Showing 207001 words to 210000 words out of 210919 words

Chapter 70 - CIWON SO

10 Oct 2024

4241

turaruka masu kamshi da kyau sannan muka isa gidan. Na yi mamakin yadda ta tarbe ni a nan na lura ta fini wayo da kuma wayewa domin har ga Allah ni ba zan iya hadeye kishina na sakar mata fuska da jiki kamar yadda ta yi min ba. Amman sai gata tana jana da hira har da su dauko waya ta dauke mu hoto da Abiey sannan ta yi mana ni da ita daga karshe kuma ta dauke mu a tare gaba daya, da gangan na rike hannun Abiey na shiga dakunanta ina dubawa ita ma dai an narka mata dukiya, ko da yake ba abun mamaki ba ne domin yar manyan mutane ce ba kamar ni ba, hakan kuma be kara min komai ba sai kaunar Ammy wanda ta tsaya ta tsara min komai da na zo na tarar da shi a gidana.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: A falonta Abiey ya tambaye kwana nawa muke ganin zai yi mana a tsakaminmu, a karshe muka zabi kwana biyu biyu domin shi yafi dadi da kuma adalci, da zamu fito ta dauko wasu daga cikin kayanta na lefe ta yi min kyauta da su, Abiey ya rika min jakar muka shiga mota tana daga min hannu har muka fice. Isowarmu gida da kamar minti talatin ta kira number ta tambaye ni ko mun iso lafiya, na yi mamakin a inda ta samu number wayata sai Abiey ya warware min ta hanyar fada min da yayi cewar ta karbi number tun a shekaranjiya, har yake nanata min wai ban fada miki Yasmim bata kishinki ba yarinyar tana da hankali ai, a nan na gane wayayyiyar yarinya ce Abiey ya auro kuma idan ban tashi tsaye ba zata iya kwance min mijina.
Daren mun kure junanmu da soyayyar da kuma kewar juna da muka yi na tsawon sati daya ba a tare.
Kwana biyu yayi ya koma gurin Yasmin, hakan ya taimaka miki gurin gyara kaina na shiryawa shimfidar mijina kamin girkina ya dawo. Yasmin na cika sati biyu a gidan Abiey na shiga makarantar koyon girki, a nan na hadu da wata kawa mai kirki ashe ba ni kadai ce matar auren dake fama da rashin iya girki ba, wasu kuma yan mata ne da aka kawo su koyi kalolin girki kamin aurensu. A ka'idar koyon girkin wata uku ne, kuma kullum ake zuwa domin ko wace da kalar abun da ake girkawa, idan ka dawo gida zaka kara gwadawa ne, haka nima nake idan na dawo ranar abun da na koyo shi zamu ci domin shi zan girka. A haka kachar aka yi wata biyu da ni saboda laulayin da na fara, da farko na yi zaton ko nauyin jiki ne kawai saboda aikace aikacen da nake fama da shi a yanzu, sai dai ganin ina yawan Amai da kwadayi ya saka na fahimci laulayi ne, daman watan nan gaba daya ban ga al'adata ba, a gidan Deen ma sai da na yi wata uku sannan na samu ciki. Ranar da abun yayi min tsanani har Abiey ya fahimci haka, a asibiti muka wuni domin baya wasa da lafiyata. Daga Asibitin ya dauke ni muka biya a masarauta muka gaishe da Mai Martaba kuma muka duba Mama Lami da aka yi ma aikin ido.
Daga ranar Abiey ya dauke min aikin komai, motsi mai karfi ma idan na yi sai yace babynsa, kamar akansa aka fara haibuwa. Yanayin wannan cikin yayi min kama da na farko domin laulayin kusan iri daya nake, hakan ya dawo min da tunanin ??ana sosai a raina ina ta jin kewarsa har ta kai ko ruwa na sha sai na tuna da shi na tambaye kaina ko a wane hali yake a yanzu. Cikina na wata shida na yi ma Abiey zancen ina son naje na duba Amir a take na ga yanayin fuskarsa ya canja, kuma ya kasa amsa min da mu tafi din ko kar mu tafi, a madadin haka sai ya dauke ni muka tafi muka gaishe da Baba da Hajiya yayi musu alheri, ba laifi Baba ya dan sauko domin har godiya yayi da abun da Abiey yayi masa kuma ya saka mana albarka sai dai na lura Hajiya ko kallon fuskata bata son yi.
A lokacin da cikina ya fara tsufa, sai abun ya zame ma Abiey biyu domin a lokacin ne Yasmin ta fara nata laulayin, gashi nata ya zo da wahala ba kamar nawa ba, domin ita har gida sai da aka maida ita saboda yawan rashin lafiyar da take.
Wani gata da ban taba saka ran samu ba, shi ne haihuwa a wata kasar da ba mahaifata ba, domin ina daf da haihuwa aka shirya min komai ciki har da mutanen da za su rakani a England, a can na haihu kyakkyawan Saurayi bayan na yi awa uku ina nakuda, domin fara nakudata a tsaye ne tun a lokacin da na shiga watan haihuwa ta, sai dai a lokacin da haihuwar ta gabata gadan gadan sai na samu sauki taltalo ??ana fari tas kyakkyawa. A ranar lashe ni ne kawai Abiey be yi ba, amman tsabar farinciki ni da shi duk sai da muka zubar da kwalla. Kwana na biyu a kasar ran na uku muka dawo Nigeria, a gidan Mama na sauka duk kuwa da kasancewar Ammy da Abiey ba su so haka ba. Na samu kyakkyawar kulawa a gurin mahaifiyata da kuma yan'uwanta ciki har da kanwarta wancce ta dawo da zama a gidan.
Cikin rashin lafiyar Yasmin ta zo duba ??ana tare da katon akwatin na barka da ta yi masa, a gaskiya na jidadi ko da a munafunce take nuna min sosai hakan ya faranta raina ballantana ma yadda na tabbatar babu wata zuciyata a zuciyarta domin a dan zaman da muka yi na fahimci haka har ina sha'awar a hade mu a tare.
Daga ni har yaro mun ga fuskoki kala kala daga dangina har na Abiey, yan'uwana sun yi min kyauta daidai gwagwado hali, na Abiey kam ba a magana har rasa bakin godiya na yi. Ana sauran kwana biyu suna aka tafi da yaron gurin Mai Martaba ya gan shi ya saka masa albarka, da kuma Mama Lami wanda gani yayi wa karanci a yanzu duk kuwa da kasancewar an mata aikin idon kusan sau uku a maimakon ta samu lafiya sai abun ya kara lalacewa.
Ranar suna yaro ya ci sunan Mai Martaba aka yi masa alkunya da Malik. Daga ni har shi mun ga gata irin wanda ban taba ayyana samunsa a rayuwata ba, kamin na cika arba jikina yayi kyau saboda kulawar da nake bashi da kuma kayan gyara jiki da gyara gado da na siya a gurin Hajiya Aisha. Arba'in dina da kwana sati daya aka soma shirye shiryen bikin Aisha wato yar Anty Ammy, Ammy da ni ce kirjin biki, domin Ammy ta zama kamar wata uwarta ni kuma na zama matar babban yaya duk da kasancewar ba ni ce kadai matar yayanta ba domin akwai manyan yayan Mai Martaba da matansu sai dai kasancewa da Abiey suke shiri hakan ya maida ni wata babba a gurinsu. Duk wata hidima da aka yi ta bikin da Aisha ba ayi ta da Yasmin ba domin cikin dake jikinta be barta ta samu lafiya ba har ta shiga watan haihuwarta, hankalinmu ya tashi matuka a lokacin da likiton suka tabbatar mana da cewar ba zata iya haihuwa yan biyun dake cikinta da kanta ba, daman can Abiey yayi mata bukin din asibitin da zata haihu a England domin shi ne adalci yayi mata kamar yadda yayi min. Ana sauran sati biyu edd dinta ya cika muka kwasa har da ni da Abiey da mahaifiyarta da wata yayarta da suke uwa daya muka tare a kasar, ashe wanda ba shi da shi ne yake mamakin idan an fada masa wani abun har ya karyata ko yayi mamaki domin na samu labarin yayan manya da kuma matan masu kudin da suke zo wa haihuwa a asibitin da aka yi ma kyakkyawar shaida. A lokacin na tabbatar da Yasmin ta yi gadon kirki a gurin mahaifiyarta ne domin da ita muke ta zancen, a hannunta Malik yake wuni idan na karbe shi sai idan nono zai sha ko kuma yayi bachi. Yasmin ta samu kyakkyawar kulawa daga gurina kuma hakan ya kara mana fahimtar juna da kuma kaunar junanmu, sai dai ashe sayyanar ta mu ba mai dadewa ba ce domin an fasa cikinta aka cire mana yan biyu duka mata masu rai da lafiya ita kuma ta kasa survived sai gawarta aka ba mu.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: A ranar mun ga tashin hankali domin mun samu rai biyu muka rasa daya, har na kan ina ma yayan muka rasa ita a bar mana ita, sai dai Allah baya barin wani dan wani haka kuma ya tsata abun da zai faru tun ranar gini tun ranar zane.
Ni da Abiey aka rasa wanda ya fi sonta da kewarta, na dauki yaran da suka ci sunan Nimra da Namra wato sunan mahaifiyarta da kuma na Ammy na da da Malik ina shayarwa, abun nan is not easy amman a haka na yi ta dawainiya da su ana hada musu da madara har suka isa yaye na yaye su. Wata rana na saka yara a gaba muka tafi gidan Dr a gidan muka wuni, na kwance mata cikina na son sanin halin da ??ana Amir yake ciki, domin idan na yi ma Abiey maganar sai ya nuna min bacin ransa, sam baya son maganar Amir har cewa yake baya son ina masa maganar abun da ya shafi Deen.

%??mi ma ba ni da labarinsu a yanzu, domin Dr Hamid ya yanke alaka da ni, ya daina aiki a asibitin da nake aiki a yanzu, kwana kin baya ma na ji ance yayi gobara har ya rasa yarsa daya, amman dai zan bincika na ji%???

Na sauke Nimra daga cinyata ina kallonta.

%??mmman kina ganin zai fada miki? Bayan Mr Bashir ya rabu da kanwarsa ko kuma ya maida ta ne?%???

%??me maida ta ba, ai ba gurin Dr Hamid zan bincika ba, zan tuntubi Mr Bashir din ne da kaina domin har yanzu muna da contact din juna, sai dai mun dade ba mu yi magana ba%???

Tana rufe baki ta dauko wayarta ta duba numbersa.

%??mllah sarki...%???

Ta fada sannan ta miko min wayarta, hoton Amir ne a dp Mr Bashir din, rabin kamanin fuskarsa na fuskata ne, a yayinda rabin kuma ya so ya dauko Deen kuma be yi kama da Deen din sosai ba. A take na cire hoton na turawa kaina ina sharce kwalla.
A daren na kwana da begen ??ana na yi kuka sosai kukan da ban san na me zan kira shi ba, tausayin ??ana ko tausayin kaina ko kuma na kaunarsa, ko na rashinsa a kusa da ni, a yanzu na fi jin kaunar Amir fiye da da, duk kuwa da kasancewar a yanzu ina da wasu yayan da za su cire min kewarsa, ina ta kallon hoton da aka yi masa tare da yayan turawa yana sanye da kayan sanyi an rufe masa jiki ruf. Washe gari bayan mun karya nake nunawa Abiey hotonsa ina murmushi hawaye na kwaranya daga idona. Sai ya ki karbar wayar a take yanayinsa ya canja.

%??muk damuwar da zaki shiga bata kai wanda iyayensa Deen za su shiga ba, domin su sun rasa ??a kuma ba su da jikan da za su rika kallo a matsayin ??anta%???

Na share hawayen.

%??mbban Malik ai su ba su san Amir a matsayin jikansu ba, saboda ba su san zafin rashinsa ba, amman ni na sani domin na zauna da shi na shayar da shi dole na san zafin rashinsa%???

A lokacin ne Abiey ya kalli kwayar idona yayi min wani kalami marar dadin ji.

%??mahra baki da godiyar Allah, duk kyautar nan da yayi miki baki gode ba sai kin daga hankalinki a kan wani abu can dabam? Hakan yana kara tabbatar min da cewar kina son Deen har gobe%???

Na girgiza kai da sauri.

%??mna dai son ??ana kuma ina tausayinsa%???

Mikewa yayi tsaye ya saka hannu ya dauki ??ansa Malik ya fice daga falon zuwa harabar gida, share hawayena na yi na mike tsaye na bi bayansa sai na tsame shi tsaye yana rike da hannayen Malik yana sumbata, na risina a hankali na kwantar da kaina a bayansa.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: %??m Love My Son%???

%??m Love You so Much Abban Malik%???

Na tari numfashinsa a lokacin da yake furtawa ??ansa cewar yana kaunarsa, sai ya juyo ya kalleni ya sumbanci goshina.

%??m love you too, je ki dauko min Twins%???

Na mike tsaye na dawo falon na janye plate din da suke rigima akansa na goge musu hannayensu na fito da su waje, sai ya hade su su ukun yana wasa da su, ni kam ina tsaye gefe ina kallo kamin na fara shigarwa Twins har muka yi winning shi da ??ansa suka fadi. Tun daga ranar sai na tattara lamarin Amir na aje gefe, ba dan bana kaunar ??ana ba sai dan na lura kamar maganarsa ko nuna damuwa akansa ya kan haifar da matsala tsakanina da mijina, sai dai a kullum kaunarsa karuwa take a raina, har ta kai wani lokacin idan ina tsaka da tunaninsa na kan kira Malik da sunan Amir, idan Abiey ya ji ranar ba za mu kwana cikin dadin rai ba. Sai dai na kwana ni kaina shi kuma ya kwana da yaransa.

Kauna da shakuwa ta shiga tsakaninmu sosai da Twins wato Nimra da Namra, har ta kai wani lokacin idan zan fita sai dai na fita da su na bar Malik a gida, ko na yi musu abu na kyale Malik, idan Abiey ya gani sai yace ai daman ba son ??ansa na ke ba, mutane har basa sanin ba ni ce mahaifiyarsu ba sai wanda ya sani. Tun bayan haihuwar Malik sai haihuwar ta yi min shiru sai da Malik yayi wayo sosai sannan na sake haihuwar Mace.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya kamar yadda na dade ina mafarkin ta kasance a gareni, wato cikin kwanciyar hankali da farinciki, ga yarana sai tasawa suke, soyayya tsakanina da mijina kuma kamar domin mu kawai aka hallicce ta, ba ni da wata matsala ta rayuwa a yanzu, soyayya dama da hagu, ba ta bangaren Ammy ba ba ta gurin Momy ba wato mahaifiyar Yasmin ba kuma ta bangaren Mai Martaba ba, ga kuma Mahaifiyata a gafe.
A ranar da Dr ta turo min video da hotunan Amir da Mr Bashir ya turo mata na sha kuka har na gode Allah, sai dai na jidadi sosai sanin cewar ??ana yana cikin farinciki da kwanciyar hankali kuma a gurin da zai samu ingantacciyar rayuwa da tarbiya mai kyau. A gurina Baba ya cancanci alheri domin ko ba ya rike mu har girmanmu kuma ya aurarda mu, saboda haka shi ma ya cancanci cin alfarmata, hakan ya saka na biya masa kujerar makka a shekarar da Abiey yayi rabon na sa kujerun ga yan'uwanshi da nawa, mun kusan sati muna fada da juna saboda abin da na yi, a tunaninsa ina kyautatawa Baba ne saboda yana mahaifin Deen, shi kuma a gurinsa ba shi da babba makiyi kamar shi.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Baba ya ji dadi sosai yayi ta godiya yana nuna rashin jindadinsa akan abubuwan da suka faru, a sirrance na siya masa wani gidan a makwafin gidansa da aka rusa a wacan lokacin na baya, ta dalilin abun da na yi masa ya dawo yana neman yafiyar Mama har ya share dattin dake tsakaninsu zamansu ya dawo da jindadi fiye da baya.


*** *** ***

Bayan wadansu shekaru...!

A yanzu na gane iyayenmu sun sha wahala na rayuwa da mu, domin tarbiya yara ba abu ne mai sauki ba ko bari bari kawai ya isheka. Ina risine ina sakawa Mahmud safa Abban Malik ya shigo sai da ya fara kaiwa bayana duka sannan ya zauna ina gama saka masa safar ya janyo ni na fado jikinsa.

%??miayatee ki daina zancen bude gidan abincin da kike a nan%???

Na gyara zamana a jikinsa ina taba hancinsa na ce.

%??maboda me?%???

%??maboda za mu koma Abuja da zama, sai ki bude a can%???

%??mbuja kuma?%???

%??mes Mai Martaba ya bukaci haka, saboda kula da abubuwansa da suke can, ni kuma i can't say no%???

Kwantawa na yi jikinsa a shagwabe na ce.

%??ma saba da nan fa Abiey na%???

Na mitsike cikina.

%??man din ma ai sabawa zaki yi da mutane%???

%??mi dai gaskiya aa, sai dai ka rika zuwa kana dawowa%???

%??ma ba wannan maganar sai dai na kwashe yarana na tafi da su, na bar ki a nan ke kadai idan na samu wata yar shala a can na aureta...%???

A take na saka hannu na cire hular kansa na jefar na kama kan nashi na kasa a murkushe.

%??ma ma isa, ai Wallahi daga ni ba kari%???

%??mnji wa? Na yi alkawari da ke?%???

%??mana auro wata zan maka hauka, na tashi hankalinka%???

%??mi fa yanzu na gama dake, ba dai kin haifa min carbon copy ba?%???

Na yi fuska, sai ya fara kyalkyalata har sai da na yi dariya.

%??masa fa nake, ni na isa na hada Zahra da kishiya? Ke da yayan na ki ai ba za ku bar kishiya ta jidadin zama ba, shiyasa idan mata suka min signal na ke ce musu ni fa na auru tace bata son kishiya%???

Ban san lokacin da dariya ta subuce min ba, na rumgume shi, shi ma dariyar yayi ya shafa bayana.

%??m love you so much Hiayatee%???

%??m love you more Zauji%???

Na dago fuskata sai ya hade bakinsa da nawa...




_______________________________

THAMMAT BI HAMDILLAH ???i???j

Na gode Allah da ya ara min lokaci na kawo yanzu, zan yi amfani da wannan damar na nemi yafiyar wadanda na batawa, ayi hakuri a dubi rahmar Allah da jikansa ayi min afuwa. Ina fatar Allah ya yafe mana gaba daya ya hada mu akarkashin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login