Showing 30001 words to 33000 words out of 210919 words

Chapter 11 - CIWON SO

10 Oct 2024

4198

nuna tana ganinsu saboda ta bawa Ammy damar natsar da danta da kuma fada masa gaskiya irin ta uwa ta gari. Ammy na fitowa daga falon Anty Amarya ta kusa cin karo da Mama Lami dake kokarin shigowa falon rike da bandir din kudi a hannunta, da alama wani ya labarta mata cewar an ga shigowar tsohuwar matar sarki a gidan, domin ba kasafai kake ganinta gurin Anty Amarya ba sai irin wannan ta samu, kasancewar kowa da bangarensa kuma da masu yi masa hidima ga kuma yayansu, sai dai idan Ammy ta zo gidan da kanta take zuwa gurinta ta gaisa da ita ko kuma ta fakewa da ta zo gurin Anty, idan ba haka ba ko kusa da part din Anty Amarya bata bi, Anty Amarya dai ce take biye da su kullum kamar yarsu.

%??ma Maa Shaa Allah, Hajiya Umaima yau a gidan na mu%???

%??mi ce, ai kin san idan aka gan ni a gidan nan ??ana Aliyu aka ta?o%???

%??maba dai Hajiya ai ba a cin gira kusa da ido, ko ba komai an mun ci ki a sakaya sunan Abiey, kuma yan iya magana sun ce ka ki naka duniya ta so shi%???

%??mo ni na so ??ana, ki buga tambura ki yi shela ki ce duniya ta ki Aliyu%???

Murmushi Mama Lami ta yi tana kallon Abiey da tuni ya kai gurin motarsa domin basa shan inuwa ??aya da Mama Lami duk cikin mata mahaifinsa ya fi tsanarta kara ma Hajiya Kilishi yana daga mata kafa sosai, amman Mama Lami ko Anty Amarya ta cilasta shi gaisheta ji yake kamar tace ya cire ranshi ya bata. Dauke kai ta yi ta tura kofar dakin Anty ta shiga tana dariya, Anty na ganinta ta karasa sauko da take suna gaisawa.

%??mai ni Umaima tana ba ni mamaki, ka bar gida amman kishi baka bar shi ba? Ko gani take kamar ni na kashe mata aure da Mai Martaba ne? A duk lokacin da zan hadu da ita magana sai wance ta manta?%???

Anty Amarya dai bata ce komai ba bayan murmushin da ta yi ta mika hannu ta karbi kudin da Mama Lami take mika mata.

%??mar ribar da aka samu ce ta watan daya shige Mai Martaba ya bada yace a raba, shi na na dan debo miki ke da su Aisha%???

%??moh mun gode Allah ya saka da alheri ya karawa yi ma arziki albarka%???

Ta fada bayan ta karbi kudin, Amin ma wuyar fitowa take a bakin Mama Lami idan isar ta tashi haka tasa kai ta fice ba tare da ta amsa addu'ar da Anty ta yi ba. Sai da ta fice sannan Anty ta girgiza kai.

%??mhmm wasu mata na mulki, wato har an kawo an raba ban sani ba sai da aka debo aka sammana, akwai Allah ba a nan zamu dawwama ba Lami%???

Ta fada tana jin wani kololon bakinciki na taso mata, haka suke mata sun maida ita ba kowan kowa ba a gidan, tana cikin gidan sai a yanke hukunci ayi komai bata sani ba, yaya biyu ma da Allah ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? bata sai sun ga dama Mai Martaba yake musu abu, kuma abun da duk suka ce haka za'ayi musamman ma Mama Lami, Anty Amarya kam da ita ta banza duk daya a gidan aikinta kawai ranar girkinta ta yi girki ta shiga ta kula da mijinta, amman komai na shi bata sani ba kuma ba a iya yanke hukunci tsakaninsa da shi sai abun da abokan zamanta suka yanke.



ZAHRA POV.

Bayan sun kwantar min da shi a saman gado suka fice suna masa addu'ar samun sauki, ni kam ban da aikin hawaye babu abun da nake, na kai hannu na taba shi na dauke na tambaye shi me ke masa ciwo amman be amsa min ba, sai runtse ido yake alamar yana jin azabar ciwo. Sai can hankali na ya bani na kira Hajiya na fada mata, jiki na rawa na dauki wayar na kirata ina kuka na fada mata halin da yake ciki sai hankalinta ya tashi kamin karasa maganar ta kashe wayar, sai na kira Mama na fada mata ina ta kuka. Sannan na kashe wayar na dawo kusa da shi na zauna na kama hannunsa na rike sai ya kalleni ya lumshe idon yana matse hannuna da yake dake cikin nasa.

%??mannu%???

Na fadar daker saboda kuka, be amsa min ba, be kuma yi min wata alama ta amsawa ba, be kuma sake bude idonsa ba hakan ya saka hankalina yayi mugun tashi, da sauri na tashi na shiga daki na dauko hijabina na saka na fito da zimmar na shiga makota na samu mai taimaka min mu kai shi asibiti kamin Hajiya ko Mama su iso, sai na yi kicibus da Hajiya da ta nufo kofar gidanmu ina kuma na fito sai na nufeta ina kuka, ita ma kana ganinta ka san karfi hali ne kawai irin na manyan iyayen da basa son nuna kuka a gaban yayansu.

%??ma kuka ake ba, addu'a ake%???

Tana rufe baki na hango Baba tare da Mai Napep suka faka a inda muke tsaye sannan ya fito da saurinsa.

%??mhiga mu fito da shi a kai shi asibiti%???

Na juya da gudu kamar ba mai ciki ba na shiga cikin gidan Hajiya ta biyo bayana, da taimakon Baba da Hajiya suka fito da shi waje suka saka shi napep din, makotan da ke kusa da mu suka fito suna fadin

%??mubhanallahi Allah ya bashi lafiya%???

Ni dai ko kallonsu kasa yi na yi balle na amsa sa Amin, sanin Napep din ba zata dauke mu gaba daya ba yasa na rufe gidan na nufi titi na tari wata napep din na hau na bi bayansu. Kamin mu isa asibitin Mama ta kira tana tambayar muna ina ta zo gida a rufe sai na fada mata cewar muna hanyar asibiti. Kai tsaye mai Napep sin daya dauke su Emergency ya nufa da su ni kuma nawa mai napep din ya sauke ni a ida aka kayade ma masu abun hawa aje passengers, na saka hannu a jaka na dauko kudinsa na mika masa ban ko tsaya karbar canji ba na nufi cikin asibitin da saurina kamar na tashi sama.
Ko da na isa har sun karbe shi sun shiga da shi ciki, ni da Hajiya muka zauna a inda muka ga wasu zaune kam kace kwabo har wata nurses ta fito ta fada mana inda zamu je mu karbo file dinsa bayan ta gama tambayar cewar yana da file a asibitin, sannan likitan ya kira Baba yana tambayarsa miya faru kamin mu kawo shi asibitin, Baba ya kira ni ni kuma na fada masa abun da abokan aikinsa suka fada mine, sannan suka tambayi ciwonsa muka fada musu, a take na ga hankalinsu ya tashi.
Ana kawo file din suka ware masa wani daki dabam suka rubuta mana wasu tests da hoto da zamu je mu yi, ina mika hannu na karba Baba ya karba ya ce na zauna na yi jinyar mijina.

%??mo ba a matse mutum mai irin wannan ciwon, ke kanki kina bukatar gwaji a yanzu, duk wanda yake tare da shi yana bukatar a gwada shi, balle ke ma da kike da ciki%???

Likitan ya fada, sai na daga ido na kalleshi.

%??maboda me?%???

%??miwonsa ya kai matakin da zai iya shafawa wani%???

Na kalli Deen hawaye na sauko min, can cikin kuka na ji Hajiya ta mika hannu ta karbi wayar hannuna tana amsawa Mama dake kirana tare da fada mata inda muke. Yanayin yadda jikin Deen yake ya saka sai a dorashi saman gadon zuwa gwajin da aka rubuta masa da kuma hoton, wannan karon kudin da muka kashe ya fi wacan yawa saboda sun ce wannan babban hoto ne gwajin ma babba ne. Kam kace kwabo mun kashe kusan 100k+ a rana daya na gwaji kawai sai na dan maganin da muka siyo masa.
Bayan sallah La'asar muna zaune office din likitan ya dubu ni ya ce.

%??marki ji kunya ko nauyin tambayar da zan miki, kuma karki boye min komai%???

Na daga masa kai idanuwa a kumbure saboda kukan da na sha.

%??mor how long kika san mijinki yana dauke da wannan cutar%???

Na fada masa, sai ya dora min da wata tambayar.

%??mdan mijinki zai yi mu'alama da ke yana saka condoms? Kuma ya yanayin mu'alamarku yake? Kuna sharing the same room%???

%??mar abinci tare muke ci, kuma baya amfani da wata kariya%???

%??ma taba fada miki cewar likitoci sun ce ya kebe kansa?%???

Na girgiza masa kai alamar aa.

%??meriously kina bukatar a gwada ki, gwaji na gaggawa ba ke kadai ba har iyayensa suna bukatar gwaji%???

Gaba daya sai kaina ya kulle taya ciwon anta yake iya shafar wani? A zatona hiv ne kawai yake irin wannan illar! Ban ankaro ba na cinkayo muryarsa yana fadar.

%??maskiya idan har kuna son rayuwarsa dole ne, ku samo kudin nan idan ba haka zai iya rasa rayuwarsa, domin ciwon ya kai matakin da baku tsammanin mataki ne da ake kiransa da stage 4, and for now on ba za a sharing komai da shi ba har sai idan ya samu lafiya%???

%??mmman zai warke likita?%???

Na tambaya domin shi ne kawai abun da nake burin ji a yanzu, sai ya kalleni kamar ma nazarin yadda zai furta min amsar da zata fito bakinsa.

%??mn Shaa Allah%???

Ban ga alamun haka a furucinsa da yanayinsa ba, sai dai hakan be isa ya karya min guiwar nemawa mijina kudin maganin ba. Ba mu bar office din ba sai da ya rubuta min gwaje gwajen da zan je na yi ni da Hajiya, duk yadda uwa zata yi ta karfafawa yarta guiwa Mama ta yi sai dai hakan be hana ni kuka ba, kuma be hanani shiga dakin da Deen yake ba, na ja kujera na zauna. Na yi zaton bachi yake sai ya bude ido ya kalleni kamin ya miko min hannunsa, ba tare da tunanin komai ba na mika masa nawa hannunsa sai ya maida idon ya lumshe, wanda hakan yayi daidai da shigowar Mama. Kallona ta yi kamin ta kalli hannunmu dake tsarke da na juna.

%??mi bar shi ya samu bachi mana%???

Bana son musa mata ko ba komai be kamata na rike hannunsa a gaban idonta ba hakan ya saka na sake shi, sai ta yi alama da na fita da ido, a take na mike tsaye na nufi kofar, ina fitowa ita ma ta fito.

%??mi tafi ayi miki gwajin, kina jin abun da likita ya fada%???

%??mabu wani gwajin da za ayi min Mama, idan ma na kamu da ciwon ko ban kamu da shi ba, ba zan nisanci mijina ba%???

%??mo baki yi dan kanki ba ai kyayi dan abun da yake cikinki ko?%???

Na sauke ajiyar zuciya, ba dan na so ba tafi aka min gwajin a anan ma kudi aka kashe kan kace kwabo dan abun da Hajiya da Baba suka tara ya kusa karewa abu ga talaka.
10/1/22, 22:03 - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/GeA5I4zviDSCnz8xJdG885

*B??0? ?]Mq?? CIWON - SO B??0? ?]Mq??*

By Khadeeja Candy


*For special advert contact 08036126660*


1??_/Q1??_/Q

Jinina suka diba sannan aka shiga dashi dakin gwaje gwaje, bayan mun fito ina jin yadda Hajiya ke fadawa Mama likita ya tabbatar musu ciwon ya kusan lalata hantarsa, sai dai gaba daya hankalin Mama yana kaina ne, na lura tsoro take tana ala ala kar ace ina dauke da ciwon ni kuwa a yanzu ba shi ne a gabana ba, burina ya za'ayi mijina ya samu lafiya.
Alhamdulillah shi ne abun da Mama ta furta lokacin da likitocin suka tabbatar dacewar lafiya kalau nake babu wani ciwo a tare da ni, sai dai hankali ya tashi sosai ganin likitocin da suke zuwa duba Deen, idan wannan ua shiga ya fita wannan ya shiga, basa ce mana komai sai dai su yi magana a tsakaninsu, a kuma yawan shiga da fitan da suke bana jin Deen ya ga fuskar daya daga cikinsu domin idonsa a rufe yake kamar mai bachi wata kila kuma bachin yake ban sani ba.
Bayan mun gama sallah isha'i, Bahijja ta kawo mana taliyar da Hajiya ta buga mata tace ta dafa, kusan lokaci daya suka shigo da Yaya Maryam da wanta ta kawo mana tuwo tare da mijinta, gaba daya hankalinta yana kaina, har mijinta na lura ni kawai yake kallo da alama sun yi zance na ita da mijin nata, ni dai kallo daya na musu na dauke kaina mijinta ma tun da muka gaisa yace min ya mai miji bakina da na shi be kara haduwa ba. Sai kusan tara da rabi suka fito ganin ban motsa da zimmar rakata ba ta kalle ni ta ce.

%??manwata babu rakiya%???

Na dago na kalleta da fuskata data gama bayyana rama ta ta wuni daya da tashin hankalina.

%??mi rakata mana, tun dazun kina zaune guri daya%???

Mama ta saka baki, hakan ya tabbatar min cewar akwai maganar da Yaya Maryam take son yi da ni, a dole na yunkura na tashi ina jin cikin na min wani irin nauyi da be taba yi min ba. Ko da muka fito dakin mijinta har ya bace a ward din, muka jero a tare muna tafiya.

%??manwata ki kwantar da hankalinki Deen zai samu sauki, kuma kin ga likitoci sun ce a nisance shi ya kamata ki kiyaye wannan ko dan babynki%???

Na kalleta ina mamakin yadda zata iya bude baki ta furta kalmar na nisanci mijina.

%??ma kike magana kamar baki san tsakanina da Deen ba?%???

Sai ta yi saurin dafa ni.

%??ma sani, wata kila shi ya saka ya kasa fada miki gaskiyar cewar likitoci sun ce yana bukatar kariya saboda akwai shakuwa sosai a tsakaninku wata kila kuma....%???

Bata karasa ba, ni da ita muka huya muna kallon Mama da ta kira sunana tana ta zuba sauri.

%??mahra... Ki bi Yayarki ki kwana a gidanta, idan kuma gidana kike son kwana sai mu tafi%???

Shi ne abun da Mama ta fada a lokacin data karasa kusa da mu.

%??man kwana a nan%???

Na fada muryar a sanyaye kamar cike da damuwa.

%??ma ba zaki kwana a nan ba, damuwar kuma ta isa haka, idan kika kwana a a nan ba zaki dauke masa ciwo ba, ki yi ta addu'a kawai%???

Zan bude baki na yi magana Yaya Maryam ta rika fuskarsa.

%??mar kanwata ki rika jin magana jin? Tun da Mama tace mu tafi ki bini mu tafi mana%???

Na daga kai a hankali akamar toh ba san ina son zuwan ba, sai dan bana son na yi musu a yanzu, domin bani da karfin musun da dai a da ne zan iya har sai sun yarda sun barni.

%??mari na yi ma Mama sallama%???

Na fada ina juyaawa na koma inda na fito, tafiya kamar wanda ke jin nauyin kafa haka nake takawa har na isa cikin dakin na tura na shiga sai na samu Hajiya ita kadai a dakin Bahijja ta fita, wata kila an aike ta siyo wani abun ne ko kuma waya take oho.

%??majiya zan bi Yaya Maryam ma kwana a can%???

%??moh Allah ya tashe mu lafiya, Zahra dan Allah ki kwantar da hankalinki kin ji%???

Na kalleta kawai na dauke kai na kalli Deen na matsa kusa da shi na kai hannu zan taba na ji ko jikinsa da zafi ko akasin haka sai Hajiya ta yi saurin rike hannuna.

%??marki taba shi, baki ji abun da likitoci suka ce ba?%???

Na kalleta da sauri ina mamakin yadda yau ciwo zai hana ni taba mijina, kamin na juyo na kalli Deen da ya bude idonsa a hankali ya kalleni har yanzu idonsa ba su koma daidai ba, suna nan da kalar rawaya wato yellow sai ma kara kala da suka yi, murmushi ya sakar min, a yau kuma sai murmushinsa yafi min kyau fiye da ko yaushe, sai na ji kamar be taba murmushi mai kyau irin wannan ba, hawayen da ya cika idona ya sauko a fuskarta be riga na shi saukowa ba, wata kila shi ma yaji wani banbara gwai ance kar na taba shi abun da ni da shi ba mu saba ba.

%??mshe wannan ranar zata zo Zahra, ranar da wani zai mana shamaki%???

Ban san lokacin dana kurfa a gurin ba na fara kuka, sai ya maida dubansa a gurin cikina.

%??mllah ya raya min abun da zaki haifa min%???

Har lokacin hawaye yake irin hawayen da ke nuna shi kansa ya yanke kauna daga samun lafiya. A take Hajiya ta tashi ta fice dakin da sauri tana kuka, ni kuma sai na matsa kusa da shi na kama hannunsa na dora saman cikin na kasa magana sai kuka.

%??m'm sorry soyayyarki da kaunar kasancewa da ke ta saka, na kasa yanke mu'ala da alaka da ke, ina son ki Zahra ina kaunarki sosai, ina kishin ace bayan rayuwata zaki sake auren wani namijin, ina jin kamar zuciyarki ta kasance dan ni ni kadai...%???

Ya yunkura ya tashi zaune sai ya kasa hakan yasa ni na dago na kama hannunsa na rike dai ya jimke hannun nawa.

%??mi min alkawari Zahra... Ki daukar min alkawarin da ko da bana raye ba zaki karya shi ba...%???

Shigowar Mama ce ta katse komai ciki har da furucin da Deen be karasa ba, balle na san wane irin alkawarin da yake son na yi masa, wanda na tabbatar da zan iya masa shi ko da kuwa rai na zai bar jikina.

%??mahra... Yayarki na kiranki%???

Mama ta fada tana kallona ta kalleshi tana kokarin fahimtar abun da yake faruwa, domin har lokacin hannuna yana tsarke cikin nasa. Sai dai jin furucin Mama ya saka ya zare hannunsa daga nawa ya lumshe ido.

%??mama zaki iya ba mu minti biyu?%???

Na tambaya daker saboda kuka.

%??mkwai wata matsala ne? Baki tunanin mijinki na bukatar hutu? Da safe ai sai ku karasa maganar%???

Na saka hannuna na share hawayena na mike tsaye ina jin kamar ba zan iya tafiya ba, zuciyata na raya min kamar idan na tafi zan dawo na tararda gawar Deen ne. Sai da na kai kofa sai kuma na juyo na kalleshi ni yake kallo fuskarsa na nuna akwai magana a tare da shi, sai dai ban iya komai ba na juya na fita taku daya biyu ana uku sai ga Mama ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login