Showing 81001 words to 84000 words out of 210919 words

Chapter 28 - CIWON SO

10 Oct 2024

4227

lafiya bata isheni ba ga kuma kuka da na sha, ga kuma tafiyar kasa da na yi sai kashi ya game min. Ina shigowa na fadi kwance saman tabarma sai hawaye suka fara taruwa a idona. Mama na ganin haka ta taso daga inda take zaune tana alwala ta karaso kusa da ni ta taba ni.

%??mahra?%???

%??mama ban samu magana da Dr Hamid ba, tun a lokacin da na tafi be saurare ni awa biyar da ni ina jiransa daga karshe da ya fito ma rufe ni yayi da fada%???

%??maboda?%???

%??man sani ba, be ma saurare ni balle ya ji abun da ke tafe da ni%???

%??mahra...%???

Na kalleta sai ta ce.

%??mashi zaune%???

Na tashi zaune sai na jingina da kujerar dake bayana ta zaman tsakar gida.

%??min san dai ni mahaifiyarki ce ko? Ba zan baki gurbatacacciyar shawara ba?%???

Na daga mata kai.

%??mi yi hakuri ki karbi wannan kaddara da hannu biyu, ki barwa Allah komai, da be rubuto miki haka ba da komai be faru ba, ki cire yaron nan a ranki%???

%??mama so nake na sake ganinsa ko sau daya ne, wata kila shi ne ganina na karshe%???

%??mi cire wannan a ranki, ka rasa rai ma ka hakura balle wannan da kika san yana raye? Kuma a inda zai samu kulawa mai kyau? Dan Allah ki kwantar da hankali ni ma nawa hankalin ya kwanta kin ji Yata%???

Na daga mata kai na lumshe ido ina hawaye.

%??man gwada Mama Allah yasa zan iya%???

Ya rumgume sai na fashe da wani irin kuka mai taba zuciya.

%??mama na ga Abiey%???

Na fada cikin kukan da nake.

%??m ina?%???

%??m can Mama na tsane Shi%???

Bata ce min komai ba ta cigaba da rarrashina har na samu natsuwa.



ABIEY POV.

%??ma yi magana da ita?%???

Dr ta tambaye ayayinda suka jero suna tafiya.

%??meah but...%???

Sai kuma yayi shiru.

%??mi fa tun dazun kai na tsaya jira and you keep telling me kana cikin asibiti nan all this while baka shigo ba%???

%??mna shigowa na zan wuce na hangota tana ta safa da marwa i hide somewhere ina ta kallonta you have no idea i feel right now God i love that girl, i love her so much...%???

Dr ta girgiza kai tana murmushi.

%??mhe even called my name Abiey.... And she nailed it%???

%??must like that tace Abiey%???

%??mace what now Abiey? But tana cikin damuwa sosai na ga damuwa a idonta kuma na ga kaunata a idonta%???

%??mdonka sun maka karya bana tunanin zaka ga kaunarka a idon Zahra a halin yanzu ban sani ba dai ko gaba maganar damuwa ita kam na yarda 100% tana ciki saboda ta rasa mijinta couple months yanzu kuma ta rasa babynta%???

%??me's not more her miji, kuma wannan tsanar da kika ganin Zahra na min soyayya ce and her first love, Zahra ba zata taba manta rayuwar da muka yi ba, ba zata taba son wani kamar yadda take so na ba, na yarda tana son Deen but not as much as she love me%???

Wannan karon Dr tsayawa ta yi kallonsa sai yayi murmushi.

%??mna son sanin wanene likitan nan kuma me take nema a gurinsa har yake nuna mata yatsa%???

%??mane likita?%???

%??man san shi ba, ban ma taba ganinsa ba sai yau%???

%??mon't tell me you're jealous?%???

%??m have a right to, but it's not about that it's about pointing his finger on her face%???

%??mo sannu baban soyayya, yanzu fada min miya kawo ka a gurina?%???

%??maman ina son na ce ki je ki bincika min lafiyarta ne, but yanzu ba zan sake saka kowa ba i will go by myself, saboda na gane zuciyata tana kirana izuwa gareta ne kai tsaye, abu na biyu na yi magana da Yasmin amman ina son ke ma ki yi na san tana jin maganarki kuma zata fi fahimtarki, so nake tsakanin yau zuwa gobe a lalata maganar nan%???

%??mata saurareka ba ne?%???

%??ma saurare ni mana na shiga gidan....%???

Dr ta yi murmushi bayan ta gama sauraren yadda Abiey yayi da Yasmin.

%??man yi magana da ita you can rest now%???

%??mhank you%???

Ya furta sannan ya saka hannunsa aljihu yana lalaba keys dinsa, a gurin ya barta tsaye ya nufi gurin da ya faka motarsa domin gurin da nata motar yake aje daban da inda kowa ke ajewa.
10/10/22, 14:03 - Buhainat: *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*

Farinciki ganin Zahra da yayi a yau ya saka shi manta duk wata damuwa da yake ciki.

%??mou look beautiful when you are looking at me%???

Ya furta yana murmushi kallon tsana take masa amman a gurinsa kallo ne mai muhimmanci da ace bata kaunarsa da yanzu ta manta komai da ya faru ta masa magana kamar ba au taba samun matsala ba, but ta kasa mantawa saboda ta kasa cire sonsa a zuciyarta.

%??met give love another life%???

Ya furta yana shafa kansa, a maimakon ya tafi gida sai ya juya motarsa zuwa unguwarsu Zahra, ya faka motarsa nesa da gidansu sosai ta jingina da kujerar motar yana hangen gidansu sai ya samu kansa da murmushi yana tuna lokacin da yake fakawa ta fito da gudu wani lokacin saboda ta saci kafa ta shige motarsa ya dauke zuwa wani gurin ko gurin Ammy.

%??m missed those days, i miss you Zahra so much%???

Sosai ya kurawa kofar gidan ido yana jin kamar ya sallama ta fito. Ya dora hannunsa kan karjinsa saitin da inda zuciyarsa take yana sauraren yadda take buga masa. Ya dade a gurin kamin ya hango ta ta fito ta hanyar dake facing din inda ya aje motarsa sai dai bata san shi ba ne saboda bata san shi da wannan kalar motarta, gaba daya kuma hankalinta baya jikinta balle zuciyarta ta raya mata zai biyo har ta tsaya kallon ko'ina ta hango shi, tashi yayi zaune da sauri yana kallonta har ta shige cikin gidan.

%??mukata ta biya%???

Ya furta kana ya yi reversed ya juya motar ya fita daga unguwar ya dauki hanyar gidansu Ammy.



ZAHRA POV.

Bayan sallah Isha'i ina zaune bayan Mama dake sallah Baba ya shigo, na gyara zama na gaishe shi ya amsa ya zauna kusa da ni yana aje ledar dake hannunsa.

%??memu ne bude ki gani idan zaki iya sha%???

Kallonsa na fi sai na yi murmushi duk da kasancewar ba lallai ne ya gani ba, domin babu nepa a gidan sai hasken fitilar da aka juya kanta zuwa kofar waje. Hausawa suka ce kamar kumbo kamar korensa, salinsa sak irin na ??ansa haka Deen yake min baya som shigowa gida ba tare da ya riko min komai ba, ban ankara ba na ji hawaye suna sauko min.

%??mannu da zuwa%???

Na ji Mama ta fada sai na share hawayena na ina jin zuciyata tana min wani iri.

%??ma gode Baba, ya Hajiya?%???

%??mafiya kalau take, na yi magana da wanda zai kawo rago jibi idan Allah ya kai mu mahauci shi zai yanka ya gyara...%???


Yana rufe baki wayar Mama ta yi ringing alamar kira, sai na ga Mama ta yi saurin yanke kiran.

%??mahra ina kawarki Hameeda ce ta yi flashing duba ki ga idan akwai kudi sai kirata%???

Na karba ba dan na san ina da kawa Hameeda ba kuma ban fahimci Dr Hamid ne ya canjawa suna ba har sai da na duba kiran.

%??mh bari na kirata%???

Na tashi da sauri na nufi daki na bar Mama da Baba a waje, ina shiga na kuma can karshen dakin na zauna a kasa na rage muryar wayar sosai kuma na yi kasa da tawa muryar saboda kar a aji na kira shi. Ringing daya yayi picking.

%??mello%???

%??mello%???

Ni ma fada ba tare na san da wace kalmar zan biyo baya ba, domin shi ya kira ni ba ni na kira ba ban kuma manta da wulakancin da yayi min dazun ba.

%??mahra%???

%??ma'am%???

%??ma gida?%???

%??mafiya Kalau%???

%??ma kira kika yanke%???

%??mh wayar ta Mama ce daman line na na saka a ciki, kuma ka kira a lokacin akwai mutane shiyasa aka yanke kiran%???

%??manzu fa? Allah yasa ke kadai kike%???

%??ma kebe ni kadai a yanzu%???

%??mi yi hakuri da abun da ya faru a dazun, ina cikin bacin rai ne sosai shiyasa%???

Magana yake min ba kamar ba shi ne ya fusata sosai dazun ba akan abun da ban san dalili ba

%??mmman ya kuke da Abiey?%???

%??ma san shi ne?%???

%??mitaccen mutum ne, zai yi wahala wani yace miki be san shi ba%???

%??mun yi zama makota da shi ne%???

%??mawai?%???

%??mh%???

%??mkay....%???

Ya amsa kamar be yarda ba, sai kuma ya ce.

%??mnyway dazun me kika zo yi a gurina%???

%??ma komai%???

Na amsa domin ban ga amfanin fadin matsalar a yanzu ba.

%??mm.. Uh.... Yaron nan... Idan aka ba shi nono yana saka shi ciwon ciki...%???

Faduwa gabana yayi sai na mike tsaye da sauri ina dafe da kirjina.

%??miya faru? Miya same shi?%???

%??mna son na tambaya ko ki bashi wani abu ne lokacin da na bar miki shi a asibiti?%???

%??mallahi ban masa komai, taya zam cutar da ??ana%???

%??ma maganar cutarwaba ce ina nufin ko kin ba shi wani abu da zai saka shi gurbacewar ciki?%???

%??man masa komai ba%???

%??mdan kin san kin yi ki fada so that a samu mafita tun wuri karki je ki kashe shi%???

%??man masa komai, dan Allah ka fada min miya same shi? Me zai saka na yi ma masa wani abu?%???

Na tambaya wani kuka mai karfi na zo mini, gaba daya jikina yayi sanyi gabana kuma sai faduwa yake.

%??mabu.. Abun da ya same shi... da farko mun dauka ko matsalar daga rashin kyau nonon Jamila ne... Amman an gwada ba shi nonon wata wasu matan har biyu shi ma ya saka su ciwon ciki, kuma ana bashi madara ita ma tana ba shi matsala%???

%??man masa komai ba ka bincika nononta wata kila ba shi da kyau%???

%??mononta lafiya kalau yake, kuma ba nononta kadai ke saka shi ciwon ciki ba, so ki fada tun wuri idan kin san da wata matsalar%???

%??man san da matsalar komai ba, da na sani da fada ko dan a ceto rayuwarsa%???

Ya sauke ajiyar zuciya ina jin kamar akwai abun da yake boye min, sai ya sauke wayar ba tare da yace min komai ba, ni kam tuni hawaye suka wanke min fuska ina jin kamar ??ana mutuwa zai yi a hannun wata wanda ba mahaifiyarsa ba. Fitowa na yi dakin na ajewa Mama wayarta na nufi dakin da nake kwana tana tambayar na gama waya da Hameeda kai kawai na iya daga mata na shige, ina shiga na maida kofar na rufe na kife saman katifa sai kuka, shi na kwana yi har safe daman ni da kuka mun dade da kullo abota tun a lokacin da Deen ya fara yin bakwana da duniya ban san wata rana sa zan ce farinciki ya rabe ni ba.
Ana gama sallah asuba Mama ta dora min ruwan zafi, daman can da zarar ta gama sallah azuba take dora min ruwa idan ya tafasa sai ta dama min kunu sannan ta zuba min na wanka. Sai da na fito daga wankan na sha nunu sannan na fito waje na aje kofin da na sha da shi da zimmar na hada sauran kayan na wanke.

%??m a ban saka ki ba, tashi ki je ki kwanta jiya ba ki samu bachi ba%???

Ya daga kai na kalleta mahaifiyata ce ko ban fada ba zata iya fahimtar halin da nake ciki domin idanuwa da fuskata sun nuna haka, sai dai na san bata son ta yi min maganar saboda Baba yana cikin gidan. Tashi na yi na koma dakina na kwanta sai kuma na ji katifar bata min dadi, na tashi zaune na ranka tagumi ina tunanin anya ban zalinci ??ana ba? Da kuma ni kaina? Sai dai wata zuciyar kokarin nuna min take ba ni da laifi na aikata abun da na aikata ne saboda neman mafita, tashi na yi na fito waje na karbi wayar Mama na dawo dakin na kira number Dr Hamid be daga ba sai na ji wani zazzabi ya sauko min, gaba daya na rasa abun da ke min dadi. Na sake kira be daga ba sai na yanke shawarar kira Jamila kai tsaye domin zuciyata ta kwadaitu da son sanin halin da ??ana yake ciki, kowane ringing daya tare da bugun zuciyata yake shiga, tsoro nake kar ta ki dauka ta dayan bangaren kuma ina fargabar abun da zan fada mata idan ta daga kiran.

%??ma aka yi?%???

Jikina ya hau rawa na tsoronta can kuma sai na samu kaina da murmushi hawaye na sauko min sakamakon jin sautin kukan ??ana da na yi yana fitowa daga cikin wayar.

%??mna jinki?%???

Na kasa magana sai hannu na saka na dafe kirjina.

%??mtssssss%???

Taja guntun tsaki zata yanke wayar sai na yi saurin dakatar da ita.

%??maman tambayar jikinsa zan yi%???

%??mhi wa?%???

%??mana.....%???

%??manki babu ko kunya babu tsoron Allah? Wato Dr fada miki abun da ya ke ko? To bari na gargade ki idan baki da hankali zan miki shi, daga yau sai yau karki kuskura kiran ??ana da sunan ??anki, and daga karki sake kiran wayata sannan idan wani abu kika masa dake saka shi ciwon ciki idan ya kama nono to ki fada tun wuri, domin Wallahi zan iya shari'a dake akan ??ana, idan wani abu ya same shi ba zan barwa Allah ba%???

%??man masa komai ba, ina rokon alfarmar ki dan Allah ki taimaka min ki rufa min asiri ki bari na ganshi ko sau daya ne%???

%??maki da hankali Zahra%???

%??mi kira ni da ko wane kalar suna, ki wulakanta ni yadda ranki yake so zan dauka saboda na ga....%???

Na kasa karasawa saboda kar na furta kalmar ??ana ranta ya bace.

%??manki... Dan Allah ki min wannan lamanin dan alfarmar da Allah yayi miki, ki taimaka ki cece rayuwata wata kila ba zan yi tsawon ran da zan sake saka shi a idona ba, waya sani ko nonon mahaifiyarsa yake so?%???

%??mana ba shi da wata uwa sai ni, ki daina yin abu kamar kin fini sonsa kuma na fada miki tun wuri idan kin san wani abu kika masa ki fada tun wuri, daman can zuciyata bata natsu da baki shi da aka yi kika gani ba har na tsawon lokaci, Allah ya saukewa ??ana ya sha nononki ko zai mutu ba zai taba shan nononki har abada...!%???

Sai da na zabura a lokacin da ta yanke kiran, sai ya rumgume wayar ya runtse ido ina kuka marar sauti saboda kar Baba ya ji ni.

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un.... %???

Na furta ina jin ina ma ban aikata ba, ashe haka ko wace uwa ke ji idan ??anta yana kuka hankali ya tashi matuka da jin kukan ??ana da na yi, ina jin kamar na ruga naje agareshi a guje na bashi abun da yake bukata.

%??ma cutar da kaina na cutar da jaririn da be san komai ba.... Na saka Hajiya ta yi zaton bata da jika... Na yi dalilin fitar jinin Deen a hannuna, na rasa Deen na rasa ??ana wayyo Allah%???

Wannan karon da da ihu ya ambaci Mahallincina ina jin kamar na yi hauka kuka na zo ta ko'ina Mama ta shigo ??akin da sauri.

%??mafiya?%???

Sai na tashi da sauri na rumgume ta ina jin kamar ita ce zata min maganin matsalolina na fashe da wani sabon kuka wanda ya saka Baba shigowa yana tambayar ba'asi.
10/10/22, 19:32 - Buhainat: *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*


%??marinyar nan tana cikin damuwa%???

Shi ne abun da ya fito daga bakin Baba a tunanin Baba ina kuka ne saboda rashin Deen da baby kawai, Mama dai bata ce komai ba ta yi ta rarrashina har sai da na samu sukuni sannan ta fita ta bar ni a dakin ina ta faman sauke ajiyar zuciya, sai na yi kamar na dauki wayar na kira Dr Hamid sai kuma wata zuciyarta ta hana ni wata kila shi ma idan na kira ya fada min magana marar dadi ko ma ya rufe ni da fada kamar Jamila. Sai da Mama ta sallami Baba sannan ta shigo dakin ta tambaye ni abun da ya faru tun jiya har kawowa yau. Damuwa na gani karara a fuskarta wanda hakan ya saka hankali ya kara tashi.

%??mama mutuwa zai yi ko?%???

Ta sauke ajiyar zuciya ta kalleni.

%??mabu wanda ya san mutuwar wani sai Allah, ina tunanin na ce ki cire yaron nan a ranki, karki sake kiran wani daga cikinsu da sunan tambayar lafiyarsa, indai na isa na baki shawara ki ji%???

Na daga mata kaina da ke min wani mugun ciwo sannan na lumshe idona na kwanta. Nan da nan bachi ya dauke ni ban farka ba sai da na ji muryar Yaya Maryam da kuma hayaniyar yaranta ita ta farkar da ni, na taso na fito waje na zauna kusa da ita sai ta kalleni tana murmushi.

%??ma jikin Zahra?%???

%??mlhamdulillah%???

Na amsa da muryarta da bata fita sosai.

%??min ci abinci?%???

%??mh na sha koko da safe%???

%??ma danwake na miki na san kina son shi%???

Ban ce mata komai ba na kwantar da kaina jikin kafadarta sai na ji wani sanyi.

%??mama ta fada min abun da ya faru ki barwa Allah komai kin ji Zahra ki saka ma ikonsa da sarautarsa ido, yadda Allah ya so haka yake kasancewa%???

Na daga mata kai, ina kallon yaranta dake wasa a tsakar gida gwanin sha'awa, sai gani ina murmushi a da can mi ba gwanar son yara bace amman daga daukar cikin nan da na yi zuwa haihuwa Allah ya saka min son Yaya sosai. Ban daga jikinta ba sai da aka kira sallah azahar sannan na daga ta tashi ta yi alwala ta dawo kusa da ni ta yi sallah ta dauko plate ta zuba min danwaken Husna ta dauko min spoon amman sai na samu kaina da kasa ci.

%??mi daure ko ci mana, idan kina zama da yunwa zaki jefa kanki cikin wani hali ne kawai sannan hakan yana nuna baki yardar da kaddarar da Allah ya dora miki ba%???

%??mna jin tausayin yaron nan, ina jin tsoron hakkinsa da Allah zai tambaye ni%???

Na dauki spoon na na debi ??an

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login