Showing 129001 words to 132000 words out of 210919 words

Chapter 44 - CIWON SO

10 Oct 2024

4257

zuwa gurinki sai da na sanar da Abiey, after mun fara shakuwa da juna na sanar masa kudina saboda bama boyewa juna sirri ni da shi, kuma ya nuna min ya jidadin haka, har ya fada min zai fi kowa farinciki idan Zahra ta yarda da aureka, ko ba komai kusancimu zai karu kuma na san zaka rika ta tsakani da Allah%???

%??mata kila ya fada maka haka ne, saboda yana kaunarka a matsayinsa na abokinka, baya son ya nuna maka damuwarsa ranka ya bace, amman na tabbatar Abiey yana so na, kuma dole zai ji kishi idan aka ce muna soyayya ma balle kuma ace na aure ka, ba zan iya haddasa masa bacikin ba, ba zan iya cin amanarsa ba%???

Na fada hawaye na rige rigen sauko min, lallai na yarda dan'adam butulu ne yanzu duk amincin dake tsakanin Abiey da Sauban ace Sauban zai iya tunkarata kai tsaye ya fada min cewar yana kaunata wane irin so ne wannan da zai saka ka manta aminci da abotar dake tsakaninka da amininka ka murje ido ka aure budurwarsa.

%??mi tsaya ki yi tunani Zahra karki yanke hukunci cikin bacin rai, kuma ki duba halin da zan shiga idan kika amsa min da a'a%???

%??mabu wani hali da zaka shiga domin babu komai a zuciyarka sai tsantsar budulci, karka sake ganinka a kusa da ni, kuma kar ka sake kiran wayata ko ka bi a gurin da na bi, idan ka sake min wata maganar sai na sami Abiey da kaina na sanar da shi abun da kake shiryawa%???

Na bude motar na fice a fusace, sai ya bude bangarensa ya fito.

%??mamin ki sanar da ni abun da kika shirya zan riga ki sanar da Mr Bashir abun da kika shirya ke da matarsa, sannan na sanar da Mahaifan Deen abun da kika boye musu%???

Cak na tsaya gabana yayi dukan shida shida, na juyo a matukar firgice na kalleshi.

%??min siyar da ??an cikinki saboda ki ceto rayuwar Deen, kin hada kai da matarsa da yayan matarsa kin mallaka masa ??anki a matsayin nasa, ya kike tunanin zai ji idan ya gane gaskiyar dan da yake alfahari da tutiya ba nasa ba ne? Wane irin hukunci kike tunanin zai yanke miki? Idan ma ya kyale ki yan jaridu da Mahaifan Deen za su saka miki ido ne? Kin ga daga lokacin kin bata sunanki da sunan danki kuma kin yankawa kanki tikitin zuwa gidan yari, wata kila ma zuciyar Mr Bashir ta buga ya mutu a daureki%???

Na tako na dawo a inda yake tsaye hawaye na sauko min kamar ba gobe.

%??m ina ka ji wannan?%???

%??m gurin wanda kuka nemi ta rufa muku asiri ta boye sirrin, wannan abun da kika aikata ya saka Abiey da Ammy da ita kanta Dr Zainab suna murna da yi ma Allah godiya da baki auri ??ansu ba, idan kika san yadda Abiey ya tsane ki a yanzu saboda abun da kika aikata sai kin gode Allah da ya saka ba ku ganin juna a yanzu%???

%??ma da son raina na aikata hakan ba, talauci ne ya saka ni haka%???

%??man jarida zaki yi ma wannan bayanin, rai ya fi rai ne da zaki da zaki siyar da ran da be miki komai ba, tun kamin ya zo duniya? An fada miki talauci hauka ne? Talauci ke saka rai fita daga jiki ne? Ko kuma kina tunanin arziki zai hana mutuwa aiwatar da aikinta ne? Da kika samu kudin kika biya ya tsaya ne? Sai kika yi biyu babu da ace kin yi tawakkali ki bar wa Allah komai da yanzu ba ki shiga wannan halin ba%???

Ba ni da wata dabara sai ta kuka har numfashina yana kokarin fin karfina, cikin saldewar halshe na ce.

%??mauban baka da wannan kusanci da zaka nemi wargaza rayuwata ko da Mr Bashir akan abun da be kamata ya shafe ka%???

%??ma gaske? Baki san ina da kusanci da mutanen gidan ba? Ranar da na shiga cikin gidan na zauna a falo har na aika aka kiraki ba ki yi mamaki? Jamila yaya ce a gurin matar da nake aure a yanzu, ko Matata kadai na sanarwa zata iya ruguza komai naki, saboda haka ina baki shawarar ki yi tunanin abun da zai zame miki mafita tun wuri wanda zai fitar da dake daga taskon dana sani, kwana biyu na baki ki yi shawara%???

%??ma zan aikata abun da kake bukata ba, ba zan yarda na yi butulci ba%???

Na bashi amsa da kakkausar murya sannan na juya na nufi kofar gidan na shiga na bar shi a tsaye. Ina shiga daki sai an samu yancin yin kuka yadda raina yake so, ina nadamar abun da na aikata, gashi sanadin haka na jefa mahaifiyata cikin tashin hankali ni ma kuma na jefa kaina, har ana min bazarana da shi, a cikin kalaman da ya fada min ba wanda ta fi daga min hankali da saka ni bakinciki kamar cewar da yayi Abiey ya tsane ni saboda abun da na aikata.
Na yi zaton Sauban zai sauya shawara ya kyale ni amman sakon karta kwana na gani ya shigo a wayata da sunansa.

%??mi yi shawara da zuciyarki, karki yarda ko Mama ta san da wannan maganar, Wallahi Zahra kin ji na rantse miki da Allah ko? Son da nake miki zai iya sakawa na aikata komai a yanzu, fiye da abun da Deen ya aikata ya shiga tsakaninku da Abiey, kuma ina mai kara tabbatar miki kwana biyu na baki karki yarda ki bijirewa umarnina, idan ba haka ba zaki jefa kanki a babbar matsala%???

Ban yi zaton wata matsalar zata bullon min a bayan wannan da nake ciki ba, da san abun da Sauban zai zo min da shi kenan da ban yarda na kira shi ba, kuma a lokacin da ya zo da ban yarda mun hadu ba. Ko da Mama ta dawo ta tararda ni kwance galala na ci kuka har na gode Allah idanuwana sun yi sundun sundun, daman can bana dauka abu da wasa balle kuma wannan, yaushe Sauban ya lalace ya fara gurbata tunaninsa har zuciyarsa ta daya masa yayi min bazarana da wannan, da gaske zai aikata abun da yake da kudiri akai idan na ki amincewa ko kuma dai ya fada ne! Na rasa amsar tambayar tunani da tashin hankali suka ki sakin kwakwalwata, duk juyin duniyar da Mama ta yi na fada mata dalilin kuka ban fada mata ba, a lokacin da na lura da ta damu sai na fake da cewar korar da Jamila ta yi mana ne ya saka ni kuka, Mama ta yi ta tausasar zuciyata sannan ta yi min albishir da cewar gobe zamu koma gidansu da zama wato family house dinsu da muka baro, kamin a samu gidan haya.
Ana gama sallah Magariba sai ga Dr Hamid ya shigo gidan, kamin ya shiga bangaren Hajiya Jamila ya kira ya sanar da ni yana waje kuma yana son na nema masa izini gurin Mama zai shigo yayi magana da ita. Na sanar da Mama ta bada umarni sannan na fada masa sai yace na fito na yi masa iso, ba tare da tunanin komai ba na saka mayafina na fito, sai na same shi a inda ya saba tsayawa, cikin rashin kuzari irin na wadanda suka rasa madafa na karasa gurin na yi sallama ya amsa min, muka gaisa sannan ya mika min ledar hannunsa.

%??ma na gode%???

%??mllah yasa ba laifin da kanwata ta yi zai shafe ni, na kira na sanar da ita cewar ina nan zuwa sai ta fada min irin kwabar da ta yi%???

%??mana da gaskiya wani gurin ai, ko ni ce ba zan yarda mijina ya kula wasu ba%???

%??mshe ke ma kina da kishi kenan, ki ce na shirya wa kishinki ba sauke kenan%???

Na sauke kai kasa cike da tunanin manufar furucinsa, dariya ce ta biyon bayan maganar da yayi sannan ya dara da cewa.

%??mo ma dai minene bata kyauta ba, kuma ba ta yi abun da ya dace ba, ai hallacin da kika yi mata ko da mijinta kika ce kina son auren be kamata ta daga ido ta kalleki ba balle har ta nuna kishinta akai, amman dai na yi mata fada sosai kuma na nuna mata illar abun da ta aikata, na kwantar mata da hankali na fada mata cewar kina da wanda zaki aura Allah yasa ban yi karanbani ba%???

Wannan karon da kamar zolaya yake maganar, ni kam tawa ma ta isheni yanzu ba zancen tashin gidan ko wulakancin Jamila ne a gabana ba, matsalar Sauban ce data kunno min take chaja min kwakwalwa a yanzu.

%??mahra kamar akwai damuwa sosai a tare da ke%???

%??ma komai%???

Na amsa ina saka hannu na share hawayena.

%??mi kwantar da hankalinki ba, zamu cigaba da zama nan na wani lokaci kawai ba sai an dade ba%???

%??ma zai yiyu mu zauna ba, Mama ta riga ta yi magana da Yan'uwanta za su sama mata gurin da zamu zauna na gode da kulawa%???

%??mhiyasa nake son na yi magana da ita, wata kila zata fiki fahimta da saurin saukowa%???

Na daga kai na kalleshi a kaikaice.

%??ma yi nadamar duk wani abu da na yi Dr Hamid, da ban yarda zan iya ceton rayuwar da ba a hannuna take ba da yanzu ban shiga duk wannan halin ba, na kasa ganewa talauci ya saka na aikata abun da na aikata ko kuma wauta da rashin yardar da kaddara%???

%??mdan har magana kike ta yarda da kaddara to ya kamata wannan kadarrar ma ki yarda da ita ki watsar da komai ki dauka haka Allah ya hukunta miki a yanzu ma ki rumgumi komai da hannu biyu, kuma ina mai tabbatar miki komai zai wuce nan ba da jimawa ba%???

%??mna fatar haka, ni kadai na san abun da nake ji a zuciyata, ji kadai na san halin da nake ciki, na rasa abubuwa da suka kamata su kasance da ni, na ruguza farincikina da kaina, na rasa makama, da ban aikara abun dan na aikata ba da kanwarka bata zarge ni akan mijinta ba%???

Na durkushe a gurin ina jin zuciyata na mini wani irin zafi da zogi na azabar bakincikin da nake ciki.

%??ma ke kika bukaci zama a gidan nan ba, Jamila ta janyo ki saboda haka babu laifinki idan mijinta ya nuna miki kulawa, kuma ai ita da bakinta ta fada cewar mijinta yana neman hanyar da zai saka miki da abun da kika masa, shin tana tunanin zai rika daure miki fuska ne ko kuma ya kareki? Daman can Mr Bashir mutum ne mai son mutane, kar abun da ta yi ya dame ki%???

A tunaninsa ina kuka ne saboda abun da Jamila ta yi min ne kawai, na haka na kaune kashina daya tsaya min a w?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 uya na share hawayena na masa iso gurin Mama, a gaban ya aje ledar hannunsa sannan na durkusa har kasa yana bata hakurin abun da kanwarsa ta yi, wata kila ya cilasta shigowa bangarenmu ne domin yana tsaka da bata hakurin Hajiya Jamila ta shigo ita na ta soma bata hakuri sannan ta dawo kaina tana neman yafiyar abun da ta yi min. Uffan ban ce mata ba domin bata da kimar da zan iya yi mata wani furucin a yanzu, Mama ma ina tunanin ta hakura ne kawai saboda Dr Hamid dake ta yi mata magiya, sai dai hakurin da ta yi ba yarda ta zauna a gidan ba ne ta tabbatar musu da cewar ta hakura amman zancen tashi yana nan domin ta sanar da yan'uwanta.

%??mo ko dai sai na kira Mijina ya baku hakuri ne%???

%??maki bukutar haka ranki ya dade, ai na riga da na hakura, amman idan na ce zan zauna a yanzu ai abun ya zama da rainin hankali yan'uwana ma za su ga kamar na mayar da su kananan mutane%???

%??man iya zuwa da mijina mu ba su hakuri%???

%??majiya ba sai kun yi haka ba, zuwan ku zai kara bata lamarin ne kawai domin ban fada musu cewar kin kore mu ba, kawai dai na fake da cewar ina son na bar gidan ne saboda tsare tsaren gidan basa min dadi%???

%??mama idan haka ne ai zamu iya zuwa mu baku hakuri mu ce su lallaba ku zu zauna, ni kaina ba wai ina son ku zauna na lokaci mai tsawo ba ne, zaman ku a nan ba zai wuce wata daya ba, na miki alkawari Mama zan sama muku gidan da zaku zauna na kanku, ko bayan ni Mr Bashir ma bana tunanin zai barku haka%???

Da ??a??an kalamai da kallamewa da komai suka tirsasa Mama da amince da zama a gidan, bayan Dr Hamid yayi alkawarin zai dauki yar'uwarsa su tafi har gurin dangin Mama su ba su hakuri da neman su barsu su cigaba da zaman gidan.
Kamar yadda ya fada washe garin ranar Dr Hamid da Hajiya Jamila suka saka mu a mota ni da Mama zuwa family house dinsu, su kansu su yi na'am da Dr Hamid da kuma kanwarsa a tunaninsa tana son mu ne tsakani da Allah ba dan wata manufa ba, sai bawa suke suna saka musu albarka. Goma ta arziki Dr Hamid yayi musu sannan muka fito gidan, a hanyar mu ta dawowa gida na ke jin Jamila na fadawa Dr Hamid cewar mijinta yayi balaguron wani aiki na kwana biyu, da muka dawo gidan yana ta kara bawa Mama hakuri, ni kam na zama kamar wani hoto domin babu wata wadatacciyar walwala a tare da ni, hirar da zan iya cewa ma tursasa ni yayi ma tsaya ina yinta ba dadi take min ba.

Ban dauka da gaske Sauban yake ba har sai da na lurar da barazanarsa na kokarin yin yawa, domin kullum sai ya turo min sako yana kara jaddada min kudirinsa, idan na koshe wannan line sai ya aiko min da wani, daga baya sai na kashe wayar gaba daya na aje, da ya fahimci na daina amfani da wayar sai ya koma aiko min sako ta hanyar masu gadin gidan, kamar wani dan'adan haka Sauban ya rikide min ina ta mamakin abun da ya same shi har haka.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Na dauki damuwa da tunanin abun na saka a raina har ta kai bana iya zaunawa na ci abinci yadda ya kamata, ga kuma tsutsata da Amir yake sai ya kara sakawa na zama wata yar tsana daman can ba wani abun kwarai ke a jikin ba balle kuma yanzu da bana da wani abun yi sai tunani da neman mafita, idan kuma na nemi shawarar zuciyata sai ta fada min na amince da kudirin Sauban gudun kar na sake jefa kaina da mahaifiyata a cikin wata damuwar, Dr Hamid ma yayi ta neman sanin abun da yake damuna amman na gagara sanar da Mama ma balle kuma shi da nake ganin ba shi da wata alaka da ni. Sati daya na sakwana bana komai sai addu'a da raya dare da sallah nafila ina neman Allah ya kawo min mafita sai dai ban ga alamar bullowar wata hanyar ba.
Ranar da muka cika kwana takwas da maganar Sauban ya sake zuwa gidan ya faka a harabar gidan ya aiko yana min sallama, ina jin sunansa gabana ya fadi domin na san ba alheri ne ka kawo shi a yanzu ba, tun daga wacan lokacin da yayi min barazana zuwa yau idan ya sallamo a gidan sai na ji kamar na haka rame na binne kaina na huta, a yau sai na kekashe kasa na ce ba zan fito ba.

%??maboda me? Tun farko ba sai da na gargade ki akan zuwa gidan nan da yake ba? Da mai gidan yayi miki magana kika masa magana a wajen gidan kuke tsayawa, yanzu kuma ya riga ya shigo cikin gida ki ce ba zaki fito ba?%???

Na yamutsa fuska cike da damuwa, kalaman na ratsa ni.

%??mdan ma baki son zuwan gidan nan sai ki je ki sallame shi daga yau sallama ta har abada, kin ga daga nan zai daina zuwa, daman can na fada miki ba son zuwanshi nake ba%???


Na nisa ina tunanin tafiyar tawa, domin ban san da wacce ya zo ba tun da har ya iya shigowa cikin gidan kai tsaye bayan kuma na fada masa ba sau daya ba cewar Mai gidan baya son ganinsa a cikin gidan.
Tashin hankali da ba a saka masa rana inji hausawa, sai kawai na ji sallamar Sauban a bakin kofar dakinmu, da sauri na dauki Hijab na saka domin kokarin shigowa yake tun kamin a masa izninin shiga. Mama ma ta tashi ta sauri ta gyara zamanta daman bata rabo da hijabi tun da muka dawo gidan.

%??ma'alaikassalam%???

Mama ta amsa masa, hakan ya bashi damar matsowa sosai kusa da labulen kofar yana tambayar.

%??mama barka da dare, ko zan iya shigowa%???

Cikin sauri na girgiza mata kai alamar ta ce aa amman ba yi min yadda nake so ba, sai ta bashi umarnin shigowa.

%??mh Bismillah%???

Sallama yayi ya shigo cikin dakin ya zauna kusa da kofa ya gaisa da Mama.

%??mauban ka tafi gani nan zuwa%???

%??mannan zuwan ba naki ba ne ke kadai, na zo ne har saboda Mama, saboda na gaji da yawo da hankali da kike min%???

A kaikace na kalleshi ina mamakin yadda zai buga min wata kwallo a ragar da ban san da zamanta ba. Kamin na yi wani unkuri ya fara shimfidawa Mama karyar da ta daure ni da manyan tsarkoki da ba zan iya kwance kaina ba.

%??mama ina son magana dake ne saboda abun da Zahra ta yi min, kuma ina son ki yanke hukunci tsakani da Allah karki duba kusanci da Zahra ko rashin alakarki da ni%???

Yayi shiru ni kuma na zuba masa ido domin na ga iya gudun ruwansa, Mama kuma ta gyara zama ganin babu wasa a tare da shi sai zallar tausayi da ke fita a muryarsa.

%??mama tun ba yau ba mun yi magana da Zahra, magana kuma ba ta soyayyar ba ce ta aure ce, kuma da farko ta nuna min kamar babu matsalar komai, sai daga bayan nan take nuna min kamar ke ce baki son tarayya ta da ita, ni kuma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login