Showing 141001 words to 144000 words out of 210919 words

Chapter 48 - CIWON SO

10 Oct 2024

4218

shayar da su ko tufatar da su ke kayar masa da gaba ba, ko daya, dama ya saba, abu ne da yake yi sai dai a taimaka masa idan an yi niya, abinda ya fi kayar masa da gaba a yanzu fitowar da zai yi ya yi tsaye a gabansu a matsayin UBA, ya zamto zasu rataya a wuyansa ne, zai daina rayuwa da tunanin kansa shi shi daya, dole zai zauna ya dube su ya fuskance su ya ji damuwarsu, dole zai san hanyar magancewa, dole zai dauki mataki a lokacin da bashi da karfin hakan, dole zai dube su ya biya masu bukatunsu koda kuwa shi zai tauye nasa bukatun, dole zai shiga hurumin tsagairunsu da kansa, dole zai yi hira da yan matan baki daya dan ya san su waye su me suke nufi da rayuwarsu ta yau da kulun

Kiraye kirayen sallar magariba ya saka shi dole fitowa daga motar yana bin kowa da kallo

A nutse ya dakatar da masu shiga tsakaninsa da mutane ya hanna su aikata hakan sannan ya ringa amsa gaisuwar nan a tsanake har ya fice ya daura alwallah ya karasa masallaci da gaggawa ya bi sallah

A masallaci wata doguwar hira dole ya tsaya ya bi dan masu masa ta'aziya ga kuma kannensa maza duk a gefensa hakan ya saka shi kara jin wani girma na sake hawansa har suka gama suka nufo gida shi da yan uwansa da Aban Ahmad bangaren samarin gidan suka zauna a falo sunna sake yi masa ta'aziya da ban baki sosai shi kuma yana sauraronsu yana kuma amsa su yadda yaa kamata


Jalaluddeen ne ya shigo da kayan abinci ya ajiye ya koma ya sake kawo kayan shayi ya ajiye sannan ya zauna kansa a kasa ya ce" Babangida Wai maman Furera tace ka ci abincin nan Mamah tace masu baka ci komai ba"

Dan tsai ya yi yana kallonsa, sai kuma ya ce" Ita maman ka ganta ne? Yaya jikinta ne?"

Jalaluddeen da dan mamakin jin yayansa na masa tambayoyi , duda abinda ya shafe shi yake tambayarsa, ama a sanyaye haka ya dan dago ya kalle shi, yannayin da ya gani a shinfide a saman fuskarsa ya sake saka shi jin wani irin tausayi na yayan nasa a cen kasan zuciyarsa , a hankali ya ce" Eh ta ci, tana tare da ZAHRA tana tausa mata kafafuwanta yanzu haka"

A hankali ya lumshe idannuwansa ya gyada kai yana fadin" To zuba mana mu ci abincin "

Yanzun kam dolema mamakinsa ya kasa boyuwa, ya zubawa yayansa ido sosai, sai kuma ya zuba abincin duk da yana yi a ransa yana jin tsoron kar ya yi ba daidai ba har dai ya gama ya ajiye ya dan duka da nufin tafia Babangida ya idasa kashe masa mamakinsa ta hanyar saka shi zama dan su ci tare

Gaskiya ya yi mamaki, hannunsa hannun yayansu da Aban Ahmad sunna cin abinci hankali kwonce har ya dan tataba ya basu waje suka gama ci ya kwashe ya mayar da sauran bangaren Maman ya tarda yan uwansa suka hade a zuciyarsa maganar na mintsininsa , karshe ya ajiye hakan a mizanin halin da yayansu yake ciki na rasa ABAH ne, babu wanda bai san irin kusancinsa da Abah ba, a yanzu da yake cikin halin nan dole a tausaya masa, ya rasa uba, amini, abokin shawara, idan ka gansu sun taho shi da ABAH sai sun baka sha'awa, ko me zai yi sai ya shawarci mahaifinsa, bashi da wajen hira ko wajen kai kuka sama da Abansa, yau ya wayi gari ya laluba babu, mutuwa kennan mai yanke duk wani launi na jin dadi ko akasinsa, mai mayar da mata zawarawa mai mayar da yaro maraya....Allah ka bamu kyakyawan karshe

Washe gari mahaifiyar marigayiya da kanwarta da ?ba?banta biyu wa'inda zata wanke din nan suka iso gidan makokin

Tunda suka zo suka sauka a bangaren na Maman ita ta zagene ta shige cikin yan gida, irin yadda take shige da fice kai kace da igiyoyon auren MARSHAL a wuyanta, tunda ta zo ta ce da Laraba kauce bani waje ke karamar yar bariki ce, domin itama Laraban har kwana ta yi a gidan, amma ita a dari dari take hasalima cakule take da yaran gidan wajen su Furera, amma ita tana zuwa ya zamto a bangaren iyayen ta fi zama sannan ta fi bauta masu, dukkan wani abu da ya dace ace an yi da shishigi da iya damawa da mutane ta ringa sani tana shigewa jikinsu sannu a hankali kafin ake zuwa kwana bakwai har ya zamto idan wani abin ne sai ka ji an ce aunty MINAL kaza ake so, ko kaza aka ce, ita kuma da karfinta zata je ta yi, haka kuma babu dakin da bata shiga kanta tsaye, babu wace bata yiwa shishigi har ta gane wace wa a cikin iyayen MARSHAL din
Su da kansu iyayen tun sunna mamakin ita kuma yaya haka kamar wata sarakuwar gidan bayan yayar matarsa ce har suka harbo jirginya suka kuma zuba ido da tarin mamakin gannin wannan kwabi, to kwabi yake a idannuwansu mana itama mimin da ta rasu ta girmeshi bale yayarta, duk da mutun ce mai karamin jiki ga kuma.iya kula da jikin nata dan kana ganninta zaka fahimci a waye take tass, ama kuma ai abin wani banbarakwai da shi

Mamah kam tana daga gefe, carbinta shi ya fi komai yi mata dadi a hannunta a irin wannan lokacin
Bata kwana a bangaren Abah, takan je dai tunda safe, dare na yi su juya da ?ba?banta bangarenta su kwonta
A zaman da take yi a bangaren na Abah hankalce take da kowa, tun ba'aje ko'ina da rasuwar ABAH ba take fuskantar abinda ke iya zuwa ya zo, hakan ya sa ta sake tsananta addu'a sannan ta hanna kanta shiga huruminsu dan kar su matsewa junna waje a zo a yi abinda ba shikenan ba, domin ta kula a tsakanin nan nasu kowace kiris take jira ta dankarawa yar uwarta magana bayan su dukansu sunna cikin hali ne na rufin kai, hakan baya hanna su shagalta da hiraraki da yan uwansu da dai sauransu, shi yasa ta iya kanta ta kuma iya ?ba?banta, domin sau daya aka dankarawa Fatima maganar da bata yi mata dadi ba, ya sa ta sake jajircewa kan Y'arta a hakarkarinta, idan me suke nufi su kuma su yi rayuwa ce, dan Maman Abul ce da kanta wai tace da Fatima oh yan matan Mama kuma sai a fara bankwana da Maman ko?, Tunda lokacin a kara gaba ya yi a je a bi wani sarkin........, Wannan magana sam Mama bata ji dadinta ba, ta kuma sake gannin rashin wayonta sannan ta sake kama kanta dan ta tabbata itama dama ake jira , wanda ya hada dinma ya rasu amma ba zasu sasautawa kansu zafin kishi ba


A haka kwanaki suke ta tafiya, MARSHAL dai bai koma bakin aiki dindindin ba sai da aka wayi gari aka yi sadakar Arba'in ta ABAH, a washe gari ya ringa sallamar mutanen da suka masu karra suka zauna har wannan lokacin ciki harda Minal

Da kanta ta same shi a inda yake zaune, watau wajen gerding ta duka har kasa kanta a kasa cike da kisa irin ta wace ta goge tana dan make murya kamar zata yi kuka ta ce" Allah ya taimakeka muma muna so mu juyo ko gobe ma in sha Allah"


Jaridar dake hannunsa ya ninke a hankali yana dan kallon yannayinta,
A katse ya ce" Allah ya nuna mana"

Kai ta dago ta zuba masa ido a ranta tana ayyana shikenan? Bakin maganarsu kennan?, Shikenan ya kare magana kennan?, Sai kuma ta dan sake sada kanta a tausashe ta ce"


27
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Kai ta dago ta zuba masa ido, ita gaba daya wani kara bijime mata yake a idannuwanta, kyansa kwarjininsa, tsarin mulkinsa sake cika idannuwanta suke yi, buga mata zuciya yake ko sunnansa bale shi din da kansa, shan kanshinsa shine tak abinda take nema a wajen maza, ta fi so yana shan kanshin nan dan gudun kawo rainin yan matan zamani a duniyarsa, a haka dai da yake a haka ya yi mata dari bisa dari, sai kuma ta lumshe idannuwan nata gannin kamar zai kalleta, muryarta na rawa sosai ta shiga share hawayen karya, shikenan ? Bakin maganarsu kennan? Shikenan idan ta tafi kuma sai yaushe? Babu shi babu labarinsa fa, kiran nan sai ta wuni tana yi da kyar ya daga idan kuma ya daga din kayya de mata maganarta yake yi a kullum baya bari su zurfafa zaurance ko yayane, muryarta na rawar nan a tausashe ta ce" Baban Abah, shikenan idan na tafi kuma babu wani maganar da muka tsayar ? "

Sai da ya gama dan rike rike maganarsa sannan ya ce" Dangane da me?"

Dik irin iya takunta sai ta ji wani dar dar da kuma nauyin maganar a harshenta bayan ta riga ta shirya tsaf yaki da duk wanda zai nemi tare hanyarta a kan maganar Babangida ciki kuwa koda shi ne.
Muryarta a sanyaye ta ce " MARSHAL, shin baka amshi soyayata bane?, Ina nufin ko na maka tsufa ne?....."


Tsabar rigima irin ta MARSHAL sai ya samu kansa da yin dan murmushi, domin shi ai bai ga wani girman da wannan zata wani yi masa ba, duka duka shekarar nawa cema tsakaninsu? Ai yarinya ce mana!.....zai kuma tabbatar mata cewa yarinyar ce ita a hankali

Gannin murmushi a saman lebensa ya sakata a halin rudu da rabuwar tunani kashi biyu
Sai dai jin muryarsa a nutse yana fadin magana kamar haka ya sakata lumshe idannuwanta tana ji a ranta eh lalle wannan din shine daya tak namijin da ya isa ya ganta a matsayin matar aure" Minal, ai ba wannan maganar......., Kar ki wani damu kanki da wannan, lokaci nake jira..........ke fa jinnin mimi ce, dole kece zaki iya bani farin ciki............, Ki dan bani time na sake daidaita lamarin gidanmu,zan zo da kaina"


Hankali kwonce take ta murmushi da wani sassada kai irin ta ji kunyar nan, sosai kalamansa suka sakata farin ciki marar misaltuwa dan bai taba fada mata haka ba gaskiya

Farin cikinta bai katse ba ya dora da fadin" Yaushe ne auren Yaran nan?"

Da dan karsashi ta sanar masa cewa bai fi saura sati biyu ba

Kai ya gyada a hankali ya ce" Kin san na ce ba zan yi masu gadaje ba, dan hurumin mahaifinsu ne ko?"

Kai ta sake gyadawa tana jin kamar tace masa mahaifinsun banza mahaifinsun wofi, mema yake da shi da zai iya yiwa ?ba?banta gadajen daki?, Mutumen da ya so nuna dayar ba zai badata wa Elhaji tanko ba wai bincike ya nuna baa mutumen kirki bane? Ai maganar mutumen kirki ta kare tunda ya tara ?ba?ban banki, shi da bashi da su sai ya yi hakuri kawai yaa tattare tsohuwar dardumarsa, mutun sai shegiyar akidar tsiya shi mai talautaciyar zuciya

"Amma Amir zai ganki kafin ki tafi, plz ki kula da kanki......" Ya karashe a dan gajiye da hayaniyar sannan ya bude jaridarsa ya dora daga inda ya tsaya


Kai subahanalah, kwarankwatsa wannan gayen duniya ne, bama irin da ya wani sasauta murya ya furta mata ta kula da kan nan nata sai ya sakata sakin baki tana kallon tsararan gys tana hango abubuwa da dama a cikin kwakwaluwarta

Da kyar ta iya rarashin kanta ta bar inda yake ta koma bangaren su sai watsa hakora take suka idasa kimtsawa ta kuma haye wajen Mama

Sallama ta yi a lokacin Maman na zaune saman gado, hijabin nan dai da ta mayar abin zama koda yaushe zumbulele mai kaurin tsiya da kuma duhu ne a jikinta, baka gannin komai na jikinta sai carbinta dake hannunta tana ja, tana zaune a saman gado ne tana jan carbin bayanta kuwa wannan shegiyar yarinyar mai kama da ya'yan nasaru ce kwonce tana barci ita yar gata kafafuwanta daya a saman cinyar ta Mama wai bigewa ta yi kuma ta saka Maman a gaba tana hawaye shine aka shafa mata man zafi barci ya kwasheta bata fara harbe harben gigin barcin ba da tuni sun raba wajen zaman

Gashin kan yarinyar take kallo bayan ta duka nan kusan gadon sai kuma taa dauke kanta tana jin wannan yarinyar sam bata yi mata ba, ita fa in zata tuna bata taba gaisheta ba, yarinyar kamar wata mai asali sai shegen girman kan tsiya, ita da ta fahimci wacece ita sai da ta yi mamaki ta zata ai Yar Maman ce itama ta cikinta dan ta ga ai su MARSHALma farare ne ko farin ABAH ta yi, sai kuma ta gane inda zancen ya dosa, itama Maman in ba wani neman fitina ba meye dadinka da kishiya har da zaka dauki shegenta ka runguma? Idan wata yar mai kunnar bakin wake ce ta tashi dare daya ta kone uban kowa a huta ko? Jarabar yayume yayumen tsiya

Murya a tausashe ta ce" Mama mu mun gama shiryawa, zamu tafi in sha Allah, dan Allah idan na bata maki ki yafe min Mama"

Mama ta yi murmushi tana fadin" Haba dai yata, ai ba wani batawa, ni dai zan nemi afuwa masha Allah kin zo banda aiki babu abinda aka ringa saka ki, na gode na gode sosai Minal Allah ya saja maki da alkhairi ya biya, dan gaskiya ni ban isa in biyaki ba, na gode sosai, ki ce yau zaku wuce kuma?"

Minal na murmushi ta ce" Eh mama yau zamu tafi gidan Aunty kawar Hajia sai mu wuce da asuba wannan wace suka zo gaisuwar nan kusan sau uku"

Mama na sauke kafar Zahra daga cinyarta ta muzguna ta mike tana fadin" Allah sarki, eh kwarai na gane matar mai mutunci, na gode sosai Minal Allah ya biya , gaskiya kin kyauta mun gode sosai Minal"

Wajen sif dinta ta je ta ja zata bude amma ta ji a rufe, dole ta dawo inda Fatima take kwonce ta shiga tashinta a hankali tana dan taba wajen wuyanta tana kiran sunnanta, hakan ya sa ta yi mika ta bude idannuwanta masu shanye da launin ja na abin barci tana kallon Maman da yannayin tambayar me yasa aka tasheta?

Mama ta ce" Ina ky din sif ?"

Dan luuuuu ta yi da idannuwan nata sannan ta mike tana ziro kaffafuwanta kasa, a lokacin suka yi ido hudu da Minal dake binta da wani kallon da bata san ko na meye ba, dama ga abin barci ga bakinta da bata budewa sam idan ta farka a barci har sai ta kuskure sai ta dauke dubanta bayan ta mata alamun gaisheta da hannunta sannan ta karasa wajen ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  jakar Maman ta hannu ta bude ta lalubo key din ta je ta budewa Maman sif din ta wuce bayi
Baki Minal ta dan tabe a ranta tana ayyana ' Lalle kin samu guri yarinya, kece harda saka hannu a jakar Mama kai tsaye abinki kina tafe kina wani bude duwawu ke ga mai lasisin iskanci........., Ba damuwa kin sakan shaku a kanki ni kuma zan yi maganinki in dai na shigo gidan nan, dan in sha Allah sai gannin mamah ya gagareki ki je cen ki karata da uwarki, koda yake ta yiwu kafin na shigo din kun bar gidan ke da uwar taki baki daya dan ai Doctern ya mutu du wata wace aure ya hada sai ta dan harhada tarkacenta ta je gidan uba nata'


Alkhairi irin na su atampopi da turare Mama ta yi mata, kasan cewar dama bata rabo da tara yan atampopi a kayanta, turarurruka kuwa gidan kennan, Mamah sarkin turare, har Zahra ta samu daya itama bayan an ja mata kunnen sauran a jishi kauuuuu a jikinta kamar zata je gasar gwada kanshi ta zuba mata a babbar leda blue tace dan Allah kadan ne ba yawa, ita kuma ta ringa nuna ai ba zata amsa ba su da suka zo ta'aziya kuma sai a masu kyauta?, Da kyar dai Mama ta shawo kanta ta yarda ta amsa din ta dauko kayanta Maman na biye da ita dan ta yiwa mamansu godiya da kuma bankwana


Gashin kanta ta hade ta daure tana ta murmushin turaren nan, bude kwalbar ta yi ta shiga dan fesawa a wajen wuyanta da kuma tafukan hannayenta, sai kuma ta shafo ta sinsina tana wani lumshe ido tana jin farin ciki a cikin zuciyarta da kwanciyar hankali kai ta yi missing din turare, irin sosai din nan wallahi, gashi mai yawa ne ga sansanyan kamshi a tare da shi...............


Wayarta ce ta shiga kuka da kida a hankali na kasida yana tashi mai taken bari mu gaida batula...............

Daukowa ta yi tana kallon sunnan da ta dora masa, BAKONA hade da heart a jiki, ba dan komai ba sai dan ma'anar hakan kennan....bako ne shi a zuciyarta

Dan murmushi ta yi, dabi'unsa baki ne a duniyarta, irin yadda yake ba soyayya dama da lokaci bakin abubuwa ne a rayuwarta......kalamansa kansu baki ne a dduniyarta


Ajiyewa ta yi har sai da ya sake kira sannan ta daga a sanyaye ta yi sallama tana mikewa ta kashe ACn dake kunne dan sauka zata yi kitchen wajen su aunty

A sanyaye ta amsa sallamarsa sannan ta yi shiru tana sauraronsa

Hassan ya yi murmushi ya ce" Gimbiyata, yaushe zan zo na yi gaisuwa ne? Ina so na zo na yiwa Mama gaisuwa da su yaya please"

Murmushin da take yawaita yi masa ta yi masa yanzunma, a hankali ta buda manyan idannuwanta ta kafe waje daya da kallo, abu daya ke yawan kayar mata da gaba wanda kuma take so duk rintsi kafin ya ga Mamah sai ta sanar masa idan har ya ga zai iya ya mike a haka in kuwa ba zai iya ba tun kafin abu ya fi karfinsu daga ita har shi gwara su hakura ke kayar mata da gaba
Watau ta sanar masa wacece ita a dunkule ba a zayane ba, tunda itama bata san a zayanan wacece ita din ba, ita dai ta san shegiya ce ita kawai, bayan wannan sauran bayanan gaskiya a rufe suke a kwakwaluwarta , inama ace ta san waye baban nata? Da dan sauki, sai dai gashi ita bata sanshi ba, bata taba ganninsa ba, tana amsar sakamakon aikin da ya aikata a duniya

A

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login