Showing 138001 words to 141000 words out of 210919 words

Chapter 47 - CIWON SO

10 Oct 2024

4206

bude hannunta da carbi tana ja idannuwanta ya sauka a kan hannun Rukaya da ta miko mata wayar ta ce" Aunty Mama ce tace bata samunki"

Amsa ta yi itama ta juya tana jin gabanta na faduwa ta amsar wayar maman su kuwa sun yi tsuru tsuru an rasa mai iya yin tambayar jikin na Abah ne ko menene? Kowa tsoron amsar da za'a bashi yake yi, jim kadan ta dawo masu da wayar ta mika masu muryarta na rawa sosai ta ce" Ku je ku daura alwallah, kowa ya gabatar da abinda ya iya wa mahaifinku, Allah ya bashi lafiya"

Adawiya mai saurin kuka ce ta shiga yi tana matsowa kusa da Aunty Amarya ta ce" Aunty, ya rasu ne Aban?"

Idannuwanta da suke dauke da kwallah ta dora a saman fuskar Adawiyar a sanyaye ta girgiza kanta ta ce" Bai rasu ba, ama bashi da lafiya, su Hajia ba gobe zasu juyo ba, dole sai sun sake kwana dan a ga yadda hali zai bada, ku dai ku rike carbi Allah ya tashi kafadunsa"

Da wannan ta salame su ta juya nata dakin ta karasa saman salayarta ta zauna

A hankali ta sada kanta waje daya, sai kuma ta fashe da kuka, kuka mai tsatsanin gaske tana jin tamkar zuciyarta zata bar gangar jikinta......., Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ga abinda suke fada mata.....ga abinda maman Abul ke fada mata da kuma maman Furera, .....a lokacin da suke tunanin itace ta tsiga tsakaninsu da mijinsu ba zuwa ba zowa gan lamarin aurataya sai suka sakota a gaba da yan habaice habaice kamar haka :sukan ce mata ta fa yi aniya a dakan da take saka shi ya bata koda cikin y'a mace daya ne, dan idan tana da hankali zata kula Docter dai shekaru karta ja suke ita kuma a cikinsu itace yarinya futul itace ba d'a ba jika tsakaninta da shi, ta kuma sani sarai cewa wannan gida da ake ciki gida ne da yake malakin MARSHAL, gidan docter wanda suka taso suka dawo wannan ko rabin rabin wannam bai kai ba duda shima gida ne na masu kudi gaskiya, sai dai a lokacin da ya fito ya ringa dauka gaba daya ya raja'a ya maka ginnin nan bulo da bulo hawa da hawa wajajen shakatawa kala daban daban wajen karatun islamiya kai babu ce kawai babu ya zuba mahaifinsa da makarabansa dan karra samun jin dadin rayuwa, ta fa sani idan har Docter ya mutu a lokacin da bata da d'a ba jika tsakaninta da shi tana cikin matsala, dan kuwa cimilin takaba ne kawai zata iya samu, gwara gwara su idan aka dan duduba ta yiwu da yan motoci da gonaki haka jefi jefi sai gidajen nan nasa uku wa'inda ake haya a cikinsu baki daya, idan aka raba ta yiwu su samu matsugunni , ita kam sai dai a koma rayuwar da........watau rayuwa a bakin titi ana neman na abinci , ana bara ana karuwa ................ Wadinnan kalamai su suka fi daga mata hankali, dan ta san wace rayuwa ce ta baro ta bakin titin, lalle bara kam ta yita ama kuma karuwancin bata taba yi bama, sai dai ta fuskanci kalubale da tashin hankali daga wasu mazan azalumai masu son wulakantar da mace, wa'inda idan suka ganki a halin kaka naka yi baban burinsu su ribanceki su idasa wulakantar da darajarki a banza a wofi dan baki da yadda zaki yi........., Magangannu mararsa dadi da sauransu, shi yasa tunda ta samu kilacewar nan sai ta sake kilace kanta, abu biyu kawai ke fitr da ita koyon girki a lokacin da take amarya, sai kuma islamiya....summa tana samun abinda ta samu ta dawo ta kilace kanta, bata da kawa, bata da abokin shawara sama da Docter, bata iya sakin karinta ta yi hira da kowama in ba shi din ba....................
Wannan zulumin ya hannata barci, kira kuwa ta yiwa Mamah ya fi a irga har sai da Maman ta kashe wayarta dan gaba dayansu ta sanarwa ama Aunty amarya ta gaza zama waje daya , karshema haka asuba ta risketa garin Allah ya waye tana cikin hali na kuncin zuciya da tashin hankali, har suka fito suka tafi wajen karatun da aka yi kiran kowa aka hadu ana sauke Alkur'ani da sadaka.....jikin Docter kam ya kiya sai fatan samun lafiya ko wace iri ce, hankalin iyalansa gaba daya a tashe yake, basu taba yin wuni tare ba dai a wannan lokacin, abinci zubawa ake ana kaiwa cen bangaren na docter domin a cen suke iyalan nasa baki daya, hankali du ba a jiki ba, babu mai hararar kowa, kowa yana cikin zulumi

A hankali yayansa na nesa suka fara matsowa sanadiyar kiran da suka ringa samu da iyayensu
Mazan ne, da matan masu aure, daidaiku ne basu samu zuwa ba dan mazajensu sun ce su bari ya dawo mana mutumen da ba rasuwa ya yi ba zasu ringa zuwa sunna dagawa junna hankali, aduarsu yake da bukata fiye da komai

A irin wannan hali ahalin gidan Docter suka dauki kwana biyu bayan kiran Mamah sunna cikin hali na zulumi, sunna karatu ba ji ba gani da sauke Alkur'ani, ana sadaka ta launin abinci kala kala da ta suturu da ta kudi, sosai suka ninka alkhairansu , wanda hakan ya zamto baban abu mai daraja, domin har a masalacin Docter abinda ake yi kennan, ana cikin roka masa gafarar ubangijinsa domin su Marshal ya fito masu karara ya sanar masu ne Docter na bukatar addu'a, dan tunda ya shige halin comar nan bai kuma sannin inda kansa yake ba

Tun karfe hudu da rabi Amir ke kai kawo a baban tsakar gidan yana sanye da jalabiya fara hannunsa rike da carbi, idannuwansa sun gaza daina zubar da hawayen da suke tarawa yana kai kawo yana ankare da dukkan wani motsin dake kai kawo sanadiyar abinda ya same su iya mazan suka ji banda matan da suke falon Abah yanzu yake sa ran gannin sun bude dan ya sanar masu domin baya so su ji daga bakin wani


Alamun an fara kukunna wutacen falon ya saka shi sake sauke wani hawayen mai zafin gaske, a hankali ya karasa ya dan dakata dan ya basu damar kimtsa kansu, dan tashi daga barci ai ba kowa ke yi tsaf tsaf a nutse ba

Ya dauki minti kusan goma a tsayen nan ya shiga bubugawa a hankali sannan ya dakata

Ba'a jima ba aka tambayi wanene, dan du sai suka tsayar da abinda suke yi na shirye shiryen daura alwallah da hawa saman salaya, shake falon yake da iyayensu da ?ba?bansu a haka ya shigo yana dan cicira ido ya rasa inda zai fara nufa dan a gaskiya bashi da wannan courage din a yanzu a gabansu

Uman Abul ne take saukowa daga saman Abah hankalinta a kan abinda yake faruwa

Jiki babu karfi ta karaso tana fadin" Lafiya du kuka yi tsaye kunna kallonsa? Yayansu lafiya dai ko wani ne ya aikata laifi?"

A hankali ya ja numfashi ya sada kansa, muryarsa a sanyaye ya ce" Aa, babu wanda ya aikata wani abu, shigowa na yi na sanar maku cewa, yau mun tashi da kyautar Ubangiji"

Da sauri ta sake kureshi da ido, lokaci daya kuma Aunty Amarya dake tsaye saman salaya ta silale ta zauna tana tataro kafafuwanta ta dora gwuiwoyin hannayenta sannan ta kai tafukan wajen kanta tana yamutsar kan nata bskinta ya kasa furta komai

Mahaifiyar Furera ce ta ringa ambaton innalilahi wa inna ilaihi raj'une, domin yannayinsa zai sanar masu kyautar ubangijin me take nufi

"Kana nufin Docter ya rasu?" Maman Abul ta fada muryarta na wani irin rawa, hajan ya sa yan matan da yayunsu masu auren barkewa da kuka kowa na rungumar wanda ya fi kusa da shi, shi kuma ya karaso jikinsa tamkar an zare laka ya zauna a saman kujera a sanyaye ya ce" Allah ya amshi ran Abah, karfe uku na dare da wasu yan mintuna"

A hankali itama ta bi ayarin matansa dake kuka da ya'yansa, muryarta a matukar jigace tana kallon Amir ta ce" Shikenan Amir Abah ya rasu? Wayo Allah mun shiga uku mun lalace, innalilahi wa inna ilaihi raj'une innalilahi wa inna ilaihi raj'une, dama tafiyarsa ba ta dawowa bace?"


"Amir yanzu shikenan a akwati za'a sako gawar Docter a kawo a wuce da shi makwontai mu ko ganninsa ba zamu yi ba?, Shikenan mun rasa uban y'ayanmu ya tafi da kaffafuwansa a dawo mana da gawarsa a cikin sanduki? Menene zai saka mu samun nutsuwar zuciya bayan bamu ga gawarsa ba?, Menene zai sanyayar mana da zuciyarmu? Shi yasa yake gudun fita wajen nan, fin karfin Docter aka yi aka fitar da shi waje, gayacen ya rasu za'a kunkuma mana shi a cikin samduki a kawo a wuce da shi a turnutse a kabari ba tare da mun yi ban kwana ba?" Maman furera ta fada tana hawaye hankalinta du ba a jikinta ba

Murya a sanyaye Aunty amarya bayan ta bi yan matan da kallo du sun warwatsu kowa yana neman inda zai saka ransa ta ce" A nasihar Abah, yace du inda ransa ya fita a birne shi a nan, kasa ta kai shi"


A zabure Maman Abul ta dubeta ta ce" Kina nufin ba za'a kawo mana uban y'ayanmu kasarsa garinsa inda aka san darajarsa aka san mutincinsa a birne shi ba?, Ai ba zai taba yiwuwa ba, in dan tashi ne ai shi komaima ya yi yadda ba zai wahalar da dan gwal din ba!, Dole a kawo mana mijinmu a birne a garin da muke ko dan ya samu kyakyawar ziyara da addu'a ta kirki "

Uhum, wasa farin girki, Amir sai ya rasa bakin magana , ya ringa bin wani gagarumin rikici da tashin hankali da yake gani a gaban idannuwansa wanda Mahaifinsa ya tafi ya bari, ama ya bar wa da shi? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une abinda yake kallo a yanzu ya karra daga masa hankali da shiga tashin hankali da tonon asiri irin na mutuwa, wai wadinnan ahalin da Docter ya bari wa ya barawa, ya Allah, wannan lamari ya sake gigita shi, ya sake saka shi shiga a hali na tarin tunanin shin yaya zasu yi?


Da kyar ya iya budar bakinsa ya shiga tunasar da su ya dace a yanzu su fahimci gawa a shinfide take, ya dace su bi ?ba?bansu da suka fice sunna kuka su tsawatar masu su saka su daukan carbi su nunawa mahaifinsu soyayyar da ya dace, ya kamata su gane rigimar nan da suke neman balowa a yanzu bata da wani anfani, komai dai na Allah ne, Docter ya rasu a kasar musulmai, yau ko a kasar wa'inda basa sallah ya rasu ai ni'ima ta ubangiji ce, maganar abinda zai sheda maku ya rasu ko bai rasu ba kun san dole za'a basu shaida, ya zama wajibi a gabatar masu da shaidar komai dan rasuwa aka ce ba abin wasa ba, in har basu yarda da fada masun da aka yi ba ya kuma tabatar masu tabas za'a yiwa docter sutura ne a garin da ya rasu, shine ya bukaci haka, karshe dai shine ya mike ya fice ransa na baci dan har an shige masalaci an fara sallah ya karasa da sauri ya kurkure bakinsa ya shige masalaci dan niyarsu idan aka salamce a dora da dukkan abinda ya sawaka dan yiwa docter shinfida


Garin Allah na wayewa gaba daya gari ya dauka
Tururuwar mutane ne kawai kake gani ta ko'ina domin a kafafen yada labarai an sanar cewa za'a yi jana'izarsa a yau din a cen kasar da ya rasu, sai dai ahalinsa zasu mike da amsar gaisuwa, hakan ya sa du wani wanda abin ya shafa da al'umar annabi suka ringa tururuwar zuwa gidan ya dinke da kofar gidan dake dauke da dankara dankaran runfunna wa'inda mazan gidan suka girka shake da jama'a ana ta karatu sama sama idan ka nufo sai ka ji tsigar jikinka na tashi bama a lokacin da Mamah ta sanar an tafi kai Docter gidansa na gaskiya a lokacin kowa ya sake bada hima da dukkan abinda ya samu ana binsa da addu'a har kusan sha biyu na rana sannan aka ringa watsewa wadu kuwa sunna nan dan sai sun tarbi MARSHAL sun masa ta'aziya sannan su tafi hakan ya sa wasu na tafia ne wasu na karuwa gidan na sake daukan al'uma





Tun karfe goma sha daya suka kamo hanya, sai kusan sallar magariba suka karaso garinsu

Mota daya tak ce aka zo daukansu da ita, Amir ne da kansa ya tuko ya zo daukansu

Motar bak'a ce mai bakaken gilas , tunda ya tsayar da ita yake tsaye ta wajen da masu tarban baki suke tsayawa har suka ringa fitowa yana binsu da kallo kafin yake hango Mamah ta dan rabu da jikin MARSHAL sunna tahowa a hankali a hankali kanta a saman damtsen hannunsa nikaf a rufe a fuskarta yana sake talabarta a jikinsa ya nufo motar da Amir ya bude da sauri yana sada kansa dan fuskar MARSHAL ba zata iya kwatantuwar irin yannayinsa ba, danma ya saka bakin gilas ne ba zaka gane halin da idannuwansa suke ciki ba, ama ta yadda fuskar ta dauki ja haka jijiyoyin jikinsa dole zaka fahimci a damuwa yake


A hankali ya sake riketa zai sakata a motar ta dago idannuwanta tana kallonsa, muryarta na hadewa da kyar ta bude bakinta bayan ta shafa sajen dake fuskarsa ta ce"


26
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Muryarta na hadewa da kyar, ta zuba idannuwanta a saman fuskarsa ta dora a gefen fuskar nasa ta shafa a birkice ta ce" Abahn docter....., abahna.....
Shikenan na tafi da docter na dawo ni kadai.....? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une" ta fashe da matsanancin kukan da ya saka shi yin dan taga taga da ita din ya kusan dirkuwa a kasa , Allah ya sa Amir na kusa da sauri ya tare ta hanyar saka hannayensa ta wajen cikin MARSHAL ya tare da karfin da Allah ya bashi a birkice yana fadin" Subahanalah Yaya"

Da sauri security din dake ta kai kawo na airport%?oin suka nemi kawo agaji
Su suka taimaka masu daga MARSHAL din har Maman suka nemi a kaisu asibiti amma ya kiya dole aka saka su a cikin motar daga baya su dukansu Shi kuma Amir ya koma gaba ya tayar da motar sai kuka yake yana share hawayensa hankalinsa duk a kansu yana kula da irin yadda Marshal yake rike da hannun MAMAH har ya ga ta dora kanta a gefen damtsen hannunsa hakan ya saka shi jan numfashi a hankali ya dora kansa a jikin madubin motar ya zubawa hanya ido a lokacin da Amir ke tuki shi kuma ya lula a duniyar abinda yake cikin kwakwaluwarsa da kansa

Magangannun Abah a lokacin da suka kamo hanya har a cikin jirgi har suka sauka na neman halaka masa zuciya

Ya rasa ta inda zai kamo , ko a inda zai ajiye magangannun nan
Abah fa ya jima da gane cewa wannan ciwon nasa na ajali ne shi yasa ya ringa saka shi a ukun rayuwa da tunani kala daban daban

Yanzu yaya zai yi da ransa? Ina zai kai wannan nauyin?

A lokacin da ya gama gyarawa Abah zama a cikin jirgi bayan zasu daga Abah ya nace kan sai ya dauki waya ya saka masa ya yi recording din magangannun nan da ya masa su suke dawo masa tamkar mutun ya hadu da fatalwarsa

Yaya zai yi da ransa ne? Ina zai dosa?

Tsayuwar motarsu a kofar gidan, da saurin zuwan sojawa sunna kare mutanen da suka nufo motar rututu sunna fadin su bari ya fito da kansa sai su gaisa ya saka shi zubawa kofar gidan ido har zuwa jan motar da Amir ya yi ya shige da ita ciki dan ba zasu bari ya fito a tsanake a haka ba ya gangara har bangaren Abah shi kuma yana bin komai da ido tamkar ana zana masa ne a cikin kwakwaluwarsa ya sake zubawa kofar ido tarin matan dake zazaune da irin tarin jama'ar da yake hange daga ciki ya sake daga masa hankali, wadannan din dukansu sun zo zaman makokin Abah ne? Shikenan Abansa?

"Babana, ka daina son katse maganata kuma ka saurara har na gama mana, dole fa ka jajirce bakinka ya bude , kaine ubansu dan kaine babba, lalle shekarunka sun dauko rigima dan kuwa ina tsoron rikicinsu ya hadasa maka furfura da wuri, ka ga dai ni yadda Allah ya yi da ni, dole kaine zaka jajirce, Babana wuka da nama a hannunka yake , Ahalina sun rataya a wuyanka Sulaimana......" Da sauri ya rintse idannuwansa tuna wannann magangannun, a hankali ya kali Amir ya ya duko kadan yana sheda masa sun fa karaso, ina zai kai Mamah ne?


A hankali Maman ta dago kanta dake sara mata%??ja ce" Amir, kai ka raka ni wajen yan uwana, shi kuma ya fita wajen mutane ya zauna, Aban Docter ka dan taba wani abin ka ji? Kar yinwa ta kayar da kai"

Idannuwansa kawai ya iya lumshe mata a hankali kuma ya budi bakinsa ya ce" Mamah, zaki ga docter, Please kar ki sha abu mai siga kin ji Mamah?"

Da kyar ta kakaro dan yannayi na son kwantar masa da hankali lokaci daya kuma ta ce" Bani wayar nan mai recording din docter"

Sai da ya ji gabansa ya fadi, niyarsa zai je ne ya zauna ya goge du wani abinda bai masa a hirar ba, dan akwai manyan abubuwan da Aban ya fada wa'inda baya tunanin in har shi din nan zai iya zaunawa da ahalin Docter su saurara tare ba, tun daga maganar gidan nan da ta aure, baya tunanin in har yana da abinda zai saurara daga gare su baki daya kalaman nan, sai dai gashi Mama na so ta masa abinda ba shikenan ba, dan ya tabata kamar yadda ta dauki alkawari a lokacin da aka rufe fuskar Abah da likafani sai ta aikata


Jiki ba karfi ya laluba aljihun wandonsa ya ciro karamar wayar baka ya saka a hannun Maman sannnan ya bita da ido har aka taimaka mata ta fita a motar aka nufi ciki da ita

Idannuwansa ya sake lumshewa ya sake jinginar da kansa a jikin kujerar kirjinsa na dokawa da karfin gaske, duka duka yau aka fara, ba yau ciyar da su

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login