Showing 168001 words to 171000 words out of 210919 words

Chapter 57 - CIWON SO

10 Oct 2024

4211

gidan ya gaisa da Mama idonsa akaina duk wani motsi da zan yi baya dauke ido akaina, da zai fita sai ya bukaci na rakashi zuwa kofar gida, a can ya fara karantar min wadansu labarai da suka sanyaya min guiwa, wai Abiey yayi haka ne kawai saboda ya zamu damar shiga jikina kuma da zarar ya samu abun da yake so zai guje ni, shi dai yana min tsoron ranar da Abiey zai kunyata. Labaransa ba su tasirin hana ni amincewa ba, sai dai na kagagara na ga Abiey domin na tambaye shi ko zai guje min amman samu dama ba saboda ban samu saka Abiey a ido ba sai a ranar da aka yi mana baiko. A ranar unguwar mu ta dauka domin kayan baikon da aka kawo irin masu janyo magana ne da tseguma abu ne da ba kasafai ake ganinsa a gidajen talakawa ba sai yayan manya. Mama ta boyewa kowa wanda zan aura sai dai ko da wanda yake fada har da masu cewar tsoho aka bawa ni saboda an ga kudi a tunaninsa idan ba tsoho ba ne babu abun da zai saka mu boye ko waye.
A ranar da aka yi min baikon Deen ya wuni yana bachi kamar matacce tun daga lokacin kuma be saka lafiya ba, daga ni har Mama muka rasa gane abun da yake damunsa, idan muka tambayi Baba sai yace mana ulcer ce.

Daga lokacin muka fara cin arzikin Ammy, ta saka aka gyara mana gidanmu inda gini yayi kadan aka kara inda ke bukar gambu aka saka sannan aka yi mana tayis ko'ina a gidan. Idan Abiey zai zo hira zai so a bakar mota saboda kawaice idon mutane wani lokacin kuma sai na tafi gidan Yaya Maryam a can zamu yi hira. Wata rana na shirya da kaina na tafi sabon gidansu Abiey, domin a ganina ba komai ba ne na shiga gidan Ammy a yanzu, ban samu Abiey a gidan ba, Ammy ma na same a cikin wani yanayi dake nuna kuka ta yi, tana ta kawar da fuska kar na kalleta amman hakan be hana ni fahimtar tana cikin damuwa ba, na ritsara a dakinta na tsareta da tambayar damuwarta sai ta ki fada min ni kuma na saka kuka domin ganinta a cikin wannan halin ya daga min hankali sosai ina kallon Ammy kamar uwar da ta haife ni, idan ba uwarka ba a gidan wa zaka je kayi yadda kake so ka hau gado ka kwanta ka ci abun da ranka yake so ba za a ce maka komai ba ko a nuna maka yar fuska. Bayan na sha kuka na koshi Ammy ta kama hannuna tana dariya.

%??maba Autana ta zo mana%???

%??mo Ammy me ke damunki? Idan baki fada min ba zan daina kuka ba ko da na tafi gida, saboda zan rika tunanin kina da wata matsala ne%???

Sai ta zaunar da ni kusa da ita wasu hawayen na taruwa a idonta.

%??mna da matsala Zahra, matsalar da bata da magani, amman ina jin kamar na samu magani a lokacin da na same ki, saboda hankalin Aliyu yanzu yana gareki, kullum ba shi da magana sai ta ki, Zahra ina son ki zame masa cikakkiyar yar halak karki butulce masa, akwai mata da yawa da suka fi komai ba amman idonsa be sauka akan kowa ba sai ke, kuma zuciyarsa bata natsu da ko wace mace ba sai ke%???

%??ma miki alkawari Ammy ba zan taba cin amanar Abiey ba%???

%??mahra na aikata wani abu, wanda shi ya saka ni kuka a yau kuma yake saka ni kuka a ko wane dare, zan fada miki wannan ne saboda ina son kamar yadda nake son Aliyu ban taba fadawa kowa wannan sirrin ba, amman abu ne da ya dade yana cina kuma ina fatar ba zaki fadawa kowa ba, ke ma zan sanar da ke ne saboda ki kara natsuwa da ??ana kuma ki tausayawa masa%???

A take hankalina ya tashi domin na san duk wani abu da zai saka uba zubar da hawaye a kowane dare ba karamin abu ba ne.

%??ma miki alkawari babu wanda zai ji Ammy%???

Sai da ta share hawayenta ta sake kama hannayena ta rike sannan ta ce.

%??mahra karki taba yarda ki mu'amalanci wani da aurenki, kara ki yi shi a waje ko kuma bayan mutuwar aure ba a aure ba, maza basa yafe irin wannan kuma basa mantawa, kuma wannan abun yana shafar yayan da mace zata haifa, ni da Momy wato abokiyar zamana a gidan mahaifin Zainab mun sake aure bayan rasuwar mijinmu, sai dai ni na rigata auren saboda na fita kurciya da kyau, kuma ni na yi sa'ar aurene saboda tsohon manemina ne na aura, ya nuna min so irin wanda Aliyu yake kokarin nuna miki a yanzu, har ta kai baya iya adalci a tsakanina da sauran matansa, wannan ya haddasa fitina kuma zazzafan kishin da ya saka sai da aka ware ni dabam, domin ni ina yaki da bakina ne da anyi min sai na yi magana bana shiru, amman Wallahi ban san hanyar zuwa gidan ko wane boka ba, a lokacin kuma sai hankalinsu ya kara tashi suna ganin kamar zan kara dauke masa hankali ne, sanadin haka sai suka shiga bin bokaye suna kokarin raba ni da mijina, sai kuma suka yi nasara Mai Martaba ya juya min baya irin Juyowar da idan na rabe shi sai ya rika jin warina, idan ya taba ni sai yace jin yake kamar ya taba itace, har tambayar yake miya samu jikinki haka ni kuma ban san miye ba, da abun ya fara yawa sai ya daina zuwa gidana sai dai aiko min da duk wani abun bukata da kuma sakon gaisuwa, bayan ya kaurace min sai na fahimci ina da cikin Aliyu, wanda yace min idan na haife shi sunan mahaifinsa za a saka masa duk kuwa da kasancewar ya hana ko wace mace saka sunan Abban sa amman ni soyayya ta saka ya karya wannan alkawarin da ya dauka. Wata rana kamar an turo shi sai ya shigo gidan fuska babu annuri ban masa laifin komai ?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
ba,a nan na samu damar sanar masa halin da nake cikin ina ganin kamar samun cikin zai kawar da komai a tsakaninmu ya dawo da zaman lafiyarmu, sai dai a lokacin da na sanar da shi ina dauke da cikin sai ya kasa farinciki a aka danna jindadinsa akan cikin ya gagara nuna min murnarsa, sai Allah ya raba lafiya kawai yace min, a ranar na yi kukan na yi bakinciki sosai, a dayan bangaren kuma na yi farinciki da kyautar da Allah yayi mine. Na yi bakinciki na kaurace min da yayi ya saka na shiga damuwa sosai har ta kai kanensa da suke uba daya wato Galadima wanda shi kadai yake so na a familyn ya fahimci haka, maganinsu ba tsaya a iya farraku tsakanina da Mai Martaba ba ni ma ya taba tafiyata ya shafi kwakwalwata ya kai bana iya tsayawa na natsu akan wasu abubuwa, ga ciwon kafafuwan da na yi ta neman magani har india na je na kasa samun lafiya. A cikin Aliyu na wata na biyar zuciya da sheirin shaidan suka debe ni suka na aikata masha'a tare da kanensa da zan iya cewa cilasta ni yayi domin yayi ta lallashina har na amince, ashe ban sani ba wani karin damuwa ce ta fuskanto ni, domin muna a cikin halin da be kamata ba Mai Martaba ya shigo cikin gidan sai dai be shiga inda muke ba sai ya zauna a falo, bayan mun fito muka same shi. Daga ni har kanensa mutuwa ce kawai ba mu yi ba, amman mun sha kuka na fitar hankali. Ya saka muka yi masa alkawarin babu wanda zai ji wannan maganar daga ni sai shi sai Allah, saboda idan maganar ta fita zai zama abun magana kuma abun kunya. Bayan kanenshi ya fita sai ya tambaye ni tsawon yaushe muke tare, na fada masa gaskiya cewar yau ne kawai, amman be yarda ba.

%??mikinki da ke jikinki zai cigaba da zama a matsayin ??ana ko da kuwa ba nawa ba ne, domin jinin ??an'uwana jinina ne, kuma babu wanda zai san da wannan maganar, sannan ina son ki sani na sauwake miki ma'ana na sake ki%???

Cikin tashin hankali na fara bashi hakuri ina kuka ina fada masa cewar cikin dake jikina nasa ne.

%??mdan har zan iya zaman aure da uwar da ta haife ni, to zan sake zaman aure da ke Umaima!%???

Furuncin da yayi kenan ya banranta kansa da ni, daga lokacin sai na dawo gida gurin iyeyena na zauna, damuwa ta shiga kaina ga kuma sihirin da suka min har ya zama na ina yin abu kamar marar hankali, ana ta nema min magani ana min addu'a cikin iyawar Allah na samu sauki. Sai Allah ya dauki kaunar Aliyu ya saka min tun yana ciki domin mahaifinsa be taba zuwa duba lafiyata ba bayan ya sake ni, mutane suna ta fadar cewar maganin da suka min ne ya saka ya sake ni kuma ya dauke idona a kaina domin ina fadawa kowa cewar haka nan sidda ya sake ni ba tare da na masa komai ba.
Kamin na haifi Aliyu kanen mahaifinsa yayi hatsarin mota ya rasu, sai ya zamana ni kadai na rayu da wannan bakincikin har zuwa yau. Bayan na haifi Aliyu Mai Martaba be taba ganin fuskarsa ba be taba aiko masa da komai ba, be taba yi masa komai ba ??ana ya girma hannuna yayi wayo na yi masa komai da uwa take yi ma ??anta, sai dai kowa ya kalli Aliyu ya san ??an Mai Martaba ne domin babu inda ya rago Mai Martaba a kamanin. A lokacin da Momy ta haifi Yasmin sai muka je barka daga gidanta na dauki ??ana na kai shi gidan Mai Martaba, yana kallonsa sai hawaye suka zubo masa, domin be taba saka shi a ido ba sai a ranar. Sai dai haka be canja tsanar da yake masa ba, be saka ya kula da shi ba, ni kuma ban fasa nunawa ??ana shi ne ubansa ba saboda shi ne ubansa din na gaskiya, a kokarinsa na mantawa da ni ya auro mahaifiyarsu Aisha da Narjis, ita kuma ta zo sai ta zama mace mai sanyin hali da son gaskiya, tana ta kokarin sada Aliyu da mahaifinsa sanadin haka har aurenta ya taba mutuwa daga baya aka dawo da ita, amman bata fasa abun da take ba har ta yi nasarar samawa Aliyu ??aki a bangarenta ya zamana shi ma zai shiga yayi yadda yake so kamar ??an gidan, tun daga lokacin nake matukar kaunar Aliyu kuma nake tausayinsa domin laifina ne ya shafe shi, wata kila har da maganin da abokan zamana suka yi na shiga tsakakaninshi da mahaifinsa amman wannan abun da na aikata shi ma ya shafe shi, ya shafa masa bakin fenti da idan Mai Martaba ya kalleshi yana tuna abin da ya faru. Da iyayena suka rasu aka raba gidan mu sai na dawo a wannan gidan da tsohon mijina ya bar mine wato na ci gado, na cigaba da kula da kaina da yayana. Kuma Allah ya taimake ni yayana suka samu tarbiya da suka gama karatu na suka samu aiki, Aliyu kuma ya karkara a bangaren kwallon kafa domin abun da ya fi so kenan ni kuma na goya masa baya%???
12/28/22, 11:06 - Buhainat: %??mashin samun kula daga mahaifi yana matukar tayarwa Aliyu hankali yana damunsa sosai, har yan'uwansa suke son yi masa gori da haka, wata rana da kaina na aka shi a mota na shiga dashi har cikin fadar na zaunar da shi a gaban matan Mai Martaba da yayansa na ce ya fadawa Aliyu da duniyar cewar ba shi ya haifi Aliyu ba, sai ya girgiza kai yace Aliyu ??ansa ne ko be fada ba kowa ya kalli fuskarsa zai san da haka, yace Aliyu jininsa ne, a gaban matansa yace Zainab ma da ba yata ba ina sonta kamar yata Umaima saboda ta fito daga cikinki balle Abiey da yake jinina.
Daga lokacin sai ya samu kwanciyar hankali, nima na dan samu amman na gagara mantawa, sai dai samun ki da Aliyu yayi, na ga farinciki a tare da shi irin wanda ban taba gani ba, kuma kin kawarda tunaninsa kin dauke hankalinsa daga damuwar da mahaifinsa ya saka masa, neman aurenki ma da aka je sai kanensa ne da yan'uwa suka je, amman shi be ce komai ba%???

A rayuwata ban taba jin tausayin wani mutun kamar yadda zuciyata take tausayin Ammy a yanzu ba, daker na iya takaita kukana na share hawayena na ce.

%??mmmy babu wanda baya kuskure, kuma abun da kika aikata Allah ya kaddara sai kin aikata haka din saboda haka ba ki isa ki tsallake haka din ba, ki saka a ranki komai be faru ba, kuma na miki alkawari ba zan taba gudun Abiey ba%???

Rumgume ni ta yi tana dariya tare da kuka a lokaci daya tana saka min albarka. Muna cikin wannan halin Abiey ya shigo dakin ya same mu a lokacin da har mun dauko wata hirar ta duniya, sai dai ina jikin Ammy ne idanuwana da nata sum kumbura.

%??me kuke yi ma kuka%???

Abiey ya tambaya cikin fargaba duk da kasancewar ya ga murmushi a fuskarmu, ni kuma sai na amsa masa da cewar, ina bawa Ammy labarin mahaifina da ya rasu ne shi ne abun ya saka mu kuka, ya fada cikin labarin da muke aka dasa wata sabuwar hira. Na dade a gidan sannan Abiey ya maida ni bayan ya bi da ni ta gida. Hiayatee haka Abiey yake kirana tun daga lokacin da aka yi ana baiko, muka cigaba da rayuwa da nunawa juna soyayyah, Ranar da na gama graduation na Secondary school na ga gata kamar yar wani minister duk wani abu da zan rawa kawaye da kuma wanda na yi amfani da shi Ammy ce ta yi min, sannan ta tara yan'uwanta da Anty Amarya daga bangaren Mai Martaba suka zo. A lokacin ne Abiey yayi min kyauta da wayar hannu daman na dade ina mafarkin samun wayar amman ba dama domin Mama ba zata siya min ba, na san kuma idan na yi ma Ammy ko wani magana za a ce na bari sai nan gaba, ashe gaban a kusa take. Daga lokacin sai shakuwa da soyayya ta karu tsakanina da Abiey wayar safe dabam ta rana dabam haka ma ta dare, ban tabbatar ina Abiey sosai da sosai ba har sai da na fara damuwa da alakar dake tsakaninsa da Safeena, duk kuwa da na san kawarsa ce tun kamin ya hadu da ni, sai dai a yanzu kawance su na cutar da ni, ko dariya yayi mata sai na ji raina ya bace, sanadin haka na shata musu line da ban yi zaton Abiey zai bi ba, sai gashi ya saurareni kuma ya jingine abotarsu a gafe.

Bayan kammala bikin makarantar sai aka fara maganar aure a tsakanina da Abiey, a lokacin ne Mama ta tuntubi Baba domin ya fara bata wani abu a cikin kudin gadon mu da ta bashi ta fara siya min wasu abubuwan, sai ya fara kame kame daga karshe ya sanar da ita cewar ya taba kudin kuma sa'ar siyar da Furnitures da ya fara abun be karbu ba, ba Mama kadai ba ni ma kaina na shiga tashin hankali a lokacin, domin na san da kudin Mama ta dogara kamar yadda ta yi ma Yaya Maryam hidima da su. Yaya Maryam da Mama suka rika siyen abubuwa da be fi karfinsu ba suna aje min. Ana sauran wata biyu bikinmu Ammy ta samu Mama ta fada mata cewar ba za su kawo lefe a yanzu ba saboda gujewa idon mutane tace za a aje min komai a dakina sai dai na tararda shi acan, amman za su min tufafin da zan saka na biki, a nan ta yi ma Mama albishir da cewar bata bukatar komai daga garemu apart from kayan daki har zuwa na kitchen ta tanadi komai, idan an daura aure ni kawai za a kai musu, a ranar Mama ta kwana da farinciki domin samun mace irin Ammy abu ne mai matukar wahala.
Bayan sati daya da faruwar hakan Ammy ta maida ni gidanta aka fara min gyaran jiki ana ba ni kulawa, kar ka so ganin yadda fatata ta zama, fari na ya kara fitowa kyauna ma ba a magana, hankalina a kwance muna ta zuba soyayya ni da Abiey, sai dai duk tsawon lokaci Deen ya dauke kafa daga zuwa gidanmu sai dai dukanmu mun dora hakan a kan rashin lafiyar da aka ce yana yi, na sha zuwa duba shi kamar yadda Mama ma take zuwa, sai dai daga lokacin da na koma gidan Ammy da zama sai ya zamana bana fita ko'ina daga gida sai gida, Abiey ma sai a waya muke hira, idan kuma yana son ganina sai dai yayi irin shigowar nan da babu sanarwa ko kuma ya ritsamu a falo ko ??aki.
Ba ni da wani damuwa ko tashin hankali ina rayuwar kamar wata yar sarki kauna ake nuna min ga ko'ina, har auren mu ya gabato ban ga wani canji a gurin Abiey ko iyayensa ba har sai da ya rage sauran kwana biyu bikimmu, duk wasu shagulgula an gabatar kamin ranar sai dai na lura Ammy da Dr Zainab kamar akwai abun da suke boye min, Abiey ma na fahimci akwai damuwa a tare da shi ta hanyar hirar da muke, Dr Zainab ta zo ta dauki jinina ta fada min cewar ta dauki na Abiey zata je ta gwada, ban kawo komai a raina ba duk da kasancewar an dauki na farko tun kamin a saka mana rana, sai na dogara da abun da ta fada cewar ba zata bari a daura auren ba tare da ta sake yi mana gwaji ba, ba a matsayinta na yayar miji kuma likita, ni kam ban dauki abun da muhimmanci ba, har zuwa ranar da za a daura aure ban samu wata matsala

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login