Showing 189001 words to 192000 words out of 210919 words

Chapter 64 - CIWON SO

10 Oct 2024

4216

yayan sarakuna ba ma zaban matan aure, sai dai a zaba mana wannan ce kaddarata ta farko da, rabon a same ka ya kashe mijinta ya mallaka min ita, kamin mai faruwa ta faru mu kasance a haka a yanzu, wannan ya saka a lokacin da Lami ta shigo min da labarin abun da aka ce ka aikata, amaimakon raina ya bace sai na ji tausayi, ka rasa abubuwa da yawa da suke saka ka farinciki, na kudirta a raina idan har da haske ne ka aikata haka, zan maka uzuri domin idan na matsa maka ban san abun da zai biyo baya ba, indai kana son matarka mu masu yi maka marhabun ne, tunanin Babba be taba zama irin an yaro ba, babban dole ne ya kasance ta mai hakuri da kawar da kai kuma yin tunanin kamin yanke hukunci...%???

Abiey be san lokacin da ya rumgume mahaifinsa ya fashe da kuka kamar mace, lallai a yau ya tabbatar mai hakuri mawadaci ne, kuma kowa yayi hakuri ya ce be ci riba ba to kadan yayi, abubuwa biyu masu matukar tsada a rayuwarsa sun zo masa a lokacin da be yi tsammani ba.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Mai Martaba ya dauke kai daga kallon tv da yake ya kalli Abiey da ya doso inda yake kadan sannan amsa sallamar cikin isa irin ta manya sarakun, sannan ya maida hankalinsa girin Tv ya cigaba da kallo, Abiey ya karasa kusa da shi ga zuba gafensa ya kwashi gaisuwa sannan ya sauke kai kasa be sake cewa komai ba.

%??mkwai wata matsala ne?%???

Abiey yayi fuskar tsoro da fargaba da kuma tausayi a lokacin daya, sannan ya fara magana murya can kasa cikin ladabi da tsantsan da kai.

%??mai Martaba kai uba a gurin kowa balle kuma a garemu, Ammy tana yawam fada min cewar na yi duk wani abu da zai saka ka kauna ce ni, domin na taso a cikin wata rayuwa da ban san dadinka ba, balle dadin zama da kai, ban isa na matsa a kusa da kai ba, ban iya na nunawa kai ubana ne a gaban jama'a ba, saboda tsanar da kake nuna min wanda ta banbanta ni dabam da sauran yayanka, soyayyar da kake min bata kai ta yayanka ba na sani, kuma ba tare da na maka laifin komai ba, domin Ammy bata fada min wani laifi da na aikata wanda ya saka ka tsane ni ba, ina tunanin tsanar ta darsu a zuciyarka ne, saboda Allah ya rubuta kaddarar kiyayyar mahaifi ba tare da hakki ba, na yadda wannan jarabawa ta ce, kuma ban isa na tsallake ta ba, ban isa na canja ta ba, da ace ina da iko na wanke zuciyarka ko kuma na canja kaina, na zo a matsayin wani yaro da mahaifinsa yake matukar kaunarsa%???

Mai martaba ya ake cup din hannunsa, cikin wani lafazi mai kama da na izza ya ce

%??mmaima ta zaunar da kai ta yi ta karanta maka karatukan banza ko? Shiyasa zuciyarka take raya abubuwa marasa kyau%???

%??mlif bata taba karanta min akanka, sai dai tana yawan fada min na yi hakuri da duk halin da zan samu kaina, kuma kar na yarda na butulce maka kar kuma na bata rananka%???

Mai Martaba ya yi masa alama ada zo da hannu, sai Abiey ya baro inda yake zaune ya dawo kusa da Mai Martaba ya zauna for the first time har jikinsa na gugan na Mai Martaba, Mai Martaba ya kalleshi ya sauke numfashi a hankali.

%??m cikin yayana babu wanda ya dauko ni a kamanin da siffa irinka, haka kuma ban taba haihuwa ??an na ji bana kaunarsa shi, sai dai son da nake yi ma wani ??an ko yar ya dara na wani, wannan kuma wani abu da Allah yake saka shi a zuciyar bawa, sai kuma yawan kyautatawa da yaya suke yi ta biyo baya dole ne zuciya ta fi kaunar mai kyautata mata, ba ayi wani ??a da zuciya take kauna take son kusanci da shi ba kamar kai Abiey, zancen bana sonka wannan wani abu ne na dabam da zuciyarka ta fahimta, na sha fadar maganar nan babu abun da zai fito a cikin Umaima na gagara sonsa balle kuma jinina, sai dai an haifo ka ka zo duniya a yanayin da ba haka na so ba, sai kuma aka yi min shamaki da yadda zan nuna maka kauna ko soyayya, a duk lokacin da zan yi unkurin haka sai na kasa%???

Mai Martaba yayi shiru kamar ba zai sake magana ba.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: %??mna yawan tunani, tun kana karami ko wane hali kake ciki? Me kake bukata? Amman bana iya yunkurawa na yi maka komai, cutar da kai da na yi na tsawon shekarun nan yana daga cikin abun da ya haifar min da hawan jinin da nake ganin zai iya ajalina a ko da yaushe, rayuwa zata dauwwama a guri daya Abiey idan ina raye a yau bana raye gobe, kuma idan ban nuna maka soyayya da kauna a dan wannan lokacin da ya rage mana yaushe zan nuna maka? Ba zan bari na mutu na koma ga Ubangijina ya tambaye kiwonka da ya bani ba na rasa bakin amsa masa, yaya suna da hakki akan iyaye kamar yadda iyaye suke da hakki a kan yayansu%???

Ya juyo ya kalli Abiey

%??ma ji dadin yadda Umaima ta tarbiyantar da kai, kuma ta nuna maka bin iyaye da amincewa da duk abin da suke so, wannan ya kwara min gwarin guiwar na shiga cikin rayuwarka na yi maka duk abun da ya dace%???

Abiey ya sauke ajiyar zuciya hawayen farinciki na sauko a idonsa.

%??manar yau ta zame min wata farar rana mai cike da tarin alheri da ban taba mafarkin zai zo ba, kalaman nan sai na ke jin kamar ba daga bakinka suke fitowa ba Mai Martaba, yau ni Aliyu ni nake zaune a kusa da kai kuma kai da bakinka kake fada min kana kauna ta, Allahu Akbar....!%???

Abiey ya kama hannayen Mai Martaba ya sumbanta.

%??mo a yau na mutu na cika burina, na samu soyayyar mahaifina%???

Mai Martaba ya shafa kansa.

%??mllah ya maka albarka, kuma ya sanya albarka a cikin aurenku ya saka abokiyar zamanka ce har aljanna%???

Da tsoro da mamaki Abiey ya kalli Mahaifinsa dake murmushi.

%??mai Martaba....Mai Martaba...Mai Martaba....%???

Sunansa kawai yake kira rudewa da tsabar farinciki ya kasa barinsa ya furta komai.

%??ma samu labari, ban jidadin abun da ka aikata ba, amman hakan ba zai saka saka ka aikata abun da shaida zai yi murna da faruwarsa ba, al'arshin Allah kuma ta girgiza saboda shi, ba a biyayye ga iyaye a tsabawa mahallinci, idan ban saka maka albarka ba zan tsine maka ne? Ka aikata boye ne saboda kana tsorona kuma a yanzu ka fuskance ka nemi yafiyata hakan ya faranta min rai sosai, baka fito kai tsaye ka nuna min kai sai ita zaka aura ba, wannan kadai ya isa ya saka na daga maka kafa, na cilasta aje kwallo kuma ka bi umarnin a lokacin da kake tsaka da kaunar sana'arka duniya take yayinka, bayan kuma baka girma a tare da ni ba, amma a haka ka godewa Allah ya ba ni ??a irinka Abeiy wannan ma wani abu ne abun alfahari%???

%??mmman a ina ka samu labarin nan Mai Martaba...? Akan wannan auren Ammy ta daga hankalinta tana ganin kamar zaka yi fushi da ni, tana ganin kamar zan lalata yar ga6ar da na samu zan lalata, ta jaddamin idan har ka zabi na rabu da Zahra to dole na rabu da ita ko kuwa hakan na nufin rasa rayuwata ne, kuma da gaske Mai Martaba da ace ka zabi rabani da yarinyar nan da ka rabani da duniyar nan gaba daya%???

%??mhiyasa na yi saurin fahintarka ??ana saboda na taba kasancewa a irin halin da na kasance a wani lokaci can ba, na kaunaci Mahaifiyarka irin kaunar da har yanzu babu wata mace da ta maye gurbinta a gurina, a wacan lokaci mu yayan sarakuna ba ma zaban matan aure, sai dai a zaba mana wannan ce kaddarata ta farko da, rabon a same ka ya kashe mijinta ya mallaka min ita, kamin mai faruwa ta faru mu kasance a haka a yanzu, wannan ya saka a lokacin da Lami ta shigo min da labarin abun da aka ce ka aikata, amaimakon raina ya bace sai na ji tausayi, ka rasa abubuwa da yawa da suke saka ka farinciki, na kudirta a raina idan har da haske ne ka aikata haka, zan maka uzuri domin idan na matsa maka ban san abun da zai biyo baya ba, indai kana son matarka mu masu yi maka marhabun ne, tunanin Babba be taba zama irin an yaro ba, babban dole ne ya kasance ta mai hakuri da kawar da kai kuma yin tunanin kamin yanke hukunci...%???

Abiey be san lokacin da ya rumgume mahaifinsa ya fashe da kuka kamar mace, lallai a yau ya tabbatar mai hakuri mawadaci ne, kuma kowa yayi hakuri ya ce be ci riba ba to kadan yayi, abubuwa biyu masu matukar tsada a rayuwarsa sun zo masa a lokacin da be yi tsammani ba.
12/28/22, 11:23 - Buhainat: 7??_/Q0??_/Q


Tun da na shiga falon ban yarda na kalli inda yake ba balle har mu hada ido, kaina an kasa har na zauna a kusa da kofar ba tare da na ce komai ba.

%??mahra na kira ki ne akan maganar yaronki, ke da Jamila dukanku ba ku yi tunani Mai Kyau ba kamin aikata abun, sai dai za a duba miki domin talauci da rashin mafita ne ya saka kika aikata, a yayinda ita kuma ta yi amfani da damar da take da shi ta aikata wannan laifi, wanda ya haifar mata da bakinciki a yanzu, ni ma kuma ya haifar min zai kuma haifarwa yan'uwana, kuma zai zame min abun magana a gari da dangi, abun da zai saka makiya na su jidadi su yi dariya, amman haka Allah ya kaddara ba mu sa mu zabi abun da zai faru da mu ba, kuma ba a mana ikon kawar da abun da bama so ba sai abunda Allah ya rubuta mana%???

Yanayin yadda yake magana akwai matukar tawakkali da tausayi, muryarsa har rawa take wata na hawa kan wata.

%??man aikata hakan saboda na cutar da daya daga cikinku ba, ban kuma yi tunanin nima hakan zai cutar da ni ba, idona ya rufe a lokacin da nake neman mafita akan rayuwar Deen, na manta da iyayensa, da kanwarsa da yan'uwansa, na siyar da Amir ba dan bana kaunarsa ba, sai dan ina ganin kamar hakan mafita ce a gareni, ina neman yafiyarki hakika mun cutar da kai na sani, kuma zaka iya daukar ko wane irin mataki amman baka dauka ba saboda hallaci irin naka%???

%??man hannata miki ??anki a hannunki, sai ki tanadi bayanin da zaki gabatar ma kakaninsa da zai wanke ki ke a gurinsu%???

Na dago na kalleshi idanuwana cike da kwalla.

%??mabu wani bayani da zan tana, abun da ya faru sirrina ne, babu wanda zai san da wannan sirrin har abada%???

%??man fahimci ki ba Zahra%???

%??mdan har akwai wanda ya cancanta ya rike Amir a yanzu to kai ne, yan'uwanka sun san Amir a matsayin ??anka, su kuma ba su san shi ba, ba su san dadinsa ba, amman kai kasan dadinsa domin ka rike shi na tsawon watanin a hannunka, duniya tana kallon Amir a matsayin ??anka abun tozarci ne a gareka a yanzu labarin nan ya fita cewar yaron da kake ikirarin naka ne an gano ba ??anka ba ne, nasadin haka labarinka da nawa da kuma na matarka zai fita, wata kila har ya janyo maka wata matsalar, idan har zaka rike Amir tsakani da Allah kamar ??anka da ka haifa, ni kuwa zan bar maka shi kuma ba zan tana siffanta kaina a matsayin uwarsa ba haka ba zai san wani a matsayin ubansa ba sai kai, wannan sirrin zai cigaba da rufuwa har kasa ta rufe idona%???

Baki sake yake kallona, kamin ya girgiza min kai.

%??marki yarda ki sake aikata wani abun ba tare da neman shawara ba, ina tunanin yana daga cikin abun da ya haifar min da matsalar da kike ciki a yanzu, kuma idan mu ka yi haka kamar kin cutar da kakanin yaron nan ne, domin su ma suna da hakki akan dansu, kuma idan ban manta ba a cikin labarin da kika ba ni kin fada min cewar su biyu kawai ta haifa a yanzu kuma ya rasu, na tabbatar da ace ta san da cewar jikanta yana raye ba za ta bar ki da shi ba%???

%??mmman kai kuma fa?%???

Ajiyar zuciya ya sauke ya kishingida jikin kujerar da yake zaune, yana kokarin magana sai ga Ummiter ta shigo hankali a tashi jikinta har rawa yake.

%??maya ban ga Amir ba, na duba a dakinsa ban ganshi ba%???

Mr Bashir ne ya riga ni zabura ya mike tsaye.

%??mhat...! Kin duba da kyau kuwa?%???

A lokacin ni ma na mike tsaye ina kallon Ummiter hankalina a tashe.

%??mallahi na duba ko'ina a dakin ban ganshi ba!%???

%??min duba dakin Jamila%???

%??ma ban duba ba%???

A gaba daya muka dugunzuma muka fice zuwa bangaren Jamila, da wani kalar sauri mai kamar gudu na bi bayan Mr Bashir na shiga dakin Jamila, sai muka sameta kwance a kasa rumgume da Amir tana rusar kuka, gaba daya ta hargitsa dakin ta watse tufafinta kamar dakin mahaukaciya. Mr Bashir ya karasa kusa da ita da sauri ya saka hannu ya dauki Amir.

%??mkan me zaki dauki yaron mutane%???

Sai ta tashi da sauri ta rumgume kafarsa ta fashe da kuka.

%??ma yi hakuri dan Allah, ka yafe min mijina%???

%??mi ba mijinki ba ne a yanzu, kuma ki yi gaggauwar fice min daga gida tun kamin raina ya kara bace%???

Martanin da ya maida mata ne na fahimci cewar sakinta yayi, ban san yadda saki yake ba ba a taba domin ba a taba min ba, amman na ji babu dadi musamman yadda take ta kukan nan akwai matukar tausayi, kamar ta san tausayinta ne ya cika min zuciya sai ta juyo gurina tana rokona.

%??mahra ki yi hakuri, ki ce yayi hakuri ya yafe min%???

%??ma zan iya cigaba da zama dake ba Jamila, ko da na zauna da ke zuciyata ba zata sake natsuwa da ke ba, zan yi ta dubanki da wannan abun ne%???

Mr Bashir ya fada sannan ya miko min Amir.

%??ma danki, hakan kuma ba zai hana na kyautata miki kamar yadda na yi alkwari ba%???

Sai na tara hannu biyu na karba ina hawaye.

%??mkwai kyautatawar da ta wuce wannan ne? Ni ka gama min komai tun da ka zabi rufa min asiri a lokacin da nake tsoron bayyanarsa%???

Uffan be sake cewa ba ya dauke kai ya fice daga dakin. Ummiter kuma ta zo gabana ta tsaya tana kallon Amir ta kalleni

%??man ki rufa asiri karki fadawa kowa abun da ya faru, Saboda ba ma son sirrin nan ya fita, babban mutum kamar yayana ace haka ta faru da shi ba zamu jidadi ba%???
12/28/22, 11:23 - Buhainat: Ta juya hawaye na sauko mata ta fice daga dakin, sai ya rage daga ni sai Hajiya Jamila dake kuka ni kuma ina hawaye.

%??maninki be yi min rana ba Zahra, gashi yanzu zamanki a nan ya haifar min da ciwon da na dade ina tsoron ya kamani, da ace na san da zuwanki a gidan nan ba alheri ba ne, da na bar yaron nan a yadda yake ko kuwa idan ya sha nono mutuwa zai yi, da yanzu duk wannan be faru ba, da ban rabu da mijina ba, da yanzu asirina be tono ba, daman can kin ba ni dan ne ba da zuciya daya ba, shiyasa komai yake faruwa%???

%??maico yanzu duk abun nan da ya faru be isa ya saka ki nadama ba? Baki fahimci kin aikata kuskure ba balle har ki tuba? Sai neman kakabawa wani laifi kike? Ashe ke din ba abar tausayi ba ce, na yi kuskure da tausayinki ya darsu a zuciyata a yanzu, Wallahi kin cutar da mijinki kin haifar masa da bakinciki da damuwa marar misaltuwa kuma ya kamata ki gane haka%???

Kamin ta sake ce min komai na juyo na fito ??akin rumgume da Amir, har na iso BQ ban daina kallon ??ana ba ina shiga da shi dakin sai ya fara kuka sosai har wani fisga yake. Mama dake karyawa ta dago tana kallonmu.

%??mau kuma ta barki kin taho da ??an?%???

%??mama Amir ya rabu da Jamila da mijinta a yau, ya dawo a matsayin ??ana na asali, Mr Bashir ya mallaka min shi%???

A take Mama ta tsame hannunta a abincin da take ci ta mike tsaye.

%??miya faru?%???

%??ma saki Jamila, saboda ya gane gaskiya tun da dadewa amman ya saka mana ido ya ga iya gudun ruwan mu, ya tambayi labarina na fada masa komai na rayuwata sai ya biyo min da abun da na aikata, shi ya nemi na fasa auren Sauban indai saboda tsoron tonuwar asirina ne har ya bukaci aurena a yanzu kuma da komai ya faru, sai ya mallaka min ??ana kuma ya zabi rabuwa da matarsa%???

Mama ta saka hannu ta karbi Amir idonta na cika da hawaye.

%??mukunta ki zai yi kenan?%???

%??ma yace ba zai yi komai ba, domin abun kunya ne a gurinsa, Mama tausayinsa ya kama ni, ban ga wani mutum mai hakuri da kawaici irinsa ba, wata kila da zai yardar da karbi Amir a matsayin ??ansa ina da tabbacin zai rike shi amana%???

%??mu kuma iyayen Deen ki yi yaya da su?%???

%??ma su da Amir ba, na riga na sanar musu cewar ??an ya mutu, babu san dadinsa amman Mr Bashir ya saba da shi, kuma ya riga ya nunawa duniya Amir a matsayin ??ansa, idan Amir ya zauna tare da su zai samu rayuwa mai kyau ya kamu karatu da tarbiya, kuma na tabbatar idan ya girma ya san abun da na aikata ba zai jidadi ba, musamman idan suka nuna masa irin soyayyar da suka nunawa Deen wanda ta saka ya lalace ya zama ba shi da aiki sai shaye shaye da abokanan banza, wanda ya zama silar faruwar komai a yanzu. Mama

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login