Showing 108001 words to 111000 words out of 210919 words

Chapter 37 - CIWON SO

10 Oct 2024

4200

ita masa fada ba, kuma ya fika gaskiya domin kai ka tarar da shi a gidanshi kuma ka karya dokarshi%???

%??mdan baya son ganina a gidanki ya sallame ki mana dokarshi dokar banza ce tun da har ya aje kyakkyawar mace irinki%???

Murmushin da ya kusan zama dariya na yi, ina ta saurarenshi har ya gama maganar da zai yi yayi min sallama, kiranshi na sauka na Dr Hamid ya shigo sai da na gyara kwanciyata sannan na amsa kiran sai ya sanar min cewar yana bangaren Hajiya Jamila na same shi a can, kamar wanda bata son motsa jiki haka na aje wayar na sauko saman katifar na fito waje, Mama na fadin na tsaya na karya na fada mata cewar ba zan dade ba. A bude na tararda kofar part din da alama an shiryawa zuwa, abun ka da marar gaskiya kamin na shiga cikin falon tsoro ya kamani domin na san ni da shi da Hajiya Jamila duk muna cikin wani yanayi ne mai kama da kwai da zarar ya fashe zamu kunyata ba mu san iya abun da zai biyo baya ba. Murmushin sa ne abun da na fara yin arba da shi, Hajiya Jamila tana zaune a kujerar dake fuskata ta shi fuskarta ba yabo ba fallasa.

%??marki tashi hankalinki ba laifi kika yi ba, na ga tsoro a tare da ke wani albishir na ce ni zan miki shi da kaina%???

Cikin rashin fahimta na karasa na zauna. Sai da ya waiga ko'ina na falon ya tabbatar mu ne kadai a falon sannan yayi kasa da murya ya ce.

%??mr Zainab ta mince ta karbi kudin kuma ta ba ni takardun yau zan maida nata da su, bayan na canja shiyasa na ce ni da kaina zan miki wannan albishir din kin ga sai ki kwantar da hankalinki ki sake yadda kike so a yanzu%???

Ya san kwanciyar hankalin nawa domin wannan maganar na daya cikin abun da ya kwantar min da hankali a yanzu, fargaba be wuce ace watan tonuwar asirina ya kama ba, amman amincewar da ta yi zai sanya salama a zukantan mu, sai dai ban san miya na kasa murna da haka ba ina ta jin kamar ba mu aikata abu mai kyau ba.

%??mo ba ki yi farinciki ba ne Zahra?%???

%??ma yi murna mana na ji dadi%???

Na fada ba domin na ji dadin ba sai domin na kare kaina, idon Hajiya Jamila yana kaina wani kalar kallo take min da ban san na minene ba, har sai da na soma tsawalla ina unkurin tashi na musu sallama Dr Hamid ya riga ni.

%??mari na tafi saboda ina da aiki da yawa yau kuma ya kamata na maida takardun hannun Dr Zainab kamin lokacin ya kure%???

%??mmman Yaya da zaka dan dakatar da zuwa domin na kura idon Hubby kamar yana kan mu bana son ya kula da yawan zuwanka ko kuma yawan kebewa da Zahra%???

Dr Hamid ya kalleta.

%??ma miki wata maganar ne?%???

%??ma lura dai na yi da hakan, ya kamata mu yi taka tsantsan dukanmu%???

%??meah you're right, zan kiyaye see you later%???

Ya karasa yana kallona tare da sakar min murmushi, kofar da Dr Hamid ya rufe bayan ya fita falon bana tunanin ta gama rufuwa aka bude yar'uwarta dake can kusa da stairs. Mijin Hajiya Jamila ne sanye da kananan kaya da suka karbe domin ni ma kaina sai da na yaba yadda kyaushi ya kara bayyana a tufafi balle kuma ita da take matarshi. Da sauri ta mike tsaye ta nufi shi sai dai hakan be hana shi barinta ya karaso gurin Set din kujerun da muke zaune ba zauna a kujerar da Dr Hamid ya tashi, cikin hanzari na mike tsaye ina mika masa gaisuwa.

%??mna kwana Yallabai%???

%??mn tashi lafiya%???

%??mafiya kalau%???

Na juya da zimmar ficewa sai ya kira ni.

%??mahra%???

Na juyo sai dai ban yarda na kalleshi ba, duk kuwa da jikina ya ba ni cewar shi din kallona yake.

%??madam me kika shirya mana na breakfast?%???

Hajiya Jamila da a yanzu ta karaso kusa da mijina ta amsa tana kallon yadda yake kallona.

%??mun makara ba mu barka da wuri ba, shiyasa ban dora komai ba Ummiter ma yau ba zata je aiki ba kai ma i thought bachi kake yi shiyasa ban girka komai ba, amman zan dora yanzu%???

Ya daga mata hannu yana kallona ni ma kallonshi nake a munafunce ina dauke ido.

%??mo no ya kamata ki huta, bari Zahra ta shirya mana abun karyawa, Zahra kin iya girki?%???

A take ido suka rain fata a duniyar nan ba abun da na tsana kamar ace min na yi girki ba dan bana son girkin ba sai dan ban iya ba, gudun na kunyata kaina ya saka na daga kaina har sau uku a na hudu na samu na iya furta.

%??mh na iya%???

%??mood the kitchen is yours now ki girka mana farfesu sai ki soya mana dankali bana cin kwai amman Matata tana ci ke ma idan kina ra'ayi zaki iya soyawa Ummiter ma tana so, and Wife ina ganin a maida girkin su tare da na mu gaba daya ba dole sai sun girka na su dabam ba%???

Karashe maganar yayi yana kallonta kamar mai neman shawara.

%??mo ba zan iya ba, girkin mutum uku na ya nake yinsa balle na mutun biyar? Already ka zuba musu abin ci a store to miye na neman a hade abinci da masu gida?%???

%??mdan ba zaki iya ba Zahra sai ta cigaba da girka mana%???

Ni kaina mamakinshi na ke balle kuma ita da mamakin ya bayyana a fuskarta.

%??mxcuse me, Hubby baka cin abincin masu aiki fa?%???

Kallona yayi sai na yi saurin sauke ido kasa ina jin bugawar gaba.

%??mannan tana da tsabta kuma na ga kin aminta da ita, daman ni kazanta ce bana so a kula da tsabta kin ji Zahra%???

Na daga mashi kai sannan na juya na nufi kofa sai ya sake kirana ina juyowa ya nuna min kitchen.

%??mi girka mana abu na ce%???

Kamar a rikice na nufi kitchen din ina jin wani abu mai kama da kuka na neman hanya a idona, katon kitchen da komai a akwai a ciki wani abun ma ban san amfaninshi ba ban kuma san abun da ake da shi ba balle na san yadda ake kunnawa ko kashewa, ba abun da ya tsaya min a rai kamar dafa farfesu, har ga Allah ban san yadda ake yin farfasu ba domin ban taba yi ba, a gidan Ammy ma na ga ana yi ban tana tsayawa na kalli yadda ake ba, haka ma Mama da take girkawa wani lokacin ban san yadda take ba sai dai idan ta girka ta na ci.

%??marfesun ma na miye zan yi?%???

Na tambaya kaina da muryar da kuka ke son ya ci karfinta, dankalin na fara gyarawa na kunna gas sannan na dora fraying pan na bude cabinet ina dubawa sai ko zan ga mai, daker na gano inda take aje mai na dauka an zuba, da na lura ba rawa ba tumame sai na cire hijab dina na aje gefe daya na takarkade ina ta soya dankalin sai da na yi kwasar farko, sannan na leka falon ban ga kowa ba daga ita Hajiyar uwar izza har mijin nata, sai dai idona ya sauka akan wayar dake hannun kujerar da Alhaji Bashir ya zauna, kafafuwan na sauko na fito daga kitchen din ina kallon stairs na karaso gurin wayar kamar na kai hannu na dauka sai kuma tsoro ya kamani, na juya na koma kitchen din cikin tsanda.

%??mdan ban dauko wayar ba kuma da me zan yi farfesun? Ko kuma na ce musu ba iya ba? Ai kuma dai da kunya ace ban iya ba, to ko dai na tafi na dauko tawa wayar? Kuma ai ba ni da data, ko kyma na kira Mama ta zo ta girka musu?%???

Haka dai na yi ta magana da kaina, saga karshe na yanke shawarar dauko wayar da nake kyautata zaton ta Alhaji Bashir din ce ya manta na duba yadda ake farfesun. Kamar wanda zata yi sata haka na dawo falon ina ta waige waige har na samu nasarar kai hannu na dauki wayar, tun da nake a rayuwata ban taba daukar wayar na ji tana neman subucewa a hannuna ba irin wannan saboda sulbin da take da shi, lallai kayan kamfani daban da na shago abun manya na manya ne a duk inda yake, maida kofar kitchen din na yi na rufe a hankali ba tare da na bari kara ta fito ba, sannan na taba wayar hoton Amir ne a gaban wayar yana bachi, a take tausayin Alhaji Bashir ya kamani ,domin yana kallon Amir a matsayin ??anshi ne alhalin ba jininshi ba ne, a yanzu kam ina jin rashin kyautawa a abun da na aikata, ko da yake ni dole ce ta saka amman Hajiya Jamila ta yaudari mijinta yaudara mai girma kuma yaudarar da babu wanda zai san gaskiya sai Allah. Na raba kaina da ??ana zai girma be san ni a matsayin mahaifiyarshi ba, ban san Mama a matsayin kakarshi ba sai wasu familyn na dabam a matsayin familynshi, anya hakkin yaron nan ba zai kamani ba? Da kuma amanar Alhaji Bashir din na hada baki da ni a zalinci mutun da na lura babu komai a tare da shi sai alheri da son kyautatawa?
Na share hawayen da suka zubo miki na nisa ina taushe wani numfashi mai wuyar zama a masarafarsa.

%??man yi da mugun nufi ba Amir, kuma ban aikata hakan saboda bana sonka ba, sai dai na ceto rayuwar mahaifinka rayuwar da bata tsaya ba%???

Na aje wayar na dora hannuna akan sink hawaye wasu na rigan wasu sauko min, ina matukar jin kaunar yarona kalaman da Deen ya taba yi min da kuma wasikar da na karanta a gidan Hajiya suka tsaya min a rai.

%?pii kula min da abun da zaki haifa ko da bana raye ki tarbiyantar da shi%???

%?piarki tsani yayana saboda abun da na aikata%???

Kuka na yi sosai sannan na share hawayena na wanke hannuna da fuskata a jikin fanfon kitchen ko na kwashe dankalin daya soya, na rage wutar gas din na maida hankalina gurin wayar sai a lokacin tunanin pin din wayar ya zo a kai, ga mamakina ina taba samn wayar sai ta bude ashe babu password a jiki, ba karamin dadi hakan yayi min ba a take na kunna data wayar na saka wayar a silent na shiga cikin ina dubawa har na gano YouTube, kai tsaye na shiga na rubuta farfesu, a take aka nuna min video kala kala, farfesun kaza na kifi na kan garo na kayan ciki and so on. Freezer na nufa na bude na ina dubawa, babu komai a cikin sai kayan marmari, rufeta na yi na nufi dayar dake kwance na bude sai na yi arba da nama kala kala.
Da taimakon video dake playing na yi musu farfesun nama zallarshi, yadda na ga suna zuba abubuwa haka na yi sai dai ban saka kayan kamshi ba domin ban ga ko daya ba, sinadarin dandano ma daker na ganoshi, sai da na gama na sauke sannan na fasa kwai na soya, ban yi tunanin dandanawa na ji yadda girki yake ba domin na gama girkin ne cikin rashin natsuwa ina ta fargabar kar Hajiya Jamila ko Mijinta su shigo su same ni da wayar, wannan yasa idan na kalla sai na boye wayar a cikin zane, domin idan wani ya same ni da ita ban san me zan ce ba musamman ma shi wata kila zai ce sata na yi, sai dai cikin hikimar Allah babu wanda leko kitchen din har na gama girkin. Manyan kuloli na dauko na zuba komai a dabam dabam sannan na dauka na nufi dinning na jera sannan koma kitchen din na dauki wayar na da na aje bayan cups na yi clearing video din da na kalla na rufe data na fito ina ta kalle kalle har na yi nasarar aje wayar a gurin da na dauke ta, wani wawan tsalle na daka ina jindadin yadda na shirya komai ba tare da kowa ya gane komai ba, ba tare da tunanin komai ba na haura sama ba kwankwasa kofar dakinta tun kamin, daga inda nake tsaye ina jiyo sautin Ummiter, hakan ya fahimtar da ni hira suke mai cike da nishadi, ashe kuwa na canka a daidai domin dariyar dake take yi a yanzu ya tabbatar min da haka.

%??mahra%???

%??ma'am Hajiya tana ciki%???

Na amsa ba tare da na gaishe ta ba daman can zuciyata bata taba raya min na gaishe ta ba, taya zan gaishe da matar da bata wuce sa'a ta ba.

%??mh tana ciki%???

Ta bude kofar dakin gaba daya, hakan ya bani damar hango Alhaji Bashir dake zaune kan kujera Hajiya Jamila kuma tana zaune kusa da shi, sai dai na ga tsabanin abun da na gani a fuskar Ummiter da Alhaji Bashir, ita kam sam babu ko kufan murmushi a tare da ita balle dariya har ya kaita ga nishadi.
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Bayan na sanar musu cewar na gama na sauko na daya a dayan set din cushion din domin bana son na tsaya a kusa da inda ya zauna dazun yayi zaton ko na taba mashi waya, babu mai iya sanin farincikina sai Allah da ya amince min na girka wannan breakfast a yau na shirya komai ba tare da sanin kowa ba, balle a gane cewar ban iya ba. Ummiter ce ta fara saukowa jikinta sanye da tufafin bachi wando da riga ta nade kanta da wani abun da nake kyautata zaton tawul ne. Alhaji Bashir ne na biyu sannan Hajiya Jamila, a duk lokacin da muka hada ido harara take aiko min da ita, mijinta kam ban da murmushi babu abun da yake, ba na ce ina ganinshi kullum ba balle na ba da shaidar kyakkyawan murmushin sake fita tsakanin kumatunshi amman tabbas tsakanin jiya da na fara bashi labarina zuwa yau na lura nishadin shi dabam yake.

%??min cire na ki ko?%???

%??ma ban zuba ba%???

%??me da girki, mu da fara ci zo ki zuba na ki mana%???

Na dauki plate din da yake nan na bude cooler na zuba, na sake daukar dayan na zuba dankali da kwai, sannan na dauka zan tafi.

%??mea fa?%???

Na juyo na kalleshi sai kuma na kalli Hajiya Jamila wacce ta hade min fuska.

%??ma wannan ya isa%???

Ban jira ya sake cewa wani abu ba na fito falon da saurina, kamin na karasa bq na tsaya na dandana abinci domin tun a cikin yawuna ya tsinke, saranda na yi ina fidda ido waje, anyi ba'ayi ba kenan ni kaina ban taba cin girki marar dadi irin wannan gashi dai be nuna ba kuma ga rashin dadi wani gurin ma kamar gishiri ya zarce.

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un%???

Na fada cikin tashin hankali, da gudu na karasa bq din a waje na aje plates din hannuna na dawo da gudu zuwa main house din jikina har mazari yake, ala ala nake idan ba su ci ba ina shiga cikin falon muryar Hajiya Jamila ta dira a kunne

%??mi gaskiya ba zan iya cin wannan abincin ba%???

Ummiter kuma sai kwasar dariya take, tsaye na yi jikin kofar falon irin yadda yara suke idan sun yi laifi fuskana na bayyana rashin jindadin abun da na aikata, sai suka dago suna dubana, Alhaji Bashir da fuskarsa take sake har yanzu ya ce.

%??mahra karaso mana%???

Kamar ance karasa ki jr ga ajalinki haka na ji, sai na samu kaina da kara matsawa baya na kwalla sharrr daman can haka nake zarar zan aikata laifi to kuka ne zai biyo baya tun kam ayi min hukunci.

%??man iskanci kin san baki iya girki ba kika karba kika yi? Shi wannan abinci mai kama da guba da kika girka mana so kike mu ci mu mutu ne?%???

Na girgiza kai daga inda nake tsaye, sai Alhaji Bashir yayi alama da na zo da hannu, cikin karfin hali na taka na karasa gurin ina mai tsananin jin kunya taya mace kamar ni ace ban iya girki ba, ai da kunya ba ma karama ba.

%??miriniya bata barki kin tsaya kin ko yi girki ba ko Zahra?%???

Na sauke kai na kasa ina jin sautin murmushinsa.

%??mideo da kika gani a waya suna tsallaken time ne ke kuma kin yi amfani da yadda suke kika girka mana wannan ba ki yi la'akari da haka ba%???

Wata kunya ce ta kama ni, ya aka yi ya san na dauki wayar har na duba?ko dai akwai camera a falon da kitchen din ne? Wata kila Hajiya Jamila ta boye min ne saboda na saki jiki na aikata wani abun ta gani, wannan maganar da mijinta yayi ya tabbatar min da akwai camera a falon ba kamar yadda Hajiya Jamila tace min a waje kawai aka saka camerar tsaron ba. Yanayin yadda muryarsa ke fita ya isa ya karantar da ni cewar ranshi be bace ba, musamman da na daga kai na kalli fuskarsa sai na yi arba da murmushi irin na mazan dake da kokarin fin karfin zuciyarsu ko da an musu ba daidai ba su kasa nunawa. Ummiter kallon mamaki take min tana yi ma Alhaji Bashir sai kuma ta kalli Hajiya Jamila da ta kusa mutuwa tsaye.

%??ma ki iya girki ba Zahra?%???

Ya tambaya, sai na daga masa kai ina dan turo baki ji nake kamar ya muzantani a bainar nasi.

%??ma kamata ki koya ko dan gaba, maza suna son mace da ta iya girki misali irina ina son mace mai girki kala kala, kuma ya kamata ki koyi amfani da wasu abubuwan like wannan dankali akwai inda ake soya shi ba sai an saka cikin ruwan mai ba, Wife ina tunanin catering school zamu nema mata what do you think?%???

Ya karasa yana kallonta wata uwar harara da ta jefo masa ni kaina sai da na nemi natsuwata na rasa, Ummiter kam abun da take nema ne ya bude mata kofa wato gulma har bakin Alhaji Bashir dake motsi kallon take balle kuma reaction dina da na Hajiya Jamila.

%??mubby ina son magana da kai%???

Tana fadar haka ta mike tsaye har wani hura hanci take

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login