Showing 171001 words to 174000 words out of 210919 words

Chapter 58 - CIWON SO

10 Oct 2024

4219

ba, ina wani dakin Ammy ana min kwalliya na kira Abiey na tambaye wane kalar tufafi ya saka sai yace min farare kamar nawa. Bayan na aje wayar ya sake kirana yace yana son magana da ni a kebe, na ji tsoro sosai kuma na samu kaina da faduwar gaba. Shi ya fada min dakin da zan same shi na taka da kafa cikin farin lace da mayafi na isa har gurin na shiga cikin dakin, sai na same shi rai a matukar bace har baya iya kallona.

%??mahra.... %???

Sai yayi shiru, hakan ya saka na tari gabansa ina kallonsa fuskata da murmushi.

%??minene?%???

Be iya fada min ba ya fice ya bar ni, cikin tunani da sake sake kala kala, dawowa na yi dakin Ammy na zauna cikin damuwa da sanyin jiki, mutane da ke cike da dakin sai tambayar damuwata amman na kasa furta komai domin ni ma ban san damuwar tawa ba, kawai dai na fahimci akwai matsala ne. Babu wanda ya iya fada min komai sai Ammy da kanta ta kori kowa a dakin ta zaunar da ni tana karantamin yadda kaddara take zuwa da yadda ake son bawa ya karbe ta.

%??mmmy duk ban gane wannan ba, mi ke faruwa ne?%???

%??mahra ina son ki dauki wannan a cikin kaddararki, ina mai baki hakuri kuma ina mai bakinciki sanar da ke cewar ba za a iya daura aurenki da Abiey ba a yau...%???

With full confidence Ammy ta fada min haka, da farko ban yarda ba sai na dauka wasa suke min, har sai da ta jaddamin cewar da gaske ne ba za a daura ba, da na nemi hujja sai ta dauko takardar gwajin da Dr Zainab ta yi ta, bana bukatar wani ya karanta min abun da takardar da kunsa domin ni ma na yi karatu kuma ina cikin yan gaba gaban da makaranta take alfahari da su saboda kokarinsu.

%??mmmy ko dai ba daidai ba ne%???

Na tambaya bayan hawayen idona sun gama jika takardar jikina yana ta rawa.

%??mi yi hakuri Zahra kadarar ku kenan, shi kansa Aliyu yana cikin wani, shiyasa ya kasa sanar da ke%???

%??mna son na ganshi Ammy, Ammy wannan takardar da gaske ne?%???

Kai kawai ta daga min ta share hawayen da suka cika idonta ta juya ta fice a daki, kamar makauniya haka na fadi ina lalaben abun da be bata ba, kuka ya hado kayansa yayi masauki a gurina. Abiey na shigo yana ta kallona ya gagara ce min komai, sai na isa gabansa na nuna masa takardar.

%??malli abun da suka ce amman na san ba gaskiya ba ne, kalli Abiey wai ina dauke da kwayar dake karya garkuwar jiki%???

Be duba takardar ba sai kawai ya dauke kai.

%??makuri zamu Zahra, na so na aureki a haka amman ban isa na taka dokar Ammy ba, saboda bata yarda ba%???

A ranar na ga rashin imanin Abiey kuma na yi mamaki, domin a irin soyayyar da yake nuna min na yi zaton zai iya aurena a haka amman sai ya juya min baya, har kasa na kai ina rokonsa ina masa magiya kar ya ba wa iyayena kunya, kar ya watsa jama'ar da aka tara mana, amman ina be saurareni ba, da na fahimci ba shi da niyar canja kudinsa sai na roki ya amince a daura auren daga baya sai ya sake ni, nan ma ban samu ba daga gareshi. Ni da Mama da Yaya Maryam muka shiga cikin tashin hankali saboda abun da ya faru, Baba ma ya nuna damuwarsa sosai musamman ganin sa'a daya ta rage a daura auren taya za a sanar da mutane cewar an fasa auren. A nan ya kawo shawarar a daura da Deen albashi idan ma bana son sa sai ya sake ni bayan an fita kunya, a lokacin na yaba da kokarin Baba da kuma na Deen duk da kasancewar ba shi a gidan a lokacin, haka kuwa aka yi sai aka daura auren da Deen a maimakon Abiey. Kamar wanda aka yi ma mutuwa haka nake ta rusar kuka Mama na ba ni hakuri, ita ma kukan take Yaya Maryam ma haka. Washe garin ranar da aka daura auren aka sake yin gwaji har kala uku yana bada results daya cewar bana dauke da cutar daga lokacin sai na gane yaudara ne Abiey yayi, kuma na gasgata maganar Deen. Daga lokacin sai ala ta yanke tsakanin mu da su Ammy. A lokacin sai na zama wata sarauniya a gurin Deen ya fara nuna min kaunar ba shi ba, duk wani abu da yake marar kyau ya daina kuma yayi min alkawarin cewar har a abada ba zai sake kusantar kayan maye ba, ni kuma na yarda da yi zaman aure da shi domin na karbi kaddarar da ta zo Baba ya kama mana haya, Mama da siyar da daya daga cikin gidan da Baba ya bar mana ta yi min kayan daki, aka bar dayan. Na sha wahala kamin na saba da Deen, sai dai na same shi ba a yadda na yi zatonsa ba, a lokacin na fahimci Deen mutum ne mai sauki kai kuma mai kauna ta fiye da Abiey ma wacan lokacin da ban san komai akai ba, ya mayar da ni sarauniya.......%???

Na numfasa bayan na dire a linen da na yi masa karyar cewar na haifi cikin da Deen ya mutu ya bar ni da shi babu rai, sai dai ban boye masa cewar yana da ciwon hanta ba da kuma zancen aikin da aka yi masa haka ma na gano cewar shi ya shirya duk abun da ya faru tsakanina da Abiey ba da irin tsabanin da muka samu da Hajiya da Baba ta dalilin haka, har zuwa hana Abiey aurena da Ammy da Mai Martaba suka yi.
Na saka hannuna na share hawayena, ina jin wani abun kamar a lokacin yake faruwa. Sai ya koma jikin kujera ya zauna yana kallona.

%??mkwai abun tausayi akwai abun dariya a labarinki, haka ma akwai abun takaici da bakinciki da bacin rai, sai dai kin rage wani abu daga cikin labarinki%???

Na dago na kalleshi da idanuwan da hawaye suka ki tsaya min.

%??min manta baki fada min cewar kin siyar da ??an da kika haifa saboda ki nemawa Deen kudin magani ba%???

A razane na koma baya ina kamar wanda ta ga wani abun tsoro.

%??mi.... Ban siyar ba....%???

%??min siyar Zahra kin siyarwa Jamila da ??anki wanda ta yaudare ni da shi a matsayin ??ana%???

Ban san lokacin da na rufe baki na mike tsaye da sauri ina girgiza masa kai.

%??ma haka ba ne...%???

Sai yayi murmushin da na tabbatar iyakarsa a fatar bakinsa yayi min alama da na zauna, amman na kasa zaman.

%??maka ne, Zahra na san gaskiya saboda na saka a yi min bincike akanki kuma jinin da na saka aka dauka na ki, Dr Zainab ta kawo min gwajin na farko wanda shi ne na gaskiya ba wanda Jamila da dan'uwanta suka bukaci a ba ni ba, Dr Zainab ta fada min gaskiyar wacece ke tun kamin ki ba ni wannan labarin, kuma na tabbatar da gaskiyar haka domin babu banbanci da abun da Dr ta fada min cewar kin yi soyayya da kanenta, kuma kin siyar da cikin ne saboda ki biya kudin aikin da za'ayi ma mijinki%???

Na fadi gurfane a gabansa.

%??m yanzu na gane dalilin Jamila na kin yarda kowa ya dubata tun tana da cikin har zuwa haihuwar da a nan ba so ayi ta ba, kuma ta ki yarda kowa ya duba yaron nan sai Dr Hamid, ina ta zargin wani abu amman ban zafafa gudun kar na yi zaton abun da ba shi ne ba%???

Na hade hannayena guri daya na mika masa daga inda nake zauna.

%??mana da damar ka hukunta ni, ka dauki duk matakin da ya dace a kaina, ka yi kokari ace ka san gaskiya kuma zuba mana ido, daman Sauban yace zai fada maka gaskiya, yayi min barazana da wannan, a kokarina na rufawa kaina asiri na amince zan aureshi, shi ne albishir din da Hajiya Jamila take maka domin a yau za a daura aurena na uku da mutum da be dace da ni ba, kuma na san da cewar ka san wannan gaskiyar da ban amince masa ba, na amince ne saboda na rufawa kaina asiri saboda kar duniya ta ji kuma kae iyayen Deen su ji, kai ma kuma sani saboda ina tsoron abun da zai biyo baya, ashe ba zan tserewa tambayoyin yan jarida ba, ashe Hajiya zata hukunta ni, ashe kuka be kare min ba zan kunyata a idon duniya, kuma ??ana zai yi Allah wadai da abun da na yi, kaico na ni Zahra%???

Na karasa ina jin wani irin nadama da bakincikin kuskuren da na aikata, wani irin kuka ya ci karfina. Bakinsa ya cika da iska ya busar yana girgiza kai.

%??ma jidadi da ya kasance ??an sunna ne Amir ba shege ba, hakan zai karfafa min guiwar rainonsa a matsayin ??ana, duniya ta sheidi cewar Amir ??ana ne, taya zan fito a idon na fadi cewar ??an da Jamila take ikirarin ta haifa min ba ??ana ba ne? Ya za'a kalleni? Na san Amir ba jinina ba ne amman ina sonsa a haka saboda ban taba haihuwa ba, ina son na rike shi a matsayin ??ana, na miki alkawari Zahra babu wanda zai san da wannan kar barazanar kowa ta daga miki hankali, na saka muku idone saboda na ga iya gudun ruwanku, kuma na kara karantarki, ina da security camera a ko'ina a gidana ba dan na rashin yarda da matata ba, sai dan taimakawa tsoro, hakan kuma ya taimaka min makura gaya wajen fahimtar wasu abubuwan, karki cilastawa kanki auren mutumen da baki ra'ayi saboda neman rufi asirin da ya dade a rufe, idan har akwai wanda ya dace dake a yanzu Zahra to ni, ko dan saboda ki rika ??anki kuma ya tashi a hannunki, kuma ina d yakinin ta dalilin zan iya samun farincikin da na gagara samu a baya, wata kila ke Alheri ce a gareni%???

Sam sam sam ban fahimci inda kalamansa suka dosa ba, ba dan ban fahimci da yare da yake magana ba, sai dan rikicewar tunani domin abun da ya fi karfin kwakwalwa ya shiga cikinta, mikewa na yi tsaye ina rangaji kamar yar maye.

Ya kalli agogon dake falon.

%??mokacin Sallah yayi, amman kamin na tafi ina son na tambayeki shin baki son ki zama silar farincikin wani ne Zahra? Ba ki son ta dalilinki ni ma na samu magaji? Shin baki bukatar kasancewa da ??anki ne? Ki kira yan'uwanki sanar musu kar a daura auren saboda zaki yi shi ne akan cilastawa ba dan kina son shi ba%???

Na saka hannayena na dafe kaina, wani abu nake ji mai kama da juwa kamar mafarki yake daukata, da sauri na juyo na fito daga falon ina takawa kafafuwana suna yin kamar ba za su dauke ni ba. Daker na iya jan kafafuwan na kawo kaina BQ, Mama da bakinta sai kallona suke kamin Mama ta fara tambayar

%??mafiya kike?%???

Bana tunanin ina cikin hayyacin da zan iya amsa mata, sai faduwa na yi kan katifa na runtse ina jin bachi nake a yanzu ne zan farka daga mafarkin da nake. Tunawa da Sauban ya saka na bude na murza idon na tabbatar ba mafarki nake ba, kuma na nemi tsarin Allah daga sherin shedan kana na zabura da dan kuzarin da yayi min saura na nufi wayata na dauka na kwada nasa kira. Be daga ba na sake kiransa nan ma be daga ba sai na fita waje da sauri gurin Mama na mika mata wayar.

%??mama ki kira su Baba ki ce a dakatar da daurin auren nan dan Allah?%???

%??ma lafiya ba, zan miki bayani daga baya, ki yi magana da su yanzu dan Allah%???

%??me Lafiyarki? Baki fada min komai ba zan kira waya na ce kar a daura aure?%???

Ta zaunar da ni ganin yadda nake ta lilo kamar zan fadi sai haki nake irin na wanda ta yi gudun fanfalaki.

%??miya faru?%???

%??mana son shi Mama bana son shi, daman cilasta ni yayi kuma yanzu na gane gaskiyar bana son shi%???

%??mahra? Ni fa kwana biyun nan ban gane miki ba? Mi ke damunki%???

Ganin zata bata min lokaci ya saka na kira Baban da kaina, sai dai na yi rashin sa'a shi ma be amsa kirana ba, na sake kiran dayan shi ma the same be daga ba, wata kila suna cikin masallaci. Wata Gwaggota na kira tana dagawa na ce

%??mwaggo Baba na kusa? Ki fada musu a fasa daurin auren nan, kar a daura dan Allah%???

%??mafiya kike?%???

%??mkwai matsala, Gwaggo kar a daura%???

Sai ta nemi na sadata da mahaifiyata, a take na mika mata wayar ta karba tana amsar mata da cewar ita ma bata san dalilina na fadar haka ba, amman tun da nace kar a daura to a haka kura kawai kar a daura. Gwaggo ta amsa mata da to, kanen mahaifiyata da suka zo suma suka hau buga waya wasu ba su daga ba, wadanda suka daga kuma aka sanar musu cewar a fasa daura auren saboda an samu wata matsala. Sai kashhhhh mun yi latti aikin gama ya gama lokaci ya kure mai afkuwa da afku, domin daya daga cikinsu ya sanar mana cewar an daura. Baya baya na yi na fadi zaune.

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un...%???

Shi ne abun da nake ta fada ina girgiza kai, hawaye na cin karfina.

%??miya faru Zahra? Ki yi min magana mana?%???

Kasa magana na yi sai kuka na ke, na sake daga wayata cikin karfin hali na sake kiran wayar Sauban wannan karon ya amsa muryarsa radau.

%??mello Zahra kin kira wayar tana silent lafiya?%???

%??mna son ganinka yanzu yanzun nan%???

%??mafiya?%???

%??mna son ganinka na ce%???

Na daka masa tsawa da muryar da ban taba sanin ina da irinta ba.

%??mkay gani nan zuwa%???

Ina sauke wayar Mama ta rika hannuna ta shiga dani dayan dakin.

%??min fi karfin awa hudu a bangaren Hajiya Jamila, yanzu kuma kin fito a cikin yanayin dake nuna ba ki cikin hayyacinki kina cewa a fasa daura aure miya faru?%???

%??mama Sauban ya cilasta ni amincewa da aurensa ne, saboda yayi min barazana da siyar da cikin da na yi, zuwan da na yi a yanzu kuma Mr Bashir ya riga ya gane gaskiyar komai%???

%??mnnalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un%???

Mama ta dora hannu akai, ni kuma na zauna domin ina jin idan na kara minti biyar a tsaye zan iya faduwa. Mama kasa cewa komai ta yi tashin hankali ya hana ta kuka, ni kuma ya saka ni zubar hawayen da ban san adadinsu ba. Kamar kyabtawa da Bismillah yan'uwan mahaifina da na mahaifiyata suka kira cewar suna son su shigo an hana su, sai Mama ta fita domin shigowa da su tana ta sake saken karyar da zata yi musu, domin ba zata fada musu gaskiya a yanzu ba sai idan komai ya fito fili su ji. A daidai wannan lokacin Sauban ya kira wayata ina amsawa ya sanar min cewar yana waje yana jirana. Kamar mahaukaciya haka na fito dakin ko talkami ban tsaya sakawa ba na nufi BQ, jikina ma ya samu rufin asiri ne daga hijabin da na saka a dazun da zN tafi gurin Mr Bashir domin da a yanzu ne ina da tabbacin da ba zan saka shi ba. Kamar aljana haka na isa gurin da ya faka motar ina jin kamar na makureshi na huta.

%??ma cutar da ni a banza, abun da nake yi ma gudu ban tsira ba, Mr Bashir ya san komai%???

%??malm down Zahra%???

Ya fada yana kwantar min da hannayensa.

%??ma zan kwantar da hankalin ba, daman sha'awar jikina ya saka ka cilasta ni ko to ga jikin nawa ka yi abun da kake so, saboda kun maida ni bola kowa ya dauko shararsa akai%???

Ina kware cinyar hannuna na mika masa cikin kuka, sai yayi baya.

%??mubhanallahi, ni ba Muhamminki ba ne%???

Wani kallon uku saura kwata na yi masa, sai ya fadada fuskarsa da murmushi.

%??ma da ni aka daura auren ba%???

%??ma....wake....%???

Na bukata bakina a bushe ina motsa shi daker na hada kalmomin. Zagayawa yayi ta dayan side din motarsa mai bakin gilashin da ba a iya ganin abun da ke ciki, ya bude.
Komai na duniyata sai ya tsaya cak.....! Ciki har da tunanina da numfashina da kuma hawayena, lallai a yanzu kam na tabbatar duk abun da ya faru a yau mafarki ne ba zahiri ba...!








_______________
Ni kam me Zahra ta gani ne? ??9?
Ina Yan Team Team kowa ya dauki nasa ???b
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Kamar hoto haka na tsaya a gurin ina kallonsa, har ya karaso kusa da ni fuskarsa da murmushi ya kai hannunsa ya share hawayen da gudunsu ya tsaya a kumatuna.

%??mikar burina...%???

Ya kama hannayena ya murza yatsun a hankali.

%??man... Ban...%???

Sai na kasa furtawa ganina yayi nisa irin nisan da kafafuwana suka gagara daukar jiki har sai da taimakon Abiey na tsaya tsaye rabin jikina kuma a kirjinsa. Ba bachi na yi ba kuma ba zan kira shi da suma ba, haka kuma ba zan ce ina a cikin hayyacina ba.

%??momai ya kare you're mine now%???

Na ji maganarshi muryarsa saitin kunnena kamar mai rada, ni da shi muka sulale jikin motar sai dai kamin na kai kasa na ji an yi sama da ni, sai hankali yayi kaura daga jikina ban sake sanin inda nake ba. Sauyar iskar da nake shaka da kuma sanyin dakin ya tabbatar min da a gida nake ba, karfin halin da na yi na bude idanuwana ne na sai na yi arba da kyakkyawar fuskar da har yanzu nake ganinta kamar a mafarki, kwance nake shi kuma yana zaune rumgume da rabin jikina, fuskarsa saitin fuskata. Wani irin tarayya idanuwanmu suka yi wanda na kasa ko da kyabta su balle na dauke kai daga barin kallonsa, sakon lallausan murmushin da yake aiko min ya hana ko dan yatsana na daga balle kuma raba jikina da na shi. Bakinsa ya kai ya sumbanci hancina, a nan na yi nasarar rufe idon nawa na ina sauraren yadda yayi sama ya sumbacin goshi hawayen idonshi suka sauka akan fatar idona dake rufe, yana

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login