinsa tana daga kafadunta.

%??muk wata biyayya da ya kama ??a yayi ma ubansa na yi ma Mai Martaba, amman hakan be saka ya so ni, ya kamata ku yarda cewar Mai Martaba ba zai taba so na ba, bayan kuma ni ya kamata na tsane shi, domin tun ina jariri ban san wani abu gatan mahaifi ba, kala daya Mai Martaba be tana dinka min ba, ko da rana daya be taba tambayar lafiyata ba, na ci abinci? Ban ci ba? Mi nafi so, wa na tsana me ke burge ni Mai Martaba be sani ba, saboda ya tsane ni mi na masa wa na kashe masa? Please i want to live in peace!%???

Ya karasa yana hade mata hannayensa alamar rokon yake ta bar shi ya huta. A maimakon ta yi shirun kamar yadda ya bukata sai ta rufe shi da fada.

%??mhut the fu*k up boy, komai Mai Martaba yayi maka mahaifinka ne, kuma dole ka bi shi matukar kana son samun rahamar Allah da albarka%???

Tashi ya yi daga jingine da yake da kujera ya zauna daidai yana mata wani kallo.

%??malleki kin tsaya a gabana kina kokarin nuna min yadda zan yi rayuwa, macen data kasa sadaukar da farincikinta saboda farincikin dan'uwanta kanenta daya tilo! Kika kasa sallama natsuwa da farinciki dake zuciyarki saboda dan'uwanki%???

Ammy dake saukowa ta daka masa tsawa.

%??mliyu.... Enough...%???

Daga kansa yayi ya kalli mahaifiyarsa. A take idon Dr Zainab ya cika da hawaye da bata sa ran zuwansu a yanzu ba.

%??mna son mijina Abiey, kwankwacin yadda kake son Zahra, can you please put yourself in my shoes? Taya zan sadaukarda rayuwar mijina da farincikin 'ya'yana saboda...%???

Ta kasa karasawa muryarta sai rawa take hawaye na mata zirya. Sai ya karasa mata yana yamutsa fuska.

%??maboda ni right? You're the reason why i lost Zahra, and because of that i hate you Doctor%???

%??meen forced me...%???

Ta fada kuka na daf da subuce mata.

%??mou're so selfish, ke ce kika lalata komai and because of that i lose her forever%???

%??mliyu tashi ka fita daga falon nan, i don't want to see you in my side please leave%???

Ya kalli Ammy sai yayi murmushi ya mike tsaye.

%??mow...%???

Daga haka be sake cewa komai ba ya juya ya nufi kofar da ya shigo ya bude ta slowly ya fita. Dr Zainab ta bishi da kallo hawaye na sauko mata.

%??mmmy Abiey yana da gaskiya, ya rasa soyayyar mahaifi, kuma ya rasa wanda ya fi so fiye da kowa a duniya, he deserved Happiness, kuma yana da damar da zai tsane ni, da ace ban biye tsoro da son zuciya na aikata abun da Deen ya umarce ni da shi ba, da yanzu Abiey be shiga cikin wannan halin ba, kuma da yanzu be dora min laifi ba, duk cikin yan'uwa babu wanda Abiey ya shaku da ita kamar ni, kuma a haka na zama silar rasa farincikinsa%???

%??mi daina biye shi Ciwon So ne yake damunsa, ta ya zaki salwantar da rayuwar mijinki uban yayanki saboda shi? Ki ma daina saka wannan a ranki%???

Kujerar da Abiey ya tashi Dr ta nufa ta zauna tana hawaye jikinta gaba daya yayi sanyi.

Abiey na fita falon cikin motarsa ya shiga ya yi reversed kamin ya isa gate mai aikin kula da gate din ya bude masa, sai ya fisgi motar ya hau titi kamar wanda baya son ransa.
Driving yake hawaye na cika idonsa suna saukowa tun yana daurewa har sai da ya kai ga dukan sitiyarin motar da karfin tsiya kamar zai raba shi biyu.

%??m miss you Zahra i miss you so much....%???

Tafiyar minti ashirin da wani abu ya nade hanyar da gudun motarsa ya isa gidan Mommy Uwani cikin minti goma sha biyu. Sau daya ya danna horn aka bude masa gate ya shiga ya faka harabar gidan sai kuma ya samu kansa da kasa bude motar ya fito, ya ji kamar zaman motar zai fi yi masa dadi fiye da shiga cikin gidan ma, kwantar da kujerar motar yayi ya jingina ya kwanta ba tare daya kashe motar ba ya lumshe idonsa ya rungume hannayensa.
After like 30min ya ji ana kwankwasa glass din motar, hakan ya saka shi bude ido, sai ya yi arba da Yasmin step sister din Dr Zainab ta uku, sai dai ita bata iya ganinsa kasancewar motarsa mai bakin glass ce. Tashi ya yi zaune ya bude motar sai ta matsa gefe ya fito.

%??mommy ta ce na duba ka ko lafiya?%???

A maimakon ya amsa mata sai kawai ya rumgumeta ya lumshe ido. Kamar wanda ta mutu haka komai nata ya tsaya cak with shock kamin numfashinta ya dawo jikinta a hankali. Kasa motsawa ta yi duk da kasancewar a compound din gidan suke, tana gudun wani ya gansu domin ba halinta ba ne, shi ma kuma na halinsa ba ne, be taba gwada yi mata haka ba ko a mafarki.

%??mbiey do you need someone to talk to?%???

Ya daga mata kai da sauri.

%??mkay... Bari mu shiga cikin gida sai ka sha ruwa mu yi magana ka ji?%???

Ya kara rumgumeta.

%??mlease let me hug you%???

Ya furta calmly har lokacin idonsa a rufe suke.



ZAHRA POV.

Bayan na sha cornflakes din daya siyo min, na kwanta saman kujera shi kuma ya fita tsakar madaidacin gidanmu ya fara gyara kayan miyar da zai dora mana jalof din da su, tun ina jin motsinsa da yadda yake kai da kawo har bachi ya sace ni, daman ni da bachi kamar 5&6 ne, indai zan ci na koshi sai kuma bachi duk inda na samu kuma yinsa nake tun ina karama har zuwa yanzu da nake da da shekara ashirin da daya. Ina farkawa na gan a lullube ni an dora kaina saman filo, na san ba kowa zai min wannan ba sai abokin shigata aljanna wato Deen mijina masoyina. Cikin shagwaba da na saba na dan juya kaina kadan na kalleshi yana zaune tsakiyar falonmu yana goge tufafin daya wanke min jiya.

%??mabe na kin farka?%???

Na dan mitsintsinka ido kamar wata yar baby ta turo baki gaba ba tare da amin komai ba sai dan tsabar shagwaba da na saba da ita tun ina karama har zuwa yanzu.

%??mbincin ya yi?%???

%??mo acici mala'ikun tauna, bari na zo na rika ki ki wanke bakin sai mu ci abincin tare daman ke nake jiran ki farka%???

Yana fadar hakan ya nufo inda nake cike da so da kauna ya ya rika ni na tashi zaune kana ya mikar da ni tsaye yana gyara min dauren zanen dake kokarin subuce min, daman can ni raguwace aiki ko na daukar tsintsiya ne bana so balle kuma yanzu da nake dauke da cikin wata bakwai. Tare muka shiga bandakin dake bedroom dina, shi yayi fitsari ni ma na yi na wanke bakina da fuskata sannan ya rika hannuna kamar ance masa koyon tafiya nake.

%??maka a hankali%???

Ya fada yana kallon yadda nake takawa har muka isa a inda muka saba zama mu ci abincin. Center carpet ya shimfida mana na zauna sannan ya fita waje ya shiga kitchen ya dauko mana abincin daya dafa. A plate daya ya zuba mana spoon ma daya ne, kofin ruwanmu ma daya ne, daman can indai zamu ci abincin a tare to bana bata hannuna shi zai min komai da hannunsa idan kuma spoon ne daya zamu yi amfani da shi. Sai da ya fara ba ni ina ci sannan shi ma ya soma ci, ba karya mijina gwanine ta kowane fanni, ga kyau ga tsabta ga soyayyar ga iya mu'alama ga kuma iya girki. Dadin abincin ya saka na fara masa santi.

%??meen idan muka yi kudi ka gina mana katon gida%???

%??mi dole, kin ga sai mu shuka shimkafa, mai, magi, da kifi, kayan miya da komai da mun tashi girka jalof sai dai kawai mu diba mu girka%???

Ya fada yana min kallon zolaya, aiko sai dariya ta ce min salamu alaikum, har sai da abincin ya sarke ni, da sauri ya dauko ruwa ya bani na sha kadan sannan ya cigaba da ba ni abincin.

%??mdan na yi katon gida, duk sai kin cika min shi da yaya, ki yi ta haihuwa kamar kaza%???

Na turo baki gaba.

%??mab Wallahi ba zan iya ba, sai dai ka auro wata, daman maza da sun yi kudi sai aure%???

Ya aje spoon din hannunsa ya kama hannuna ya rike yana kallon cikin idona da wani irin tsantsar kauna da soyayya marar algus.

%??mna son ki Zahra, ina mik??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i wani irin so da wani dan'adam be taba miki irinsa ba, ina miki wani irin so da bana son kallon mata saboda na taya ki tsare kaina, kullum kece nake tunanin yadda zan faranta miki me zan yi na burge ki, Alhamdulillah na fi karfin abun da zan ci yau da kullum amman da zan yi arziki na fi kowa kudi a duniya, ko wace kaddara tawa sai na saka mata sunanki, Wallahi Zahra na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba, ina nufin ko da a zuciyata ne wata rana ta kyasa min son wata mace ba zan taba bari ba, balle har na hada ku a karkashin inuwa daya har abada Zahra, Ciwon Sonki ya riga ya so ke ni kuma ba zan taba warkewa ba%???

Idona ya cika da tausayinsa ba tausayi na rasa ni ko wani abun ba, sai dan yadda kaunata take dawainiya da shi, ni kaina ina masa son da bana jin akwai mace da take yi ma mijinta irinsa.

%??meen wani lokacin tsoro kake ba ni, kana min wasu kalamai kamar ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login