Showing 45001 words to 48000 words out of 210919 words

Chapter 16 - CIWON SO

10 Oct 2024

4194

da yafi kama da na wahala yayi gaba da ni.
Babu komai a cikin mafarkina sai Deen saboda bachi ya dauke ni da tunaninsa a raina, kadan daga rayuwar da muka yi ta zo min kamin wata sabuwar rayuwar da ba mu taba yi ba ta biyo baya, a wani katon gidan sama muke rayuwa a dubiyar mafarki, yana ta kuka ni kuma ina dariya sai yayi baya baya yana miko min hannu sai ni ma na mika masa sai dai kamin na kama hannun nasa sai ya fada a kasa cikin wani abu mai kama da giragira kuma kamar hayaki, na leka gurin da saurin sai na gane gidan saman irin wannan ne da bashi da stairs balle na taka na sauka, har kuma lokacin dariya nake sosai na dukushe a gurin ina leken gurin da Deen ya fada kamar ni ma zan fada din, jin na yi an taba kafada ta bayana, sai na juyo da sauri ina kallon wanda ya dafa ni, sai dai kamin na ga fuskarsa wani ya miko min hannu alamar na kama hannunsa na mike tsaye, shi ma ban ga fuskarsa sai na ji an mikar da ni tsaye an share min hawayena an rumgume ni, a take dariyar tawa ta koma hawaye.

%??me Malama tashi Malama...%???

Firgigit na farka daga mafarkin ina kallon matar dake rike da danta tana tayar da ni daga bachin da be dade da daukata ba, abun da ban sani ba hawayen da nake a mafarki ashe sun fito a idona da gaske.

%??muka kike yi da dariya kina bachi%???

Na yi saurin taba fuska sai kuwa na yi arba da hawayena, saurin sharewa na yi na mike tsaye ina mata godiya, na fara tafiya ina ta tunanin manufar mafarki, a iya sanina mafarkin kana dariya a cikin mafarki to zaka yi kuka a zahiri ne, idan kuma ka yi mafarki kana hawaye a mafarki zaka yi farinciki ne a zahiri kamar yadda masana suke fada, to amman fadawar da Deen yayi daga gidan saman zuwa kasa fa? Me hakan ke nufi?

%??mutuwa?%???

Na furta kamar wanda aka matsi bakinta kalmar ta fito, hankali yayi mugun tashi sai gani ina karawa kafafuwana mai kamar ba mai ciki ba na koma dakin da Deen yake da sauri, sai na samu Bahijja zaune har lokacin tana kuka kawarta na tsaye kanta tana bata hakuri, har kuma lokacin idon Deen a bude suke numfashi kuma yana tafiya a na'urar lura da numfashi, na karasa kusa da shi da sauri ina dubawa.

%??maba ya zo ya karbi takardar maganin, likitan ma ya sake zuwa ya duba shi amman be ce komai ba%???

Bahijja ta fada min, sai na kai hannu kamar na rufe masa idon unexpected na ji ya rika hannuna sai na kalli hannu hankali a tashe na sake kallon fuskarsa sai na yi arba da murmushi a fuskarsa sai dai har lokacin idanuwansa ba su nuna alamar yana kallona ba ko kuma ya san ni din ce ko akasin haka.

%??meen...%???

Na fada da sauri Bahijja ma ta taso tana kallonsa. Be amsa min ba a take na ji wani sabon kuka ya taso min sai nake ganin kamar bankwana yake min, na saki hannunsa da sauri na fice daga dakin, kai tsaye dakin da likitan yake na nufa sai na samu ba shi a ciki office din ma a kulle yake, na fito da saurina ina tambayar nurse din dazun inda likitan yaje.

%??mna tunanin ya fita%???

%??man girman Allah ku kira min shi%???

%??ma komai ba, ku kura shi ko kuma ku bani number shi akwai abun da zan tambaye shi%???

%??mamar me?%???

%??me shafe ki ba, ki taimaka min dan girman Allah%???

Sai suka kalli junansu, kamin dayar ta ciro karamar wayarta ta kira shi.

%??moctor Good afternoon wata ke nemanka%???

Kamar na san zai tambaya yace wacece sai na ce.

%??mi ce masa Zahra ce mai ciki matar Zaharadeen wanda suka yi magana dazun%???

Ta fada masa kamar yadda na fada, sai ta miko min wayar, kamar mai tunani haka na tsaya kallon wayar sannan na mika hannu na karba na kara wayar a kunne.

%??mafiya kike nema na? Babu wani abun da zan iya yi ma mijinki a yanzu sai dai mu duba ma sarautar Allah ido%???

%??mna son magana da kai ne akan maganar dazun%???

Jin nayi yayi shiru sai kuma yace.

%??mo wacan maganar ta wuce ai, na samu wata%???

Kamin na ce komai ya yanke wayar, sai na mika mata hawaye na sauko min, na juya jiki a sanyaye na koma inda na fito wato dakin da Deen yake, sai dai wannan karon na samu idonsa a rufe.

%??me kika rufe masa idon?%???

Na tambayi Bahijja sai ta ce.

%??ma%???

Na matsa ina ta kallon fuskarsa, mafarkin da na yi dazun yana ta dawo min.

%??m'm sorry...%???

Na furta ina jin wani sabon kuka na taso min. A kusa da shi na zauna, ni da su muna dakin har Baba ya dawo daga siyen maganin yana shigowa Likitan dazun shi ma ya turo kofar dakin ya shigo, da farko na yi zaton ko gurina ya zo, sai dai ganin ko kallona be yi ba ya karbi alurar da Baba ya siyo yayi ma Deen ya kuma fadi ka'idar bada maganin da abun da za ki masa idan ya farka sai na fahimci ba saboda ni ya zi nan ba. Har ya gama abun da yake ya fice be kalle ni ba, hakan ya saka na fita daga dakin ba tare da nace da kowa komai ba, salin salin na isa office din ina turawa sai na same shi a bude, da sallama ta na shiga sai ya dago ya kalleni yana magana da wani da nake kyautata zaton shi ma Likita ne.

%??ma aka yi?%???

Ya tambaya kamar be gane ni ba.

%??magana nake son yi da kai%???

%??mkwai abun da nake yi a yanzu, ki dawo anjima%???

%??ma taimaka min dan girman Allah%???

Na roka da magiya kamar na fasshe da kuka, mutumen da suke magana ya kalleshi sai kuma ya juyo ya kalleni.

%??mr Sadiq excuse us please%???

Wanda aka kira da Dr Sadiq ya mike tsaye ba tare da yace komai ba ya fice daga office din sai na karasa kusa da teburinsa, shi kuma ya jingina da kujerar da yake zaune yana lilo.

%??ma akai?%???

Cike da nauyin baki da hade yawu na furta.

%??ma amince%???

Sai yayi murmushi irin na iko.

%??mou late, damar da na baki ta riga ta wuce%???

Ban san lokacin da na kai kasa ba na hade hannayena ina rokonsa.

%??ma taimaka min da girman Allah, dan Allah ka taimaka bani da wata mafitar bayan wannan%???

%??mashi tashi tashi%???

Ya fada da sauri yana min alama dana tashi tsaye da hannu yana kallo kofa cike da tsoron kar wani ya zo ya tararda da mu a haka. Ya dauki wata farar takardar yayi rubutu akai ya miko min.

%??mi same ni a wannan addiren yanzu, kuma karki bari kowa ya sani%???

%??moh%???

Na fada ina share hawaye ina jin kamar damuwata ta yaye, na juya da sauri na fita. Sai da na lake addireshin a cikin jikina sannan na koma dakin na bude jakata ma dauki yan canjin da na san zasu isheni na hau abun hawa, na fito ba tare da na fadawa Bahijja inda zan je ba, daman ban tararda Baba dakin ba. Ina kusa fita ward din na hango Yaya Maryam da Mama tafe sai na yi saurin canja direction har sai da suka wuce sannan na fito ina ta zuba sauri na fice. Tafiyar minti arba'in ta kai ni unguwar Zoo road ciki har da fitowa daga cikin asbiti da kuma tsayawa taron abun hawa. Daidai inda ya fada min na tsaya ko minti uku ba ayi ba wata mota fara mai bakin gilashi ta faka kusa da ni, gilashin motar aka sauke sai na yi arba da likitan alama yayi min da na shigo, sai na shiga cikin motar.

%??mahra har a zuciyarki kin shirya yin wannan abun%???

Na daga masa kai.

%??msakani da Allah ba wai zan yi dan na cuce ki ba, kuma bana son ya zama kamar na cilasta ki%???

%??ma shirya%???

%??mmman miyasa yanzu kika yarda a rana daya bayan dazun da na miki magana baki aminta ba?%???

%??maboda na ceci rayuwar mijina bana da wata mafita bayan wannan, idan ya rayu zamu samu wasu yayan, idan kuma na rasa shi na rasa shi kenan fa har a bada%???

Tare da hawaye na karasa maganar, sai na ji ya sauke ajiyar zuciya.

%??mi da ke duka taimakon juna zamu yi, so yanzu zan kaiki gurin matar, amman ina son idan mun tafi ki nuna mata cewar mun kare magana da ke, ni na fada mata kudin da zata bada kin ga idan mun gama komai cikin lokaci sai a shiga aikin da shi%???

%??ma a iya gama komai a yau ayi masa aikin a yau?%???

%??ma sai dai ayi gama komai a yau, inya so gobe sai a shiga aikin da shi, domin ba ni kadai zan yi aikin ba, kuma dole sai an shirya amman zamu iya saka kudin aikin a yau, sannan wannan kuka da kike kar ki kuskura ki yi shi a gabanta, kuma daga yanzu har zuwa lokacin da zaki haihu karki sake tuntubar wani Likita sai ni%???

Na daga masa kai ina kokarin ganin na tsayar da hawayen tun a yanzu. Gorar ruwa ya dauko ya miko min sai na karba na sha, sannan ya tashi motar, cikon Allah da karfin hali sai idanuwa suka washe kamar ban taba kuka ba, sai dai idona ya kumbura saboda kukan da na yi a dazun, amman hawayen ya tsaya min. Ba mu yi wata tafiya mai isa ba muka iso gaban wani gida mai kyau, sai ya ciro wayarsa ya kira wanda nake kyautata zaton namiji ne saboda yanayin maganarsa.

%??marrister gamu kofar gidan%???

Sai kuma na ga ya kashe ya sake kiran wata number.

%??min iso?%???

%??mkay%???

Ya furta sannan ya sauke wayar ya hanna horn aka bude masa, ya shiga ciki, kusa da wata motar ya faka ya bude ya fita.

%??mito%???

Na bude na fita kamar yadda ya bukata na zagaya na bi bayansa domin tuni ya nufi wata karamar kofa dake can nisa da inda ya aje motarsa. Yana gaba ina biye sai a lokacin tsoro ya fara kamani idan wani abun zai min, hakan yasa na ja na tsaya sai da be lura ba har sai da ya kai bakin kofar shiga.

%??mafiya?%???

Ya dawo kusa da ni yana sake tambaya sai na ce.

%??mllah yasa ba cutar da ni zaka yi ba%???

%??mallahi ba zan cutar da ke ba Zahra, wannan abun ma idan baki aminta ba ba zan yi ba, idan kuma kin canja shawara ne zamu iya komawa%???

Na girgiza masa kai sai dai kamin na furta komai na hango wani mutum ya fito daga dakin da Dr ya nufa dazun.

%??mr Hamid Bismillah ku karaso mana%???

A tare muka rika takawa har muka isa gurin, Dr Hamid din ne ya bude min kofa na shiga sannan suka shigo, tun kamin su ce na zauna na zauna sai muka gaisa da wanda nake zaton shi ne Barrister sannan na koro min da bayanin abun da zayi ya kuma tambayi ko da amincewa za ayi ko kuma cilasta min aka yi, na amsa masa cewar ni nayi ra'ayi da kaina, sai ya tambaye ni cikin yana da uba ko shege.

%??man sunna ne%???

Na amsa ina jin wani abu har cikin raina sai dai babu damar hawaye domin Dr Hamid ya gargade ne tun kamin mu shigo.

%??mmman miyasa zaki siyar da dan cikinki?%???

A wannan gabar Dr Hamid ne yayi masa bayani da kansa, sai ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan dauki wata jaka dake kusa da shi ya bude ya dauko takardu ya fara rubutu akai, yana tsaka da rubutu sai ga matar ta shigo da katon cikinta da sallamarta. Da na kalleta da kyau sai na ga suna kama sosai da Dr Hamid din kamar yan'uwa. Kusa da ni ta zauna fuskarta da murmushi kana ganinta ka san matar manya ce kuma yar manyan mutane, domin fatar jikinta da suturarta sun nuna haka. Cike da far'a muka gaisa da ita ta tambayi sunana na fada mata, sannan Barrister ya gabatar mana da bayani a tare na yadda komai zai waka ciki har da rubutun da yayi, sannan ya miko min takardar na karba na karanta tsab. Cewar A yau 23 ga watan biyar shekara ta.... Ni Fatima Aminu Umar Matar Zaharadeen na aminta na siyar da abun da na haifa ko zan haifa mace ko namiji ga Jamila Abdullahi bisa da kudi naira miliyan bakwai da rabi siyar ta har abada, ba zan tana tutuya cewar dana ko yata ba ce, kuma ba zan taba fadawa kowa ba har abada, babu cilastawa babu tsoratarwa, bisa amincewa ta yarda ta, idan kuma har na karya doka zan biya tara naira miliyan ashiri, an yi haka gaban shaidu a gaban kamar haka Barrister Akilu Kamalu, Dr Hamid Abdallah, sai kuma bayan na gama kara karantawa na lura da inda aka bukaci sa hannu a gurin sheidu sai kuma gurin da zan saka ni da Jamila.

%??min karanta?%???

Barrister ya tambaya sai na daga masa kai.

%??min aminta? Dan karki dawo daga baya ki ce zaki danki ne ko zaki bukaci danki ko kuma ki tona asiri%???

%??ma zan yi ba, amman ina neman alfarmar, ki kula min da da ko abun da zan haifa da amana, ki rike shi tsakani da Allah, kuma ina son ki rada masa suna Zaharadeen, idan kuma mace ce ki saka mata Zahra%???

Ta kalli Dr Hamid.

%??mula da shi, dole ne wannan domin na dade ina wannan mafarkin, karki damu ko dan shugaban kasa ba zai nuna masa gata ba, domin muna da rufi asiri irin wanda baki tsammani, sai dai zancen kasa suna, ba zan iya miki alkwari ba, idan mijina ya bukaci saka mahaifinsa ko mahaifiyarsa babu wata damar hana shi, amman zan iya kokarina na ganin na saka daga daga cikin sunan sai idan abun ya gagara%???

Sai kuma ta kalli Dr Hamid.

%??ma tabbatar da lafiyar Baby%???

%??mdan ban tabbatar ba zan kira a nan ne?%???

Sai ta kai hannu ta taba cikin nawa ta saman hijabi.

%??mannu Allah ya sauke ki lafiya%???

Na daga nata kai ina jin kamar kar na aikata sannan ya miko min nata na karanta suka ba ni biro na saka hannu ita ma ta saka sheidu suka saka, sannan Barrister ya mike tsaye ya fita, sai ta bude jakarta ta dauko kudi dubu goma sha biyar ta miko min.

%??mashi ki hau abun hawa, na gode sosai Allah ya ba mijinki lafiya%???

Na karba, amman na kasa amsawa da Ameen zuciyata ta yi min wani abu babu dadi. Ba mu dade ba Barrister ya dawo ya mika min copy takardun ita ma ya bata ya mikawa Dr Hamid sannan shi ya aje original din. Kamar wata matacciya haka na taso muka fito daga gidan na bude motar na shiga, bayan ya zagayo ya shigo ya kalleni.

%??mahra lafiya kike?%???

Na kalleshi hawaye na sauko min.

%??ma siyar da cikina ka tambaye lafiya nake? No am not%???

Ya sauke ajiyar zuciya ni kuma na kara rike takardun a hannuna.

%??myi masa aikin gobe da wuri, kuma ka fadawa iyayensa da iyeyena cewar wani ne ya dauki nauyi yace kar a fadi sunansa%???

%??mnshallah%???

A inda ya dauke ni ya aje ni, na tari wani abun hawa na hau, bayan ya rubuta min number a wata takardar ya bani. Ko da na dawo asibitin hankalin su duk ya tashi suna ta nema na, da suka tambaya sai na yi karya nace gurin Baba Salihu abokin Abbah na tafi ko zan samu wani abu, kana ganina kasan ba lafiya ba, sai dai sun sun dauka saboda rashin lafiyar Deen ne, sai kwantar min da hankali suke, lokaci lokaci sai na kai hannu na taba cikina. Dare nayi sai labari ya canja Hajiya da Baba Da Mama da Yaya Maryam, Bahijja suka fara murna suna jindadi saboda domin likita ya sanar da su cewar Wani mutun ya dauki nauyin aikin Deen, ni kaina na nuna murna ta amman ba sosai domin duk yadda na so na ji dadin sai na kasa. A daren kowa farin ciki yake saboda Doctor ya jadada musu washe garin karfe 8am za a shiga da shi sai suka gargadi kar mu bashi komai yaci.
Misalin karfe takwas na dare Deen ya farka, babu alamar sauki a jikinsa, banbancin dazun da yanzu, yanzu yana magana sai dai alamu be nuna yana ganin mutane ba, sai dai da muka kira sunansa ya amsa, hakan kuma ya saka na ji sanyi a raina. Hajiya ta yi masa albishir da cewar gobe za a shiga da shi aiki domin wani ya dauki nauyi, har lokacin addu'ar alheri suke yi ma mutumen, Deen be ce komai ba sai na kama hannunsa.

%??meen...%???

%??mahra ta%???

Wani irin sanyi na ji kamar wanda aka cewa an yi ma gafara.

%??mannu Allah ya baka lafiya%???

%??mmin, bana iya ganin fuskarki matso na taba ki%???

Sai na kama hannunsa na kai a fuskata yana ta shafawa, Ina lura da yadda hankalin Mama ya tashi saboda taba ni da Deen yake, hawayen da ya ji a fuskata ya share min.

%??mi daina kuka jinki, i love you ki kula min da abun da zaki haifa, kuma na yafe miki duk abun da kika min, ni ma ki yafe min, ina son ki Zahra ina kishinki dan Allah ki min alkawari bayan mutuwa ba zaki taba auren wani namiji ba, domin ina son kasance dake a aljanna, saboda Malamai da Hadisai sun nuna duk matar da mutu da auren mijinta na karshe da shi Allah zai tashe ya aljanna, ko da kuwa mijin ya tafi ya barta ne, saboda matan Manzon Allah Sallalahu Alaihi Wassalam%???

%??meen ba zaka mutu ba, ba zaka tafi ka bar ni ba, tare zamu rayu mu mutu tare, na maka alkawari ba zan auri kowa ba bayan kai...%???

Mama ce ta rufe min baki ta jani da karfi zata fitar da ni waje saboda kuka nake na tashin hankali ina kururuwa kamar mahaukaciya, kamin Mama da Yaya Maryam su fice da ni ina jin yana rokon mahaifiyar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login