Showing 36001 words to 39000 words out of 210919 words

Chapter 13 - CIWON SO

10 Oct 2024

4228

ya gujeta i will never ever forgive him%???

Sauban ya sauke ajiyar zuciya.

%??mna fatar Zahra zata gane gaskiya wata rana, but sometimes so yana rufe mana ido mu aikata abubuwan da basu dace ba, i think yana son ta sosai kamar yadda kake son ta, shiyasa har ya aikata abun da ya aikata%???

Abiey ya kalleshi yana wani murmushin gefen baki.

%??meally? Is that what you think? Hmmm%???

Ya shiga ya zauna yayi ma motar key ba tare da yace komai ba, yayi reverse kamin ya isa gate mai gadin Sauban ya bude masa gate din sai ya fita gidan ya bar Sauban a tsaye yana bin motarsa da kallo. Driving yake a hankali zuciyashi na mashi ba dadi har ya isa gida, horn daya aka bude masa katon gate din gidansu ya kunna kai ciki be faka ko'ina ba sai harabar entrance din Ammy ya bude motar ya fito kamar marar lafiya ya karasa gurin kofar yana tabawa sai ya ji ta a rufe abun da ba a saba ba, domin ba kasafai Ammy take rufe kofar falonta ba, kara ma ada can lokacin da Zahra take zuwa gidan tana rufe kofar musamman idan tace zata yi ma Ammy girki. Har ya kai hannunsa ya danna door bell din sai kuma ya fasa ya kwankwasa. In right time Yasmin ta bude masa kofar tana sanye da doguwar rigar atamfa hannunta rike da albasa.

%??masmin?%???

%??ma'am Sannu da zuwa%???

%??me kike yi?%???

%??momy ce ta aiko ni, sai Ammy ta ce na mata girki saboda Jummai bata kusa%???

Kallonta yayi from head to toe ya kai hannu ya taba ta, sai ta matsa baya.

%??mmmy tana sama%???

Murmushi yayi ya dauke kansa, because she did exactly yadda Zahra take masa.

%??mhy are you behaving like her?%???

Bata ce masa komai ba, bayan kallonsa da take sai ya raba gefenta ya shiga falon ya kalli kofar kitchen din yana jin kamar ya hango Zahra a tsaye tana masa gwalo ko tana kashe masa ido daya.

%??ma zo a daidai, yanzu Anty Amarya ta kira ni%???

Ammy ta fada tana saukowa downstairs din rike da wayarta a hannuna, juyowa yayi ya maida dubansa a gurin Ammy, kallonta kawai yake kamar wanda be fahimci abun da take fada masa ba, hakan ya karanta da ita danta autan danta ba lafiya yake ba.
10/1/22, 22:03 - Buhainat: *B??0? ?]Mq?? CIWON - SO B??0? ?]Mq??*

By Khadeeja Candy


1??_/Q2??_/Q

Hannu ya mika a hankali ya karbi wayar da ke hannun Ammy sannan ya sake kiran Anty Amaryar ta line Ammy.

%??mello%???

%??m'ana tun da Ammy ta tafi da kai baka dawo ba, shiyasa na kira na yi biko har yanzu baka huce ba?%???

%??man yi fushi ba, Ammy ce tace min Mai Martaba yana bukatar space%???

%??mpace din ai yayi yawa haka, kanenka ma suna ta marmarinka%???

%??man zo idan na dawo daga England%???

%??mo ka taho kamin ka tafi sai ka yi ma Mai Martaba bankwana daga nan%???

%??mhikenan zan zo%???

Ya sauke wayar cikin yanayin dake kara karantar da Ammy damuwarsa. Ya mika mata wayarta ya nufi stairs.

%??mliyu...%???

Ta kira shi sai ya juyo ya kalleta.

%??me ke damunka?%???

A maimakon ya amsa mata sai kawai ya dawo kusa da ita ya tsaya.

%??mna jin wani yanayi ne marar dadi, ban san miyasa ba amman ina jin wani bangare na jikina da zuciyata na raya min kamar Zahra tana cikin damuwa%???

Ammy ta dafe kanta cikin tsananin damuwa.

%??maba Aliyu Aliyu Aliyu yaushe zaka cire kanka daga cikin wannan damuwar ne?%???

%??mmmy ba zaki fahimci yadda nake ji ba%???

Ya fada sannan ya juya ya hau stairs din da saurinsa ya shige dakinsa. Ammy ta juyo ta kalli Yasmin dake tsaye.

%??maka yake mana kamar wani mahaukaci%???

Yasmin ta kalli stairs din sannan ta sauke kansa ta juya ta nufi kitchen.

%??masmin idan kin gama girkin ki saka naki ki ci, ni zan fita karki je gida sai na dawo%???

%??moh Ammy%???

Ta amsa cike da ladabi Ammy ta juya ta nufi dakinta mayafinta ta dauko ta jakarta ta fito, ko da ta fito harabar gidan direbam ta har ya janzo motar ya matso da ita daman ta fada masa cewar fita zata yi. Bayan Yasmin ta gama girkin ta zuba nata ta zo falo ta zauna a kasa ta nade kafafuwanta sai kuma ta samu kanta da kasa ci, minti daya biyu sai ta daga kai ta kalli stairs din kamar mai jiran saukowar wani, haka ta gaji ta dauki abincin ta kai kitchen ta dauki kofi ta sha ruwa sannan ta bude firij ta dauko apple ta fito ta zauna. Kusan a gidan ta wuni duk kuma tsawon wunin da ta yi bata ga saukowar Abiey ba, sai da aka kira sallah la'asar a lokacin ta shiga dakin Ammy ta yi alwala tana jin motsinsa sai ta fito da sauri ta bude kofar motsin bude kofar ne ya saka shi juyowa ya kalli kofar dakin Ammy kamin ya dauke kansa ya cigaba da sauka stairs din, juyawa ta yi a hankali ta koma ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?dakin ta shiga bathroom ta yi alwala, bata fito bayan gama sallah har sai da Jummai ta dawo sannan ta sauko shi ma saboda ta fadawa Jummai cewar Ammy ta fita ne. A falo suka tare ita da Jummai suna ta hira har aka kira sallah magariba sannan Jummai ta fita daga bangaren zuwa bangarenta wato BQ Yasmin kuma ta koma dakin Ammy domin yin sallah, kamar tashinta ake jira sai ga Abiey ya sake saukowa daure da alwalarsa ya nufi dinning ya bude abun da Yasmin ta dafa faten doya ne, shi kuman daman bayan son doya haka ya yatsina fuska ya fice zuwa masalllacin dake cikin gidan. Bayan sallame sallah isha'i ya zauna yana ta lazimi har aka kira sallah isha'i, yana a sahun gaba da masu aiki da masu gadin kula da gidan suka yi sallah isha'i sannan ya fito mallasacin ya dawo cikin gidan.
Kai tsaye kitchen ya nufi yana shiga ya ya dauki electric kettle ya zubar da ruwan da ke ciki ya zuba wasu, domin baya shan tea ko coffe da ruwan da aka aje sai wanda aka tafasa yanzu yanzu. Wayarsa ya ciro yana dannawa har ruwan ya tafasa, sannan ya hadawa kansa tea.

%??mmmy ki zo ki dafa min wani abu na ci%???

Ya fada yana sauraren yadda cikinsa ke kukan yunwa, yana tsaka da hada tea telephone din dake falon ta yi kara, be kula ta ba har aka gaji aka daina kiran. Sannan ya dauko mug ya fito kitchen din idonsa be sauko ko'ina ba sai akan Yasmin dake saukowa sanye da Hijab dinta da jakarta da dukan alama ta gaji da zaman ne zata tafi gida, sai kuma ya juya a hankali yana kallon kofar falon da aka murda aka bude daga can waje, a take mug din dake hannunsa ya subuce ya fadi kasa zuciyarsa ta buga da mugun karfi.



ZAHRA POV.

Da ace hawaye za su iya taruwa kamar ruwa mai yinsu yayi iyo a cikin, tabbas da hawayen da na zubar a yawan sun isa na yi iyo a cikin, da ace wani zai fada min ranar yau zata zo da zan yi kuka kamar na mutu ba zan yarda, ashe wacan kukam da na yi ranar da aka fasa aurena da Abiey sharar fage ne, yanzu ne kukan na gaske yake zuwa, a inda nake kuka babu kowa sai ni kadai da duniyata, babu wanda zai ce Zahra yi hakuri balle ya karfafa min guiwa, babu wanda zai min albishir cewar Deen ba zai mutu ba, ya gobena zata kasance idan na rasa mijina? Waye zai nuna min soyayya ta gaskiya da kaunar kamar mijina? Da wa zuciyata zata shaku kamar mijina?

%??muka ba zai miki maganin komai ba Zahra%???

Wata murya mai kama da ta Hajiya ta fada min a bayana, sai na juyo a hankali domin na tabbatar Hajiya ce ko kuma kunnuwa ne suka fara min yaye yaye. Ganin Hajiya yasa na mike tsaye gaba daya ina kallonta fuskata har ta gama kumbura.

%??ma kuka zai magance matsala da wanda kika a matsayinki na matarsa da wanda na yi a matsayina na mahaifiyarsa ya isa ya saka komai ya gyaru, amman kuka baya maganin komai%???

Sai tausayinta ya kamani domin ita ma kukan take. Matsawo ta yi kusa da ni.

%??ma sani, kin sani Abiey, kuma Deen ya tsane shi, amman a yanzu ba mu da wata mafita sai ta shi%???

Na mata kallon rashin fahimta.

%??man gane ba?%???

%??mbiey ne kawai zai iya taimaka mana mu ceto rayuwar Deen, Abiey yana da kudi Zahra kuma zai iya taimaka mana saboda ke%???

Na yi saurin matsawa baya cike da mamaki da kuma tsoro a lokaci daya.

%??mbiey fa kika ce Hajiya, kin san yadda na sani Abiey kuwa? Kin san yadda Deen zai ji idan ya san kin yi wannan maganar? Kin fi kowa sanin abun da Abiey yayi min%???

%??ma saboda kowa zaki yi ba Zahra, saboda mijinki idan ba haka ba kina ji kina gani zamu rasa shi, karki tunanin abun da Abiey yayi miki a yanzu, ko kuma abun da Deen zai ji, rayuwarsa muke bukata%???

Na girgiza mata kai.

%??ma zan iya ba%???

Sai ta fadi kasa ta rike hannayena tana wani irin kuka da ban taba ganin tana yi ba.

%??mi taimaka min dan girman Allah, daga Deen sai Bahijja na haifa bayan su ba ni da kowa Zahra, ki taimaka kar na rasa dana, Zahra ki tuna irin son da Deen yake miki wane irin hali ne ba zai shiga ba saboda ya faranta miki? Deen zai iya jefa kansa ko wane irin hali saboda ke Zahra, ki taimaka ki ceto rayuwar ??ana%???

Tana fadar hakan sai na ji an yaye min duk wani abu da nake da zai hana ko tare ni daga zuwa gurin Abiey, Tabbas Deen zai yi abun da ya fi wannan ma saboda ya faranta min balle kuma ace na rasa lafiyata.

%??ma miki alkawari Deen ba zai tana sani ba, wannan a tsakaninmu ne, ko mahaifiyarki ba zata ji ba%???

Na daga mata kai cikin kuka, sai ta mike tsaye ta rumgume ni tana kuka tana fadin.

%??mole ce ta saka Zahra dole ce%???

Gaba daya sai na jikina ya kara yin sanyi kuzarin kukan ya cire min, sai dai hawayen ba su daina zuba ba. Mun dade a haka sannan ta sake ni fuskarta har ta kumbura, tabbas ko ban akan kowa ba zan yi akan Hajiya domin bata taba nuna min tsana ba ko ta rana daya, a lokacin da nake zuwa gidanta har hana Bahijja take abu ni ta bani ko ta yi min saboda tana so na.

%??mna Mama%???

Na tambaya muryata a dakishe kana ji kasan na sha kuka har na gode Allah.

%??mun tafi gida tare da Maryam, saboda Maryam ta roka miki cewar kina son ki kwana a nan ni ma kuma na saka baki sai ta amince%???

%??maya fada miki ina nan?%???

%??mabu nima zuwa na yi na samu guri na yi kuka sai na tarar ke ma kukan kike%???

Na sauke ajiyar zuciya na share hawayena.

%??manzu nake da damar zuwa, saboda Mama da Yaya Maryam basa nan%???

Ta daga min kai da sauri, ni kaina ji nake kamar ba zan iya kara bata lokaci ba, amman taya zan tunkari Abiey? Anya ya cancanci na kalleshi ma? Abiey ya cancanci jin furucina? Balle har na je neman alfarma a gurinsa? Kamar Hajiya tasan abun da nake sakawa a zuciya sai tace.

%??maboda Mijinki zaki yi Zahra%???

Na sake sauke numfashi sannan na ce.

%??mari naje na dauki jakata%???

A tare muka jero duk wanda zai kalli fuskata ko ya kalli Hajiya ya san ni da ita mun sha kuka, ni na fara shiga dakin na karasa kusa da Deen ina kallon fuskarsa hawaye ya sake cika idona, lallai dan a'adan ba abakin komai yake ba, yadda yake nishadi da walwala na ke hangowa yau kuma gashi kwance kamar gawa yana neman dauki. A dakin na samu jakata da alama Hajiya ta kawo min ita a nan domin ni a waje na bar ta gurin da muka zauna da su Mama dazun, jakar na nufa na dauka ya juyo ya kalli Hajiya sai ta daga min kai cikin siffar tausayi da damuwa ni kuma na sauke kai na fara takawa kadan kadan har na fice, kamin na isa gate din na samu abun hawa ma aiki ba, ba dan ina jin wahalar tafiyar ba, sai dan nauyi yadda zan tunkari gidansu Abiey na nan ma ko baya nan? Ba kasafai yake zama kasar ba, kasancewar dan kwallo, kuma ko yana nan be zama lallai ace yana gidan Ammy ba wata kila yana gidan Mai Martaba gurin Anty ko wani gurin, duk kuwa da kasancewar ya fi zama a gurin Ammy.
Ki tafi ko dan saboda Deen, ba dan ke ba, saboda shi da mahaifiyarsa. Aa karki tafi mutum da ya watsa miki kasa a idon duniya zaki je neman taimakonsa? Wanda ya guje a ranar da aka taru da sunan daurin aurenki? Anya ma idan na je zai saurare ni? Ya cancanci na roki alfarma a gurinsa? Haka dai zuciyata ta yi ta raba min dayan biyu na rasa na dauka a tsakanin tafiyar da kuma fasa zuwan. Daker na samu na yaki fushi na kawar da komai na tari napep na shiga, domin gaskiya Hajita ta fada idan ni ce a wannan halin Deen zai aikata fiye da haka domin ya ceto rayuwata, shin bana masa alkawarin zamu samu kudin ba? Mi zai hana na cika masa alwarinsa?
Kamar na shigo wata sabuwar duniyar haka na ji a lokacin da dan sahu ya shiga unguwarsu Abiey, kusan ko a mafarki na dade ban bi ta hanyar ba balle kuma a zahiri balle kuma yanzu da gidansu zan nufa kai tsaye, cikin wani irin yanayi da shi bana tsoro ba ba kuma na fargaba ya sauke ni a kofar gidan ta futulu suka haske kamar rana. Dari biyu na ciro na mika masa sannan na juya na nufi gate din, sai kuma na samu kaina da tsayuwa ina kallon gate din kamar matacciyar gawa, sau biyar ina kai hannu da zimmar na kwankwasa kofar sai na kasa daga karshe wata zuciyar tace min na juya na koma kar na aikata abun da nake da niya. Haka kuwa aika yi sai na juya na fara sauri da zimmar barin gurin.

%??mahra ba zaki iya ba, wannan ce kadai damarki ta karshe kuma damar da zaki iya ceton Deen%???

Wata zuciyar da nake kyautata zaton sahibar zuciyace mai son Deen ta tunatar da ni abun da nake kokarin mantawa. Sai kuma na juyo na dawo na kai hannu na kwankwasa gate din, kamar mai gadin gate din jira yake na kwankwasa sai gashi ya bude da kuzarinsa bayan ya leko ta karamar kofar ya ga mai buga gate din.

%??ma nake gani kamar Zahra...%???

Almu ya fada yana kara tantance ni, domin ya san ni farin sani ni ma kuma na san shi a lokacin da gidan yake min dadin zuwa.

%??mi ce ina wuni%???

%??mllahu Akbar, Zahra rai kan ga rai?%???

%??mmmy tana ciki?%???

Na tambaya Ammy amaimakon Abiey, domin damuwata ba zata bar ni na iya tsayawa amsa masa ba.

%??mmmy ta fita tun rana, amman Abiey yana cikin gidan Yasmin ma tana ciki%???

%??maushe zata dawo%???

Na tambaya numfashina na rawa jin ya ambaci Abiey.

%??moh Wallahi ban sani ba, amman dai tun rana ta fita, ba zaki shiga ciki ba%???

Ya fada yana kallon yanayi domin ya fahimci akwai damuwa a tare da ni.

%??ma dai zaka taimaka ka tambaya min yaushe zata dawo sai na jirata%???

%??moh Zahra kin san manyan nan ba son takura suke ba, ni ban aiketa ba zan ce yaushe zata dawo? Sai dai ko nace ke kika tambaya?%???

Na daga masa kai zuciyata na bugawa fiye da kima.

%??moh shigo ciki mana kika tsaya kamar bakuwa%???

Na kusan second ashiri ina deciding tsakanin shiga da kuma tsayawa, kamin na mika kafa na shiga cikin gidan har lokacin wani bangaren fada min yake be dace na aikata haka ba. Dakin mai gadi ya nufa daman a iya sanina a can telephone take idan za a kira cikin gidan, sai dai masu gadin da masu aikin da na gani suka baki ne ba wadanda na sani ba. Ya dan jima a ciki sannan ya fito yana sanar da ni cewar ba a dauki wayar ba.

%??ma dai kin daure kin shiga ciki inya so sai ki jirata%???

Da gangan na ki na musa masa domin ba a gurin Ammy na zo ba a gurin Abiey. Ban ce masa komai ba na fara takawa zuwa inda main door din take, katon gidan yana nan da kyaunsa da ado kamar yadda na sanshi, sai dau an sabunta fenti kamar yadda aka saba duk bayan wata biyar. Sai da na fara taka entrance din na ji zuciyata ta yi min wani irin nauyi kamar ba tawa ba, yawu na hade yafi a kirga sannan na cika kafar da nake jin ta yi min nauyi sosai na doshi kofar, sai kuma na samu kaina da matse hannu na rumtse ido ina jin kamar idan na bude wani mugun abu zan gani, kamar na juyo na dawo sai na ji ba zan iya ba.

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un%???

Shi ne abun da na furta sannan na bude ido ina jin kamar na dan samu kwarin guiwa na kai hannu na murda kofar falon na nasa kafata sai na arba da abun da na fi tsana, idonsa ya sauka a cikin nawa a take mug din dake hannunsa ya subuce ya fadi kasa, kallo daya na yi masa na dauke kaina domin bakin maciji zai fi min sha'awar kallo fiye da Abiey. Kamar wanda aka dasa haka na tsaya rike da kofar ni ban shigo ba ni ban koma ba har sai da Yasmin ta kira sunana.

%??mahra%???

Na kalleta sai dai ban amsa mata ba na shigo cikin falon na tsaya, Yasmin ta karaso kusa ni, ni kuma na kasa furta komai kuma na kasa juya na fita, a lokacin ne sai kuma ya koma min kamar mafarki.

%??maman...daman.... %???

Sai na kasa furta komai, hawaye suka wanke min fuska. Da sauri Abiey ya juya ya ba ni baya,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login