Showing 33001 words to 36000 words out of 210919 words

Chapter 12 - CIWON SO

10 Oct 2024

4196

fito, sai dai bata ce min komai ba har sai da muka yi nisa da gurin.

%??mi kiyaye abun da likita ya fada kuma ki yi ta addu'a%???

Na daga mata kai.

%??mmman Mama ina son na yi magana da Deen akwai abun da yake son ya fada min%???

%??mkan ciwonsa ne? Ko akanki%???

%??man sani ba, ni dai yace na masa alkawari ko bayan ba ransa to be karasa min ba kika shigo ban san mi yake son na masa ba%???

Tsayawa kallona Mama ta yi sannan ta hade yawu ta ce.

%??ma safe ai sai ku yi magana kinji ko? Ki tafi kar ki barta tana ta jira ita da mijinta mi zan koma gurin Deen din%???

%??moh%???

Na amsa sannan ya cigaba da tafiyar na barta a nan tsaye kamar mai tunani, ina fitowa na samu Yaya Maryam tana jira ita da mijinta bata ce min komai ba muka fara tafiya sai suka yi gaba suka bar a baya ina ta waigen ward din ina jin kamar na koma gurin mijina. Ganin hakan ya saka Yaya Maryam ta dawo ta rika ni.

%??mahra...%???

Sai na fashe da kuka marar sauti.

%??mallahi ji nake kamar idan na tafi ba zan dawo na tararda Deen ba%???

%??mabu abun da zai faru da yardar Allah, ki kwantar da hankalinki abun da yafi ma yanzu ki fara tunanin hanyar da zamu bi mu samu kudin aiki%???

Na daga nata kai ina hawaye sai ta rumgume ni muka nufi inda mijinta ya faka motarsa. Ba dan raina ya so ba na bi ta gidanta na kwana, ita da mijinta suka yi ta kokarin kwantar min da hankali, haka dai na daure na sha ruwan tea ba dan na ji ina son komai ba, gaba daya tunanina ya tafi akan yadda zan yi na samu kudin aikin Deen. Cikin kwana uku na bi na lalace na rame kamar ni ce mai ciwon, muna ta fafutukar neman kudin amman hanyoyi sun taushe mana, muka rasa mai siyen gidan sai muka koma neman wanda zamu bawa jingina ya bamu kudi, Yaya Maryam ta siyar da wayarta da kayan dakinta ta damka min kudin, mijinta ma ya taimake mu da abun da zai iya, Hajiya ma ta yi iya nata Baba ma haka sai dai gaba daya kudin da muka hada be wuce miliyan uku da rabi ba, shi ma daker da sudin goshi muka samu muka hada ciki kuwa da da gidan da muka siyar a arha banza saboda muna bukatar kudin, ni ma na siyar da kayan dakina da Mama ta yi min, har na koma bibiyar dangin mahaifina wai ko zan samu a taimaka mana saboda suna da rufin asiri amman sai dai su yi mana alkawari wasu kuma su dauki abun da be taka kara balle ya karya ba su bani, sai dai ba laifi sun yi ta zuwa ganinsa a asibiti daga su har dangin mahaifiyata, ta bangare Hajiya da Baba ma an samu taimako sai dai taimako ba irin wanda muke bukata ba, gashi kudin da muka tara a cikin ake cira ana masa wasu kanann magungunan da scanning.
Gashi na lura ciwon nasa sai kara gaba yake, domin a yanzu kamar ma bata gane wanda ya zo kansa, duk kuma yadda na so na samu damar kebewa na yi magana da shi Mama bata bari ba, idan kuma bata nan Hajiya na nan idan Hajiya bata nan yana bachi, tun daga wacan rana ban samu wata rana da yi wata doguwar magana da shi ba, ko sannu na yi masa sai dai ya daga min kai ko hannu shi ma daker, a haka kuma yake karfin halin yi min murmushi sai kuma yawan kallon cikina da yake.
Kusan yau ita ce rana ta karshe da Likitoci suka tabbatar mana idan har ba mu samu kawo kudin aikin a cikin satin nan ba, zamu iya rasa shi, kuma na lura da haka domin ciwo ya ci shi har ya sauya kamanin, cikin abun da be fi sati biyu zuwa uku ba, Deen ya canja ya koma kwance baya iya komai zai an masa. Ba tare da sanin kowa ba na silala na fita asibitin zuwa gidan wani dan'uwan mahaifina, domin mutum ne mai rufin asibiti kuma mahaifina ya taimake shi sosai a lokacin da yake raye, ba tare da tunanin komai na shiga gidansa duk da kasancewar na sanar da shi halin da nake ciki a wacan karon yace min zai waiwayeni sai dai shiri gashi yau kusan kwana hudu kenan. A lokacin da na shiga gidansa matarsa ta tarbeni da far'a kamar yadda ta saba, ta saka aka kawo min abinci da abun sha, ni dai ko ruwan da aka kawo min ban taba ba balle na ci abinci domin ba shi ne gabana ba. Haka na zauna a falon tun zaman na min dadi har na fara takura na mike tsaye na sake zama, be fito ba da matarsa ta fito na sake mata magana sai tace min ta fada masa yace na jira yana da baki ne, a take zuciyata ta sosu ina tuna lokacin da yake zuwa gurin mahaifina idan ya shigo Abbana na maraba da shi yana girmama shi, mu kuma yana nuna mana so kamar ya cinye mu saboda mahaifinmu yana raye kuma yana da rufin asiri a lokacin, yanzu kuma da ba shi a raye yana da wasu bakin da suka yayan yan'uwanshi kuma amininsa.
Nema babu yadda zai yi sai hakuri haka na zauna har kusa la'asar sai da ya sallami kowa abokan siyasarshi sannan matarsa ta sake tuna masa sai gashi ya shigo falon da shirinsa na fita, cikin jikina be hanani risinawa na gaishe shi ba, ya amsa min fuska a sake yana tambayar jikin Deen.

%??ma sauki, Baba na dawo na tuna maka ne, likitoci sun ce idan ba mu hada kudin a yan kwanakin nan ba komai zai iya faruwa%???

Na fada muryata na rawa ban yi dan ya tauyasa min ba, sai dan kukan nawa yake kusa.

%??mubhanallahi Allah ya ba shi lafiya%???

Ya fada yana saka hannunsa aljihu ya ciro bandir din yan dubu dubu ya kirga dubu talatin ya miko min.

%??mashi a kara, Allah ya kawo sauki ni Wallahi sam na manta ma sai da Mamanki take tuna min%???

Tsayawa na yi kallon kudin, a kimanci a mutunce yafi karfin ya dauki miliyan biyu ko uku ya bani ma, zai iya daukar nauyin aikin Deen idan ya so, amman be yi ba ko rabin miliyan be ba ni ba sai dubu talatin.

%??ma gode Allah ya saka da alheri ya karawa sauran albarka%???

Na fada zuciyata na min wani irin zafi, sai ya amsa da Ameen ya mike tsaye alamar sauri yake yana fadin.

%??mireba ya sauke ni gida%???

Ni dan ban kara ce masa komai ba, na bishi da kallo bayan ya fice na saka kudin saka na mike tsaye hawaye na sauko min.

%??momy zan tafi%???

Na fada domin haka muke kiranta tun a lokacin da Abbah yake a raye.

%??mauna ina zuwa Zahra%???

Sai na koma na zauna, ita kuma ta tashi ta shiga bedroom dinta bata dade bata fito ta mika min kudin da nake kyautata zaton zai kai dubu dari da hansi.

%??mllah yayi ma babakin Rahma, mijinki kuma ya bashi lafiya%???

%??mmin Momy na gode%???

Na amsa hawaye na sauko min ba dan ina kuka ba, na saka kudin a jaka na fito kamar zan fadi na fice daga gidan. Daga gidan na wuce gidan wani abokin Abbah shi ma yana da rufi asiri shi ma kuma na kai masa kukana tun wacan lokacin sai ya dauko dubu goma ya bani, ma fito ina nadamar zuwan gidan, ban yi fushi ba na sake zuwa gidan wani kanen Abbana shi kam na san ba shi da shi kamar sauran hakan yasa da ya min alkawarin cewa zai kawo min har gidan ban yi tunanin komai a rana na domin na san idan yana da shi ba zai ki yi min ba. A gidansa na yi sallah sannan na fito na nufi gidan abokin Abbah shi kam ban ma samu ganinsa ba sai ce min aka yi baya gari ba dan kuma baya garin sai dan sanin abun da ya kawo ni, haka na fito jiri na dibata kamar zan fadi na biyo hanya, by this time kam na san hankali kowa ya tashi domin ban fada musu inda zanje ba balle su sani, yar wayar tawa kuma na siyar balle akira a ji inda nake, ina tafe a hanya ina hawaye da tunanin yadda Abbah yake kaunar yan'uwansa yana nuna musu kulawa, da kuma irin gatan da yake yi ma yaransa.

%??mbbah yau ga ranar ka, da kana raye da ban yi kuka ba Abbah, yan'uwanka da abokanka duk sun guje ni%???

Na fada ina tuna yadda Mama ta yi da wahala da mu ko a gurin aurena ita ce ta yi komai, yan'uwa sai dan taimakon da ba a rasa ba wasu ma dan ma kar ace ba su ba. Na tari napep na shiga na ina ta tunanin mijina ina jin kamar ace idan na koma asbitin na tararda ya warke, bakin asibitin na sauka na sallame shi na karasa ciki da kafata. Hajiya na hango ni ta taso da sauri ta tare ni.

%??mahra ina kika je? Kin tashi hankalinmu tun dazun ake nemanki%???

Daman na san za a rina wai an ari zanen mahaukaciya, domin ban fada musu inda zan je ba, sai da muka zauna ta bani ruwa na sha sannan ta dauki wayarta ta kira Mama da Yaya Maryam ta fada musu na dawo sannan ta sauke wayar tana kallona.

%??mna kika je Zahra?%???

Sai da na sauke ajiyar zuciya ina hade ruwan ke min dacin sannan na fada mata mata ina jin kamar na fashe da kuka, sai ta yi murmushi.

%??me yanzun idan ban da kurciya, ai masu kudin yanzu babu ruwansu da kai, kadan ne kake samu masu taimakon yan'uwa, Zahra yanzu fa idan ka rasa kai na yi rashi sai dai ka yi ta rokon Allah kawai%???

Na yi shiru har lokacin wata mafitar nake ta tunanin inda zan samu.

%??mama ko dai muje gidan Tv mu sanar musu a saka mana neman taimako ko samu dacewa%???

%??ma a aki ta mutane ba, amman hakan sai nake ganin kamar ba dacewa ba ne ban sani ba ko ana samun taimakon%???

%??mo kuma mu saka a social media ko zamu samu wani ya dauki nauyi, wani lokacin ana samu%???

Na sake fada ba tare da tunanin komai ba. Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke sai na kalleta ita ma ta yi rama sosai kamar ni, daman ai dole ta yi ramar saboda tunani da zullumin rasa danta.

%??majiya wai ba a cire hantar wani a dasawa wani ne?%???

Sai ta yi murmushi.

%??ma ba a haka, ai da kin ji likitan ya fada%???

%??ma rasa yadda zan yi, duk wanda ya kamata ya taimaka na tafi be min wani abun azo a gani ba, bana son na rasa mijina%???

Na karasa cikin kuka mai kama da na shagwaba, ba dan kuma shagwabar ba sai dan abun ya zame min jiki.

%??mahra... Mijinki ya ce na hana ki kuma na fada miki, kar neman taimako ya saka ki tafi gurin da be kamata ba%???

Na kalleta da mamaki domin sam ban fahimci inda zancenta ya dosa ba.

%??munanin kike zan iya aikata wani abu saboda neman kudin magani?%???

%??ma Wallahi ba haka nake nufi ba, Deen ya roki na hana ki duk wani yunkuri da zaki yi akan Abiey, balle har ki je neman taimakonsa, ko da mun samu kudin maganin sai idan Allah ya so zai tashi kin san da wannan%???

Maganar da Hajiya ta yi tunatar da ni abun da na dade da mantawa, wato neman wani abu a gurin makirin mutum Abiey, sai dai duk wahalar da nake ciki bana tunanin zan iya zuwa gurinsa neman taimakon ba.

%??ma zan taba yi ba, ni na dade da rufe babinsa na shafe labarinsa na manta da an taba halittarsa%???

Na karasa ina juya na kalli Mama da Yaya Maryam da suka shigo ward din da saurinsu.

%??maba Zahra ya zaki kama ki fita baki fadawa kowa ba? Kin tada mana hankali%???

Mama ta fada cikin fada sai Hajiya ta tare ta tana kokarin hana ta yi min fada, kamin na fada mata komai Hajiya ta yi mata bayanin inda naje. Yaya Maryam ta ce.

%??mbbansu ma yace akwai wani dan siyasa da ke taimaka sosai yace zai yi ma abokinsa magana yayi mana hanya sai muje mu yi masa magana ko Allah zai sa mu dace%???

%??moh Allah yasa mu samu, ya jikin nasa%???

Na karasa ina kallon Hajiya.

%??ma sauki%???

Yunkurin tashi na yi da zimmar na taka na leka dakin na duba shi, sai Mama ta yi saurin ta mike tsaye tana fadin.

%??mo ki ci abinci na san wunin yau baki saka komai a cikinki ba%???

%??mari na duba shi sai na zo na ci%???

%??ma ki dai fara cin abincin%???

Hajiya ta fada, bana son musa musu dan haka na dawo na zauna Yaya Maryam ta zuba min jalof din shimkafa ta zuba min ruwa a kofi, daukar plate din na yi na rike ina kai abincin bakina ba dan ina jindadinsa ba, ina labarta musu yadda na tararda yan'uwan Abbah da abokansa. Bayan na gama cin abinci na tashi sai Hajiya ta ce.

%??mna tunanin fa bachi yake yi likitoci sun ce yana bukatar bachi, da kin hakura har zuwa gobe da safe sai ki duba shi%???

%??ma magana zan yi da shi ba, duba shi kawai zan yi%???

%??mi hakura sai da safe mana Zahra, miyasa kike gardama ne?%???

Mama ta fada, sai na kalleta na kalli Yaya Maryam na sake kallon Hajiya a take zuciyata ta raya min ba lafiya ba.

%??maninshi kawai zan yi na fito%???

Na sake fada tare da fara takawa na nufi hanyar danki, sai Yaya Maryam ta kira ni.

%??mahra miyasa wai baki jin magana wani lokacin? Ance ki bar shi ya samu bachi mana%???

Na juyo na kalleta.

%??mdan wani abun ne ya faru ku fada min, ba wai ku hana ni gashin ba%???

Ina fadar haka ya juya na cigaba da tafiya, ina kaiwa kofar dakin sai na samu kaina da faduwar gaba da tsoron abun da zan tarar. Haka da dai na dake na daure na murda kofar na bude na shiga. Sai na hangoshi kwance an saka masa oxygen a baki ga wata katuwar tukunyar oxygen din aje a kasa da alama ita take ba shi iskar numfashin da yake shaka. Gaba daya sai zuciyata ta karaya a take hawaye ya cika idona na taka a hankaki na karasa kusa da shi ina kallon kyakkyawar fuskarsa mai cika da haiba amman a yau ta canja kyausa ya gushe saboda ramar da yayi ta ciwo, hannu na kai na taba jikinsa sai na jishi da wani irin sanyi kamar ba jikinsa ba.

%??mahra%???

Na juyo na kalli Yaya Maryam.

%??maushe suka saka masa wannan abun?%???

%??mazu%???

Na lumshe ido ina jin zuciyata kamar zata fado saboda bakinciki, hawaye kan daman hanya kawai suke nema, ji na yi Yaya Maryam ta rumgume ni tana tarrashina sai dai ita ma hawayen take. Mun dade a haka kamin na daga daga jikinta na zauna.

%??man Allah ki roki Mama ta bar ni na kwana a nan yau%???

%??moh, amman...%???

%??man Allah%???

Na sake roko a dole ta daga min kai.

%??mhikenan zan yi magana da ita%???

Ta juya ta bude kofar ta fita, sai na miki tsaye na nufi kofar na bude na fita hawaye na sauko min kamar ba gobe. Ban yarda na bi ta inda za su gan ni ba sai na sauya hanya na fita ward din ba tare da sun gan ni ba. Wani gurin na samu inda babu mutane na zauna na bude babin kukana ina tunanin yadda gobena zata kasance idan na wayi gari babu Deen.





ABIEY POV.

Duk labarin da Sauban yake masa hankalinsa baya gurin, har sai da ya dafa shi.

%??mey Abiey%???

Ya kalleshi da sauri, kamin ya kalli Nuratu dake zaune kusa da mijinta sanye da Hijab.

%??mafiya kake kuwa?%???

Ya dan jimmm alamar tunani, sannan ya mike tsaye.

%??mafiya Kalau%???

Ya nufi kofar fita falon, Nuratu ta bishi da kallon mamaki Sauban kan ya saba ganinsa a irin wannan yanayin time to time.

%??mi kwashe kayan bari na raka shi%???

%??mkay%???

Kusan a tare suka mike tsaye shi ya nufi kofar fita ita kuma ta fara kwashe kayan da Abiey ya ci abincin da su. Jingine da motarsa Sauban ya same shi ya rumgume hannayensa har lokacin muryarsa na nuna alamar yana cikin damuwa.

%??mbiey lafiya dai?%???

Ya dago ya kalleshi.

%??momething is wrong somewhere%???

%??mhat do you mean%???

%??m kusa ko a nesa duk inda Zahra take tana cikin wata matsala%???

%??muba kake yi ne? Ko kuma abun naka ne ya kara yin worse?%???

%??m use to feel that a lokacin da muke tare, if wani abun ya same ta ina jin wani yanayi na daban jikina yana fada min, and tun da na baro gidan Mai Martaba na dawo gida kullum sai na yi mafarkinta, and bana gane wane irin mafarki ne every day%???

%??mole ai ka yi mafarkin tun da ka saka ta a ranka%???

%??ma irin wannan nake nufi ba, ni na san me nake ji, and kwana biyun nan tunaninta yana damuna fiye da da%???

%??mahra matar wani ce Abiey, ya kamata ka cireta a ranka, is she not the one that warning you ki manta da ita ka fita daga komai nata? Be kamata kana tunanin matar wani ba%???

Abiey ya hade yawun bakinsa.

%??maka ne, and i do hope ba mutumen nan ya cutar da ita ba, because she choose the wrong person...%???

%??mtill thinking about her talking about her? Kana ganin haka zai fitar da kai?%???

%??mabu yadda zan hana kaina tunanin Zahra, domin ta zama wani bangare na rayuwata kuma ta shiga cikin jinina, a zuciyata take rayuwa, duk wata mu'amala ta da ita na saba, ita kuma da ni ta saba sometimes i wonder yadda take farinciki ta manta da komai nawa%???

Ya juya ya bude motarsa sai kuma ya tsaya yana bawa kansa amsa.

%??mhy won't she? Deen ya riga ya nuna mata mi macuci ne wanda ya kunyatata da kunyata iyayenta da yan'uwanta kuma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login