Showing 99001 words to 102000 words out of 210919 words

Chapter 34 - CIWON SO

10 Oct 2024

4209

Jamila domin ta yi musu rakiya har bakin kofar falon. Gefe na ja na tsaya har sai da suka fice sannan na shiga cikin falon akan kujera na zauna ina jin sanyin ac kamar yayi min yawa, kasa kasa nake kara karewa daular falon kallo lallai mai gidan nan be san zafi dukiya ba sam, idan ba haka ba wannan gyara da falon ya sha kamar ba za a mutu ba, Allah yasa ma duniyar ta Allah ce...

%??mahra...%???

Ina tsaka da gulmar zuci Hajiya Jamila ta kirani a tsawace, ai ko a razane na juyo na kalleta.

%??mor the last time karki sake zauna min akan kujera, ya zama na karshe da zan sake miki magana%???

Na kalli wata tsohuwa da kuma wani matashiyar yarinya da zan kanwa ta uku da ita da suke falon sannan na sauke kaina kasa na sauka daga kan kujerar.

%??moh Hajiya%???

Na amsa zuciyata na sosuwa domin ko kadan ban jidadin yadda ta yi min a yanzu ba, idan a dazun saboda mutane ne yanzu kuma fa?

%??ma so mu je%???

Ta saks fada a tsawace, sai na mike na bi bayanta domin tuni ta yi gaba abun ta, inda muka bi dazun muka sake bi sai dai wannan karon dakin dake kusa da ke kusa da na dazun ta shiga na bi bayanta sai na tsinci kaina a cikin wani daki mai cike da kayan wasa yara an kawata ko'ina kamar yadda ake yi ma ??akin yaran turawa yaran ma yan gata, wutar ??akin ma wata kala ce mai kama da blue da ratsin pink a ciki, Wani karami gado na hango jaririn kwance yana ta sharar bachi, na dunkule shi da kayan sanyi irin masu tsadar nan.

%??mhiga ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?bandakin nan ki wanke hannunki%???

Ta fada tana nuna min bandaki fuska babu annuri kamar wanda ta yi arba da makiyiyarta. Kamar na ce wani abu sai kuma na nufi bandakin na bude na shiga, ashe a nan din ma wata duniyar ce mai abun kallo da mamaki, domin ban ga wani mai na wanke hannuna ba sai tawul ko gurin da ruwa zai zuba ban gani ba, hausawa sun ce ??an hausa ba bobawa ba, dan sink din da na gani na duka ina karantawa sai na ga an yi hoton omo a na farko a na biyun kuma ruwa, latsawa na yi a zatona zai zubo min detergent din ne, amman shiru hakan yasa na kai hannuna kasa da zimmar latsa kasan sai kawai na ga sabulun ya zubo, tsabar mamaki ban san lokacin da na bude baki ba.

%??maaa....%???

Na janye hannun na murza sabulun na wanke sannan na tara inda aka yi hoton ruwa sai ruwa suka zubo a hannuna na wanke sannan na saka tawul din na goge na fito.

%??mauko shi a hankali%???

Wani irin shauki na ji ya kamani, jikina rawa na mika hannu na dauko ??ana ina kallon fuskarsa zuciyata na kara cika da kaunarsa, ji na yi kamar na rumgume shi a kirjina amman ba dama dogon hancinsa be yi min kama da na rowa ba sai Deen, a take idona ya cika da hawaye har suna kokarin zubo min, juyawa ta yi ta fice ba tare da tace min komai ba, sai na bi bayanta a lokacin ne na samu damar sumbantar ??ana. Muna fitowa mu ka kusa cin karo da wata budurwar da ba zata wuce sa'a ta ba idan kuma ta dara ni kadan tana sanye da doguwar rigar da tafi kama da bachi, sai ta nuna ni tana murmushi.

%??me ce Zahra ko?%???

Na kasa amsa hawayen da suke makalle suka zubo min a fuska. Hajiya Jamila ta juyo ta kalleni.

%??mta ce ya aka yi?%???

%??maya yace na kirata zata gaisa da su Gwaggo%???

Budurwar ta fada tana yatsina ma Hajiya Jamila fuska, sai da Hajiya Jamila ta kalleni daga sama har kasa sannan ta mika hannu zata karbi yaron.

%??man iya zuwa da shi%???

Na fada da sauri ina kauce domin ji nake kamar kar a raba ni da shi.

%??mi je da shi gidan uban wa? Dallah ba ni yaro na%???

Ta karbeshi da karfi wanda hakan yayi sanadiyar tashinsa daga bachi ya fara mika da hannayensa dake sanye da safa, na saka hannu na share hawaye sannan na kalli yarinyar wasu hawayen na sauko min, Hajiya Jamila kuma ta ja tsaki ta wuce ta bar mu a tsaye black beauty din ta bita da harara tana tabe baki, sannan ta rika hannuna ta nufi wata hayar da ni, sai da muka fita daga corridor sannan ta sake tana fadin.

%??mi wacan matar sai kin yi hakuri da ita, bata da halin kirki sam, ni ma nan karfen kafa na zame mata da yanzu ta kare ni kamar yadda ta kori yar'uwata%???

Na saka hannuna na dama na share hawayen sai dai ban ce mata kofar ba har muka isa gaban wata kofar bude kofar ta yi sai gani a cikin wani madaidacin falo mai kyau ga sanyi kamar kasar turawa, sai da ta kai farkon falon ta bude wata kofar muka fita waje, a nan ma wani bangare ne na harabar gidan iska sai kadawa yake saboda hadarin dake haduwa a samaniya, wani apartment din muka nufa da be yi girman wanda muka fito ba, sai da ta yi knocking sannan ta tura sai da ta fara shiga sannan na bi bayanta. Madaidacin falo ne mai cike da kayan kallo da kujeru sai dai be yi kyau sauran ba, Mijin Hajiya Jamila na zaune a kasa kusa da wata tsohuwa, sai kuma wasu manyan mata su hudu suna zaune saman kujera, budurwar ta karasa kusa da matan tana fadin.

%??mata nan%???

Na zauna daga nesa da su a kasa, sai Alhajin ya ce

%??mo ta so ki zauna kan kujera%???

%??ma nan ya isa%???

Na fada ina maida kaina kasa.

%??mllah sarki yarinya mai hankali, ya sunanta%???

%??mama ce amman dai ita Zahra ake ce mata%???

Alhajin ya amsa mata da muryar da nake iya karantar murmushi yake yi.

%??mllah sarki Fadimatu ce, an gode kin ji Allah yayi albarka ya kawo miji na gari idan kuma akwai ya bada zaman lafiya%???

%??mamila tace mijinta ya rasu, lokacin da abun ya faru tana da ciki ina tunanin na fari ne ko?%???

Na daga mashi kai sai ya dora da

%??manadin abun da ya faru yasa ta rasa ??an saboda ta zubar da jini da yawa sosai gaskiya%???

%??myyah Allah ya jikan mijinki ya baki wani mai albarka kinji, an gode an gode Alhaji yana ta nemanki ashe zaki tararshi har gida ba in ji Allah%???

Daya daga jikin matan dake zaune kan kujera ta fada sannan sauran ma suka min addu'a.

%??maya yanzu ita zata rika kula da Babyn kenan?%???

Budurwar ta tambaya tana sotsan kanta da babu dankwali.

%??mh Haka Jamila tace, zata dan taimaka tana rika mata shi kamin yagi gwari%???

Ya amsa sannan ya kalli budurwar mai kama da shi ya ce.

%??mmmiter rakata ta koma daman dai zaki gaisa da iyeyena ne%???

Wannan karon yana kallona ya karasa maganar, sai na mike tsaye wanda aka kira da Ummiter ta biyo bayana muka fito.
10/20/22, 09:24 - Buhainat: *Littafin nan na kudi ne, karanta na sata daukarwa kanki hakki ne, domin sauke nauyi biya ki karanta cikin aminci, pay 500 to Zenith Bank Hadiza Abubakar 2451879008 and send the evidence of payment to 08036126660*


ABIEY POV.

A hankali ya busar da iskar bakinsa ya gyara zaman hannunsa na hagu dake aljihu, hannunsa na dama kuma na rike da kofin ruwa. Can kuma ya ciro hannun ya duba agogon dake daure a hannunsa.

%???9:13pm%???

Ya furta sannan ya aje daga kai yana kallon harabar gidan tare da kurba ruwan, ajiyar zuciya ya sauke ya sunkuya ya aje ruwan ya dauki keys dinsa dake kan mini center tebur dake gurin ya juyo ya fito daga backyard din ya dawo cikin dakinsa, kai tsaye ya zarce zuwa kofar fita dakin kamar an korashi haka ya sauko stair ba karamin dadi ya ji ba ganin falon ba kowa, balle ya tsaya amsa tambayayiyin Ammy na ina zai je. Yana isa gurin kofar falon ya bude ya fita be san key din wace motar ce a hannunsa ba har sai da ya latsa key din wata kafirar BMW ta yi kara, sai ya zagaya tsakamin motocin ya nufi inda take ya bude ya shiga yana reverse ya kunna kai daman masu kula da shiga da ficen gidan tuni suka wangale masa gate. Driving kawai yake yana tunanin yadda zai wanke Zahra a gurin Ammy da Anty, musamman ma Anty da yake ganin ta fi kowa daukar abun da zafi.
In 35min ya iso kofar gidansu Yasmin horn yayi aka bude masa sai ya samu guri a harabar gidan ya faka, hakan nan kawai yake jin baya bukatar shiga ciki daman ba gurin Momy ya zo ba balle yace zai shiga ya gaishe ta, wannan zuwan na Yasmin ne kawai, wayarsa ya ciro dake aljihu ya kiran number Yasmin kamar ba zata dauka ba sai kuma ta yi picking.

%??mito gani nan waje%???

Jimmm ta yi kamar ba ta ji abun da ya fada mata ba.

%??moh%???

Ta amsa ya yanke sannan ya maida dubansa gurin kofar falon yana jiran fitowar Yasmin. After like ten min aka bude kofar ta fito tana sanye da doguwar rigar atamta sai mayafin da ta rufe jikin, bude motar yayi ya fito yana jiran karasowarta ita kam bata yarda ta kalleshi ba har ta iso inda yake tsaye.

%??marka da dare%???

%??mow are you?%???

Ya bukata kamar an masa dole sai a lokacin da kalleshi hawaye na sauko mata wasu kuma na taruwa a idonta.

%??m'm not fine%???

%??me too%???

Ya furta yana dauke kansa ya kalli sararin samaniya da iskar hadari ke kadawa.

%??ma zo na yi magana da ke ne akan maganar mu shiyasa ban shiga ciki na gaisa da Momy ba%???

Yana maganar tana masa wani irin kallo kamar ta hade shi.

%??ma yi magana da Abbah Musa na fada masa ina son a fasa zancen baiko...%???

Sai kuma ta yi shiru, Abiey ya tattara dukan hankalinsa da natsuwarsa ya mika mata zuciyarsa na wani bugawar dadi.

%??mhen... Ina jinki%???

%??ma ce ba zan raina musu hankali ba, ban isa na zubar musu da mutunci ba, miyasa ban fadi haka tun kamin su amsawa Mai Martaba ba, sai bayan sun amsa zan taso musu da wata maganar, wai ban isa na maida su kananan mutane ba, ba za su yarda matsala ta taso daga garesu ba, kuma babu fashin aure sai idan kai kace ka fasa....%???

A take annashuwa da farincikin dake tare da Abiey suka gushe.

%??mhat...! What do you mean? Yasmin ya zaki saka ni a matsala... Ya salam.. %???

Ya fada yana juyawa ya daki motar da mugun karfi, kana ya juyo ya rika hade kafadunta yana jijjigata da karfi.

%??masmin ya zaki min haka? Tun abun na sabo da kin yi abun da na fada miki da yanzu haka be faru ba! Miyasa zaki saka mi a matsala?%???

Sai ta amsa masa cikin kuka.

%??mai ka saka kanka a matsala Abiey, miyasa zaka saka zobe a yatsan da ka san idan har za a cire shi sai dai a gutsure shi? Miyasa zaka ambaci sunana a bagirin da zuciyata ta dade tana nema? Na sani ba zaka taba so ba Abiey ni kuma ban isa na bude zuciyata na cire soyayyarka ba....!%???

Sakinta yayi ya matsa baya ya nuna kansa with shock, sai ta daga masa kai ta saka hannayenta biyu ta rufe fuskarta ta fashe da kuka. Baya baya Abiey yayi har sai da ya jingina da motarsa ya dafe kanshi ya duka a gurin yana jin wani zazzabi na taso mashi.

%??ma shiga uku... Yau na ga Idi zigidir%???

Sai kuma ya mike tsaye yana girgiza mata kai.

%??masmin ba zaki iya zama da ni%???

Ta cire hannayenta daga fuskarta tana kuka.

%??man iya%???

%??muciyata babu wanda take so sai Zahra da Zahra ita kadai...%???

%??man roka maka Allah ya sassautawa maka son Zahra Abiey%???

Addu'ar da tace zata yi ta yi farraku tsakaninsa da Zahra sai ya saka a take ya ji ya fara tsanarta.

%??mmadadin kin min addu'a ki raba ni da Zahra, me zai hana ki yi ma kanki addu'a so na ya fita daga zuciyarki?%???

%??mamin yau... Na roka a dare mabanbanta, ka min a kawo yanzu na roka amman ba a amsa min ba sai ma aka kara kawo kusanci a tsakanina da kai ta inda ban zata ba%???

%??masmin indai kina so so na hakika to ba zaki so na shiga matsala ba, kuma zaki so abun da na ke so%???

%??mndai har da gaske kana son Zahra to zaka fi kowa fahimtar halin da nake ciki, Ciwon So masifa ne Abiey da ace ina da iko da ban bari Son ka ya shiga zuciyata ba%???

Ta fadi durkushe kasan guiwoyinta tana kuka, ita kadai ta san abun da take ji, ita kadai ta san halin da take ciki akan Abiey kuma tabbas da zata iya da ta cire soyayyarsa a zuciyarsa, gana daya sai jikin Abiey yayi sanyi, durkusawa yayi kasa ya rika hannunta sannan ya matsa kusa da ita sosai ya rumgume ta a hankali.

%??m'm sorry....%???

Lumshe ido ta yi tana jin kamar ta saka wuka ta tsaka kirjinsa ta shiga cikin jininsa ta kwanta, sai da ya tabbatar ta samu natsuwa sannan ya mike tare da ita tsaye.

%??mi shiga ciki ki huta zamu yi magana daga baya okay%???

Dagowa kai ta yi ta kalleshi sannan ta daga da ga jikinshi tana jin kamar ta rayu a kirjinsa rayuwa ta har abada.

%??ma yi hakuri idan na bata maka rai...%???

Ya hade yawun bakinsa.

%??mo dukanmu ba ma iya sakawa junanmu abu kuma ba ma iya cirewa, ko wace zuciyata tana juyawa bisa ga ikon da Ubangiji ya bata, da ace dan adam zai iya wani abu, na tabbatar da yanzu Zahra ta cire so na a zuciyarta, amman ta kasa saboda bata da iko akan komai, abun da ta yi min dazun yanzu ya kara tabbatar da da har gobe Zahra tana kaunata%???

Yasmin ta yi murmushi irin murmushin nan da hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo.

%??mahra ta yi dace Abiey ka rayu da soyayyarta na tsawon lokaci%???

%??masmin.... Zahra ta so ni ba dan wani abu nawa ba, ni da ita mun kamu da kaunar junanmu ba tare da mun sani ba, sannan Zahra ta cika duk wani sharadi da na ke so a mace, ko kadan bana son na auri mace da ita take so na ni bana son ta, saboda zan iya cutar da ita, Yasmin na shiga a zuciyar Zahra na nuna mata kauna kamin abubuwa su canja mana, ba zan manta lokacin data durkusa har masa tana rokon kar na fasa aurenta ba amman ban iya yin komai ba saboda Deen ya shiryar mana gadar zare, wannan ce damar da nake da ita wanda zan nuna Zahra cewar ina kaunarta irin kaunar da babu wanda ya taba yi mata irinta, ina son na rayu da Zahra fiye da yadda kike jin kina son rayuwa da ni....!%???

Yana kaiwa nan ya bude motarsa ya shiga ya yi mata key ya bar Yasmin a tsaye ta bishi da kallo.

%??miwon so yana dawainiya da kai Abiey, ni kuma be bar ni ba, %?}io%??? baka kyauta mana ba%???

Yasmin ta fada tana hawaye jikinta sai kamshin turaren masoyinta yake.


*** *** ****

Tuki kawai yake yana jin kamar bata son komawa gida, kuma be san inda zai je ba da ma ace irin da ne da Sauban be yi aure da a gurinsa zai tare.

%??miyasa abubuwa suke tasowa su shiga tsakanina da ke Zahra! Why why...%???

Ya buga sitiyarin motar da mugun karfi.

%??mnd kullum daga gurina matsalar nan take tasowa why me?%???

Kamar mahaukaci haka yake fada da kanshi tana jin wani kalar bakinciki marar misaltuwa. Daker ya kalli wayarsa dake ringing ba dan Sauban ne mai kiran ba da ba zai taba dagawa ba.

%??miye?%???

Shi ne abun da ya fada bayan ya amsa kiran.

%??mre okay%???

%??m'm not%???

%??mkay maybe later%???

%??mada min yanzu minene?%???

%??muratu ce tace min ta ga Zahra a gidan yayarta wai an gabatar da ita a matsayin yar aiki%???

Guri ya samu ya faka motar sannan ya gyara zaman wayar a kunnesa.

%??mahra tawa?%???

%??mh yanzu ta dawo daga gidan take fada min%???

%??mahra fa? Anya ta san Zahra da kyau kuwa?%???

%??ma santa mana kasan da ita suka je yi mata gaisuwa tare da Ammy da Dr, kuma na nuna mata hotonta a waya tace min ita ce%???

%??mait.. kana da hotunan Zahra a wayarka?%???

%??mmman dai ka san ba wani abu ke tsakanina da ita ba ko?%???

%??mna aka ce maka an ganta?%???

%??mace gidan yayarta ubansu daya da ita, tace tana zaune aka gabatar da Zahra a matsayin wanda zata rika kula da babyn da yayar ta haifa%???

%??me Zahra ta rasa da zata je ta yi aiki a gidan wani? Ina raye?%???

%??mi ma abun da nake tunani kenan, tace yanzu haka tana gidan%???

%??mna ne gidan?%???

%??me zaka yi?%???

%??m need to see her%???

%??mo idan ma magana kake son yin da ita ka same ta a gidansu zai fi%???

%??man tabbatar ne idan ita din ce, fada min wace area ce?%???

%??man maka text din address din, maybe ma ka san shi wani Alhaji Bashir mai kudi ne sosai kwana baya ma yayi hadarin jirgi, kuma ance be taba haihuwa ba sai wannan karon%???

%??man san shi ba, amman turo min address din%???

Ya sauke wayar da matukar mamaki.

%??mi zai saka Zahra aiki a wani guri?%???

Tambayar da yayi ma kansa kenan har lokacin be daina mamaki ba. Few minutes later Sauban ya turo masa sakon address din, da hannu daya Abiey yake driving dayan hannunsa kuma rike da waya har ya isa unguwar.

Tun daga yanayin area kasan area ce da manyan mutane masu fada aji kuma wandanda suka taka nesa da kafafuwansu suka tsaya, babu gidan da be nuna isar mai shi a unguwar titi ma tsif yake kamar an yi ruwa an dauke baka jin komai sai motsi dogayen itatuwan dake kadawa saboda hadarin da ha hadu a samaniya har ya rufe taurari. Police din da ya gani a kofar gidan da ya banbanta da saura ya tabbatar masa da cewar gidan ne, kai tsaye

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login