Showing 144001 words to 147000 words out of 210919 words

Chapter 49 - CIWON SO

10 Oct 2024

4248

dan sanyaye ta ce" Zan tambayi izinin haka a wajen Mamah"

Murmushi ya yi yana jin farin ciki a zuciyarsa, yar gidan Docter ce fa, wannan labarin sai ya fi komai dadawa a zuciyar Hajia Baba, watau yayar mahaifinsa, tabbas wannan labari sai ya sakata farin ciki marar misaltuwa, idan ya samu auren yarinyar nan shima ya san ya huta, bashi da damuwa da tarbiyar ya'yansa tunda ya dauko mai tarbiya, yarinyar ga kyau ga tsari ga jan aji....gaba daya ita din ce ta dace da shi rayuwar zaman duniya......
Da wannan suka yi salama ita kuma ta mike ta saka hijjab din Mamah blue mai hannaye lafcece har kasa tana tafe tana dan dage shi ta sauko kasa a lokacin da ake fitar da kayan su Minal niki niki kaya kamar wa'inda suka zo siyyaya ba gidan rasuwa ba ana sakawa a motar da Amir ya zo da ita dan a kaisu inda zasu kwana kafin su wuce

Minal din sai Fara'a take na rikitaciyyar kyautar da aka yi mata na gudunmuwar auren ?ba?banta, tabbas ta yi farin ciki da kyautar nan har kamar ta yi kuka, ai na gado ya samu kam sai dai MARSHAL ya yi hakuri ya yi gadaje ya gama, wannan kudi ai sun fi karfin wai a kara a yi gara, garar me ? Ita babu wata gara da take gabanta shi uban nasu ya yi garar ai an rage masa ita zata gwongwaje ?ba?banta ne su je gidan kishiyoyi a ci uban sabada ana daga kai da rantsatsun kaya, ta san ?ba?banta sai sun kece raini sai sun yi ba zata dan kuwa kayan da zata yi masu sai ta bada tsoro


Haka fai suka wuce, ita kuma ta zagaya zatta wuce kitchen suka hade da Adawiyya dake dauke da wasu rantsatsun kayan shayi a wani irin plate ruwan zeiba sai kyali yake shayin kuwa sai kamshin na'a na'a yake yi irin shayin larabawa ne ya hadu iya haduwa ta damka mata tana fadin " Zahra Mama tace wa ki je cen gadin ki kai shayin nan na aminin Babnguda ne sunna cen tare , je ki zo an kanwata in gwada maki wani cake da muka yi dazu ki gani nama rage maki rabonki"

Ido ta zaro tana tura mata tana tura mata , da karfi ta tare dan Adawiyya saki ta yi ta yi ciki da gudu ira kuma ta yi tsuru tsuru tamkar zata saki fitsari tana kallon hanyar da ta bi

Fuskarta ta takwakkwabe sosai ta juyo da plate din ta nufi inda aka aiketan a ranta tana ayanna ' sai na rama walahi sai na rama aka aike ki shine kika makala min salon ni na yi laifin ya karyani ko? Kina gannin yadda nake kauce masa tunda ya shakeni ya daka ni zazabi da amai aman shine kika turani? Zan rama ne sha kuruminki zan rama ne'...............


Tana zancen zucin har ta zo ta wuce ta cikin gardin din ta wuce Aban Ahmad tsaye yana amsa waya bata kula da shi ba ta je ta ajiye ta yi gagawar barin wajen domin shima yayan nasu ya tafi wajen get dan tarbo Minister da suka zo sake yi masa ta'aziya

Da dan sauri take tafe tana tatare hijabin nata kanta a kasa, hakan ya sa ta daku da gefen hannun Aban Ahmad bata kula ba

Da sauri ta dan dago ta masa kallo a dan fizge ta ce" Yi hakuri dan Allah ban kula ba"
Sannan ta wuce da gudun tsiya dan karma a samu wata matsala


Tunda ta yi magana, ta dan kallo fuskarsa ya daskare a tsaye a inda yake har ta bar wajen ya kasa koda motsa yar yatsarsa ne har sai da Huzaifa ya zo wucewa ya gaishe shi da muryarsa mai irin amon ta MARSHAL ya dawo hayacinsa a dan firgice ya sake tsurawa hanyar ido sai kuma ya juya da sauri ya koma wajen da suke zama ya mimikawa bakin hannu suka gagaisa sannan ya samu waje ya zauna ya yi shiru sam baya cikin duniyar hirar da suke dan tabawa a tsakaninsu dan ya lula duniyar damuwar da take tasa, wace ke cen kasan zuciyarsa, nasa shima mikin mai tsauri har sai da MARSHAL ya dan taba gefen kafadarsa yana masa magana ya juyo a dan firgice yana kallonsu a lokacin da minister ke fadin" Elhaji ni yanzun yayanka nawa?"


Da kyar ya iya hade dan yawun bakinsa,yana lalubar maganar da take masa nauyi MARSHAL ya ce" wai wa wannan? Ya'yansa biyu ne , da na wajena mai sunnan Abahna da kuma kanin sa isma'ila"

Murmushi minister ya yi ya ce"

28
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Murmushi minister ya yi ya ce" Masha Allah, ai biyuma gari ne, bale na san ai sun kusa aure, kana aurar da su din sa kawo maka jikoki birjik"

Sake kakalo murmushi ya yi yana doke hannun MARSHAL dake dan tsokanarsa ya ce" rabu da shi Shugaba, wannan kannin nawa ya iya nema, yaran fa kannanu ne , dan karamin wata uku ne da aka yaye shi,, ka san auren bai jima ba "

Haka dai suka dan tatauna, MARSHAL ya masu rakiya wajen motocinsu suka tafi ya dawo yana duba agogon hannunsa ya zauna yana hankalta da yannayin Aban Ahmad

Da kula yace" Friend yaya dai?"

Aban Ahmad ya dago da sauri dan ya afka a duniyar tunani
Idannuwansa da suka dauki ja sosai ya rintse, muryarsa a raunane sosai ya ce" Friend wai sai na ga wata yarinya a gidan nan da ta tuna min..., Da ta tuna min maganar nan da na yi maka, yarinyar kuma Bama zan ce ga kamaninta ba, na dai dan kalleta na dan lokaci ta gudu, ........banma san me ya kawo tunanin nan a raina a irin wannan lokacin ba sam"

MARSHAL ya dan tabe bakinsa, wannan karron da wani yannayi shi ba na halin ko in kula ba, shi ba na damuwar abokin nasa bata shafe shi ba , a wani rashin ba abin mahinmanci ya ce" Ohk "

Aban Ahmad ya zuba masa ido, Amsar sai bata yi masa ba, duda ya san maganar tana kona ran SULAIMANE amma ai ya san babbar nadamar sa ce, sannan babban abinda ya binne, ne, tunda ya shigo garin nan ya samu hanyar samu har yau ya zama abinda ya zama damuwar dake rage masa walwala kenan, ya rasa yaya zai yi, ya rasa ta inda zai billo, ta inda zai fara

"Ka san, a yanzu, bana tunanin zaka tunkaro wani ya kasa sauraronka, ina gannin, ya dace ka ware lokaci, ka je ka binciki inda take, dan kuwa kar ka manta, Allah baya yafe laifin da bawa ya yiwa bawa sai idan bawan ya yafe ne, gashi muna cikin hali na a wuni da kai ba'a tashi da kai ba, wannan din babban laifi ne, yaya take? Tana raye? Wani hali ta shiga sanadiyar hakan? Kace yarinya ce a lokacin sosai, shekaru sun tafi, kai din yanzu ka kusan sittin, ko ba'a fada maka ba ka san shekaru sun ja......., Inaga ka samawa kanka sasauci ya fi, koda karar ka zata kai ka yi kokari ka amsa, ba wai ka je saudiyya ka tare da matarka ka yi kamar baka da wata rayuwa kafin wannan....., Kowani bawa fa na aikata aikin sabo, kowane bawa da ka gani yana da sirri mai tsauri, na wani ya fi na wani ne, rashin dadin al'amarin a yi ta tafia ba tuba, kuma a mace da hakin bayin Allah a kai, ka kuma tuna da ayar nan Kama tudini tadana,ka dan ba kanka sasaucin dacin zuciya........, A yanzu kai babban mutun ne, ka tara, ka dan waiwaya ko zaka dan taimaka mata idan tana raye biensur" Baban gida ya fada yana fuskantar Aban Ahmad da ya zuba masa ido kamar ya ga bako a gabansa

Yana ajiye maganar ya mike ya sake shan shayin nan sannan ya wuce ba tare da ya kuma ce masa uffan ba


Bayanshi ya raka da kallo har ya bacewa ganninsa sannan ya sake juyowa wajen dardumar dake shinfide
Gaskiya tsagwaronta itace ya fada masa, ba boye boye ba kwane kwane
Shi yasa yake matukar son mu'amalarsa da Babangida,ya girme shi nesa ba kusa ba amma idan ta kama ya fuskance shi tsaf zai fuskance shi ya sanar masa abinda yake zuciyarsa koda kuwa hakan zai zamto bacin rai a gareshi

Jiki a mace ya sake duban hanyar, sai kuma ya shiga lalubar matarsa ta whatsapp yana tunanin Allah ya sa bata kwanta ba duba da tazarar awannin biyar dake tsakaninsu da saudiyyya,gashi magrib ta gabato ta yiwu har ta kwata

Allah ya taimake shi tana zaune a lokacin, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Umman Ahmad"

Tana murmurshi ta amsa shi, sai dai yannayin amon muryarsa ya sakata dan yin jimmmmm,
Ita dai ba yarinya bace, hasalima tana da shekara talatin da biyar ya aureta, sun hadu ne a kan harkar kasuwanci, sun fahimci junna da wuri ya kuma share hawayenta na shekaru da ta kwasa bata samu miji ba ya gwongwajeta ya aureta, hakan ya sa tsakaninsa da ita fahimta ta fi rashin fahimta, a zamansu kuwa zuwa yanzu abinda bata sani nasa ba kauyansa da yake boye mata ya ki sanar mata bayan ya sanar mata waye shi a da, ya ki sanar mata sunnan kauyen dan
Karara ya gane idan har ya sanar mata tana iya zuwa bincikar labarin abinda ke cikin zuciyarsa, idan kuwa haka ya faru ba zai so ba, bai bar wani abin a zo a gani ba, banda boyayan tarihi marar anfani bai bar komai ba, lalle Docter Ahmad SULAIMANE ya zamo uba a gareshi kuma mafarin shiriyarsa, haka kuma hanyar samun budinsa......, Shine ya sanar masa cewa bawa na iya cenzawa daga mutumen banza zuwa na kirki idan har ya sala kansa, shi ya amshe shi ya kuma bashi damar jin zai iya cenzawar, shine ya bashi jari yake kuma taimaka masa da dukkan abinda ya dace har yau ya zama haka........
Daga haka baya jin zai iya sanar mata kai tsaye sunnan garin dan babu wanda zai gyara abinda ya bata

Muryarsa ce ta yi rauni ainun, a raunane sosai ya ce" Na takura ki ko? Me kike yi ne?"

Da kula ta ajiye zanen da take yi ta mike ta bar wajen yaran tana fadin" Aban Ahmad lafiya? Me yake faruwa ne?"

Idannuwansa ya lumshe hawayen idannuwansa suka shiga zarya a saman kuncinsa

A raunane ya ce" Ina gannin, ya dace yanzu na waiwayeta....., Umman docter tunda kina shirin zuwa gaisuwar ABAH ki zo da yara baki daya sannan ki zo min da dukkan wasu takarduna masu mahimmanci, ina gannin zan jima a kasar nan har sai na sameta"


A hankali ta lumshe idannuwanta tana jin wani iri a cen kasan zuciyarta, Allah yana gani zata fi kowa jin dadin gannin damuwar mijinta ta kau a kan wannan lamari, sai dai haka kawai take jin kamar tsoro tsoro, da kuma tunani mai rauni sosai a kan maganar, shin idan ya ganta ..... Ras bata da aure fa? Idan abinda ya barta da shi yana nan ras ras fa? Idan har a lokacin ba wai iya sha'awa bace kawai ta kaishi gareta harda so fa?, Idan wani abu na iya kasancewa tsakaninsa da ita fa.....? Shine baban firgicinta, ba wai kishiya ce damuwarta ba, farin cikin da ta samu, kwonciyar hankalin da take ciki, dan cercle dinsu ita da mijinta da ?ba?bansu biyu ne bata so ta ga wani abu da zai iya tarwatsa shi ko ya lalata masa zane komai kankantarsa, shin me haduwarsa da abinda ya tsaye masa a zuciya yake nufi?

Da kyar ta iya rarashinsa, sannan ta sanar masa in sha Allah zata yi ta gama komai ta dawo da wuri da dukkan abinda ya tambaya, ta yi masa Addu%??jr samun abinda yake nema idan har alkhairi ne hakan, sannan suka kashe wayar

Sunna kashewa ta samu kanta da zama a waje daya ta dafe gaban goshinta
Tambayoyi ke mata yawo a kwanyar ta

Shin zaman mijinta da hakin nan ya fi mata alkhairi kan son zuciyarta dan tsoron kar a lalata mata farin ciki? Sannu a hankali ta ringa kawo farin abin da bakinsa har dai ta mike kan abu daya, ko menene ta sani ba zata taba bari ko yin sanyar da wata zata zo mata rayuwa kai tsaye ta wani lalata mata kwanyarta da farin ciki a tsakaninta da mijinta bayan ta dauki lokaci cikin kunci ta kuma dauki lokaci cikin gina haka.......dolema zata matsa kusa da shi da wuri wuri dan ta san me yake ciki ta kuma taya shi nemowar dan ta kasance a wajen a lokacin da abin zai faru ko dan ya gane cewa tana nan, tana kuma tare da shi, ko menene tana hankalce babu wace zata yi mata kwacen mijinta, ko meye shi ita shine mijinta tana son abinta a haka......

Wannan kennan






Washe gari Fatima ta samu Rukaya da maganar Hasan ta sanar mata abinda yake so, sai dai ta kasa sanar mata ita kuma abinda take so kafin a kai ga hakan

Rukaya ta ji dadin haka ainun, harma tace da ita zata sanarwa Mamah da kanta abinda ta yanke sai su yi
Ita kuwa ta bar maganar a ranta cewa koda ya zo an ganshin ta yiwa kanta alkawarin sai ta sanar masa wacece ita, dan babu abinda zai sa ta yi wasa sai magana ta shiga jiki a zo ana tsunguri tsoma


.........................................................



Bayan sati biyu da yin arba'in din DOCTER , ya kama kwanaki hamsin da hudu da rasuwarsa, Yau ranar asabar da karfe goma sha daya na rana



Yana cikin aiki a office kira ya same shi daga gida, da yannayi na tashin hankali daga wajen Mamah, hakan yua saka shi dauko bak'ar rigar swuit dinsa ya fito da dan sauri ya amshi ky din motarsa ya tuka kansa da kansa ya nufi gidan a ransa yana ayyana Allah ya sa lafiya dan yadda ya ji muryar maman ya dan daga masa hankali gaskiya, bata cika yin magana a haka ba in ba abu ya shiga zuciiyarta da karfi ba


Tunfa ya fito ya nufi bangarenta ya ga kannensa a tsaitsaye kowa yannayinsa wani iri ya saka shi sake shiga da saurin da ya fi na dazu cike da tsoron ko wani ba lafiya ne a ciki?


Yana shigowa ya shiga binsu da kallo, Uman Abul a tsaye , Uman furera a zaune a saman kujera, Aunty Amarya a saman cafet kaffafuwanta a lankwashe, Mamah a zaune a saman kujera idannuwanta sun mata ja tana kallon kofar shigowar, tana ganninsa ta sauke ajiyar zuciya hadi da dauke kwalar dake kurmin idannuwanta ta fuskaceshi tana fadin" Bismillah mana Baba karaso ciki"

A hankali ya idasa shigowar yana sake yin salama a tausashe sannan ya ringa bin Maman Abul da kallo gannin ta juyo tana cikin masu amsa masa harma ta zagayo ta zauna a saman kujerar itama tana dauke dubanta a kansa

Rasa me zai fara fada ya yi, idan ya kalli wannan sai ya kalli wancen har sai da aka sanar masa zuwan daidaiku daga cikin samarin gidan magidanta wa'inda suke neman izinin shigowa, hakan ya saka shi farfadowa ya juya da kansa ya leka ya ga ko su waye, dan haka ya basu damar shigowar baki dayansu ciki harda yaren kannanu kaf dinsu har ya zamto falon Na Mamah na neman yi masu kadan dan bai kai na Abah girma ba gaskiya


Du zama kowa ya yi bayan gaishe gaishe da junnansu suka dawo da dubansu kansa shi kuma yana tsaye ne yana binsu da kallo gaba dayansa yana shawarar shin ya tafi ne ko ya tsaya......? Me zai ce da su idan ya tsaya din? In wata rigimarsu ce suke yi shi yaya zai yi da su? A nan dai iyayensa ne sai kuma kannensa, iyayen nasa kamar sunne suke wani halin

A fole dai ya karasa ya zauna saman kujera yana kallon Maman Abul wace ya fi fuskantar ta fi kowa hawa sama a tausashe ya ce" Hajia wani abu ke faruwa ne?"



28
12/28/22, 11:06 - Buhainat: A tausashe ya ce" Hajia wani abu yake faruwa ne na ganku a tsaitsaye haka?"

Maman Abul ta ja numfashi, sannan ta fara magana ta ce" Na zata ka saurari voice note din da muka yi jiya a grup na familly Docter AHMAD?, Shi yasa ka ga yan uwanka du sun halarta dan tun jiya na yi magana kan kowa ya samu halartar a yau ko me yake yi kuwa ya bari ya zo"

Kai ya gyada yana dan shafa kansa ya ce" Ayya, na dan jima ban leka group din ba, amma Bismillah ina sauraro"

Lebenta ta dan dantse, sai kuma ta bude ta ce" Babangida ka yi hakuri, ni ban kawo maganar nan dan na ci zarafin kowa ba, sannan ni da na fadeta ba dan nice na fi kowa rashin hakuri ba, aa dan kawai dai nice na ga ba zan iya rikewar a cikina ba duba da jiya mamanmu tace tunda kwanaki sun ja tana so na je na gama takabata a gida, dan ka ga dai ni gaskiya ba zaman daki zan yi ba, ko yau miji ya fito min aure zan yi dan ibada ne"

Idannuwansa ya sada, a hankali ya ce" Haka ne"

Maman Abul ta dora da fadin" Kuma ka ga nauyi ne a saman kan Docter, ya dace ace tun satin rasuwar mamaci a sauke masa irin nauyin nan, sannan zai zamto taimako a gareni ne zan iya jan jari, dan komai arzikin gidanmu sunnana magidanciyar da na shekare a gidan miji da Y'ayana, dole sai ina dan tabuka wani abin dan na ji dadin zama da iyayena harma inda Allah zai kaini........, Har ga Allah na san suma sauran da haka a rayukansu sun dai fi gane su yi shiru ne bayan ba wani laifi aka aikata ba dan an sanar..........."


Idannuwansa ya dago ya zuba mata su, shi dai ba bagwari bane, a yarenta ya gane me take nufi, dan haka ya yi dan murmushi ya ce" Wannan gaskiya ne hajia, kuma na ji dadin da kika fada din, laifina ne

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login