Showing 12001 words to 15000 words out of 210919 words

Chapter 5 - CIWON SO

10 Oct 2024

4237



%??mdan ma na fada miki ai ba magani zaki masa ba, muna gudun ki shiga damuwa ne shiyasa muka boye miki, a kullum tsoronsa kar ciwonsa ya jefa ki cikin wata damuwa%???

Hawayen da na gani yana sauka a idon Hajiya, da kuma kalamanta sai suka ba ni mamaki kuma suka tabbatar min cewar ba a yanzu Deen ya fara ciwon nan and that's mean akwai abun da suke boye min, ina tsaka da tunanin abun da zan fada ko na tambaye ta da zai kara fito min da ainahin abun da yake damun mijina sai na ji ta yi sara a gabar da nake so.

%??m duk lokacin da na yi masa maganar neman magani, sai Hajiya dan Allah a boye maganar nan saboda Zahra, mijinki yana sonki Zahra, irin son da ban taba gani ko jin wani yayi ma matarsa a tahirin rayuwata, ni kuma dole na so abun da yake so%???

Ta karasa min daker kuka na cinta, wanda hakan yayi sanadiyar shigowar Bahijja dakin da sauri.

%??mafiya?%???

Na kalleta da danuwa da babu kuka kuma babu alamunsa a kusa da idon na ce.

%??me ma kin san Deen be da lafiya?%???

A take yanayinta ya canja sai ta matsa kusa da ni ta zauna.

%??ma sani...%???

%??mi miyasa kuka boye min me hakan zai amfana min?%???

%??mhi ya bukaci a boye miki, cewa ya yi idan kika sani hankalinki zai tashi shi kuma baya son abun da zai daga miki hankali%???

%??mun yaushe yake fama da ciwo?%???

Ta share hawayen da suka zubo mata.

%??mai bayan ya aureki muka sani, amman yace mana tun kamin ya aureki yake fama da ciwo%???

%??miyasa ba a nemi magani ba?%???

Na tambaya ba dan na sani ba, sai dan na kara ba su damar fito da abun da suke boye min.

%??meman magani Zahra ba na mai karamin karfi ba ne, ya je asibiti ance ciwon hantar ya kai wani mataki da yake bukatar naira miliyan bakwai ko sama da haka ma inda hala%???

Wallahi ban san lokacin da na sake duban Hajiya dake maganar ba, ina kokarin sauke numfashi sai ya makale min a kirjina ya ki sauka.

%??miliyan Hajiya? Hajiya Mijina?%???

Na kama hannayenta na rike abun da ke cikina sai motsi yake da karfi, a lokacin ne na gane hawaye ma kala kala ne.

%??ma cire rai daga rayuwa ko? Shiyasa kuka rumgume hannayena ke da shi kuka saka ido kuna jiran mutuwarsa? In ya so ni na shiga duk halin da zan shiga?%???

Ina magana muryata na rawa saboda numfashina yaki ya daidai ga kuma cikina sai haye min yake saman zuciya, da sauri na kwanta a gurin wasu hawaye masu mugun zafi na sauko min. Hajiya ta yi saurin kai hannu ta taba ni

%??mahra? Lafiya? Shiyasa ya ce kar a fada miki saboda zaki shiga tashin hankali%???

%??mashin hankalin da zan shiga idan na rasa mijina ya fi gaban duk wani tashin hankali a duniyar nan! Hajiya ina son mijina%???

Na fada kuka na fin karfina sai na yi saurin saka hannu na rufe bakina, na lumshe ido ina jin kamar na bude na gan ni a kusa da mijina. Daker nake iya hade yawun dake tararmun a baki.

%??mahijja dauko ruwa%???

Hajiya ta fada ganin ina numfashi daker. Da sauri Bahijja ta miko mata ruwan da aka kawo min na ci abinci sai na karba da sauri na fasa pure water na sha daga kwancen da nake, a lokacin ne na ji na samu sa'ida, a take na zabura na tashi zaune.

%??mahijja samo min Napep kofar gida%???

%??mna zaki je?%???

%??mida%???

Na amsawa Hajiya ina dannar zuciyata. Sai Bahijja ta jefo min wata maganar da ban san lokacin da na daka mata tsawa ba.

%??moh ki ci abincin mana ki karya%???

%??ma zan ci ba...%???

Na amsa mata da karfi hawaye na sauko min. Tashi ta yi tana share hawayenta ta dauki hijab dinta ta fice, cikin karfi hali na mike tsaye na nufi inda Hijab dina yake na dauka na saka ban tsaya bin ta kan niqab ba na dauki jakata na nufi inda talkamina suke ina kokarin sakawa wani irin kuka marar misaltuwa ya subuce min har sai da na jingina da kofa ina jin zuciyata na mini wani irin zafi kamar an hura wuta. Ban taba jin tashin hankali irin na wannan ba, ko a lokacin da aka fasa aurena na farko ban shiga tashin hankali irin wanda nake jin kaina a yanzu ba, balle kuma ace na rasa mijina?

%?}iubhanallahi A'uzubillah ba zan taba rasa Deen ba%???

Wani bangare na zuciyata mafi alheri yana kore bangaren da ke min wani bakin sashe da ban taba kawowa a raina ba, kamar an yaye min komai a zuciyata haka na ji na daga kaina na saka talkamina da kuzarina na fara takawa ina jin Hajiya na kirana amman ban amsa ta ba, domin na san ba zai wuce tace min na dawo na karya ba. A titi na na samu Bahijja tsaye ta tsayar da wani mai napep tana magana da shi ban ce mata komai ba na shiga Napep din.

%??malam zoo road%???

Juyowa ya yi ya kalleni sai Bahijja ta ce.

%??maman ita ce matar da zaka dauka%???

%??mkay Hajiya kudinki 400 ne%???

%??muje Malam%???

Na fada ina jin kamar na tashi sama.

%??mllah ya tsare%???

Bahijja ta fada, sai na kalleta na dauke ido na maida gurin titin, iyakar kokarin da na yi na kar zuciyata ya ayyana min wani mugun abu ne, sai dai hawaye kam duk kokarina ban iya tare su ba. Har kusa da kofar gida ya aje ni na fito na ciro kudinsa na mika masa, sai a lokacin na tuna da na manta wayata a gidan Hajiya, naira dari ya bani canji kasancewar dari biyar na mika masa. Na juya da sauri na karasa kofar gidan ina tabawa sai na jita a rufe, kwankwasa na yi da karfi, ba a amsa min ba kuma ban ji motsin komai ba, a take hankalina ya kara tashi, na sake dukan kofar da karfi sannan na ji amsa.

%??maye? Zahra bata nan%???

Muryarsa da na ji sai tausayinsa da kaunarsa suka kara kama zuciyata, a take idanuwana suka cika da hawaye, wannan karon a hankali na buga kofar.

%??mahra bata nan waye wai?%???

A maimakon na amsa masa sai na sake buga kofar, ina jin takun tafiyarsa har zuwa bakin kofar kamin ya bude na jingina da kofar ina jin wani kalar abu na motsa min a zuciyata.

%??mahra...%???

Ya furta da mamaki yana kallona kamar yadda nima nake masa wani irin kallo da bana jin na taba masa irinsa a rayuwata, da sauri ya kamo hannuna ya shigo da ni cikin gidan ya sannan ya leka waje ya dawo yana duba lafiyata.

%??miya faru? Miyasa kike kuka? Miya same ki?%???

Sai na kasa amsa masa sai kallonsa nake hawaye kam sai suka samu muhallin da suka dade suna nema a fuskata, hannanyensa ya saka ya share min hawayen sannan ya juya ya shiga falon be dade ba ya fito rike da wayarsa kamin ya karaso kusa da ni ya fara magana.

%??miya aka yi ma Zahra? Miya same ta?%???

Sai kuma ya yi shiru da alama amsa take ba shi.

%??maba Hajiya, kuma shi ne aka barta ta zo ita kadai? Inda wani abu ya same ta fa?%???

Ya sauke wayar sannan ya karaso kusa da ni, sai na kama hannayenta biyu na rika hannunsa daya na mai bakina na sumbanta.

%??mamuwarka kullum akan Zahra ne Deen, kullum tunaninka nawa ne%???

Rumgumoni ya yi jikinsa sai na fashe da kuka.

%??miyasa ka boye min Deen? Miyasa%???

%??maki iya yin kuka a yanzu ai%???

%??miyasa ka boye min?%???

Na tambaya cikin kuka.

%??maboda damuwa zaki shiga Zahra%???

Ya amsa da muryar dake nuna hawaye yake.

%??mow are you feeling now?%???

%??metter%???

Na amsa min yana dago ni jikinsa ya cire katon hijab din sannan ya hade goshina da na shi ya lumshe ido.

%??m love you Deen, zamu samu mafita da yardar Allah zaka warke, duniyar da kake mafarkin zamu gina zamu ginata mu cika gidanmu da yaya dukan abun da muke fata zai tabbata Inshallah%???

%??meah Inshallah%???

Ya furta hawaye na sauko masa, sannan ya kai hannayensa ya rike fuskata ya sumbanci bakina.

%??mo zauna na shirya miki wani abu ki ci, Hajiya ta ce baki ci komai ba%???

%??mana jin zan ciya cin komai Deen, ka je dai ka shirya zamu tafi asibiti%???

Murmushi na gani a fuskarsa sai ya rumgume ni.

%??mey da kudin da zamu bata a asibiti ai kara mu siye kayan jariri da shi%???

%??maboda me? Idan kai lafiyarka bata da muhimmanci a gurinka ni tana da a gurina%???

%??mikitoci sun ce sai na kashe kudi da yawa Zahra kuma babu su%???

%??mamu yi su, zamu nemo Deen zamu samu da yardar Allah%???

Dago ni yayi daga kirjinsa yana dariya ya saka yatsansa ya share min hawayena.

%??miliyoyi ake magana fa, and ....%???

%??mamu samu Deen ka yarda da ni, zamu samu kuma zaka samu lafiya zaka warke, zamu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba%???

Hannuna ya kama ya nufi cikin falon da ni, sai da ya zaunar da ni sannan ya dawo ya dauki jakar da na bari da Hijab ya shigo da su.

%??mll this while kana zuwa asibiti Deen? Kana ciwo amman baka taba nuna min%???

%??maboda gudun irin wannan damuwar%???

Na aje numfashi da karfi irin na wanda kuka ya ci shi sosai.

%??manzu da ciwon ya kai wani mataki sai dai kawai na farka na ga ka mutu? Na tsaya jiran mutuwa kai da Hajiya? To ni na yi yaya?%???

Yayi shiru yana kallona hawaye sai sauko min suke.

%??mobena tana cikin rayuwarka Deen, idan har zan rasa ka to ina rokon Allah ya dauki rayuwata kamin mutuwarka, ba zan iya rasa ka ba Deen%???

Wani irin kuka ne ya ci karfina, da sauri ya zo kusa da ni ya zauna ya jani jikinsa ya rumgume yana hawaye.

%??marki tadawa kanki wani ciwon, kin san kina da ciki kar wani abun ya same ki%???

Na dago kaina na kalleshi da idanuwana da suka yi ja, fuskata har ta kumbura.

%??ma zame min inuwa a lokacin da wasu suka saka ni a rana, ka yi min rumfa ka rumgume ni a lokacin da wani ya yaudare ni, ka yi min masauki a lokacin da wani ya watsar da ni, ka rufa min asiri a ranar da Abiey ya so ya kunyata ni ni da iyayena, Deen kai ne fitilar haska rayuwata, shim taya kake tunanin zan iya rayuwa idan babu kai? Miyasa ba zaka tausaya min ka taimaka min gurin neman lafiyarka ba? Zan iya jure rasa komai Deen amman ban da mijina, na maka alkawari sai na samo kudin nan ko ta halin yaya, zamu nemo kudi Deen kuma zaka warke i promise%???

Ya sumbanci tsakiyar goshina har sai da na ji sanyin lips dinsa na lumshe ido, hawayen da suke masa zuba suka sauko min saman fuska suka hade da nawa suka sauko min sai na saka hannayena na tare ina jin kamar ba zan iya barin hawayen mijina su zuba a kasa ba.

%??mon't mention his name again...%???

%??mar a bada%???

Na furta idanuwana a lumshe.

%??mari na samo miki wani abu ki ci%???

Ina jin lokacin da yake kokarin dagawa sai na rike rigarsa.

%??mumgume ni Deen%???

Dawowa yayi ya zauna ya rumgume tsam a kirjinsa, sai na ji kamar na saka wuka na fasa kirjinsa na shiga na zauna daidai saitin zuciyarsa.

%??ma isa haka Zahra Mom Zahra%???

Ya furta min da muryar zolaya sai na yi dariya mai sauti na bude ido na dago ina kallon kyakkyawar fuskarsa, na kai yatsuna cikin nasa ka kwantar da kaina kirjinsa ina jin yadda ??umin jikinsa ke ratsa jikina.




ABIEY POV.

Babban dakin taro ne da kama shi sai wanda ya ci ya sha kuma ya tsaya da kafafuwansa, adon da ka yi a holl din abun kallo ne balle kuma yanzu da kwararrun masu decorations suka gyara shi. Ango Sauban da Amaryarsa Nuratu a muhalinsu da aka yi ma ado na musamman, bukin da ya hada manyan mutane kuma irinsa na farko a iyalin Alhaji Sani Asusu mahaifin Sauba, kusan duk wanda ke gurin fuskarsa da sake take kowa yana farinciki amman ban da Abiey da ya kasa zama a inda ya kamata ya zauna ma, balle har ya sake yayi walwala, sai dai jifa jifa yake sakarwa Sauban murmushi musamman da aka je gurin yi ma amarya da ango niki, sai dai hakan be hana abokinsa fahimtar damuwarsa ba, kana ango kasan yana cikin farinciki but deep down inside his heart yana matukar tausayin abokinsa, domin ya san wannan ranar zata tunawa da Abiey da ranar da aka fasa aurensa ne.
Kusan duk wanda yayi ma ango riki yayi masa wasa sai ya zolayi Abiey domin duk wanda ya san Sauban yo dole ya san Abiey idan kuma ka san Abiey dole ka san Sauba kamar alif da lam haka suke, wasu su ce sauran shi wasu kuma su ce Sauban ya masa wayo ya bar shi, iyakar karfin halin da yake na murmushi ne wanda ya tsaya iya saman fatar bakinsa. Ana musu hotuna ya fadawa Sauban zai tafi gida ya kwanta domin ba zai iya tsayawa karasa bikin da shi ba.

%??mdan ka je gida tunani zaka rika yi Abiey kara ka zauna a nan cikin mutane%???

%??mo please%???

%??mkay Allah ya sauwake%???

%??mmin%???

Ya furta sannan ya dago daga gurin ango ya sauko kasan stairs din ya nufi hanyar fita ba tare da ya kula kowa ba, yana fitowa ya ji an kira shi.

%??mbiey%???

Sai ya juyo a hankali ya kalli mai kiran na shi.

%??mafeena...%???

Ya furta with surprise, ta karaso kusa da shi tana murmushi.

%??min zo ashe%???

%??me zai hana na zo? Auren Sauban ake fa!%???

Jerawa suka yi tare suna tafiya zuwa gurin motarsa dake fake.

%??mow are you Feeling now Abiey?%???

Ya sauke ajiyar zuciya secretly ya hade yawun bakinsa.

%??mlhamdulillah%???

%??ma Zahra take?%???

Wani irin dauke wuta yayi na dakiko sannan ya amsa mata, cikin wani irin yanayi da ita ma kanta ta fahimci furta sunan Zahra ya taba shi.

%??ma yi aure tana rayuwa da mijinta cikin farinciki and that's all the matters%???

%??mar yanzu tana kallonka a matsayin wanda ya ci amanarta ya yaudareta?%???

Ya kalleta yana dan murmushin takaici.

%??mhy wouldn't she? Bayan wannan sheida nen ya shafa mata bakin kwali a idonta da bata iya ganina da haske%???

%??meen be kyauta ba...%???

%??m don't want to hear his name again, ko Shedan ban tsana kamar yadda na tsani wannan mutumen ba, ba ni babban makiyi a duniya irinsa%???

%??mana da damar ka tsane shi Abiey domin shi ya datse maka farinciki, yanzu fada min ya tsakaninka da Mai Martaba?%???

Ya dan tabe baki yana saka hannayensa a cikin aljihun shaddarsa.

%??muna nan kamar yadda kika san mu, fine kamar Annabi da kafiri%???

Ya fada yana dan murmushi kadan, sai kuma ya kalleta.

%??m miss you Safeena%???

%??me all miss each other, and i so much miss Zahra, yadda take kishina bata son ma na zo kusa da kai%???

Abiey yayi murmushi.

%??mahra tana kishina Sosai, ta sha ce min na rabu da ke a tunaninta so na kike%???

%??mai ma ai kana kishinta sosai, idan kuka fita ba ko kallonta wani namijin ba shi da ikon yi Abiey%???

Ya sake yin murmushi ya sauke kansa kasa.

%??mverything is over now. Ya fiance ki?%???

%??me's fine, muma bayan sallah ne aurenmu%???

%??mh really amman shi ne ban sani ba Safeena?%???

%??mbiey baka son shiga mutane yanzu gaba daya ka canja, duk yadda mutum yake son mu'alama da kai ba kamar da ba ne, I'm glad ma baka watsar da aikinka ba, na ga winning din da kuka yi shekaranjiya I'm very happy sai zancen ka ake all over the world%???

Ya yi murmushi.

%??mo and get your bag mu zaga gari i miss you%???

%??mkay%???

Ta amsa tana murmushi sannan ta juya ta nufi kofar shiga dakin taron, shi kuma ya juya ya jingina da motarsa ya runtse ido saboda wani irin ciwo da kirjinsa yake masa.

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un%???

Ya furta yana kokarin saka hannunsa aljihu ya ciro key din motarsa sai ya ji kamar an cake shi da mashi a kahon zuciyarsa a take ya durkushe a gurin dake da zuciyarsa ya bude bakinsa yana numfashi da karfi.
10/1/22, 21:59 - Buhainat: *B??0? ?]Mq?? CIWON - SO B??0? ?]Mq??*

By Khadeeja Candy


6??_/Q


Tun kamin ta karaso hankalinta ya tashi ganin Abiey a duke gurin motar.

%??mnnalillahi Abiey%???

Ya kalleta daker idonsa har sun soma sauya kala daga fari kal zuwa ja saboda ciwon da yake ji a kirjinsa.

%??mannu bari na kira....%???

Bata karasa ba ta mike tsaye da sauri ta kuma dakin taron, da gudu ta nufi inda Ammy take tare da Dr Zainab ta fada musu hankalinta a tashe, kamin Ammy ga mike tsaye kasancewar ta mai nauyin jiki Dr Zainab har ta kusa kai wa kofa, da gudu ta karasa kusa da kanenta ta dafa shi.

%??mbiey?%???

Rumtse ido ya yi sosai kana ganinsa kasan ba karamin azaba yake ji ba, jakarta ta bude ta ciro key motarta ya nufi inda ta faka motar, sai dai ba damar fitowa da ita saboda motocin da aka faka bayana nata ba za su bari ta fito da motarta ba. Dawowa ta yi da sauri ta saka hannunta aljihunsa ta dauko key dinsa ta zagaya ta bude motar ta yi mata key sannan fito da taimakon securities din da suke gurin aka saka Abiey motarsa Ammy ta shiga baya ta rumgume danta hankalinta a tashe domin ta fara zubar da hawaye. Safeena kuma ta shiga front seat tana kuka da ambaton Allah.

%??mani abu ya same shi ko ya ci wani abu?%???

Dr Zainab ta tambaya tana tukin kamar zata tashi da motar sama. Sai Safeena ta girgiza mata kai tana kuka.

%??mo ni dai muna tare muna hira sai yace min na je ma dauko jakata mu shiga gari ina dawowa sai na same shi a haka%???

Ta daga mata kai tana da juyawa ta kalli Abiey. @360 ta isa asibitin kai tsaye ta nufi emergency ko fakin din kirki ba ta yi ba ta bude motar tana fadin

%??mu fito da shi lemme get the bed%???

Da gudu ta shiga cikin asibiti, tsakanin shigar kofar emergency din da fito nurses kamar ka rufe ido ka bude ne, domin asibiti ce da ake bawa ko wane marar lafiya da kudi suka zauna a jikinsa kyakkyawar kulawa, balle kuma shi da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login