Showing 153001 words to 156000 words out of 210919 words

Chapter 52 - CIWON SO

10 Oct 2024

4260

kina da wanda zaki aura Allah yasa ban yi karanbani ba%???

Wannan karon da kamar zolaya yake maganar, ni kam tawa ma ta isheni yanzu ba zancen tashin gidan ko wulakancin Jamila ne a gabana ba, matsalar Sauban ce data kunno min take chaja min kwakwalwa a yanzu.

%??mahra kamar akwai damuwa sosai a tare da ke%???

%??ma komai%???

Na amsa ina saka hannu na share hawayena.

%??mi kwantar da hankalinki ba, zamu cigaba da zama nan na wani lokaci kawai ba sai an dade ba%???

%??ma zai yiyu mu zauna ba, Mama ta riga ta yi magana da Yan'uwanta za su sama mata gurin da zamu zauna na gode da kulawa%???

%??mhiyasa nake son na yi magana da ita, wata kila zata fiki fahimta da saurin saukowa%???

Na daga kai na kalleshi a kaikaice.

%??ma yi nadamar duk wani abu da na yi Dr Hamid, da ban yarda zan iya ceton rayuwar da ba a hannuna take ba da yanzu ban shiga duk wannan halin ba, na kasa ganewa talauci ya saka na aikata abun da na aikata ko kuma wauta da rashin yardar da kaddara%???

%??mdan har magana kike ta yarda da kaddara to ya kamata wannan kadarrar ma ki yarda da ita ki watsar da komai ki dauka haka Allah ya hukunta miki a yanzu ma ki rumgumi komai da hannu biyu, kuma ina mai tabbatar miki komai zai wuce nan ba da jimawa ba%???

%??mna fatar haka, ni kadai na san abun da nake ji a zuciyata, ji kadai na san halin da nake ciki, na rasa abubuwa da suka kamata su kasance da ni, na ruguza farincikina da kaina, na rasa makama, da ban aikara abun dan na aikata ba da kanwarka bata zarge ni akan mijinta ba%???

Na durkushe a gurin ina jin zuciyata na mini wani irin zafi da zogi na azabar bakincikin da nake ciki.

%??ma ke kika bukaci zama a gidan nan ba, Jamila ta janyo ki saboda haka babu laifinki idan mijinta ya nuna miki kulawa, kuma ai ita da bakinta ta fada cewar mijinta yana neman hanyar da zai saka miki da abun da kika masa, shin tana tunanin zai rika daure miki fuska ne ko kuma ya kareki? Daman can Mr Bashir mutum ne mai son mutane, kar abun da ta yi ya dame ki%???

A tunaninsa ina kuka ne saboda abun da Jamila ta yi min ne kawai, na haka na kaune kashina daya tsaya min a wuya na share hawayena na masa iso gurin Mama, a gaban ya aje ledar hannunsa sannan na durkusa har kasa yana bata hakurin abun da kanwarsa ta yi, wata kila ya cilasta shigowa bangarenmu ne domin yana tsaka da bata hakurin Hajiya Jamila ta shigo ita na ta soma bata hakuri sannan ta dawo kaina tana neman yafiyar abun da ta yi min. Uffan ban ce mata ba domin bata da kimar da zan iya yi mata wani furucin a yanzu, Mama ma ina tunanin ta hakura ne kawai saboda Dr Hamid dake ta yi mata magiya, sai dai hakurin da ta yi ba yarda ta zauna a gidan ba ne ta tabbatar musu da cewar ta hakura amman zancen tashi yana nan domin ta sanar da yan'uwanta.

%??mo ko dai sai na kira Mijina ya baku hakuri ne%???

%??maki bukutar haka ranki ya dade, ai na riga da na hakura, amman idan na ce zan zauna a yanzu ai abun ya zama da rainin hankali yan'uwana ma za su ga kamar na mayar da su kananan mutane%???

%??man iya zuwa da mijina mu ba su hakuri%???

%??majiya ba sai kun yi haka ba, zuwan ku zai kara bata lamarin ne kawai domin ban fada musu cewar kin kore mu ba, kawai dai na fake da cewar ina son na bar gidan ne saboda tsare tsaren gidan basa min dadi%???

%??mama idan haka ne ai zamu iya zuwa mu baku hakuri mu ce su lallaba ku zu zauna, ni kaina ba wai ina son ku zauna na lokaci mai tsawo ba ne, zaman ku a nan ba zai wuce wata daya ba, na miki alkawari Mama zan sama muku gidan da zaku zauna na kanku, ko bayan ni Mr Bashir ma bana tunanin zai barku haka%???

Da ??a??an kalamai da kallamewa da komai suka tirsasa Mama da amince da zama a gidan, bayan Dr Hamid yayi alkawarin zai dauki yar'uwarsa su tafi har gurin dangin Mama su ba su hakuri da neman su barsu su cigaba da zaman gidan.
Kamar yadda ya fada washe garin ranar Dr Hamid da Hajiya Jamila suka saka mu a mota ni da Mama zuwa family house dinsu, su kansu su yi na'am da Dr Hamid da kuma kanwarsa a tunaninsa tana son mu ne tsakani da Allah ba dan wata manufa ba, sai bawa suke suna saka musu albarka. Goma ta arziki Dr Hamid yayi musu sannan muka fito gidan, a hanyar mu ta dawowa gida na ke jin Jamila na fadawa Dr Hamid cewar mijinta yayi balaguron wani aiki na kwana biyu, da muka dawo gidan yana ta kara bawa Mama hakuri, ni kam na zama kamar wani hoto domin babu wata wadatacciyar walwala a tare da ni, hirar da zan iya cewa ma tursasa ni yayi ma tsaya ina yinta ba dadi take min ba.

Ban dauka da gaske Sauban yake ba har sai da na lurar da barazanarsa na kokarin yin yawa, domin kullum sai ya turo min sako yana kara jaddada min kudirinsa, idan na koshe wannan line sai ya aiko min da wani, daga baya sai na kashe wayar gaba daya na aje, da ya fahimci na daina amfani da wayar sai ya koma aiko min sako ta hanyar masu gadin gidan, kamar wani dan'adan haka Sauban ya rikide min ina ta mamakin abun da ya same shi har haka.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Na dauki damuwa da tunanin abun na saka a raina har ta kai bana iya zaunawa na ci abinci yadda ya kamata, ga kuma tsutsata da Amir yake sai ya kara sakawa na zama wata yar tsana daman can ba wani abun kwarai ke a jikin ba balle kuma yanzu da bana da wani abun yi sai tunani da neman mafita, idan kuma na nemi shawarar zuciyata sai ta fada min na amince da kudirin Sauban gudun kar na sake jefa kaina da mahaifiyata a cikin wata damuwar, Dr Hamid ma yayi ta neman sanin abun da yake damuna amman na gagara sanar da Mama ma balle kuma shi da nake ganin ba shi da wata alaka da ni. Sati daya na sakwana bana komai sai addu'a da raya dare da sallah nafila ina neman Allah ya kawo min mafita sai dai ban ga alamar bullowar wata hanyar ba.
Ranar da muka cika kwana takwas da maganar Sauban ya sake zuwa gidan ya faka a harabar gidan ya aiko yana min sallama, ina jin sunansa gabana ya fadi domin na san ba alheri ne ka kawo shi a yanzu ba, tun daga wacan lokacin da yayi min barazana zuwa yau idan ya sallamo a gidan sai na ji kamar na haka rame na binne kaina na huta, a yau sai na kekashe kasa na ce ba zan fito ba.

%??maboda me? Tun farko ba sai da na gargade ki akan zuwa gidan nan da yake ba? Da mai gidan yayi miki magana kika masa magana a wajen gidan kuke tsayawa, yanzu kuma ya riga ya shigo cikin gida ki ce ba zaki fito ba?%???

Na yamutsa fuska cike da damuwa, kalaman na ratsa ni.

%??mdan ma baki son zuwan gidan nan sai ki je ki sallame shi daga yau sallama ta har abada, kin ga daga nan zai daina zuwa, daman can na fada miki ba son zuwanshi nake ba%???


Na nisa ina tunanin tafiyar tawa, domin ban san da wacce ya zo ba tun da har ya iya shigowa cikin gidan kai tsaye bayan kuma na fada masa ba sau daya ba cewar Mai gidan baya son ganinsa a cikin gidan.
Tashin hankali da ba a saka masa rana inji hausawa, sai kawai na ji sallamar Sauban a bakin kofar dakinmu, da sauri na dauki Hijab na saka domin kokarin shigowa yake tun kamin a masa izninin shiga. Mama ma ta tashi ta sauri ta gyara zamanta daman bata rabo da hijabi tun da muka dawo gidan.

%??ma'alaikassalam%???

Mama ta amsa masa, hakan ya bashi damar matsowa sosai kusa da labulen kofar yana tambayar.

%??mama barka da dare, ko zan iya shigowa%???

Cikin sauri na girgiza mata kai alamar ta ce aa amman ba yi min yadda nake so ba, sai ta bashi umarnin shigowa.

%??mh Bismillah%???

Sallama yayi ya shigo cikin dakin ya zauna kusa da kofa ya gaisa da Mama.

%??mauban ka tafi gani nan zuwa%???

%??mannan zuwan ba naki ba ne ke kadai, na zo ne har saboda Mama, saboda na gaji da yawo da hankali da kike min%???

A kaikace na kalleshi ina mamakin yadda zai buga min wata kwallo a ragar da ban san da zamanta ba. Kamin na yi wani unkuri ya fara shimfidawa Mama karyar da ta daure ni da manyan tsarkoki da ba zan iya kwance kaina ba.

%??mama ina son magana dake ne saboda abun da Zahra ta yi min, kuma ina son ki yanke hukunci tsakani da Allah karki duba kusanci da Zahra ko rashin alakarki da ni%???

Yayi shiru ni kuma na zuba masa ido domin na ga iya gudun ruwansa, Mama kuma ta gyara zama ganin babu wasa a tare da shi sai zallar tausayi da ke fita a muryarsa.

%??mama tun ba yau ba mun yi magana da Zahra, magana kuma ba ta soyayyar ba ce ta aure ce, kuma da farko ta nuna min kamar babu matsalar komai, sai daga bayan nan take nuna min kamar ke ce baki son tarayya ta da ita, ni kuma a ganina ba haramun ba ne idan kin amince kin bar Zahra ta aure ni, saboda Abiey yayi sonta shi yake nuna ni ta haramta a gurina ba, kuma Mama ba mu san inda Rana zata fadi ba, lokuta da yawa abin da ba a so shi ne alheri wanda kuma ake so sai ya zama ba alheri ba, kwana biyun nan gaba daya Zahra ta canja min hakan ya haifar min da damuwa ba yar karama ba, kullum da kalar dabarar da take bullo min da ita, tace na bata dama ta yi shawara na bata daga karshe sai ta nuna min ita yanzu matsala ba daga ita ba ne daga gurinki ne, shiyasa na zo da kaina na roki alfarma a gurinki ki dube ni a matsayin ??anki, ya zaki ji idan aka ce wata mace ta yi min alkawarin aure kuma har na sanar da iyaye akan Zahra har matsala sai da muka samu da Matata, na san zaki dubi kamar kusancina da Abiey be dace na yi haka ba, amman Mama so ya wuce nan, Abiey ya riga da ya kama gabansa a yanzu an saka masa ranar aure da Yasmin, ko wannan kadai be isa ya saka Zahra ta nemi rufawa kanta asiri ba? Shi kansa mai gidan nan da yake saka mata dokiki kamar yarsa da ace tana da miji ai ba zai fara mata haka ba%???

Da dai ace gasa ake ta marubuta tabbas Sauban zai karbi Awards a yadda ya tsaya ya marairaice fuska ya kuma shake murya ya tsarawa Mama zancen da ba ne ba. Kamar wata kyanwa haka na zama na lafe jikin ginin dake kusa da katifa ina tunanin yadda zan warware wannan mugun kullun da Sauban yayi min, muna hada ido da Mama sai ta watsa min harara irin wanda ke nuna ko dukana zata iya yi idan Sauban ya bar dakin.

%??mauban, Zahra ba ita ke aurar da kanta ba, tana da magabata bangaren uwa da uba, kuma ba wai bana son ka aureta ba ne, aa ina duba abun da zai fi zama masahala ne a tsakaninku kai abokin Abiey ne be kamata ace ka auri Zahra ba, amman tun da har ta nuna tana sonka kuma ta fada maka ni bana da matsala, indai kun sasanta kanku kuma kin ji cewar za ku iya jurewa da maganganun jama'a na wa fatan alheri kawai sai Allah%???

Mama na rufe baki sai ga Sauban ya kai goshi a kasa yana sujudar godiya, ya dago yana kara yi ma Allah godiya.

%??muk da haka dai, a kara tunani Sauban bana son ku jefa rayuwarku cikin matsala, domin Zahra bata da wayo da tunani wani lokacin%???

%??mnshallah Mama na gode Allah ya saka da alheri, kin gani ko Zahra daman ina ta fada miki Mama bata da matsala ke ce dai kika gagara tsayawa ki yi mata bayanin yadda zata fahimta ne kawai%???

Cikin wasu ruwan hawaye da ban san lokacin da suke kwararomin ba na ce.

%??mauban kana tunanin yin haka zai saka na aureka da karfi ne? Na fada maka ba zan iya cin amana ba, ba zan abun da zai zame min ciwo daga baya ba, akan me zaka zo ka shimfidawa Mama abun da ni da kai mun san be faru ba? Ya kake abu kamar yaro karami?%???

Sakin baki yayi yana kallona kamar da gaske shi ne mai gaskiyar ni ce mai karyar, Mama ta masa nuna taja dogon numfashi ta sauke ta ce.

%??mauban je ka waje zata zo ta same ka%???

%??mo Mama, amman ina fatar ban haddasawa Zahra matsala ba?%???

Mama ta yi murmushi ta girgiza kai.

%??ma komai shashashanci ne kawai irin na ta%???

Cike da nuna damuwa ka ya tashi daga dakin, kusa da Mama na dawo na zauna sai na rasa kalaman da zan hada na wanke kaina, harara kawai Mama take watsa min irin wanda na manta rabon da na aikata wani abu da ya bakanta ranta kamar wannan, cikin karfi hali irin na marasa madafa na dago na ce


%??mama Wallahi....%???

Tassss na ji sauka tafin hannun Mama a fuskata, marin da da sai da shatin yatsunta ya kwanta a farar fatar kumatuna.

%??mhashashar banza wawuya, idan ma bana son alakarki da shi dole sai kin fada masa? Sannan ke ba zaki iya tunanin abu mai kyau ba? Yadda zuciya ta raya miki haka kike? Ina ganin kamar kin yi hankali kin san abun da kike ashe haukarki ma karuwa take? Akan me zaki masa alkawari cewar zaki aurenshi bayan kin san alakar dake tsakaninsa da Abiey? Oh yanzu na gane shi ne dalilin shiga damuwar da kika yi ko abinci ba ki iya ki ci?%???

Na girgiza kai zan sake magana Mama ta buge min baki.

%??mufe min baki, ba dai kin masa alkawarin aure ba? Kuma kika kawo ni a tsakiya kika manna? Amman a nan idan na nuna miki bana son zuwanshi cewa kike ke ma ya zame miki dole ne, ashe kina can kina tsara masa aurensa za ki yi har kina dora laifin a kaina? Tabbas na isa na hana aurenku, daman abun da nake hango miki matsala ne da yadda mutane za su kalleki, amman tun ke baki san Annabi ya faku ba sai ki je ki yi duk abun da kika tunanin mafita ne a gurinki, tashi ki je ki same shi%???

Na runtse ido na bude ina jin yadda duniya da lamurran cikinta suke yamutsa tunani, kamar tsumma a cikin ruwa haka na mike tsaye jiki ba kauri zuciya babu karfi na fice daga dakin.
A lokacin da na hango Sauban jikin motarsa yana jira na fitowata sai na ji kamar ace da bindiga a hannuna na halbe shi ko na huce wannan cikin da ya saka min a yanzu.

%??m'm sorry, na yi hakan ne saboda na taimaka miki wajen shigar da ni gurin Mama, kuma idan har ba ki son kowa ya san Auren dake zamu iya yinsa a sirrance ba tare da Abiey ko wasu sun sani ba, ni dai ina son kasancewa da ke ne ko da na kwana daya ne%???

Na data kai na kalleshi da idanuwan da hawaye suka ci karfinsu, daman na dade da lura kamar ba so yake min irin na Allah da Annabi ba domin a cikin sakwannin da yake aiko min ya fi yawan jaddada cewar yana son ya kasance da ni ne ko da na kwana daya ne kamar yadda ya fada a yanzu. A iya tunanina Abiey ba mazinaci bane balle na ta kai ga na zargi Sauban, sai dai baka iya shaidar kowa a wannan zamanin sai kanka, wata kila akwai wani abu da yake burge Sauban a jiki da ya kasa hakura har ya kwadaitu da son kasancewa da ni kamar yadda ya fada, ya sani sarai idan ya zo min da maganar banza ba zan amince ba, shiyasa ya bullo ta wannan hanyar.

%??mya barazanar da ka yi min bata wadatar ba? Har sai ka biyo ta wata hanyar da ba zata bulle da kai ba? Da farko na yarda da kai Sauban ban yi zaton zaka zo min da wani wasa ta yara ba, abun da ka aikata a yanzu ba abu ne ya burgewa ba, kuma idan kana tunanin ka yi wayo ne to baka yi, kuma wannan be isa ya saka na amince da mugun kudinka ba%???

Dariya yayi.

%??mahra kenan, wato barazana kika dauki abun da na fada miki ko? To na rantse miki da Allah zan aikata matukar baki amince da kudina ba, ki yi tunanin halin da zaki shiga da kuma wanda ??anki zai shiga, da kuma wanda zaki jefa Dr Hamid, da Jamila balle kuma Mr Bashir da mahaifiyarki, ba fa kudi nake nema a gurinki ba Zahra face amincewarki ki aurene, har na baki dama idan baki son duniya ta sani zamu iya yin abun mu a boye%???

%??ma zan yi ba, ka je ka yi duk abun da zaka yi, saboda kun maida ni ba ni da kowa sai ku rika juya ni yadda kuke so%???

Na karasa cikin kuka, sai ya miko min wayarsa.

%??muba wannan, ina fatar dai baki fadawa Mama komai ba, kuma baki nemi shawarar kowa ba sai zuciyarki%???

Ban karbi wayar ba, hakan kuma be hana ni hango takardun gwajin jinin da aka fadada a cikin wayar ba.

%??ma ki ne da na ??anki, wanda aka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login