Showing 90001 words to 93000 words out of 210919 words

Chapter 31 - CIWON SO

10 Oct 2024

4208

san idan a yau na fadi a mutu ba ni da ??an da za a kasa dakiyar nan tawa a bashi kasonsa? Kin san iya kimarki da darajarki da kaunarki da ta karu a zuciyata saboda haihuwar nan da kika yi? Da ace wata uwar ce ta haifa min yaron nan ba ke da da kaunar da zan nuna mata zata saka na manta da ke na saboda soyayya da kaunar da na ke yi ma yaron nan, yanzu kuma da ya kasance ta dalilinki na samu yaron bana ganin kowa a gabana sai ke da ??anki, duk wata kauna da soyayya da na nuna miki a baya, sharar gafe ce kuma wasa ce%???

Ya rumgume shi cike da jindadi ta lumshe ido, bayanta ya shafa yana jin wani irin kaunarta marar misaltuwa na kara tsarashi, shekara tara yana neman haihu Allah be bashi ba sai wannan karon.

%??mokacin da na fara jin kukan yaron nan sai da na fashe da kuka na farinciki, wai ??ana ne na jinina nake jin sauti muryar kukansa, yaya rahama ne tabbas kuma ba zaka tana sani ba sai ranar da ka rasa ko ??aya, ko ba komai na san zan mutu na bar wanda za a kalla a tuna da ni%???

Dagowa ta yi ta kalleshi sai ta yi arba da hawayen da suka cika idonsa har suka sauko masa, hannu ta kai ta share masa hawayen nata idon ma cika da hawayen tausayin mijinta, ba da yan furta cewa zai mutu sai dan tausayinsa na sanin cewar ??an da take ikirarin nasa ba jininsa ba ne, ita kanta da take ba ??anta ba ne. Wayarsa dake ringing ya ciro daga aljihunsa yana dubawa.

%??mu gwaggo ne wata kila sun iso bari na tare su%???

Ya fada fuskarsa da annashuwa domin ya san saboda a taya shi farinciki yan'uwa na nesa da kusa suke ta zuwa yi masa barka wasu ma suna tare a gidan, ta sake tana murmushin karfin hali sai da ya shafa bayanta sannan ya fice ita kuma ya juya ta nufi gurin gadon jaririn tana takawa a hankali har ta karasa kusa da shi ta tsaya tana kallonsa.

%??mllah ya ba ni komai ban da haihuwa, na san mijina zai kaunarci yaron nan kamar ??ansa alhalin ba ??ansa ba ne, Allah ka yafe min wannan zunibin da na aikata da kuma wanda zan aikata nan gaba, ka rufa min asiri kar a gane komai har yaron nan ya girma%???

Wannan karon hawayenta tare da murmushi suke, tabbas tana jin rashin kyautawa a abun da ta aikata sai dai bata da wata mafitar ne sai wannan, idan har ba ta yi haka ba ta san Mr Bashir zai iya auro wata kamar yadda ya sha yi a baya kuma su zo su haihu ya juya mata baya shi da yan'uwanshi, kuma a raba gado ba zata tashi da komai ba sai hakkin wanka kamar an fada mata shi zai rigata mutuwa, tana duba yadda yake da tarin dukiya ace idan ya fadi ya mutu bata da komai sai hakkin wanka, amman a yanzu fa? Yan'uwanshi za su kaunace ta daga ita sai ??anta, kuma mijinta ma dole ita kadai zai so haka kuma zata samu kaso mai yawa idan ya mutu domin namiji ne ??anta. Kusan a firgice ta juyo ta kalli kofar ??akin yaron da aka turo, domin tun kamin ya zo duniya mahaifinsa ya ware masa ??aki daya a cikin ??akunan dake kusa da nata kuma aka kawata shi da duk wani abun bukata irin na yayan turawa, a part dinsa ma sai da ya shirya masa wani dakin da yafi wannan da yake a ciki tsaruwa da kyau. Da karfi ta hade yawu ta kai hannu ta share hawayenta tana jin rigar tsadadden lace din dake jikinta yana sukarta.

%??mt least ya kamata ki yi knocked kamin ki shigo Ummiter%???

%??mhekaranjiya da na yi knocked na shigo kika ce zan tashi yaro yana bachi, yau kuma kin ce ya kamata na yi knocked, Anty Jamila ya kamata ki san ni fa ba yar aiki ba ce you can't just treat me anyhow just because kina matar yayana%???

Hajiya Jamila ta yi wani gutun murmushin tana rausayar da kai.

%??mshe ma kin san matar yayanki ce, matukar kina son girmama ??an'uwanki dole ni ki bi ni sau da kafa, ban san abun da kike son yi a bangare na ba, bayan kuma mijina yayi muku part din dabam saboda kun zama abokan zamana%???

%??ma shigo nan ne saboda na dauki ??ana domin danginmu suna bukatar ganinsa kakaninsa da suka zo, sannan nan gidan ??an'uwana ne ina damar na zaga duk inda nake so a lokacin da nake so, ba uwa ba uba wa kika tunani zai rika mu bayan ??an'uwanmu?%???

%??maboda na zama kishiryarki mana, shiyasa ba ki yarda ki tare a ko'ina ba sai gidan nan%???

Ummiter ta karaso kusa da ita tana fadin.

%??mwarai da gaske, Yayana zai iya canja mata be canja yar'uwarba ina fatar kin san da wannan! A tunaninki mugun halinki zai hana mu zama a gidan ne? Kamar yadda ya hana sauran matan da yake aurowa zama? Kin dai tsira tun da kin haifo mana ??a ba dan haka ba da babu abun da zai hana ??an'uwanmu kara aure a karo na biyar%???

%??mo sai ayi mu gani, matsalar haihuwar ai ba ni kadai ba ce har da ??an'uwanki, ke ma kuma ba ki wuce matsayin ba%???

Hajiya Jamila ta fada cike da zafin rai sannan ta fice a fusace ta bar Ummiter a bedroom din, harara Ummiter ta bita da shi ta ja tsaki.

%??muk abun da kike so akaina ba zaki taba samu ba, ni ba irin Imaan ba ce da zan yi zuciya na bar miki gidan ba, nan da ke idan kika ga na bar shi to aure na yi%???

Ta saka hannu tare Bismillah ta dauki jaririn tana murmushi.

%??my sleeping handsome, da ama ace ba ta cikin wannan wicked matar ka fito ba, but hakan ba zai hana mu nuna maka kauna ba Habibi%???

Tana fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa.

%??mi Wallahi ban so yaron nan ya dauko hasken matar nan ba, na so ace bakin mu ya dauko ayi baki mai kyau Allah yasa ka zama baki kamar ni%???

Haka dai ta yi ta maganarta tana takawa a hankali gudun kar ya farka ta fice da shi.



*** *** ***

Tana shiga dakinta ya cire ??ankwalin kanta ta wulgar da shi saman gado.

%??mannan yarinyar ko? Idan ban mata sanadi da gidan nan ba, ba zata bar ni na zauna lafiya ba, ta hana ni jindadin gidan mijina%???

Ta nufi wayarta tana kai hannu ta dauka kenan sai ga wata gwaggon Mr Bashir ta shigo bakin har kunne tana mata barka, wani irin yauki take gwaggon bata fita ba Sister din Jamila ta shigo da wasu bakin, daman tun da ta haihu babu ranar da ba a zuwa yi mata barka daga bangarenta har zuwa bangaren mijinta, da kuma abokan arziki da makota wasu ma tun da ta haihu suka tare a gidan bayan sabin yan aikin uku da mijinta ya daukar mata, sai dai be yarda daya daga cikinsu ta taba masa yaro ba. A dole ta hakura da wayar da zata yi har sai da ta gama sallamar bakin sannan ta dauki wayar ta fita daga dakin zuwa can wani dakin da ba a shiga ta turo kofar ta shige bandaki sannan ta kira Dr Hamid.

%??marinyar nan gani take tana iya wasa kada a tsakiyar ruwa?%???

Ta fada bayan ta gama sauraren bayanin da Dr Hamid yayi mata na abun da Zahra ta shar'anta masa.

%??maboda tana ganin an zo nema a gurinta ne, mu kyale ta na kwana biyu idan ta ga ba mu sake yi mata magana ba zata tuntube mu%???

Ya cije lips dinta tana jinjina lamarin.

%??ma zan taba yarda yarona shiga wannan kazamin gidan na su ba, shan nononta ma saboda ya zama dole ne, gashi mijina yace daga yau zuwa gobe idan ya sake jin kukan yaronsa da kanshi zai kai shi asibiti%???

%??mmman ban baki shawarar ki dauki yaron nan ki kai mata ta shayar da shi ba, zata ma iya guduwa, ko kuma ta samu damar aikata wani abu, kin san kuma ba ke kadai ce a matsala ba har da ni%???

%??mo da wasa ba zan yarda a fitar da shi ba tare da ni ba, domin hakan zai janyo min matsala kuma dole wata rana asirina zai tonu%???

%??mo ya zamu yi yanzu?%???

%??ma fada mata zata dawo ta zauna a gidana ta cigaba da rainon ??ana har zuwa lokacin da zai samu lafiya%???

%??makan zai kara tona asirinmu ne, saboda mutane za su fara lura wata kila m iyayenta ba za su yarda ta dawo ta zauna a nan ba, kuma a nan yau da gobe dole gaskiya zata fito%???

%??ma zan taba bari a gane ba, kuma ita ma dole ta yi taka tsantsan domin ta san har da tata rayuwar tana cikin matsala, Dr Hamid yaron yana nufin komai na rayuwata ka fi kowa sanin yadda na sha wahala kamin na samu yaron nan, da asirina ya tonu a yanzu kara na rasa igiyar auren dake tsakanina da Mr Bashir, idan kuwa har zan iya yarda na rasa igiyar aurena ka san yaron nan yana nufin rayuwata ne ina nufin rayuwata gaba daya!%???

%??maina wannan abun ya saka ni a cikin matsala, ban taba aikata ko da zubar da ciki ba balle wannan! Idan gaskiya ta bayyana da wani ido zan kalli mijinki? Kuma sunana zai bace i think auren yarinyar nan zan yi idan ba haka ba zai zama kamar na kashe maciji ne ban tsare kan ba%???

%??mama ganin haka zai zame mana mafita?%???

%??mhi kadai ne mafita%???

%??marka aureta, ni na san wata mafitar amman a yanzu ina son ta zauna a tare da ni a gidana, zata dawo da zamanta a nan ne gaba daya har zuwa lokacin da ??ana zai samu lafiya%???

%??man yi magana da ita%???

Ta sauke wayar tana kashe ido.

%??mina wasa da rayuwarki, baki san Wacece Jamila ba, ke dai na taimaki rayuwarki yanzu kuma kina son wasa da damarki, hmmm yaro be san wuta ba sai ya taka, da na rasa igiyar aure ko ??ana sai dai ke ki rasa farincikinki ko ma rayuwarki gaba daya%???





ZAHRA POV.


Sai da na fara share ??akin da nake kwana na kwashe sannan fara share waje, kamar daga sama na ji sallamar Anty sai na dago na kalli kofar shigowa cikin gidanmu. Na kuwa can ka daidai domin Anty ce tare da yaranta biyu Aisha da Narjis ban amsa sallamar ba kuma ban fasa sharar da nake ba, sai na yi kamar ban san da shigowarsu cikin gidan ba.

%??mahra shara ake yi?%???

Na dago na kalleta kamar na amsa kiran sunan da ta yi sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin kazafin da Abiey yayi ma Deen a yanzu ya saka na kara tsanar Abiey ba shi ka dai ba har da yan'uwansa da duk wani da yake da alaka da shi. Mama ce ta tashi tana mata maraba daman can Mama bata iya fushi ba ko da ka bata mata rai zata iya nuna maka ta huce sai dai ta bar abun a zuciyata, amman a gurin wasu a gurin yayanta kam kamar ni da Yaya Maryam idan muka bata mata rai a take muke sani domin fushi take da mu mai tsanani kamar bata san inda muka fito ba, musamman ma ni da take cewa na fi kowa rashin jin magana. Mama ta dauko tabarma ta shimfida musu ni kam ko inda suke ban sake kallo ba.

%??mahra ko baki gane ni ba?%???

%??ma gane ki mana Anty, ai ba zan manta fuskarki ba, da kuma dalilin da ya saka na san ki ba%???

Ta yi murmushi.

%??m yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zo ki zauna mu ba bakin zafi ba ne gaisuwa muka zo%???

Kamar na musa mata sai kuma na aje tsintsiyar hannuna na nufi inda take na zauna.

%??mahra kin dauki zafi da yawa, kuma kina da yancin nuna bacin ranki amman a rika sassautawa, kuma abun da ya wuce ayi hakuri a bar shi a matsayin abun da ya wuce%???

%??mar abada abun da Abiey yayi min ba zai taba wuce ba, kuma ba zan taba mantawa ba, kuma ba zan fasa rokon Allah ya saka min ba%???

Ta yi shiru kamar ba zata ce komai ba, sai kuma ta juya gurin Mama ta yi mata gaisuwar sannan ta dora da cewa.

%??muna tare da Abiey yana waje yana son ya shigo yayi muku gaisuwa idan da hali%???

%??ma shigo mana, bari na dauko mayafina%???

Mama ta tashi ta shiga daki ta dauko mayafi ta rufe jikinta, ni kam daman da hijabi nake zama a yanzu saboda Mama tace ba a son mai jego na sakin jikinta any how. Sam ban jidadi da Mama ta amsa kai tsaye tace ya shigo ba, sai dai ba zan iya hanawa ba. Anty ta kalli yarta ta ce

%??marjis je ki ce ma Yayanki ya shigo%???

Ina jin haka na tashi na shige dakin Mama na zauna zuciyata na wani irin tafasa, sallamar ma shi ma da naji sai da na ji kamar na saka reza na yanke kunnuwana, ga wani matsifafen turare daya saka da ke ta tsokata ta har cikin dakin Mama da nake zauna.

%??mama Zahra fa...?%???

Ya tambaya bayan ya gama yi ma Mama gaisuwa, wani kololon bakinciki ne na ji ya taso min ya tsaya min a kirji, har sai da na sauke numfashi sannan na samu sukuni.

%??mahra.... Zahra...%???

Mama ta kara ni har sau biyu ba ta yi na uku ba na amsa na taso na fito, zaune yake kusa da Anty ya sadda kanshi kasa yana motsa keys din hannunsa a hankali. Zaunawa na yi kasancewar tabarmar irin mai fadin nan ce da zata wadaci mutum biyar ko fiye ma, ya dago ya kalleni da wasu mayun idanuwanshi dake kara saka ina jin haushinsa.

%??mahra ya hakuri?%???

%??maka ji kunya ba Abiey? Kai da kanka zaka tako ka iso har cikin gidanmu da sunan gaisuwa?%???

Ya sauke kansa kasa yana murmushi.

%??mubhanallahi ya kike magana kamar ba musulma ba%???

Na kalli wanda ta yi maganar.

%??ma san me na ke yi Anty, kuma ke ma kin san babu irin wulakancin da Abiey be yi min ba%???

Na juya gurin Abiey

%??mnd lemme warn you karka sake fadin wata mummunar kalma akan Mijina, Deen ya gama lafiya ya rabu da kowa lafiya, karka sake samun yar'uwarta da wani zancen banza akan mijina, macuci mayaudari kawai azzalumi so kake ka bata kanka Deen a gurin mutane? To Allah ya fika kuma Deen yayi maka nisa Abiey kuma ka karasa kanka tsana a zuciyata ka yafawa kanka bakin fentin da ba zai taba goguwa ba%???

Ima kai aya Mama ta daka min tsawa.

%??ma... Zahra kanki ??aya kuwa?%???

Ya dago ya kalleni ya fara min magana kamar da rarrashi.

%??marta ta fadi abun da take ra'ayi Mama, saboda Deen ya dorata a gadar da ba zata iya fahimtar komai ba, amman ki yi tunani Zahra a Wallahi tallahi ban guje ki haka nan kawai dam na yaudareki ba Deen ne ya shirya komai...%???

Ban san lokacin da na yunkura daga inda nake zaune har tafin hannuna ya kai a fuskarshi ba.

%??mllah ya waddaranka Abiey, ka zo da sunan gaisuwa kuma ka zauna a cikin gidanmu kana aibanta mijina...%???

Ji na yi an taba ni ina juyowa kanwarshi da suke uba daya Aisha ta dauke ni da mari.

%??mazama dake har kin isa ki daga hannu ki mari Babban mutun kamar ??an'uwana, kin san yadda yake fama saboda ke amman yau ki siffanta shi da wasu munanan kalmomi kuma ki daga hannu ki mare shi? Waye ubanki duk garin nan? Kiyayya ba hauka ba bace Zahra ??an'uwana baya neman komai a gurinki ba ki da abun da zai saka ya yaudareki, macucin mijinki ne ya shirya komai ke kuma da yake wawuyace kin kasa fahimta, Anty tashi mu tafi%???

Ta mike tsaye ni kuma na bita da kallo baki sake hawaye na sauko min na zafin kalaman da ta jefeni da su.

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un%???

Anty ta fada Mama kam zaunenta take tana kallon ikon Allah, kuma na san ba zata rasa dora min laifi ba wata kila shi ya saka bata ce komai ba. Abiey ya mike tsaye idonsa har sun kada sun yi ja kamar ba na shi ba cikin wata irin muryar da ban taba sanin yana da ita ba ya fisgo Aisha ya dawo da ita baya.

%??muka ki bata hakuri Aisha%???

%??mmman....%???

Kasa karasawa ta yi sakamakon wani mugun kallo da ya watsa mata.

%??m'm sorry%???

Ta furta.

%??mneel down%???

Ya fada tsabar bacin rai jikinsa har rawa yake, sai da ta aje numfashi da karfi sannan ta durkusa kasa guiyoyinta tana watsa min harara ta ce

%??morry%???

Tsakamin mikewarta tsaye da wanke mata fuska da yayi da mari biyu ma su kyau ban san wanda ya riga wani ba.

%??mow dare you raise your hand on her face? How dare you Aisha...%???

D muryar dake nuna tsananin bacin ransa ya furta hakan yana kallon Aisha dake dafe da gefen fuskarta tana kuka domin a gefe daya ya sauke mata marin har biyu. Sannan ya kalli ya Mama ya ce

%??mama ayi hakuri dan Allah%???

Ya juya ya fice Aisha ta bi bayansa tana kuka.

%??mn yi na farko an yi na karshe Zahra da yardar Allah indai akan Abiey ne%???

Shi ne abun da Anty ta fada min sannan ta mike tsaye ta fice daga gidan Narjis na take mata baya, ni kuma kalli Mama ina kuka.

%??m gaishe ki dai Juliet, matar Deen ma'asumin da ba shi laifi, ke ke ke Zahra ba wata ba sai Ciwon son Deen ya kashe ki, mahaukaciyar banza marar tunani ai ni Wallahi wannan bata burge ni da bata miki mugun duka na fitar hankali ba%???

Runtse ido na yi jin kalaman dake fita daga bakin Mama, sai kuka yace min ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ho mu hade, tashi na yi da sauri na shige daki na kwanta saman katifa rike da hannun da na mari Abiey, marinsa da na yi a yau ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login