Showing 165001 words to 168000 words out of 210919 words

Chapter 56 - CIWON SO

10 Oct 2024

4247

ya cika da jama'a, sai ya fara safa da marwa cikin falon kamar mai rafeti. Tsaye na yi cikin falon ina kallon ikon Allah, Sauban ya zama kamar dan maye yana ta aikin shan yaji yana shafa jikinsa da kansa, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na nufi jakata na dauka na rumgume.

%??mi dai na shiga uku ban san kuma abun da ya faru ba, miyasa suke yin layi?%???

Na tashi na karasa kusa da Abiey na bude qur'ane na fara binsa ina karanta masa ina tofawa, idan na yi kamar aya goma sai na dawo gurin abokinsa Sauban na karanta masa shi ma na tofa masa, amman ba wani canj, Sauban din sai bin kujeru yake yana son ya tashi tsaye ya kasa.

%??mayyo Jama'a a kai ni gida%???

Jin haka yasa na rufe kur'ane na maida a cikin jakata na aje jakar a gefen kujera na nufi inda suka aje keys din motar wato kan hannun kujera na nufi kofar na bude na fita na nufi motar da suka zo na saka key din ina da murdawa daker na samu kofar ta bude sai na bude ganbu na dawo falon na rika Sauban daya gagara mikewa sai cewa yake a kai shi gida.

%??macece ke?%???

%??mahra%???

%??mahra wa?%???

%??matima Zahra%???

%??m ina nake?%???

%??m idan Ammy%???

%??macece Ammy?%???

%??mahaifiyar abokinka Abiey?%???

%??minene kuma Abii?%???

Yanzu kam ban san kalar amsar da zan bashi ba, sai dai na yi iya kokarina na ganin na mikar da shi tsaye amman na kasa, domin ni babu karfi shi ma kuma sai shan yaji yake yana lasar baki kamar tsohon maye.

%??mna Matata?%???

%??mna zan sani ni, kana da mata ne?%???

%??ma dauka ina da ita, to Ina Mamata ko ita ba ba ni da ita? Kin san gidanmu? Ina ne nan?%???

%??man sani ba ni dai dan Allah ka yi shiru%???

Ya ki yayi shiru sai tambayoyi yake sako min kala kala da ban san amsarsu ba, Abiey kuma ya ki ya zauna sai zagaye falon yake yana ta yi ma bakin da ban san su waye ba maraba da zuwa, cikin iya Allah na rika Sauban na mika mike tsaye sai ya sako min nauyinsa ni da shi mika fadi a kasa, sai na yi saurin tashi ina rika shi.

%??man Allah ki kai ni gida%???

%??mo ai shi ne nake son ka shiga motar sai na tuka ka tafi gida, ni ina zan san gidanku%???

%??ma can ake bi, sai abi nan sai abi can%???

Ya nuna min kofar kitchen, jin kamar tsayawar mota yasa na sake shi da sauri na nufi inda na aje talkamina na dauka na dauki jakata na nufi kofar kitchen na bude na tsaya a kitchen din har sai da na ji shigowar Ammy, salati ta saka ita da Anty Zainab tana tambayar lafiya, amman babu mai amsa mata a cikinsu Sauban din sai kiran a kai shi gida yake, Abiey kuma yana fadin gidan da baki babu gurin zama.

%??mllah yasa ba wani sammun aka yi masa ba, matan uban nan sun saka shi gaba ga kuma makiya abokan wasansa%???

Ina jin haka sai wata zuciyar tace min na fito na fadawa Ammy abun da ya faru, wata kuma tace min na ranta a na kare, sai na bude kofar baya cikin sanda na fice daga kitchen din, kamin na isa gate din na samu na fice jinina ya hau kusan tari biyar ma domin ji nake kamae ma'aikatan gidan tare ni za su yi. Na isa na fadawa Mama da Yaya Maryam aika aikar da na yi sai Mama ta kwashi yan tufafinta da za su wadaceta ta yi kwana biyu ni ma na debi nawa muka bar unguwar, Family house dinsu muka tare babu fadan da ban sha ba a lokacin da Mama ta fada musu dalilin guduwarmu, Ba dama na san da sai Deen ya same ni a can yayi min dukan daya saba domin ya shata min line tsakanina da Abiey amman ban ji gashi na sake komawa gidan har na sake aikata laifi, sai dai ban tsira da dukanba domin Mama ta yi min nata da kanta sai dai nata dukan mai sauki be ne ba irin wanda Deen yake min ba na fitar hankali. Jin shiru ba a zo nemanmu ba Mama ta tambaya a unguwa aka fada mata cewar babu wanda ya zo nemanmu sannan muka dawo gidan, tun daga lokacin sai ya zamana idan zan tafi makarantar Islamiya sai Mama ta raka ni ta tabbatar na shiga sannan ta dawo, idan kuma muka taso bana yarda na bi ta gaban gidansu Abiey ma saboda Mama ta fada min cewar abun da na yi wata kila idan Ammy ta kama ni zata mika ni hannun sojoji yan sanda kuma za su tuhume ni da mu'amala da kayan maye, ba dan wannan tsoron ba da babu abun da zai hana na koma gidan ko dan na bawa Ammy da shi kanshi Abiey hakurin abun da ya faru.
A haka na kwashe wata biyu ko kofar gidan bana yarda na bi balle ya mutanen gidan su gan ni. Wata rana ina zaune ina wanke uniform din makarantar Islamiyar mu sai ga Ammy ta sallamo a gidan tana sanye da bakar abaya ta yafa katon mayafi a sama dayan hannunta rike da jakar alfarma, sai kamshin turare take zubawa irin na manyan matan masu kudi, fuskarta a sake tana ta murmushi. Sai dai hakan be hana na tashi na koma bayan Mama na boya ba gabana sai faduwa yake ina ganin kamar ta zo ta yi wata magana ne ko ta saka a kamani kamar yadda Mama take min hasashe.

%??min san kin yi rashin gaskiya shiyasa kike boya ko?%???

Maganarta ya saka hankalina ya dan kanta domin a cikin wani yanayi mai kama da raha ta yi min maganar, Mama ta tashi da sauri ta dauko mata tabarma ta shimfida mata ta dora carpet din sallah akai jikinta har kyarma yake.

%??mannu da zuwa Hajiya Sannu da zuwa, Allah yasa ba wanin laifin Zahra ta sake yi ba?%???

%??ma ni da na zo na ji dalilin rashin zuwan Zahra a gidana, ko dai ke kika hanata? Tare da Aliyu mike yana waje shi ya matsa min da maganar Zahra ya dame ni na zo na ji dalilin daina zuwanta%???

A yadda na kura Ammy mace ce mai far'a da son mutane, kuma bata kyamar talaka haka ma ??anta Abiey. Sun dauki lokaci suna hira da Mama sannan ta sanar min cewar Abiey yana waje yana jirana na tafi gunsa mu gaisa. Wanke kafafuwa na yi na saka hijabina na nufi kofar gida, tafiya kadan na hango inda suka faka motarsu, domin kalar motar kadai ya isa ya saka na gane cewar ita ce motar da Ammy ta shigo, tafiya nake ina jin wani abu mai kama da marmarin ganin Abiey yana sallamo min har na isa, bakin gilashin motar ya sauke karaf idonsa cikin nawa wani kalar kwarjinsa da kimarsa suka cika idona, a take na samu kaina da faduwar gaba da kuma jin kunya a lokaci daya.

%??mi idonta sarkin kiriniya how are you?%???

%??m'm fine%???

Na dan kalleshi kadan na dauke ido da sauri, kwana biyun nan da ban saka shi a ido ba na lura har wani kyau da haske ya kara. Mun dade a tsaye muna hira sannan miko min ledar chocolate yana zolayata wai ya san yara chocolate ko ice cream suke sha shiyasa ya siyo min. Daga lokacin sai wani irin shakuwa ta shiga tsakanina da shi, Mama kuma ta sabu da Ammy wani lokacin ma idan Ammy tana son wani abu a gurin Mama zata aiko ta nema mata, ni kuwa sai ya zamana ba ni da wani aboki sai Abiey komai an dauko a duniyar nan Abiey daman can ina son mutumen da zai iya daukar matsalata, kuma ya zamana yana sakar kin fuska yana nuna min kulawa ba duka ba kyara ba kamar Deen, sai dai duk da irin shakuwar da ke tsakaninmu Abiey baya yarsa ya sha abun hannuna ko ya ci sai idan tare muka siya, Ammy ma bata yarda na shigar mata kitchen idan ma zan ci abinci a gidan sai ta zuba min da kanta ko kuma na zuba a kan idonta. Ban taba yarda Deen ya san da alaka ta da Abiey ba Mama ba ban bari ta sani ba, domin na san idan ta sani zata iya hanani yawan fitar da nake da shi a sace da kuma zuwa gidajen yan'uwansa ko na Ammy da muke, kamar idan an aike mu ko kuma ziyarar ta tashi.

A duk cikin yan'uwa na lura Abiey ya fi shakuwa da Dr Zainab duk wani sirri nasa ta sani, duk wata shawara da ita yake, yana yawan zuwa gidanta da ni ko ba ni ya wuni, ban san Abiey babban mutum ba ne har sai da ya taba daukata muka shiga gidan Sarauta gurin step Mother dinsa wato Anty Amarya, ita ma tana da yara biyu mata Aisha da Narji, su ma dai babu ruwansu da daukar kai cikin kankanen lokaci muka sabu. Idan Abiey ya shirya tafiya gurin buga wasansa na kwallo sai na ji kamar zai yi tafiyar da babu dawowa ne saboda shakuwar dake tsakaninmu a ranar bana iya cin abinci haka zan wuni kamar marar lafiya, idan Mama ta lura da na daina zuwa gidan kwana biyu sai nace mata Ammy ta yi tafiya bata nan, idan ya kira waya ko video call a gidan Ammy da sunan mu gaisa sai na ji kamar na shige cikin wayar tsabar farinciki. A lokacin da Deen ya lura da hankalina ya dauke daga kan samari da kuma duk wata shiririta da nake bana da gurin zuwa sai gidan Ammy Ammy dai, ko da na zauna a gida Abiey zai aiko kirana da sunan Ammy na tafi a gidan na wuni, wani lokacin mu yi ta game ko wasan tsere tun Ammy na yi mana fada har ta gaji ta saka mana ido, idan muka yi wani abun sai dai ta yi dariya. Idan Abiey na yi arba da wata budurwa da nake ganin ya dace Abiey ya aureta ko ya so ta, sai na tareta na karbo masa numberta amman ba zai ba ni hadin kai ba, ko da ya fara waya da ita kwana biyu sai ya kawo dalilin da zai saka su yi fada. Idan kuma muka fita tare wani ya nuna yana so na sai yace musu ina da miji, idan kuma na kawo masa labarin samarina sai yayi ta fada da Ammy yana cewa ta gani ta gani ko zata ja masa matsala, kalamin Ammy daya a kullum na tsaya na maida hankali akan karatuna musamman da yake ina ajin karshe a makarantar secondary, duk wani tsadadden tufafi da zaka gani a jikin Ammy ko Abiey ya siya min, babu abun da zan je wa Ammy da shi ba zata karba min ba, har Dr Zainab da take yayarsa tana yi min hidima ta nuna min so saboda Abiey. A lokacin da Deen ya kura da abun ya fara yawa sai ya taka min burki...
12/28/22, 11:06 - Buhainat: Hana ni zuwa gidan da Deen yayi sai ya yanke min jindadi, shi kansa Abiey sai ya fara damuwa, da kansa ya aiko Ammy ta bincika masa lafiyata, Mama ta sanar da ita lafiyata kalau yayana ya dakatar da ni daga fita ko'ina ne, har ma ta kara da nata cewar bata son yadda nake da rawar kai ina shigewa mutane.

%??mi kiriniya ce kawai take damun Zahra amman bata da wani abun dake nuna rashin tarbiya a tare da ita, idan ba Zahra ta manta ba ko zama kusa da namiji bata yi sai dai tana iya mika hannu ta karbi abu ko kuma ta shiga a inda mazan suke bata dauki wannan a bakin komai ba, kin yi wa yarki tarbiya mai kyau, sai dai hali ne ko da yadda Allah ya shimfida masa nasa, kuma ina fahimtar haka na taba da ke, na yaba sosai da yadda kika tarbiyantar da yarki, sauran sai mu barwa Allah%???

Mama ta jidadin kalaman Ammy sosai, daman burinta a kullum kar na watsar da tarbiyar da tayi mini, ko zuwan da nake a gidansu Abiey tana yawan nanata min na kama kaina na rike mutuncina, a nan Ammy ke sanar da ni cewar za su koma gidansu da aka gama gyara kuma tana fatar idan zata koma ni da Mama da sauran makotan da bata sani ba za su mu rakata kuma zumunci zai daure, sam ban jidadin wannan maganar ta Ammy ba domin ina ganin zata yi nisa da ni. Daga lokacin sai na fara satar kafa ina zuwa gidan, ina ta nunawa Ammy da Abiey zan yi kewarsu idan suka bar unguwar, sai Ammy tace ke da nake son iyayenki su mallaka mana ke ki dawo tare da mu, sai dai ban fahimci abun da take nufi ba, sai dai na ce mata ai Mama ba zata yarda ta ba ni ba, ko ma ta yarda Deen ba zai bari ba.
A lokacin da Deen ya gane na sake maida hankali a gidan, sai ya zaunar da ni yana karanta min cewar Abiey ba zai taba aurena ba, domin su yayan manya basa auren yayan talakawa musamman ma shi da yake sanannen mutum da duniya ta shaide shi, sai dai na tabbatar masa da cewar ba soyayya ce tsakanina da Abiey ba, amman ya kasa yarda. Ranar da Ammy suka koma sabon gidanmu na yi kuka sosai kamar zai cire ido, a tunanin ba zan kasance da Ammy kamar da ba, ashe abun ba haka yake domin kuwa bayan tarewarsu a sabon gidan sai wata kalar shakuwa da aminta da shiga tsakanina da Ammy, idan zan tafi islamiya sai na sa ci kafa na tafi unguwar ina isa Ammy zata ba da kudin Napep na biya wanda ya kai ni, idan kuma na tashi komawa sai a kai ni da mota wani lokacin direbanta yake kai ni wani sa'in kuma Abiey zai maida ni gida, idan yayi min siyayya sai na boye ba zan bari Mama ta gani ba saboda kar ta yi min fada. Wata rana bayan na je can Abiey ya dawo da ni ya sauke ni a kusa da Islamiyar mu ashe Deen na gurin daman yana zargin ba makaranta nake zuwa ba. Tun daga gurin makarantar ya fara dukana har cikin gidanmu a ranar Deen yayi min dukan da sai da ya karya ni, Mama ta yi fushi sosai fushin da kawar da kawaicin da take masa ya saka ta gargadeshi cewar kar ya sake saka min hannu a jiki, ranta ya bace sosai domin duka yayi min wanda ya saka yan'unguwa suka yi zargin ya kamani da wani ne, cikin kankanen lokaci sunana ya bace. Da aka kwana biyu Ammy bata gan ni ba sai ta zo da kanta domin duba ni, a lokacin ne Mama ta fada mata ba zan sake zuwa gidan ba, kuma ba jidadin zuwan da nake ba a gidan ba da sunan zuwa makaranta amman Ammy bata taba koroni ba. Ran Ammy ya bace sosai irin bacin da ban yi zaton zata sake zuwa gidan ba.
Daga baya Deen ya zo ya bawa Mama da ni hakurin abun da ya faru, sai ya koma yana kula da ni kamar dai, sai dai hakan be saka Mama sake masa fuska kamar yadda ta saba ba, a lokacin da na fara warkewa ina dan fita na taka kafar Dr Zainab yayar Abiey ta zo duba ni, take min albishir da wata maganar da ta kusan ruda tunanina wai Abiey zai aiko a tambaya masa aurena, sai dai tace min sirri ne kar na fadawa kowa. A ranar na wuni a tunani daman Abiey so na yake ko kuma dai abun da ya faru ne ya saka shi yin haka, amman ban iya boye jindadina ba Mama sai da ta fahimci ina cikin farinciki a ranar, sai dai ban fada mata komai ba. Ba tabbatar da gaske Dr Zainab take ba har sai da Baba ya shigo gidan cikin wani yanayi mai kama da farinciki kuma ba farincikin ba, domin a ranar ba girkin Mama ne ba, jikinsa na dan rawa, sai da ya kalleni ya jinjina kai har sau uku sannan ya natsu ya labartawa Mama wai. Wasu mutame masu daraja daga gidan sarauta sun same shi da zancen nemawa ??ansu auren Zahra. Mama ta daki kirji tana tambayar wace Zahrar kuma su waye domin bata taba sanin Abiey ??an Mai Martaba ba ne sai a yau, ni ce kawai na sani ni ma kuma sanin da na yi ban dauka ??ansa na cikinsa ba ne domin babu wani good relationship a tsakaninsu irin na uba da ??a.

%??maman Abiey ??an Mai Martaba ne?%???

Shi ne abun da Mama ta tambaya ni dai kai kawai na iya daga mata farincikin dake raina ya isa ya hana duk wani yaki da za'a gudanar a duniyar nan a nan gaba, ba wai ina son Abiey saboda yana da kudi ko dan yana dan manyan mutane ba, sai dan ra'ayina da nasa da nake ganin kamar ya zo daya, kuma yana biyewa shirme ne idan ma shirmen ne, yana nuna kulawa baya taba gajiya da duk wani abu na bacin rai da zan yi masa, wani lokacin idan na yi ba daidai ba zai nuna min cikin hikima, yace min Zahra ba haka ake ba kaza ya kamata ki yi cikin kwanciyar hankali babu fada, idan kuma ya gan ni da wani ba zai min fada miyasa nake tsayuwa da maza ba sai dai shi ya fadawa mazan cewar ina da miji ba kamar Deen dake dukana ba.

%??ma fada musu zan tambayi yarinyar idan ta amince sai na mayar musu da amsa ranar irin ta yau%???

Abun da Baba ya fada kenan sannan ya tambaye ni ko ina son Abiey babu bata lokaci na ce masa ina sonsa, ba dan na tabbatar ina sonsa a lokacin ba sai dan ina son kasance tare da shi kuma ina son hallayarsa da ta Ammy. A ranar Deen ya shigo

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login