Showing 9001 words to 12000 words out of 210919 words

Chapter 4 - CIWON SO

10 Oct 2024

4236

baki ta yi murmushi sannan ta daga.

%??mna fatar karata aka kawo miki%???

%??me kawo min kararki ba, amman dai ya zo min abun tausayi, Ammy danki yana cikin tsananin damuwa, yana bukatar taimako na addu'a da kuma kalamai masu kwantar da hankali, kar halin da yake ciki ya jefashi cikin wata rayuwa wanda mu da ke duka mu kasa cetonsa, ki dage da addu'a ki yi duk abun da zaki yi na ganin mahaifinsa ya shirya da shi, sannan ki natsu ki samo masa wata yarinya wanda hankalinsa zai kwanta da ita su yi rayuwar aure ko da ba zai so ta kamar Zahra ba%???

%??mddu'a ina kan yi kullum Hajiya Uwani, babu dare da bana kaiwa Allah kuka akan dana, amman Inshallah zan kara dagewa zan yi duk abun da ya kamata na gode sosai%???

%??mllah ya taimaka, mu ma zamu kara yi Inshallah Allah ya yaye masa danuwarsa%???

%??mmin Hajiya uwani%???

Wannan karon da damuwa Ammy ta sauke wayar sai ta kurawa hoton Abiey dake gaban wayarta ido.

%??mllah sarki Autana%???

Motsin takowa upstairs suka ji, daga ita har Dr Zainab kofar shigowa bedroom din suka kalla, sai ya turo kofar dakin ya shigo tare da kamshinsa, ko kadan be kalli inda Dr take zaune ba, sai mahaifiyarsa yake kallo har ya karasa cikin dakin ya zauna kusa da ita.

%??mbiey...%???

Dr Zainab ta kira sunansa da muryar kuka hawaye na sauko mata, bnza ya mata kamar baya cikin dakin.

%??me zan maka na gyara kuskuren da na yi?%???

Sai a lokacin ya kalli gefenta.

%??mabu kin riga kin bata komai, kin gama komai kin yi kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba, na rasa Zahra to me zaki yi yanzu? Kin riga kin shafa min bakin fenti da ba zai taba goguwa ba, Zahra ta auri mutum da br dace da zama mijinta ba, ni kuma tana min kallon wanda ya kasa taimakon ya kasa yi mata rumfa ya zame mata inuwa a lokacin da take cikin rana, ta auri wacan banzan mashayin tana kallonsa a matsayin mai gaskiya, duk abun da abun da ya faru ke kika ja Dr%???

Ya karasa yana kallon fuskarta, ko kadan baya jin tausayin hawayen da take zubarwa.

%??mainab ta aikata abun da ya dace ta aikata a lokacin, amman so ya rufe maka ido taya kake ganin zata bada rayuwar mijinta saboda Zahra? Ka auna kanka a matsayin yadda kake son Zahra da kuma yadda ita ma take son mijinta, miyasa baka dora abun a mizani na hankali da yardar da kaddara ba? Ta ya kake iya gusar da farincikin wani saboda ka samu farincikinka Aliyu?%???

Ya kalli Ammy.

%??ma yadda Deen ya gusar da farinciki saboda ya samu nasa farincikin, ta yadda Dr ta gusar da farinciki saboda ta samu nata farincikin%???

Dr Zainab ta sauko daga saman kujera da take zaune ta zauna kasa kamar mai neman gafara.

%??mallahi ban san son da kake yi ma Zahra ya kai haka ba Abiey, da na san da cewa bayan ka rasa Zahra zaka shiga wani hali, da babu abun da zai hana na salwantar da rayuwar mijina na baka farinciki, ana canja miji Abiey amman ba a canja dan'uwa, wata kila yadda abun nan ya dame ni kai kanka be dame ka haka ba, kawai bana fada ne saboda ko na fada ba zaka yarda da ni ba, I'm so sorry Abiey%???


Ta karasa tana fashewa da kuka, lumshe ido yayi ya hade yawu.

%??muk wata yar'uwa da zata so ka a duniyar nan Aliyu tana bayan Zainab ne, haka duk wata uwa da zata so ka bata kai uwar da ta dauki cikinka ta yi nakudarka ta haife ka ba, kai ne dana na hudu, amman yadda nake nuna maka kauna da kulawa bana nunawa saurana, ka samu gata da soyayyah ta ko'ina sai dan ka rasa Zahra zaka kasa hakuri, Yanzu da ace ni Allah ya dauke ya bar maka Zahra fa? Yarinyar da ta hadu da kana kana sa hakora talatin da biyu? Haba Aliyu kana ganin dadi muke ji a halin da kake ciki? A maimakon ka kwantar da hankali muma mu samu natsuwa sai nemi daga mana hankali ka bata mana rai? Ni fa mahaifiyarka ce, wannan kuma yar'uwarka ce%???

Ya sauke ajiyar zuciya da karfi ya sauke kansa kasa, gaba daya jikinsa yayi sanyi da kalaman da Ammy ta yi masa, ta wani bangaren tana da gaskiya sai dai wani lokacin son Zahra kan rufe masa ido ya kasa ganin komai...




ZAHRA POV.

A tare muka ci naman da ya siyo mana, sannan muka sha ice cream kana muka tashi muka gabatar da Allah isha'i a tare. Bayan mun gama ya dauko min kayan bachina na saka shi ma ya saka fajamas dinsa sannan ya fita ta rufe mana gida, dawo muka haye gado muka kwanta sai ya kunna wayarsa ya shiga YouTube ya kunna mana wani american film mai kyau, Tun muna kallon tare har bachi ya fara daukata, gyara min kwanciyata yayi a jikinsa sannan ya tofe ni da addu'o'i. Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai safe.
Bayan mun gama sallah asuba ya na dauko alkur'ane na saka a gabana ina karantawa, sai ya kwanta kusa da ni yana lazimi.

%??mna kwana%???

Na fada bayan na gama karantun na mana addu'a, sai da ya sumbanci goshina sannan ya amsa min fuskarsa da murmushi kamar kullum.

%??mood Morning My Love kin tashi lafiya ya baby na%???

Ya shafa cikina, sai na kwanto jikinsa cikin shagwaba.

%??maby kan yau gurin Hajiya take son zuwa%???

%??ma ayi hakuri sai wani lokacin%???

Na kara bata fuska.

%??ma san fa mun dade ba mu tafi ba, ina dai ina marmarin Hajiya gaskiya%???

%??mhikenan, zamu je anjima%???

Na fara masa kukan shagwaba, saboda na san idan muka je tare ba dade zamu yi ba.

%??ma gaskiya ni kadai zan tafi idan dare yayi sai kaje ka dauko ni%???

Ya fada kafadunsa.

%??muk yadda kike so Babyna%???

Na yi murmushi, sannan ya dauke kur'anen ya aje ya rika ni na tashi zauna zuwa bakin gado, da taimakonsa na hau saman gadon na kwanta ya lullube ni ban farka ba sai 9:14am ko da na bude ido ya gama gada mana abun da zamu karya kuma ya share ko'ina na gidan ya wanke kayan da muka bata jiya ya goge dakin da falo komai sam kamar mace, dakina sai kamshin turaren wuta yake na burna da ya kunna.

%??meen%???

Na kira sunansa, sai ya aje wayar da yake game da ita ya shigo dakin.

%??meeeee Babe ta farka%???

Na yi dariya.

%??mannu da aiki Allah ya maka albarka%???

Yayi murmushi ya saka kansa tsakanin kirjina yana wasa da su.

%??mood morning mine...%???

Na yi dariya mai sauti na kai hannu na shafa kansa sai ya dago ya kalleni.

%??mahra wai wane bokan kika bawa sunana ne? Kullum safiya ta Allah sai na ji kaunarki ta yau ta fi ta jiya miyen sirrin fada min nima na mallakeki na huta%???

Dayan hannuna na kai ya kama lips dinsa na ja har sai da yayi kara.

%??mirrin yana cikin nan%???

Yayi murmushi mai sauti, ya hau saman gadon ya rumgume ni. Ko da sha daya ta yi har na shirya abun ka da mai neman kuka hausawa suka ce an fada masa mutuwa, daman can ni yawo a jinina yake tun kamin na yi aure da zarar safiya ta waye na bar gidan kenan sai kuma dare, babu irin dukan sa ba amin da horo amman bana dainawa akan yawo, har suka gaji suka saka min ido.
Kayan makeup ya dauko ya shafa min hoda yayi min simple makeup da dan man lefe, I'm professional makeup artist kayan yasa bana rasa kayan kwaliya a gida duk da kasancewar ya hana ni yin sana'ar yanzu, amman shi ma ta masa amfanin domin gashi ya koya har yana min.

%??min yi kyau, amman kin san nikab zaki saka ko? Idan kin je gidan Mama sai ki cire%???

%??ma gidan Mama zanje ba fa, gurin Hajiya%???

Na fada da sauri domin ko kadan bana son tafiya gurin mahaifiyara saboda ba na jituwa da ita, abu ne mai wahala na zauna a gidan na awa daya bata min fada ba, amman uwar mijina ko hararata ba zata bari ayi ba, idan ta gan ni kamar ta hade ni.

%??ma sani, amman dole ai zaki fara zuwa gidan Mama ki gaishe ta tukuna ki wuce gidan Hajiya bayan magariba zan zo na dauke ki%???

%??ma da isha'i dai%???

Na fada ina kanne kafada daya.

%??ma ji, amman yanzu tare zamu je na sauke ki gurin Mama, i just want you make sure babu abun da ya same ki%???

%??ma yarda%???

Hijab ya dauko ya saka min ya daura min nikab, sannan shi ma ya cire tawul din jikinsa ya saka shadda. A tare muka fito cikin gidan yana rike da hannuna, har muka isa babban titin da zamu samu abun hawa, soyayyar mu akun kwatancen kuma abun burgewa domin mijina baya jin kunyar nunawa duniya cewar yana kaunata, kamar yadda ni ma bana shayin nunawa duniya komai akan mijina. Napep din farko da muka tara akwai mace daya ciki kuma da alama budurwa domin yanayinta da shigarta ya nuna haka gashi sai kallon mijina take.

%??mi dai ba zan shiga wannan ba, yarinya sai kallonka take kamar mayya%???

Daga mai napep din har yarinyar kallona suka yi, Deen ya kalleta ya kalleni ya kalli mai napep

%??malam dan Allah yi hakuri ka wuce%???

Uffan mai napep din be ce bayan dariya da yayi yarinyar kuma sai hararata take kamar ta ga kishiyar uwarta.

%??ma kalleni ta ga me? Yadda ta ga na rike hannunki ai ta san ni mijin tace ne%???

%??ma ga kyau mana, ga ka fari ga kyau ga iya wanka%???

Yayi murmushi.

%??ma kamata na sama rigar da aka rubuta mijin Zahra ita kadai na saka na rika yawo da ita a gari, so that duk macen da ta gan ni ta san ni mijinki ne zata kauce%???

%??man siya maka ma%???

Na fada ina dariya. Haka dai muka yi ta hira, sannan muka samu napep ta daukemu mu kadai zuwa jan bulo. Bayan ya sallami mai napep din ya fara shiga cikin gidan na bishi a baya, daman dan gida ne kusan ma sai na ce ya fi ni gata a gidan. Mama na ganinsa ta aika aka siyo masa lemun kwalba da ruwan sanyi nima sai na ci albarkacinsa aka ba ni, ba mu yi awa daya da zama ba ya ce zai tashi sai Mama ta kalleni.

%??mashi ki bi mijinki, ba za ki zauna kina saka min kabli da ba'adi na abun da zan yi da wanda ba zan yi ba a gida%???

%??maba Mama sai ki yi da takura mata shiyasa bata son zuwa gidan nan, ace mutum da gidansu amman ba shi da ikon sakewa%???

Deen ya fada yana kallon yadda na bata rai.

%??ma nan ai gidana ne, gidancan na can gurinka ba yadda zata hanani shakatawa%???

%??mi daman ba nan gidan zan zo ba, kuskure aka samu%???

Na fada ina turo baki, sai jin na yi ta buge min bakin.

%??ma zaki daina wannan ture turen bakin ba? Tun kina gidan nan na hanaki wannan abun wato ba zaki daina ba ko Zahra%???

Kuka ne kawai Deen be yi ba, kana kallon fuskarsa kasan be jidadi ba.

%??mama zamu tafi%???

%??ma dai yafi da wannan abun haushi ba dan cikin nan ba sai na sa yayanta ya zaneta yau Wallahi%???

Shi ya riga fada ni na riga mikewa tsaye daman nikab kawai na cire a take na daura abuna na nufi kofa, shi kuma ya saka hannu aljihu ya ciro kudi ya aje mata.

%??mllah ya maka albarka ke kuma Allah ya shiryarki ya sa ki yi hankali ki gane kin girma, har yanzu tana nan da rashin iya girkin ko?%???

%??ma da zamu fito ma ita ta girka%???

Yana rufe baki na yi karaf na ce.

%??mallahi Mama ban iya ba, kullum shi yake yi, ai dai gidan mijina ne ba nan ba balle ki ce zaki doke ni da girmana%???

Wannan karon dariya ta yi ta girgiza kai, Deen ma murmushi yake sai da muka fito sannan ya rika hannuna muka kama hanyar titi. Muna shiga napep bata sauke mu ko'ina ba sai rijiyar zaki gidan surukaina. Da gudu na fada cikin gidan ina jin kamar an biya min makka ita ma ta fito da sauri ta rumgume ni.

%??myoyo 'yata%???

Bahijja ce ta firo tana hararata.

%??mi fa yau mun shiga uku, tun da ta zo ba zan sake sakewa ba a gidan nan%???

Na mata gwalo, tabbas idan na zo gidan bata da hutu komai nake so ita Hajiya take sakawa ta yi min abinci ma sai wanda nake so ake girkawa. Bayan mun shiga daki ya shigo ya gaisa da mahaifiyarsa a lokacin ba hijab ba har riga na cire na ja zanen na zuwa saman kirjina na haye gadon Hajiya ya kwanta, be wuce minti talatin ba yayi mana sallama ya fita da niyar anjima zai dawo ya dauke ni. A gidan na wuni, da rana Hajiya ta min kwadon kanzo da zogale na ci, da yamma ta siyo min cornflakes na sha da dare kuma ta yi min tuwon shimkafa da miyar ganye na ci iya cina har sai da na rasa gurin numfashi. Ina gama sallah isha'i na shirya na fito waje kasancewar an dauke nepa, kuma ba gidan masu abun duniya ba ne balle a kunna min engine, na zauna kan tabarmar da Hajiya take zaune na dora kaina a cinyarta.

%??majiya solar ku ta lalace?%???

%??mh Wallahi aikin Bahijja ne, kin san komai ita nata sai ta yi shi da hauka%???

Dariya na yi Bahijja ma dariya ta yi.

%??majiya dan kin ga Zahra kike min wulakanci?%???

%??mo ga yata me zan yi da ke?%???

%??mhmmm Hajiya fada mata dai...%???

Na fada ina hamma. Shiru shiru har goma na dare Deen be zo ba, hakan yasa na kira shi a karamar wayata, be daga ba.

%??me daga kiran ba%???

Na fada ina Kallon Hajiya, sai ta dan kalleni ta dauki wayarta ta kira shi ga mamaki na sai na ji tana magana da shi duk da kasancewar ba zan iya jin muryarsa ba, bayan ta sauke wayar ta kalleni.

%??mace wai ki kwana nan, dare yayi sosai kuma anyi fada a unguwarku wai police suna kame ba zai iya fitowa ba%???

Gabana ya fadi, domin a iya sanina Deen baya yarda na kwana a wani guri ba kusa da shi ba.

%??mmman miyasa be daga kirana ba?%???

%??mai yaje ya daga sai wayar ta tsinke, zai kira kuma sai na kirashi%???

Ban sake cewa komai ba, sai dai ina ta kallon wayata ina jiran kiransa ya shigo min domin mun saba idan har na kwana ba gida ba kamar idan tafiya ta kama zuwa wani gari to zai kira ni a waya mu yi hira, amman shiru be kira ni ba, yanayin Hajiya da Bahijja sai ya canja, sai dai ban ce musu komai ba suma kuma basu nuna min wata wani abu ba, sai dai ni na karanci damuwar dake fuskarsu wanda suke kokarin boyewa.

Washe gari bayan Hajiya ta yi min tea kuma ta dumamamin tuwon jiya, ga koko da kosai da ta saka aka siyo min duk ni kadai, amman na kasa cin ko daya saboda ban ji muryar mijina ba, na kai hannu na dauki wayata na kira shi sai ga kiransa ya shigo.
10/1/22, 21:59 - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/IjtvyonRYfu5VBfSh4VRBX

*B??0? ?]Mq?? CIWON - SO B??0? ?]Mq??*

By Khadeeja Candy


5??_/Q


*For advert contact 08036126660*


%??mna ta jiran ka kira ni tun jiya baka kira ba, kuma ka san idan ban ji muryarka bana oya bachi%???

Na fada a shagwabe bayan na dauki wayarki. Sai yayi dariya

%??mabe ayi min afuwa%???

%??miyasa baka kira ni Deen%???

Na tambaya cike da damuwa domin na ji muryarsa ba a yanayin dana saba jinsa ba. Sai yayi kamar mai tunanin abun da zai fada min.

%??ma je kallon kallo ne sai hankalina ya dauke sosai kuma a lokacin da na dawo na san kin yi bachi so bana son na tashe ki%???

%??maka saba yi min karya ba Deen, kallon kallo a daren da kace police za su kame?%???

%??meah bayan mun dawo ne muka samu labari kuma a lokacin na san kin yi bachi shiyasa ban kira ba%???

%??mmman ni na kira ai, kuma na san kallon kwallo be tana hana ka kirana ba%???

%??mes lokacin wayar tana silent ban sani ba%???

%??mt the same time Hajiya ta kira ka kuma ka amsa?%???

Ajiyar zuciya na ji ya sauke, sai ya sassauta muryarsa.

%??mahra, can you trust me?%???

%??mes one thousand percent, but that doesn't mean to lie to me...%???

%??mabe na i don't want to hurt you%???

%??murt me like how?%???

%??mo ba zan ci komai ba sai ka fada min, haka zan wuni da yunwa%???

Na fada saboda na san shi ne tashin hankalinsa rashin cin abincina, ya san duk yadda na ke fushi bana fushi da abincin, kuma bana bakunta da abincin, idan har na ki cin abinci hakan na nufi damuwar tawa babba ce sosai.

%??merious bana da lafiya Zahra kuma bana son ki sani ne saboda kar hankalinki ya tashi?%???

%??me ke damunka?%???

%??miwon kai ne, tun da na aje ki na dawo kaina ke ciwo na sha magani yaki sauka, amman dai yanzu Alhamdulillah%???

%??mo dan bana kusa da kai ne%???

%??mamar kar mu rabu Babe na%???

%??ma ci wani abu?%???

%??meah na karya, kuma yanzu zan tafi asibiti%???

%??mllah ya baka lafiya Deen%???

%??mmin i love you%???

%??m love you more%???

Sai da ya sumbanci wayar na ji karar kiss dinsa sannan ya kashe, gaba daya sai jikina yayi sanyi domin komai na mijina ina daukarsa da muhimmanci, ko da kan akaifarsa ya ce yana masa ciwo zan ji kamar nawa ne. Haka na tasa kayan karyawa na saka a gabana na kasa taba komai, gaba daya na ji bana sha'awar cin komai.

%??mahra baki ci abincin ba? Ko wani abu kike so a dafa miki?%???

Na dago cike da damuwa na kalli Hajiya da shig???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?owarta kenan take min maganar tana rike da kofin koko da alama kanta ta zubawa.

%??majiya kin san Deen ba shi da lafiya kuma ba ki fada min ba%???

Wani irin dauke numfashi ta yi ta sauke ajiyar zuciya, a take idonta ya cika da kwalla, sai ta zo kusa da ni ta zauna ta aje kofin kokon.

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login