Showing 114001 words to 117000 words out of 210919 words

Chapter 39 - CIWON SO

10 Oct 2024

4203

saka shi tausaya min, daman can kuma na san akwai tausayina a tare da shi.

%??man cire miki, amman zaki min alkawarin babu ruwanki da kowa dan Allah duk rashin da zaki yi ki yi amman ban da kula maza%???

%??moh ba zan yi ba, cire min%???

Na janye zanena na mike masa fafaren kafafuwana, ina jin motsin Mama na yi saurin janye kafafuwan domin fada take min idan ina sakin jiki a gaban Deen.

%??meeni ne?%???

%??mh Mama ya gida?%???

%??mafiya Kalau ina su Hajiya%???

%??muma suna lafiya, suna gaisheku%???

%??mna amsawa%???

%??mama na ce yanzu kam za a cirewa Zahra marin nan mu ga ko zata natsu %???

%??ma natsu ma Wallahi ba zan sake ba%???

%??mllah yasa%???

Mama ta fada sannan ta tashi ta dauko makullin ta bude min da kanta, wani tsalle na yi ina murna ina jindadi, Deen kallona kawai yake yana murmushi, a ranar na wuni cikin yanci sai dai haka be saka Mama ta bar ni na tafi ko kofar gida ba, washe gari ma Deen ya zo gidan daman kusan kullum yana gidan mu saboda ni, sai dai hakan be taba sakawa na ayyana a raina cewar so na yake ba, tunani be bani wannan ba. Da zai fita na bishi ina masa magiyar ya kai ni gidan Yaya Maryam.

%??mdan nace za tafi Mama ba zata bari ba, kuma idan muka tafi tare ma wani ba zai min magana ba%???

%??me ki fadawa Mama ki dauko Hijabinki%???

Da sauri na koma cikin na sanar da Mama sai tace ba zan bishi ba.

%??madda kike ganin idan kin keba wadanda zai miki fada yana nuna miki ba daidai ba ne, haka shi ma ba muharramin ki ba ne ya kamata ki san da wannan bana son shege masa da kike%???

%??mayyo Mama ina son zuwa dan Allah%???

%??mari sai ya tafi zan baki kudin napep ki tafi ke kadai%???

%??moh%???

Hakan da Mama ta yi ba karamin dadi yayi min ba, daman bana son da shi sai dole domin takura min yake idan muna tafiya a tare ko kallon maza na yi sai yayi ta min fada. Zuwa na yi na sanar masa cewar ba Mama ta hana ba zan tafi ba, sai ya shiga da kanshi yayi mata magana amman bata amince ba a dole ya ba ni hakuri yace na bari sai nan gaba kadan idan ta yardar zai tafi da ni. Sai da ya wuce na je na shirya Mama ta ba ni kudin Napep tana min nasihar cewar na natsu na daina abun da abun da nake.

%??mina kallona idan ana dukanki ko kasheki za ayi babu wanda zai ce ayi hakuri, shi kuma idan ya tashi dukan na ki be san yayi miki da sauki ba, ke kuma zaton kike dadi nake ji idan yana dukanki, ko baka son ??anka ai baka son ana dukanshi balle kuma kana kaunar abun ka, dan Allah ki zama mai jin magana Zahra%???

Tana rufe baki Baba ya shigo cikin gidan da sallama, ni da Mama muka amsa masa na karbi kayan hannunshi na kai daki sannan na fito na saka talkamina.

%??mna zata je?%???

%??midansu yayarta na aike ta ta karbo min sako%???

Mama ta fadi haka ne saboda ta kare ni, domin ta san Baba zai iya cewa ba zan je ba.

%??mmman dai kin san halin yarinyar nan, yaushe aka cire nata marin nan ma yanzu kuma zaki aiketa%???

%??maba to ai ba dade zan yi ba, kuma ka san ni marainiya ce Baba ya ba ku amana ta yace duk abun da nake so ayi min%???

Na fada cikin yanayin da ke nuna yana hana ni fitar zan saka masa kuka.

%??ma dadewarce matsalar ba, rashin jin maganar ne matsalarki, kuma ni babanki be bar min amanarki ba ban sani ba dai ko ya barwa Mamanki, hakan kuma ba zai hana idan kika yi laifi na hukuntaki ba ko na saka Yayanku ya hukunta ki%???

%??manzu ai na shiryu baba, ba zan sake yin komai ba%???

%??moh gamu gani ai, muna nan dake ba sai an yi nisa ba yarinyar nan zata je ta dauko mana abun magana%???

%??malam ayi ta mata fatan shiriya, abun da take ba dadi yake min ba kuma yara ne sai da addu'a%???

%??moh Allah ya shirya, zuba min ruwanka ki kai min bandaki kamin ki wuce kafar yawo%???

Na dauki bokitin wanka da sauri na cika shi da ruwa na kai masa bandaki sannan na fice gidan zuciyata fes, rabon da na ga kofar gidan yau kwana tara kenan, sai da na bi ta gidansu Hafsat muka fara shiriricewa a can sannan na fito na kama hanya, ina tafiya na ci karo da yara suna jan mahaukaci ni dai ba mahaukaciya ba ce balle na biye musu hakan kuma be hana mahaukacin biyo ni su suke jan shi amman ni yake bi, Mama ta fada min ba a yi ma mahaukaci gudu hakan yasa ban yi gudu ba duk kuwa da bina da yake sai dai na hade masa fuska saboda kar ya ga dama ta. Shuuuu na ji saukar bulala mai shegen zafi a bayana, wani tsalle na yi na fashe da kuka kamar na ce masa kara min sai ya kara auna min ta biyu har zuwa ta uku, duken da nake na yi cikinsa na kwashi kafafuwansa na mike tsaye sai gashi a kasa kamin ya tashi na yi hanzarin cire talkamina na kwada masa a kai sannan na juya na ranta a na kare, ina gudu yana bina ni, har muka iso gida da mugun gudu talkamina a hannu na shigo gidan ina fadin.

%??mahaukaci mahaukaci%???

Mama ta tsallake kwanon abincin da Baba ke ci ta fada ??aki da gudu ta rufe, ni ma dakin na nufa sai dai rufewar da Mama ta yi yasa dole na na shige bandaki daman ya fi kusa, na san Baba da nauyin jiki wata kila be yi hanzarin tashi da wuri ba ne ko kuma mahaukacin ya rike shi oho Allah kadai ya sani, ihunshi kawai na ji yana fadin.

%??ma dubi girman Allah Bawan Allah ka yi hakuri ban maka komai ba, ka dubi rahmar Allah ka yi hakuri ban maka komai, na tuba ka yi hakuri dan Allah wayyo jama'a a kawo agaji%???

Daker muryarsa take fita da dukan alama shakure wuyan Baba yayi ko kuma ya danne shi, daman mahaukacin irin manyan mazan nan ne masu kirar samudawa.

%??man Allah ka yi min rai, ni na jaka ba, Zahra ce ba ni ba ne ba a nan gidan ta shigo ba, kalli sama kalli sama gata a can sama tana maka magana, Zahra idan ba ki fito ba sai na halakaki, Malam ka dubi girman Allah ka tafi gata a can bandaki tana maka gwalo, Malam ba a nan ta shigo ba, na rantse da Allah da Al'kur'ane ban san ta, na rantse maka da Allah ban san ta ba, ba yar gidan nan ba ce, shiga uku zai kashe ni, ban maka komai ba, Zahra idan baki fito ba sai auren uwarki ya kare a gidan nan%???

Ina jin haka na rufe baki daman jikina mazari kawai yake, ruwan wanka da na kai ma Baba dazun kamin na fita na zubar na kife bokitin na daka na taura katangar bandakin daman bandakin mu irin wannan ne da baya da mufi a sama kuma gunin bashi da tsawo sosai domin irin na bayan gida ne dake tsakanin bayan gida da wani bayan gidan daga tsakiya an yi hanyar ruwa, ina hawan ginin na dire ta baya na auna da gudu na fita ta gaban wani gidan na fita ta wata hanyar, gidansu Abiey ya fi kusa hakan yasa ina fitowa kwararon na kwankwasa kofar gidan aka bude.

%??myoyo Zahra yaushe rabonki da gidan nan%???

Na watsawa Mai gadin harara na murguda masa baki na wuce cikin gidan kamar wata yar gidan, a bude na tarar da kofar falon sai na aje talkamin da suke hannuna a bakin kofar na shiga da sallama ina haki kana ganina kasan akwai abun da ya faru.

%??maraba da Autata oyoyo na yi missing dinki%???

Ammy ta ware min hannayenta sai na karasa kusa da ita na rumgume irin side hug din nan, sannan na zauna a kasa.

%??mmmy ya gidan%???

%??mafiya Kalau Zahra Aliyu yana ta damuna da nemanki, ya damu naje na duba masa ke%???

%??mmman baki je ba ai%???

%??mana son Mamanki ta ga laifina ai, kin ga zata ga kamar mu muke kara dora ki a hanya, kuma abun da yaron nan yayi min ban jidadinshi ba%???

%??mi yi hakuri Deen haka yake yana da saurin ido sosai, Ammy ina Aliyun?%???

%??mana garden yanzun ya gama matsa min Kafafuwana dake ciwo%???

Na tashi na fice daga falon ba dan na san inda Garden din take ba, sai dan na san abun da ake kira da haka, gurin da nake hango itace na nufa ina shiga na same shi yana waya a daya daga cikin kujerun da suke gurin na zauna ina kallonshi murmushi ne kwance a kyakkyawar fuskarsa gashi fari tass hanci kamar na ara masa idanuwansa da haske sosai gashin kansa ma yayi baki wulik ya kwanta gwanin sha'awa. Sai da ya gama wayar ya dube ni

%??mana da kyau Abiey%???

Na fada masa a bakin gaskiyata domin ko mace na gani mai kyau zan iya fada mata cewar tana da kyau domin ni a gurina fadar haka ba komai ba ne.

%??ma yi kyaunki?%???

%??molayata kake ko?%???

Ya daga min gira daya.

%??ma kike Zahra? Ina son Ammy taje ta duba min ke amman bata je ba, ta fada min tun tana cikin gidan nan mugun ya fara dukanki ko? Wallahi yayi sa'a da sai na hukunta shi ko dan abun da yayi miki da Ammy amman Ammy ta hanani daukar mataki%???

%??mar da mari ya saka min sai jiya aka cire min, bana zuwa ko'ina yayi min duka sosai%???

%??mari kuma? Wannan mutumen ba shi da kirki duk da dai ban taba ganinshi ba, son ki yake ne?%???

%??ma Wallahi, babu komai tsakanina da shi%???

%??mmman yanzu ba a sani ba kika zo gidan nan ko?%???

Na daga masa kai ina dariya idona ya kai gurin icen mangoro.

%??mbiey zaka ciro min mangoro daya%???

Na kalleshi ashe kallona yake har lokaci be kuma dauke idonsa.

%??miye?%???

%??mallonki dadi yake min silly girl, babu ruwanki yadda ta nuna miki haka kike yi i like your style%???

Na rufe fuskata ina dariya na dade a haka kamin na bude idon still idonsa na kai.

%??mina da saurin sabo da mutane Zahra, shiyasa mutane suke binki shi kuma wannan mahaukacin yake ta hauka%???

Kalmar mahaukaci da ya fada ta saka na tuna da mahaukacin da ya biyo ni yanzu, sai na kyalkyale da dariya ba bashi labari shi ma dariyar yayi sosai.

%??min ja masa kamar yadda kika min, har mafarki sai da na yi bayan na dawo fa%???

Na cize baki ina kallonsa.

%??mbiey ka cire min mangoro daya mana%???

Wannan karon a shagwabe na yi maganar ina son masa kuka.

%??mkay bari na dauko abun cirewar, ko na kira Haruna mai aiki ya cire miki saboda akwai zuma a gurin sai an yi a hankali%???

Ya tashi ya fita daga gurin, ni kuma sai zuciyata ta kwadaita min son ganin zumar, sai ko na tashi na karasa gurin icen na daga kai sama ina kallon, katon gidan zuma na gani a gurin.

%??maaaa%???

Na fada ina mamaki ashe haka take yin katon guri, kuma Mama ta taba fada min cewar idan aka taba ta tana bin mutane, domin na tabbatar da gaske ne ko karya na dauki katon dutse na jefa mata be kai gurin ba ya fadi sai na sake dauka na sake jefawa haka na yi ta yi har sai da na same ta, aiko sai ta yi runduna ta nufo ni kuma na auna da gudu na fice Garden din amman zumar nan da karfi hali bata fasa bina ba, da gudu na shiga falon Ammy ina fadin


%??muma zuma zuma...%???

Abiey dake tsaye ya fadi kwance kamar wanda ya ga yan bindiga, Ammy kuma dake complain din ciwon kafa sai ga ta tsalleke Abiey ta haye stairs da gudunta tabur tabur domin mace ce mai jiki, ta banko kofar dakin gam.... Ni kuma na nufi kitchen da sauri na rufe aka bar Abiey shi kadai a falon, tab na kunna na jike jikina da ruwa na cire hijab dina na fara korar sauran zumar da ta biyo ni sannan na nufi kofar baya na bude na fice da gudu.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Gurin Haruna mai gadin na tafi shi ya karasa korar min zumar sannan na fita babu ko talkami a kafata haka na na tari abun hawa na hau na fada masa gurin da zai kai ni.

%??mmman lafiya kafarki ba talkami kuma ba ki yi kama da masu tabin hankali ba%???

%??mallahi zuma na jefa ta biyo ni sai na bar talkamin a can%???

Dariya ya fara yi, shi da mutumen dake cikin napep din da alama shi ma guri daya za a kai mu.

%??mhiyasa kika jika kayan? Daman kyakkyawan mata basa jin magana kina daya daga cikinsu da alama%???

Mutumen ya fada sai na yi dariya na rufe fuskata, muna kai wa kusa da wani shago ya bukaci mai nepep din ya tsaya sai ya kalleni.

%??mize nawa kike sakawa?%???

%???37%???

Ya fita, be dade ba sai gashi ya dawo da wasu talkamin roba masu kyau ya mika min na karba cikin jindadi da murna na saka ina masa godiya, daidai kofar gidansu Yaya Maryam aka sauke ni sai ya karbi number wayar Mama da nufin zai kira ni ni kuma na fita na shige cikin gidan, ina shiga na samu Mijinta a waje suna cin abinci tare.

%??myeee masoya%???

%??mismillahi yanzu zaki dagula mana lissafi%???

Mijinta ya fada sai na saka dariya na nufi kitchen dinta na dauki plate na zuba abinci.

%??muta kin samu yanci? Ina kika fito da jikanken tufafi?%???

Ban fada mata ba saboda ina tsoron kar taje ta fadawa Mama wata rana, bayan na gama cin abincin mijin Yaya Maryam ya ara min wayarsa na yi ta game har sai da na gaji. Da yamma ba yi sallama da gidan na mijinta ya bani kudin napep bayan na sato mata sabuwar atamfar da bata saka na boyeta a hijab na fito kamar ban dauki komai ba. Idan na yi laifi bana tafi gida kai tsaye musamman idan na san Mama ko Baba na yi ma laifin na kan saka Deen agaba ne domin yana hana Mama dukana, idan har ya saka hannu ya dake ni to abun da ya shafi samari ne, ban tafi gidan kai tsaye ba sai na nufi gidan Hajiya. Ko da na shiga na tarar Hajiya ta gama soya kaji tana kasawa.

%??maa mu kan Baba be kai mana ba%???

Shi ne abun da na fara fada farkon shigata gidan, ko sallama ban yi ba daman tun daga zauren gidan nake jiyo kamshi.

%??mi ma ba kawo min Yaya ba, Yayana ya aiko min da abuna Wallahi, na san halinki zaki iya tafiya ki fada mata cewar an kawo mana nama ki hada fada%???

%??me ma Hajiya ai kin san sai na fada Wallahi%???

%??mo ko Wallahi ba zan yi kashin nan dake ba, ba ke dai ba kya jin magana ba, to ai sai ki yi mu gani%???

Ban dauka da gaske Hajiya take ba har sai da ta kasa naman ta bawa Bahijja nata na Deen kuma tace a kai masa dakinshi ta dauke nata ta shige daki. Abun ka da marar zuciya kuma kwadayayyina haka na je na zauna gindin murhun nan ina lasar tukunyar data soya kazar da ita.

%??mahra me kike nan%???

Deen da fitowarshi kenan daga wanka ya tambaya, juyowa na yi na kalleshi sai na yi dariya ina kallon kirjinsa dake kara fitarta mazantakansa wato Muscle, a zatonsa wani bangaren na jikinsa nake kallo domin yana daure da tawul ne, a take ya hade fuska.

%??miye haka Zahra? Me ke damunki ne?%???

%??mikinka nake kallo fa na ga irin na masu daukar karfi ne%???

Ya kalli jikin nasa sannan ya sake kallona.

%??ma aka yi kika fito? Ba Mama tace karki fita ba?%???

%??ma bata hakuri ne sai tace na tafi, kuma a hanyata ta tafi na ga mahaukaci ya bini shi ne nake son ka rakani gida%???

%??mo tashi a nan%???

%??mai nake lasa, Hajiya bata ba ni ko tsinke daya ba wai saboda na ce sai na fadawa Mama an siya mata nama%???

Dakin Hajiya ya nufa ya dage labulen ya leka.

%??majiya ina nama na?%???

%??mana dakinka%???

Ta amsa mishi tana cin naman, sai ya saki labulen ya juyo ya kalleni.

%??me ki dauki nawa ki ci%???

Na mike da sauri na nufi dakin na dauki na san inda ake aje masa abu sai na nufi gurin na dauki kwanon naman na hado da wata yar karamar leda dake gurin, sai da na fito sannan ya shiga ya shirya ni kuma na saka naman a gaba ina ta ci na boye ledar da na dauko ina lalabawa na ji abu mai kamar haki a ciki. Hajiya na fitowa ta same ni ina cin naman sai ta fara fada wai shi yake daure min ina kara lalacewa.

%??maba Hajiya ya za'ayi ki bani nama Zahra tana gidan nan kuma ki yi tsammanin zan iya cinsa na hanata? Ai kara ki bata abu ki hana ni da ki ba ni ki hanata, bana son abun da zai taba yarinyar nan Wallahi%???

Shi ne abun da Deen ya amsawa Hajiya da shi, sai ta bude wani sabon babin na fada

%??mo yayi kyau sai ka cigaba da yi ai, gashi nan sai kara lalacewa take kuna goya mata baya%???

Yana ganin na bata fuska zan yi kuka yayi hanzarin janyo kofar dakinsa ya rufe.

%??mashi muje%???

Haka na fito da robar naman sai da muka kawo zaure ya cire dankwalin kaina ya goge min bakina ya gyara min fuskata.

%??maya Deen ka siya min lemu dan Allah idan na je gida zan fi jindadin cin nama%???

Ya amsa min da kai fuskarsa babu yabo ba fallasa daman can be fiye dariya ba, na bude naman na ci na mika masa ragowar.

%??ma ci wannan%???

%??ma ni na bakinki%???

Ya fada yana kallon yadda nake tauna naman a bakina dariya na fara yi domin ban dauka da gaske yake ba, har sai da ya kai hannunshi cikin bakin nawa ya ciro naman ya saka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login